Showing 1 words to 3000 words out of 15735 words

Chapter 1 - MIKIYA Book Two Hausa Novel

18 Nov 2024

3447

[07/11 9:03 pm] ★~AMMEY LAYLERH🤫: *🦅 MIKIYA 🦅*

_A wonderful world & Special anti terroRism squad_
____________________

*MARYAM NASEER MIRRAH*
~AMMEY LAYLERH ✍️~

✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~*

BOOK Two…………………………񆬍✍

1&2

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

_012/09/2024_

❤🔥
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM


# OF THE LAW
# A TAITOR's
# ROMANCE
# BLOCKBUSTER
# A SOLDIER's
# Courage
# Hop0
# Is Crime


❤️❤️❤️❤️❤️

A duk loƙacin da Allah ya ƙaddara wanzuwar hallitar ɗan adam a doran ƙasa, to kuwa tabbas ko ya ƙi ko ya so akwai waɗansu tarin Ƙaddarorin da suke yin jerin gwano a gangar jiki da kuma ruhin ko wanne bawa, Inuwa wata aba ce da Ubangiji ya ke ƙaddara wanzuwarta manne a jikin kowanne abu, walau mai rai ko akasin haka...
A kodayaushe tana bibiye da mune matuƙar bawa zai zuba maganansa zai lura da haka. Kalmar ƙaddara! Kalma ce mai ɗauke da rassa biyu walau ƙaddara mai kyau ko kishiyarta. Ƙaddara abokiyar tagwaitakar inuwa ce domin bawa ba ya taɓa shallake ma tarin ƙaddarorinsa, Duk iya gudun ka duk iya saurinka baka isa kujema tarin ƙaddarar da ubangijin sammai ya ƙaddara maka ba, sanin haka ya sa na fahimci karin maganar Malam bahaushe ta
_Tun ran gini tun ran zane_ ta zauna ɗaram kwatankwacin yadda ake ɗora ƙwarya a gurbinta.

Yau gani a matsayin matar aure wacce zata ci gaba da amsar wannan sunan har zuwa numfashina na ƙarshe, tafiya me zurfi ce ta kaimu wata anguwar da bansan ko wacce anguwa bace domin zuwa loƙacin na shiga kukan gasken. Tsaiwar da motocin sukayi ne yasa na fashimci mun kawo gidan su salman kenan, dan kuwa bazan ƙira shi da gidana ba. Hajiya Umma ce ta dafa kafaɗuna tare da faɗin.
"Ki fito da ƙafar dama tare da bismillah Maryama"
Wasu hawayene masu ɗumi suka sake wanke min ido shikenan ta tabbata kenan wayyo allah rayuwa na faɗa a cikin raina ina jin wani raunin dake son ɓallowa daga can ƙasan ƙasan zuciyana. Fusgar hannuna da naji an yine ya sanya ni ambatar sunan Allah a saman laɓɓana.
Muryar gwaggo naji tana ruwan masiyar wai zaman uban me nake da har yanzu bazan fito ba, ko dan naga mota me kyau shine na maƙale. Allah sarki ita motar ta dama domin ni a loƙacin kukan tausayin kaina da kaina nake yi, ta sabuwar rayuwar da ƙaddara ta sake buɗe min sabon babinta.
Wannan kyakkyawar dattijuwar ta ɗazu itane ta ceceni daga masifar gwaggo ta hanyar kama hannuwana zuwa cikin nata tafin hannun.
"let go to ur forever home by grate of god"
Ta faɗa a loƙacin da take shiga dani mahaukacin ƙaton get ɗin gidansu salman.....
Haka suka shiga dani kaina a lulluɓe ina share ruwan hawayen da yaƙi tsayamin har zuwa loƙacin, tun a farkon shigarmu gidan na fara jiyo ihun ɓaɓatun gwaggo nata yaba gidan. Kuma ni kaina shaidar hakance ko daga yanayin yadda gidan ya ɗau haske tare da wani abu me laushin tsiya da naji ƙafana suna nitsewa a cikinsa. Amma duk hakan baisa naji wani abu daban akan auren ba haryanxu illama kalaman Anne da sukemin yawo a tsakar kaina shin me kalamanta suke nufi? Shine kawai fassarar amsar da nake nema a haukace ido rufa.
Tunanina ne ya tsaya a sadda muka kai ƙofar shiga palon gidan, wata sabuwa kenan domin tuni ɗakin ya hautsine da maganganu jama'a kowa na tofa albarkacin bakinsa game da gidan.

A falon aka zaunar dani wai wurin kakar ango a karan farko kenan da na ɗan ji mamaki, dan nasan dai salman baya da kaka a shegen surutunsa ya taɓa faɗamin shi baima san kakarshinba sai a photo ya santa.
(Mebi ta ɓangaren Maman shine) na faɗi a raina ina ƙarasa zaunawa abinda ya sake kullemin kai shine yadda matar da suka ƙira da kakar ango itama ta amshemu a mutunce cike da girmama naji suna gaisawa da hajiya umma. Hannuwana naji an kama hakan ya tilastamin ɗago kaina don ganin ko waye.
Idan nace mucu saida brain nawa ta juya karkuce nayi ƙarya domin a fusge sai naga face ɗin kyakykyawaer farar dattijuwar yamin kama da face ɗin dana taɓa sani a rayuwata. Saidai na manta inane a kuma ina hakan yasani risinar da kaina ƙasa ina jan ijiyar zuciya. Ganin yadda itama ta kafeni da nata idon. Dafa kaina tayi fuskarta ƙawace da kyakykyawan murmushi ta furta "Masha Allah da wanzuwarki a cikin tsatsona Marayma"
Daga nan ta shiga kwararomin adda'oi su kuwa sauran ƴan kawo amarya tuni sun bazu a cikin gidan da naji anacewa ba anan zan zauna ba. Kana kuma abu mafi ƙara ɗaure kaina shine yadda naji Wannan matar tana waya tana cewa gobe Insha Allah jet ɗinsu da wari zai tashi, nan na shiga tambayar zuciyana dama su salman ɗin ba ƴan nan cikin lagos bane?, to amma kuma duk wanda yasan Isa manu a garin na lagos ya sanshi, bisne tambayar nawa nayi a zuciyata don bana da mai bani Amsarta. Tunanina ya katsene loƙacin dasu Hajj Umma suka firfito zasu tafi zance suke yi a juye wanda nidai ban gane masa.

Domin ji nayi suna mata sallama suna cewa allah ya saukemu lafiya, su maman Abdalla sai wani yatsine yatsinen fuska ake. Domin makusa suke nema tako ta ina amma sun rasa. shi ya sanya suke wani huhhura hanci sama domin ba haka sukaso ganin rayuwana ta gyaruba, saidai basu sani ba duk abinda zai faru bawa rubutaccene tun daga rabbi izzati. shine yake tsara mana duk wasu tarin ƙaddarorinmu tun kamin muzo duniyar. Tunani ya sake katsewa ne a karo na biyy loƙacin da Hajiya umma take faɗin.
"To _FULANI_ mu zamu koma ubangiji Allah ya basu zaman lafiya Ku kuma Allah ya sauke ku lafiya ita kuma yasa gidan zamane" (Ba ameen ba) na amsa a zuciyata.
"To Merrah mukam zamu tafi duk abinda aka tsinta a gidan aure ɗan haƙuri ne domin kowa da haka yasa ba, barin m aure irin naki da babu ango babu dangin ango, Sai aje ata haƙuri da zaman haƙuri"
Muryan ummansu yaya Ibrahim ya doki ƙofofin kunnuwana, ban gama dawowaa daga suman wucin gadin dana tafi ba na kuma tsinkayar muryar Matar da ake ƙira da fulani tana mai bata amsa ta cewa.
"Kwarai kuwa zaman aure ɗan haƙuri! Rashin ganin ango ko danginsa kuma karki damu wata rana zaki sani domin mutane masu daraja ba a arha ko a sauƙi ake samun ganjnsu ba! Amma karfa ya zame miki wani abin damuwa very soon zaki sanshi harma ki ganshi, domin shi kamar walƙiya yake yanzu nan ƙya ganshi yanzu nan ya ɓacema ganinki don haka ki kasance cikin shiri da tsammani domin Malam bahaushe yana cewa _TSAMMACI ABINDA BA BAKA TSAMMATA BA_ don haka ki riƙe kalmar daram aranki inba da magoya bayinki saisu tayaki riƙe kalmar"

Kafaf palon kowa tsayawa yayi yana kallon wannan dattijuwar matar ciki kuwa harda ni, bazance kaina ya kulle ba domin dama a kullen ake saidai gabana daya shiga dukan tara tara bama uku ba. Na shiga uku ni merrah Auren nawa ne kuma yazo min haka ajuye tamkar amaryar buzuzu.
Ɗaya bayan ɗaya suka ringa ficewa motoci na ɗibarsu suna mayar dasu. Inaji ina gani haka a gaban idona kowa dazan ƙira da nawa ya tafi ya barni a wannan juyayyan gidan. Babu dadewa da tafiyansu matar farko da taje ɗaukana ta kama hannuna tana me kaini wani ɗaki wai anan zan kwana, baki ɗaya jikinane ya sake mutuwa mayafina na zame bayan fitar tana me sake tunasar dani tafiyar sassafene a gabanmu goben. Toilet na faɗa domin inada buƙatar sake watsama jikina ruwa kodan zafin da aka haɗama kaina. Har wani hayaƙi² ne ke fita a kaina tsabar zafin daya ɗauka...
A ƙalla na ɗauki Good 30 minutes a bathroom ɗin kafin na fito ɗaure da Alwalana kayan dana cire na mayar tunda ina da tabbacin banda ko tsinke a gidan. Amma ga mamakina kodana fito sai na tarar da wasu riga da wando na barci masu kauri tare da madarar shanu me zafi, (Ikon Allah baya ƙarewa) na faɗi a zuciyata domin kuwa shi nake ta gani sai gashin zabbin da suma aka ajje duk akan table ɗin dake gaban gadon. Saida nayi nafila tare da adda'oi masu ɗan tsayi kana na janyo plat na naman domin ba karya sammm bana wasa da cikina, tak na tafe cikina da gashin naman nan na kora da madarar shanun me dumi sosae.
Adda'ar kwanciya barci nayi ina shirin kwanciya fulani ta shigo dana rike sunanta daram.Tambayana tayi babu abinda nake da bukata nabata amsa da babu kana taja min ɗakin tana me fita,Wata sabuwa kuma tana fita na rushe da wani sabon kukan na sabuwar rayuwar dana tsinci kaina wadda ƙaddara ta kawoni izuwa wani matakin na daban. A haka har bansan tsawon loƙacin dana ɗauka ina kukanba haka bacci yayi awon gaba dani fuska fall burbushin hawaye. ƙiran sallar farko a kunne na haka na yunƙura na tashi inda na tashi da wani zazzafan zazzaɓi da ciwon kai wanda nasan kukan jiyana ya haddasa min zazzaɓi da ciwon kan. A wahala nakai kaima bathroom na yo alwala da nafila na fara ina nan zaune har aka shiga sallah nima nabi sahu nayi. Kaɗan garin ya fara haske a kuma loƙacin saiga mutane biyun nan sun shigo suna zama gefe da gefen gadon. A ladabce na gaidasu suka amsani fuska sake har suna tambayar yadda na kwana. Da lafiya na basu amsa tea me zafi suka ce na sha yanzu jet ɗinmu zai tashi in zanyi tafiya inda ta hawa motace bana iya cin komi hakan yasa nace bana sha, sukace na daure ko kadan ne dai nasha hakan ya sanya sama sama nasha na ture cup ɗin muna fita a bedroom ɗin. Kasancewar babu ƙarfi a jikina hakan ya sanya tafiyane ya koma kamar jan ƙafa nake haka muka kai gaban jet ɗin da ko a mafarki ban taɓa zaton zan taɓa hawansu. Haka jirginmu yayi landing daga farfajiyar gidan muna lulawa tare da keta gajimare......

*SALMAN*

A haukace yayi kan surry cikin yanayin fita a hayyaci baiyi duba da halinda take a ciki ba na sumewar da tayi.
Cikin zafin zuciya da amsa amon murya ya furta.

"I swear u don't die with out tell me what about my bride,nace miki matana take? ko saina yi gutsi² da sassan jikinki kafin ki buɗe baki kimin magana"

"Babban kuskure mafi muni a rayuwarka da zakay shine hannunka ya taɓa min ƴa wllh salman"
Yaji muryan mom surry ta faɗa daga ta bayansa. Wani irin juyowa yayi a matukar fusace yana watsa mata wani mugun kallo. Itama da nata kallon na kashiga uku ta bishi tana me nufar inda ƴar nata take yashe a some. " wllh wllh taku ɗaya kika fara momi saina sari fuskarki idan kin musu kuma kara ki gani" salman ya faɗi a dake yana saro wata ƴar karamar wuka a jikinsa, Ido momi ta shiga rarrabawa tanasan tijarar salman babu abinda bazai iya aikata mata ba tunda ya rantse domin dama idan ƴan haukan suka motsa masa baya shakkun kowa a gidan bare ita dama daya gama renawa duk kuwa da tana matsayin yayar uwarsa.

Wayarsa da yayi ƙara itane ta ceci momi ta fice a sace da zuwan taje ta debo masa police's. Be ankara da ficewar tan ba tunda ya ga daddy'nsa ne me ƙiran.

"Salman ina ka shiga ne tun ɗazu ina ƙiran wayarka ba ka ɗagawa? Ka san fa ba na son hakan ka barni a zaune tun dadewa ina dakon jiran zuwanka. "Daddy ka faɗamin dama kitimurmurar da kuka ƙullamin kenan na auramin wannan guntun turawan, shi yasa furr ka hanani zuwa ɗaukar amarya kace yanzu maza basa zuwa ɗaukar amarya? Ehhhhhhh " ya faɗi a matukar harzuke.
"Innalillahi, daddy's boy me me me kake nufi ka fahimtar dani, wllh bana ganewa ma ka kulle kaina tell mee tell me maza daddy's boy"
"Sauya min matar da kuka yi mana kuka ɗaura min Surayyan momi bilkisu wacce ta gama rabawa turawa jikinta"
Zumbur babu shiri Isa manu ya miƙe wani irin gumi na keto masa, "Kai kai banason zancen banza wacce surayyar kuma? Ko so kake saina zundumo maka ashar da cikin wayar ne"
"Ba wani fa zancen kare kai daddy kawai kana son raina min hankaline wllh idan baku nemomin duk inda Merrah take ba wllh² saina tada hankalin kowa a gidan"
"Kai durun uwaka dan ubanka yo aini a baybai ka kifeni ka fito kamin filla filla yadda zanfi ganewa" ya karashe maganar yana faman safa da marwa shi kadai yasan tashin hankalin da yake ciki idan har da gaske salman din yake. "Allah yasa ba shawuwa kayi da yawa ba"
Daddy ya faɗi kayan jikinsa na jikewa da zufa idan har ta tabbata ba'a ɗaurawa salman aure da yarinyar ba ta tabbata kenan wannan shegen yasan shirunsu akan shi kome?. Ya ayyana hakan a zuciyarsa yana jin zuciyarsa na kartar ƙirjinsa da yake jin zafin har a cikin jikinsa. "Kayi shiru kenan da haɗin bakin naka ta tabbata ko daddy"

"Haba haba salman kasan dai bazan taɓa ma haka ba saidai inda da wannan munafukar uwar taka suka haɗa baki suka muna fincemu dagani har hakai wllh boy"
Daddy yafaɗi "Koma dai miye gani nan zuwa gidan kuma karda ka yarda kowa ya fice a gidan nan wllh domin duk sena kone kowa da kowa na rantse da Allahn da yake busa min numfashi"

Yana fadar hakan ga gimtse wayar tare da sunkutar surry ko nauyinta baiji yayi waje, fitar san kofar gidan kuma yayi daidai da loƙacin da motocin police suka faka motarsu mom surry biye a bayansu. "Yawwa yallaɓai gashi nan ma ka gani? Ka gani da idonka ko? Wllh mahaukacine haukarsa ce ta motsa dama sanyi ya fara shigowa ai, karya kashe min ƴata ku kama shi yallaɓai" momi ta fadi tana zaga ye police ɗin.
A tsawace police ɗin ya furta..

"Your under arrest her"
Wani mugun kallo ya watsama police ɗin yana faɗin. "Akan wanne dalili kenan?" ya fada a rene yana shirin shigar da surry da take a sanƙame cikin motar police biyu sukayi rammm da shi.a fusace ya juwo da niyar naushin fuskar police ɗin ko kafin yayi wani yunƙuri ɗaya daga cikinsu yayi hanzarin buga basa ɗan kulkensa a gwiwowinsa duka biyun, hakan ne ya tilas ta shi kaiwa sukunne yana sakin ƙarar azaba. Amma duk da haka sake ƙoƙarin tashi yake jefa sury a cikin motar yayi yana zaro wuƙarsa yana wani zazzara musu ido.
"Na rantse da Allah duk wanda ya sake matsowa inda nake kafin nayi dalilin rasa aikinsa ni saina kassara rayuwarsa kafin nan, kunsan kuwa waye _SALMAN_ ba da iyaka sunan mahaifina kaɗai nake amfani ba nima kaina haɗarine" (Hatsari) wata inkiya wanda alamu ya gama bayyana shine ogansu yama ɗayan dake dab da salman inkiya ta wutsiyar ido. Karaf ya faki idon salman yana komawa ta bayanshi yana damkar hannuwansa wani cikinsu yayi saurin ɗaura masa onka nan suka jefashi bayan motarsu ita kuma mom sury taja motar salman din dake akwai car key nata ajiki.
Haka suka wuce da salman ita kuma ta kama hanyar zuwa gidanta, domin ma ba zataje gidansu salman ɗin ba kuma ta rantse wllh ko sama da ƙasa zata hade babu wanda ya isa ya raba wannan auren ya ɗauru kenan har gaban abada, domin farin cikin tilon ƴarta shine fiye da komai data mallaka a duniyar...

_MERRAH_

Ba wata tafiya me tsaho bace ta kawo mu garin kano har tsaƙiyar fadar jet ɗin mu ya sauƙe, Nan naga ikon allah yau ga merrah a gidan sarauta (kenan ɗansu suka auramin kome?) na raya a zuciyata ina mai bin bayan su fulani da kuyangai suka kewamu. wata Brai layn car ce da ɗauke mu zuwa ɓangaren Fulani uwargi ga me martaba suraj. Har bakin part ɗinta aka kaimu nan ma kewaye mu akai haka ta kama hannuna cikin nata muna tunkarar katon palon ta bayan passes passes da muka ringa wucewa.
A kan wata lallausar kilisa aka zaunar dani cikin ƙanƙanin loƙaci aka cika gabana da kayan ciye² dasu fruit babu kalan da babu, kaɗan naci domin zuwa yanzun sosae jikina ya sake tsanani taurin kai irin nawa da kuma dauriya ya sanya na shanye hakan. Wani lafiyayyen room aka kaini akace nayi wanka na huta hakan kuwa akayi nayi wankane wata farar halp bubu ɗin cotton less aka ajje min tare da blue black ɗin Alkyabba sai su undears haka na shirya bayan shiryawana da kamar 50 minutes aka aiko wata jakadiya wai nazo ana son gani na.
Haka na bita domin komi nawa a wannan loƙacin ya tsaya cakkk, kawai ganinan dai kamar wata butum butumi haka nake kallon komi da ido na kuma duk umarnin da aka gindayamin kamar ba merrah ɗin da kuka sani ba.

A salin fadar me martaba sarki suraj sunusi shureim fulani tamin jagora, zuciyata in bada bugu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login