Showing 21001 words to 24000 words out of 41765 words

Chapter 8 - YAR IYA HAUSA NOVEL

28 Oct 2024

5988

ta ta ce
“sorry zahrahty gani nan zuwa”

Bayan Badi'a ta zo suka wuce islamiyya. Yau gabaɗaya Ustaz ya kasa fahimtar Zahrah, fuskar ta ɗauke take da zunzurutun damuwa. Zuwan ma kawai tayi ne ba wai ɗin taso ba. Gani take kamar ina ta bar Mamah mutuwa zata zo ta ɗauke ta.

“Zahrah! Zahrah!! Zahrah” bakin shi uku ammah bata amsa ba. Babu alamun ma ta san MEH ake ko a Ina take. Badi'a na taɓa ta ta zabura sai wani zare ido take yi.
“zahrah baki da lafiya ne yau gabaɗaya hankalin ki baya kan aji. Baki na yafi uku ammah baki san ina yi ba"
Cike da basarwa ta ce
“lafiya ƙalau Ustaz kawai tunani ne yayi min yawa.”
“Zahrah tunani meh kike yi haka ƴar ƙarama da ke da zai sa ki shiga irin wannan yanayin?”
Bata yi tsammanin jin irin wannan tambayar ba daga Ustaz shiyasa kawai tace tunani take yi.

Murmushin da iyakar shi fuska ne tayi sannan tace
“laaaaa Ustaz ba fah wani tunani nake yi ba kawai duniyar ne ban jin daɗin ta”
“toh Allah ya sauqaqa Zahrah ammah ki rage tunani” daga haka ya wuce.

Badi'a dake nazartar ƙawar ta tunda suka fito daga gida gashi yanzu fararen idanuwan ta sun yi jazur da su.
“Zahrah, gaba ɗaya yau tunda muka fito nake nazartar ki, anything wrong?”
“just nothing” ƙura mata ido Badi'a tayi kafin tace
“ƙarya kike Zahrah akwai, kawai dai ban kai matakin ki faɗa min baneh na gode”
Ta faɗa cike da fushi. Kamo ta Zahrah tayi kafin tayi murmushi
“yi haƙuri ƙawa tah, kin kai har kin wuce ki ji damuwa ta. Ba komai ke damu na ba in banda rashin lafiyar Mamah, yau da na dawo abun yayi worst, kin ga yadda Mamah ke shan wahala, Badi'a bazan iya jurewa ba bazan iya jurar ganin Mamah a haka ba”
Ta faɗa ƙwalla na zubowa daga cikin idanun ta.
Cikin sigar rarrashi Badi'a tace

[30/09, 10:20 a.m.] 💎Diamond Bhatool 💎: ______________★★★_______________
Typing 📲
🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡
_(All in a big family🏠)_
★TAKUN FARKO★
_[Labari/Rubutawa]_
*©Fadimatu Adamu Hassan*
*A.K.A DIAMOND BHATOOL*💎

_______________★★★________________




*PROLOGUE*


*PAGE* 1️⃣2️⃣

Wannan shafi naku ne masoya littafin a babban gida. Ku ci gaba da bibiyar alƙalamin DIAMOND LADY. Much ƙauna🤩😘.

SHARE AND COMMENT PLEASE!
_______________★★★________________



Kamar daga sama ta jiyo Muryar Mamah na ƙiran sunan ta.
“Zahrah, Zahrah zahrah” ta faɗa tana lalumowa ko zata ji ta. A firgice ta tashi jin kamar mafarki take.
“mamah” ta matso daga da Mamah dake zaune,
“kunna haske” cike da mamaki take kallon Mamah.
“mamah ke kike magana haka, Alhamdulillah Alhamdulillah”

Rufe mata baki tayi sannan ta fara magana ƙasa ƙasa yadda babu wadda zai ji su
“ki kunna haske, zan nuna miki abu ne”
Lalumowa hasken tayi ta kunna sannan ta zuba wa Mamah ido.

Da ƙyar ta miƙe ta nufi wata ƴar adakar ƙarfe dake ɗakin, ɗan murɗa wasu abu dake jiki kamar zobe tayi sannan adakar ta buɗe. Wata haka da ta sha ƙura ta gani ta ɗauko sannan ta rufe adakar.

A hankali take takowa dan kuwa ba wani ƙarfin jikin ta take ji ba.
Zahrah da mamaki yayi kusan kashe ta ga wani tsoro da ya shige ta lokaci ɗaya. Ta ma rasa wane irin tunani zata yi. Ta tuna taji ana cewa idan mutum yan jinyar ajali toh yakan samu sauƙi daf da mutuwar shi. Saurin kawar da wannan tunani tayi jin an dafa kafaɗarta.

“Zahrah!", Ta ambaci sunan cikin raunananniyar murya yayin da Zahrah ta kasa amsawa sai ma wani firgici da ya mamaye ta.
“Zahrah! Ke kaɗai Allah ya bani, kuma bana so ki ci gaba da wannan rayuwar idan aka ce babu Ni. Ina ji a jiki na bazan yi tsawon rai ba, sai dai yanzu naji wani ƙarin guiwa na tunkarar ki da batun ahali na.
Tun ba yau ba kina tunkara ta da maganar ina basarwa saboda yadda nake jin wani mololo ya tare min zuciya da zarar an yi min tambayar. Yau bana jin abun shiyasa nake son sanar da ke Ni wacece, ban ce ki ci gaba da zama cikin gidan nan ba saboda babu rayuwa mai daɗi cikin shi.
Ina da rai ma baki samun kulawa daga wajen kowa sai Ni yin idan babu Ni ban san ya zaki ji ba.

Ammah a matsayi na na mahaifiyar ki kuma mai ƙaunar ki,ko da bayan raina ne bazan zo ki bar cikin gidan nan ba saboda shi ɗin tamkar gidan mahaifin ki yake. Ammah idan kika ji ba zaki iya ba ko kin takura da hakan, ko kuma anci gaba da tauye hakkin ki toh ki nemi ahali na.

Wannan jakar da kike gani mallaki na ne kuma ita ce motar da zata sada ki da dangi na, zan damƙa ta a hannun ki da zarar na sanar da ke labari na, kuma zan so ki adana ta kamar yadda nima na adana ta.”

Ɗan dakata wa Mamah tayi da bayanin tare da ƙanƙame hannun Zahrah cikin nata yayin da hawaye ke zubowa daga cikin idanun ta, ga kuma alamun gajiyawa a tare da ita. Ganin hakan yasa Zahrah share nata hawayen.

Cikin ranta kuwa tunani take
“kamata yayi ace nayi farin ciki da wannan daren, kamata yayi ace naji murnar da ban taɓa ji ba a wannan daren saboda tsantsar tarihin da zai buga cikin rayuwa ta.
Daren da zan samu abun da na daɗe ina fatan samu tun ina ƴar ƙarama ta, abun da tambayar da ke sa mahaifiya ta tayi fushi da ni gashi kuma zata bani shi a yau.

Ammah meh yasa Ni bana jin naji wannan labari da na daɗe ina son ji?, Labarin da zai kasance makullin baƙin ciki na?”

“Tabbas ina don sanin tarihin ki Mamah, ina son sani idan nace bana so toh nayi ƙarya. Ammah Mamah ba a irin wannan lokacin ba. Ina don ki sanar da Ni labarin ki ne a lokacin da in naji zanyi farin ciki, a yanzu baki da lafiya kuma bamu da kowa sai Allah, sai kuma bayin sa Ammi da Abba da ya aiko cikin rayuwar mu.
Zan so ki Dakata da faɗin labarin nan zuwa wani lokaci”

Itama Mamah ɓangaren ta tunani kawai take yi game da rayuwar ta, yarintar ta, tasawar ta i zuwa auren ta da masoyin ta Abdulkarim Kuru. Haihuwar ɗiyar ta Zahrah, da mutuwar ba zata da mijin ta yayi, auren ta da Kawu da kuma irin baƙar izayar da ya gasa mata ita da yarinyar ta.

Shiru shiru babu wanda yayi magana cikin su, Mamah na jiran amsa daga ZAHRAH kan ta fara bata labari yayin da Zahrah ta kurma cikin duniyar tunani.

Mamah da ta gaji da zama ne ta ɗan kishingiɗa, hannun ta dake cikin na Zahrah ne ya zame wannan shine dalilin farkawar su duka biyun daga duniyar da suka faɗa ta tunani.

Bubbuga ƙofar da suka daɗe basu ji anyi ba ya sa suka miƙe tsaye a tare. Har Mamah ta miƙe zata buɗe ƙofar Zahrah tayi saurin dakatar da ita.

“aah Mamah, na san bai wuce Kawu baneh kuma ba zaki buɗe masa ba" bata yi mamakin jin maganar Zahrah ba hakan yasa ta zauna bakin bed Babu musu. Jikin ƙafar ta Zahrah ta zauna tare da kwantar da kan ta kan cinyar Mamah. A hankali ta ɗago ta kalli idon Mamah sannan ta kawar da nata gefe.

“mamah ba haka kawai yasa na tsani Kawu ba sai don rashin nuna ƙaunar shi gare ki a matsayin ki ta iyalin shi. Ba ma wannan ba tunda kika kwanta bai taɓa tako ƙafar sa don ya duba jikin ki ba balle yace yau a kai ki asibiti ko ya karɓi takardar magani yace zai siyo ba bayan kuma Ni da kaina na sanar da shi baki da lafiya.”

Tabbas abun da Zahrah ta faɗa bata ga laifin ta ba ko kaɗan at least ya kamata ko sau ɗaya ace ya zo ya duba ta ɗin.

Gyangyaɗin da Zahrah ta fara ne yasa Mamah cewa ta dawo su kwanta gobe da kammala maganar su. Ba musu Zahrah ta kwanta jikin Mamah nan da nan bacci mai daɗi yayi awun gaba da su. Safiya ta gari.

Ba su suka tashi ba sai da gari ya fara wayewa Mamah ce ta fara tashi ɗauke da addu'ah a bakin ta. A hankali ta sauƙo ta fita, ɗan watsa ruwa tayi a jikin ta ta haɗo da alwala sannan ta yi sallah. Bayan ta isar da Sallah ta yi azkar ɗin ta. Miƙewa tayi don tashin Zahrah tayi arba da jakar nan, a kasalance ta ɗauke ta ta jefa ta cikin wardrobe ɗin kayan ta dake sama can.

Bayan ta tashi Zahrah ta ɗan fara kaɗe ɗakin.
Tana yin Sallah ta gaida Mamah
“ina kwana mamah”
“lafiya zahrah”
“ya kwanan jikin?"
“Alhamdulillah, yi maza ki tashi kiyi wanka kada ki makara"
“toh" tace tana miƙewa, ninke sallayar tayi sannan taje tayo wanka.
Uniform ɗin ta ta manta ba'a goge yake ba, a hanzarce ta shiga gidan Ammi ta goge lokacin Badi'ah ta tashi.

Sanya uniform ɗin ta tayi tana gamawa Mamah ta zubo mata jallof ɗin taliyar da ta musu, ita dai Zahrah mamaki take don rabin ta da cin girkin Mamah tun kwanaki basu fi biyu ba bayan kwantar da ita da aka yi a asibiti yau kuma ta tsiro girki.

Bayan ta ci abincin tana santi ta wanko hannun ta tayi brush daga nan ta zari school bag ɗin ta da kuma hijab ta zura ta fito. A bakin ƙofa suka ci karo da Badi'a ita ma ta shirya tsab”

“har kin shirya kenan, bari na miƙa wa Mamah sai mu wuce" ba tare da ta amsa mata ba tayi waje.
Tana miƙa wa tayi wa Mamah ya jikin ta fito, driver ne ya kai su school sai dai yau Zahrah tamkar ba ita ba, tunani ya addabe ta.

Babu abun da ya tsaya mata a rai irin hirar su ta jiya tare da Mamah.
Hirar da ta tsaya mata cikin zuciyar ta.

“meh Mamah take nufi kenan,idan na fahimta akwai ɓoyayyen al'amari dangane da ita, bana son rasa Mamah don ita ɗin numfashi na ne, ammah cikin maganganun ta na jiya naji zuciya ta na karye wa”
Other heart ɗin ta tace
“haba Zahrah, damah ai yanzu kam kin kai ki san tarihin mamar ki”
“ƙwarai to ammah bana so rada ta ai”
“duk da haka dai ya kamata ki saurare MEH Mamah zata sanar da ke, la'allah ƙarshen zaman ku da azzalumin kawun ki yayi”
“ai kuwa dai, nimah na ga hakan”
Haka tayi ta magana da zuciyar ta har uncle Hashim ya shigo. Dukkan students suka miƙe suna gaida shi, sai dai Zahrah hankalin ta baya ma ajin, bata san wainar da ake toyawa ba. Bai yi mata magana ba ya basu umarnin zama, har ya fara clsss ɗin bata san MEH ake ba sai da Badi'a ta buge ta.

Firgita ta waro ido tana kallon Badi'a.
“ke wai tunanin meh kike yi ne?”
“banu komai”
Ƙasa ƙasa ta harare ta tace
“kina nan kina tunani har uncle Hashim ya shigo kina zauna muka gaida shi kuma kice ba tunanin komai kike yi ba?, U better concentrate” daga haka ta zunguri ƙeyar ta.

Daf da lokacin closing PC ya sa aka kira Maryam, Badi'a da kumah Zahrah zuwa staff room.
“ba komai ne ya sa na kira ki ba sai don na sanar da ku cewa yanzu ba sai anjima ba zaku tafi Jos zaku yi representing school ɗin nan a wani programs so nayi magana da iyayen ku akan tafiyar. Yanzu ku ɗauko school Bags ɗin ku ku ajiye su a nan.
Tare zaku tafi da Academic officer da kuma Hashim. Please Behave well”
Suka haɗa baki suka ce
“ohk sir”
Ɗauko bags ɗin su suka yi suka ajiye. Lokacin Academic officer ya ce su fito. Abun mamaki PC ya tsayar da su.
“ku zo”
Zuwa suka yi ya miƙa musu sabbin uniform da gani goge su aka yi saboda ɗumin dake jiki.
“ku tafi da wannan, ina zaku tafi wajen sai ku sanya.”
Bayan sun amsa suka koma daga nan motar su ta tashi sai Jos.

RACAS FOUNDATION COLLEGE, old airport jos, plateau suka nufa. Ɗan zagayawa A. Officer yayi da su sannan suka koma zuwa destination da aka basu don sai da safe za'a yi competition ɗin.
Abinci mai rai da lafiya yayi order, bags uku ya aiki musu suma suka ɗauki two bags.

Bayan sun ci abinci sun kora da drink suka yi sallah.
Hutawa suka kwanta suka yi, ba su suka tashi ba sai 4:12pm, suna tashi suka watsa ruwa suka maida kayan su sannan suka yi sallah.

Knocking door ɗin aka yi, Badi'a ta buɗe, Academic officer ne yace su zo. Wani ɗan cool down area suka samu suka zauna.
Yayi musu bayani akan programs ɗin da kuma wanda kowa zai yi participating. Daga nan ya ƙara haska musu hanya tare da taimakon uncle Hashim, bayan an kwatanta wa kowa nashi A. Officer ya ce “ toh bari a gwada kowa Muga yadda zai yi”

Maryam zata yi representing school ɗin ne a junior spelling challenge and pronounciation yayin da Badi'a zata yi essay writing sai kuma Zahrah impromptu speech.

Marya aka fara gwada wa and Alhamdulillah she's done it well. Tayi da kyau har sun saka rai kan spelling challenge nasu..
Badi'a ma ya bata piece of paper sannan ya bata topics.
Within short period of time ta kammala, he's impressed by the way she answer the question, ita ma aka dasa alamun nasara a tattare da ita.

When it turns to Zahrah, a topic is given to her also, and tayi yadda ya kamata, her confidence, gentleness, the way she speaks like she's from Elizabeth's palace.

Bayan sun kammala ya ƙara gyara musu kowa aka faɗa nata corrections nata, and they all master it. Da yake lokacin sallah ya gabato kai tsaye komawa suka yi suka yi alwala suka yi sallah.
After they prayed suka ce su gwada playing Qur'anic trick, Zaki janyo ayah sai ki zaɓi ɗaya cikin su ta faɗi wani surah take, idan ta canka daidai sai ta karanto cigaban.
Haka suka yi tayi har lokacin ishà.

Alwala suka yi suka watso ruwa sannan suka jona sallah, suna idarwa bayan azkar suka Fara hirarrakin su.

Few minutes da fara hirarrakin su aka yi nocking, abincin su aka kawo musu sai lokacin duka tuna a na rana da aka kawo akwai extra bag da basu taɓa ba. Ɗauko ta suka yi kads ayi asara suka fara cin ta.
Bayan sun ci suka buɗe Bags ɗin daren, chips ne sai egg sauce da kuma milk drink. Bayan sun cinye tas suka ci gaba da hirar su. Ba su suka kwanta ba sai around 10:00pm. Safiya mai albarka marvelous squad.

Cikin baccin ta tayi mafarkin Mamah.
Sai ga ta nan kusa da ita suna wata magana, bayan sun gama maganar sai Mamah ta damƙa mata wata haka wacce bata san ta miye ba tare da gargaɗin ta kada ta buɗe ta kwana kusa.
Bayan ta karɓa sai Mamah ta ɓace ɓat, tana ɓacewa sai Zahrah ta fara kuka tana neman taimako, wai sai ga baba amarya ta fito tana sheƙa mata dariya can kuma ta ɓata rai.

A zabure ta miƙe gani gari har ya waye. Ɗaya bayan ɗaya ta tayar da su suka yi sallah, sannan kowacce ta shiga tayi wanka.
Suna fitowa suka shafa cream ɗin da suka ga ajiye gaban dressing mirror dake room ɗin.
Around 7:00am aka kawo breakfast, suna ci suka yi brush suka fara Sanya uniform saboda za'a fara program ɗin ne by 9:00am and suna so su je da wuri.

“Zahrah wannan kam daidai ɗin ki ne ke zaku saka” Badi'a ta faɗa tana miƙo mata wata bujen riga. Zumɓura baki tayi ta harare ta.
“u're out of your mind actually Ni zan saka wannan burgujejiyar rigar?”
Gira Maryam ta ɗaga mata wanda yasa ta cilla mata ita.
“ke maryam ke ce uwar mata cikin mu ke zaki saka ta”
“wannan rigar nimah bazan saka ta ba sai dai na mayar da tsohuwa ta”
Dariya suka kwashe da ita sannan Badi'a ta tsagaita ta ce
“wa yaga new plus old which is equivalent to mark reduction” ta ci gaba da dariyar ta.
Maryam ta ƙulu iya ƙuluwa kafin tace
“shikenan na haƙura zan sa ammah dai kun min wayo ne.
Gwalo Zahrah tayi mata sannan tace
“don't wear it if u like Mamah baby😂”
Jin sunan da Zahrah ta ƙura ta yasa ta wulla rigar.
Suna cikin haka aka yi knocking su a guje Maryam ta janyo rigar ta saka tana hararar Zahrah yayin da Zahrah ke tayi mata dariya.

“if u're ready we can go”
A nutse suka fito suka bi bayan shi zuwa motar su. Daga nan motar su ta lula sai RUCHAS FOUNDATION COLLEGE.

TOH, MU KASANCE GOBE DA KU DON JIN WACECE MAMAH DA KUMA DALILIN ZAMAN TA TARE DA KAWU?
ME KUKE TUNANI ZAHRAH ZATA YI BAYAN SANIN ASALIN MAMAH
SHIN ZASU CI COMPETITION ƊIN NE KO KUWA?
DUK CIKIN LITTAFIN BABBAN GIDA
KU CI GABA DA SAMBAƊO MIN COMMENTS REMEMBER FILIN BADA SHAWARA DA KARƁAR ƘORAFI A BUƊE YAKE

ITZ DIAMOND LADY 💎
_Oum Zainab_

[03/10, 3:43 p.m.] 💎Diamond Bhatool 💎: ______________★★★_______________
Typing 📲
🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡
_(All in a big family🏠)_
★TAKUN FARKO★
_[Labari/Rubutawa]_
*©Fadimatu Adamu Hassan*
*A.K.A DIAMOND BHATOOL*💎

_______________★★★________________️



PROLOGUE


*PAGE* 1️⃣3️⃣

kada ku mance gabaɗaya littafin sadaukarwa ne gare ku AISHATU USMAN (Baby Unah) sai dai gashi sai rabar da pages ɗin nake ba tare da sanin ki ba ammah na san ke ɗin mai fahimta ce ai... Haka wannan shafin ma dai sadaukarwa ne gare ku
A'ISHAH MB (Baby Isha) marubuciyar littafin Rayuwa da macijiya
Pinky darling marubuciyar littafin SO
FAIZA ALMUSTAPHA (Fa'eeh BG)

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login