Showing 39001 words to 41765 words out of 41765 words

Chapter 14 - YAR IYA HAUSA NOVEL

28 Oct 2024

5992

dawo hankalin sa yaga ba Madina na shiga uku...”
Tsawa boka ya daka mata nan da nan jikin ta ya hau ɓariiii
“abu ɗaya zan miki ya rage naki ko ki biya ko a'a, in kin amince toh”
Cikin rawar murya Baba AMARYA tace “eh”
“zan hana haɗuwar ƴar da uwar ta hanyar tura mata aljanun da zasu ƙara mantar da ita uwar, ladan aiki na shine....” ya faɗa yana pointing Bibalo da yatsa, fara rarraba ido tayi tana jiran taji meh baba AMARYA zata yanke kwatsam taji Baba AMARYA tace
“shi....shi....shi...shike...nan na amince” ta faɗa a rarrabe tana mai kallon Bibalo da fuskar roƙo.

Nan Bibalo fah taƙi Amincewa, a rasa wa zai sadu da ita sai wannan mummunan ƙazamij mutum ɗin toh wallahi da wannan ya kasance ta gwara kare ya kasance ta. Tab.

Tasawar da boka ya daka ne yasa suka nutsu
“keeeeee.... Har kin isa nace ina son jikik ki ki ƙi, kin ma ci Sa'a sai da na tambaya, toh ko kina so baki so sai nayi abun da nayi niyya dake” yana kai haka ya miƙe zai yi kanta, da gudu Bibalo ta arta a na kare ko taku biyar bata yi ba taji an cafke ta. Boka ne da kan shi ya cafke ta, kai tsaye ya nufi wani ɗaki da ita.

Tunda ya kaita ya ajiye ta daga nan ya zare abun da ya naɗe jikin sa da shi take ainihin suffar shi ta bayyana Abu dai babu daɗin gani a take duk ta bi ta firgice.

4Hours ya shafe yana aiki kan ta har sai da yaji shi zam yayi wani irin gurnanin a lokacin wata guguwa ta tashi da farko guguwar mugun duhu gare ta, kafin wani lokaci ta fara raguwa har haske ya bayyana.

Ɓangaren su Baba AMARYA tunda suka ga boka ya shiga da ita suka tabbatar sai yayi, saboda haka suka dawo baƙin ƙofar ɗakin suka tsaya. Ganin tsayuwar ba inda zata kai su yasa suka nemi wuri suka zauna.....hour 4 nan a wurin tayi musu har aka fara guguwa wacce tunda ta tashi suka rasa hankalin su. Bayan komai ya sarara hankalin su ya dawo ammah abun mamaki sai suka gansu a bakin titi.

Jimamin da suka tsaya yi ne har sai da suka waiwyo ta bayan su, a take Baba AMARYA ta cilla ihu ta faɗi ƙasa sume.....

Ba komai bane sai Bibalo da suka gani yashe tana numfashi sama sama ga uban jinin da yake malale a wurin da take kwance. Asabe kuwa duk ta ruɗe ta rasa wa zata fara ceto wa.
Nufar wurin da Bibalo take tayi, idanuwan ta ta zare tare da sakin ajiyar zuciya. Irin wannan cin mutuncin kamar wanda maza 100 ɗari ne suka yi aiki a kan ta!
Murmushi tayi tace
“ko ba komai na fara cin nasara a kan su, shegu miyagu”
Daga haka ta juyo wurin da Baba AMARYA take ta fara danna ƙirjij ta, a hankali ta saki ajiyar zuciya sannan ta buɗe munafikan idanuwan ta.

“saude bamu da lokaci ki tashi mu ɗauki Bibalo mu yi asibiti tunda akwai kuɗi a gun ki Jada mu rasa ta.”
Da ƙyar Baba AMARYA ta miƙe suka nufi wurin da Bibalo take a kwance suka cicciɓo ta, jinin jikin ta duk ya ɓata musu kaya, a haka suka tafi har suka fara isa cikin jama'ah, duk wanda yasan su sai ya sa ta kare, kowa suka yi wa magana kafin ya gama ji in ya kalli abun da ke hannun su sai ya cika wandon shi da iska, tunanin mutane ko kashe matar suka yi.

__Kuyi min comments ƴan albarka gobe sai mu ci gaba.__
YA KUKE TUNANI ZA AYI?
ALLAH SARKI BIBALO YAU AN WAHALA KO MUTUW TAYI DA GASKE?
AIKIN BOKA A TUNANIN KU ZAI CI?
TEAM ZAHRA KO ZAKU YI MATA RAKIYA NE?
Duk cikin littafin babban gida (PROLOGUE) saura post ɗaya mu shiga book two Wanda shine ainihin labarin...kada ayi babu ku.
[10/10, 5:51 a.m.] 💎Diamond Bhatool 💎: ______________★★★_______________
Typing 📲
🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡
_(All in a big family🏠)_
★TAKUN FARKO★
_[Labari/Rubutawa]_
*©Fadimatu Adamu Hassan*
*A.K.A DIAMOND BHATOOL*💎

_______________★★★________________





PROLOGUE


*PAGE 2️⃣0️⃣ (LAST PAGE)

I dedicated this page to u Boɗɗi Autar Ammi, the writer of _MAYU NE_, Allah ya ƙaro hazaƙa ƴar uwah.

_Masu Neman labarin daga farko, kuyi following channel ɗin nan zaku samu:_

SHARE AND COMMENT PLEASE
_______________★★★______________

Har bayan la'sar babu wanda ya kula su in fact kowa ta kan shi yake yi in ya can su. Can dai har suka isa wani asibiti bayan sun ci uwar tafiya. Babq amarya kuka Asabe kuka, Da ƙyar aka amshi Bibalo saboda case ɗin ta yayi muni da yawa. Hour uku suka share kafin a samu ta farfaɗo. Tun da ta farfaɗo take ta uban sunbatu kamar mahaukaciya

“aah boka, ka rabu da Ni don Allah wallahi iya Alhaji na nake alaƙa da shi kada ka ɓata tsakanin mu, wayyoh wayyoh Baba ta duk ke kika jawo min, ka ƙyale Ni haka babu daɗi wallahi ka barni zan mutu. Wayyoooh”

Nurses ne suka yi kanta ganin irin yadda take jijjiga kamar wata psychiatric patient. Da ƙyar suka maka mata pentazocine injection bayan danne ta da aka yi. Nan bacci yayi awun gaba da ita.


★★★★★★★★

Tunda ta shiga motar ta kifa kanta bisa cinyar ta tana kuka, tun iya hawaye ke zuba har ta fara kuka mai sauti. Babu abunda ke tashi sai shessheƙar kukan ta.
Cikin motar kuwa babu wanda yayi mata magana sai ma wata dake seat ɗin baya da ke jera uban tsaki alamun kukan na damun ta.
Matar da ke gefen Zahrah wadda ba zata wuce sa'ar Mamah ba ta ƙare mata duba kafin ta ɗaura hannun ta a bayan ta tana ɗan bugawa alamar rarrashin tace
“ƴan mata kiyi haƙuri ki daina kukan nan ko ma meyeh aka yi miki ki fauwala wa Ubangiji al'amarin ki shi zai yaye miki ba kuka ba”

Haka matar tayi ta bawa Zahrah baki har tayi shiru tana sauƙe ajiyar zuciya.. Bayan tayi shiru matar take tambayar ta ina zata je tace mata Abuja, murmushi tayi tace
“nimah can zan je ammah wace unguwar zaki je?”
Jimm Zahrah tayi kafin tace
“nimah ban san yadda na dosa ba tukun na”
Cike da tausayawa matar ta ke kallon Zahrah coz tunda suka shigo taji tana ƙaunar ta uwa uba kuma fahimtar akwai damuwa a tattare da ita yasa ta ƙara jin Zahrah a jikin ta.

“yaya sunan ki?” matar ta tambayi Zahrah
“zahrah” kawai tace
Murmushi matar tayi ta ce
“in babu damuwa ki ƙira Ni Mamah, naga kina cikin damuwa sosai, kada ki damu in munje sai ki sauƙa gida na kin yadda”
Gyaɗa kan ta tayi tana jin farin ciki ganin yadda matar ta nuna kulawar ta a kan ta.

Har suka isa Kaduna matar ke siya musu abu idan sun tsaya shan mai. A haka har bacci ya ɗauke ta.

Tana farkawa lokacin suka shigo Abuja, sannu matar tayi wa Zahrah. Bayan an sauƙewa kowa kayan sa suka tari taxi har gidan matar dake a Gwagwalada.
Ba laifi gidan da kyan shi, bayan sun shiga Zahrah tayi wanka umma (Aunty) Kamar yadda Zahrah ta ƙira sunan ta girka musu abinci bayan sun ci ta raka Zahrah guest room daga nan baccin gajiya ya ɗauke ta.

★★★★★★
Washegari aka sallamo su Bibalo suka samu motar da zata kawo su gida, bayan sun dawo a nan aka fara yiwa Bibalo sabuwar jinya ɗin kuwa ƙarfi da yaji ta zama mahaukaciyar dole, Baba AMARYA kuwa hankalin ta ya koma kan Bibalo yada bata damu da ɗauko zancen bokan ba.

Ɓangaren Zahrah da safe tayi sallah tayi wanka sannan ta ɗauki ɗaya daga cikin koɗaɗɗun atamfofin ta ta saka, fuskar ta fayau ta fito parlourn, a lokacin Aunty har ta gama breakfast, bayan sun yi breakfast Aunty ta tambayi Zahrah meyeh damuwar ta, bata ɓoye mata komai ba saboda tana buƙatar mai tallafa mata. Aunty ta yi kuka da jin irin rayuwar da Zahrah tayi daga nan ta yi addu'a Allah ya bayyana Mamah. Kuma tayi alƙawarin zata taimaka mata har ta isa zuwa ABATCHA FAMILY tunda ta san ESTATE ɗin sai dai burin ta Allah ya sa a bar su su shiga.

LA'ASAR sakaliya suka fita bayan sun tari taxi suka nufi ABATCHA ESTATE.
Tun daga round out ɗin da zai sada ka da ESTATE ɗin Zahrah dake ɗauki zuwa zuciyar ta ta fara bugawa coz Bata yi tunanin sanuwar dangin Mamah haka ba.

Daidai makeken gate ɗin ABATCHA ESTATE Wanda gefen shi ke ɗauke da wani signboard Mai ƙyalƙyali an rubuta “WELCOME TO ABATCHA ESTATE”. Bayan sun sauƙa Aunty ta have hannun Zahrah zuwa bakin gate ɗin, a hankali ta bita yayin da zuciyar ta karye tana wani irin bugu, ji take yi kamar ta koma coz wannan mansion bai dace da rayuwar ta ba.

Suna dumfaro gate ɗin Guards suka yi kansu suna tambayar lafiya.
Aunty tace “lafiya munzo wurin masu gidan ne”
Kallon baki da hankali suka yi musu kafin wani baƙi daga cikin su ya ce
“kai dallah ku bar wurin nan bana son iskanci in kun ƙi kuma toh yanzu zan harbe ku.

A tsorace Zahrah ta ja hannun Aunty zasu juya Aunty ta jijjiga mats Kai alamun A'ah kada ta sare tun yanzu. Juyawar su yayi daidai da fitowar wani tsoho wanda shima da gani ma'aikaci ne a ESTATE ɗin, duk da alamun tsufa da suka bayyana a tare da shi bai hana shi ƙura ma Zahrah ido ba, cikin ransa kuwa cewa yake
“madina?, Aah ita ai ance ta mutu to in ma ita ce sai yanzu sai dai ace ta haifi ya wannan”
Juyawa yayi ganin irin hararar da Zahrah ke aiko mishi coz ta gaji da kallon da yake banko nata.

Sunyi sunyi Guards ɗin su bar su su shiga ammah inaaaah sun ƙi, daga ƙarshe suka fafaro su da gudu, babu arziki Zahrah da Aunty suka koma.

Washegari suka ƙara komawa but jiya iyau, har sai da suka bugi Zahrah coz ta fara yi musu rashin kunya, har mamaki suke ga ta ƙazama ƴar ƙauye ammah ta san salon iskanci. Haƙuri Zahrah ta bawa Aunty tace mata ba sai ta ƙara rako ta ba har zuwa ranar da zasu bar ta ta shiga.

Sati guda Zahrah tayi tana zuwa ABATCHA ESTATE ammah ba a barin ta har Guards sun fara tunanin mayya ce.

Ranar da tayi zuwan ta na sati ne ta ɓarke musu da hauka kan lallai su barta ta shiga in ba haka ba wallahi sai ta hukunta su. Duk abun da ake yi a kunnen wannan tsohon shi dai ya kasa daina mamaki yarinya sak Madina da ta bar gida yanzu kusan tsawon shekaru goma sha takwas.
Ana cikin wannan drama wata arniyar mota ta dumfaro gare ɗin Babban gida.
Tun kafin ta ƙaraso wani guard ya jawo Zahrah da ke tsaye tsakiyar titi yana mai cilla ta gefe. A harzuƙe ta tashi tana faɗin
“Allah ya isa na Mugu kawai, wallahi duk ranar da aka barni na shiga gidan nan sai kayo da na sanin abun da kuka yi min”
Caraf a kunnen Dattijon dake cikin motar wanda tun lokacin da yarinyar ta faɗi ƙasa yaji zuciyar sa ta buga, hakan yasa yayi wa driver umarni kan yayi parking bayan ya sauƙe glass ɗin motar ne yaji abun da tace.
Cike da izza mutumin ya fito bayan driver ya buɗe mishi ƙofa, bai kuka Guards ɗin ba ya kamo hannun Zahrah wacce ta kusa mutuwa saboda mamakin yadda Dattijon ke kama da Mamahn ta. Katse mata tunani yayi da faɗin
“ƴan mata wurin wa kika zo ne, ko kin zo neman aiki ne?”
Jijjiga kan ta tayi tace “aah nazo wurin Hajjaty ne sati guda yau i a zuwa sun hana Ni shiga don Allah kayi musu magana uncle”

Uncle ɗin da ta ambata yada zuciyar shi bugawa, ba tare da ya kalli fuskar ta ba ta ce ta shiga motar, nan jikin Guards yayi sanyi suna tsoron kada ƴar nan tayi musu gwaiba.
Tafiya mai tsawo suka yi yayin da hankalin Zahrah yake kan manya manyan Mansions dake cikin babban guda, cikin zuciyar ta kuwa tunani take

“anya zan samu matsuguni a wannan aljannar kuwa?, Dubi gidaje kamar ba za'a mutu ba! Lallai Mamah tayi sakacin barin ahalin ta in dai kuwa ta tabbata nan ɗin ne”

Goge hawayen fuskar ta tayi yayin da Dattijon hankalin shi baya kan ta gabaɗaya ya sauƙe ajiyar zuciya.

Lallai duniya tana yadda take, duk yadda kake tunanin guda na alfarma toh kazo ESTATE ɗin nan sai kaji tsoro, gashi Mansions sun kai Ashirin a cikin ESTATE ɗin, parking lots baa magana kuma kowanne danƙare yake da mitoci, motocin ma waɗanda ido ba lallai ya taɓa gani ba.

Wani ƙarin mosque suka wuce wanda shima ginin shi ya tafi da zuciyar Zahrah daga nan suka yanki titin da zai sada ka da Babban Mansion. Bayan driver yayi parking PA ɗin Dattijon ya buɗe mishi ƙofa, a hankali ta fito yana yiwa Zahrah alamar ta fito, gyara riƙon bag ɗin ta tayi tana fitowa.

Dattijon ne ya ƙara kama hannun ta suka nufi cikin wannan daula, Zahrah dai baki kawai ta sake, lallai duk wayewar ka ina ka zo nan sai kayi ƙauyanci. Faɗin haɗuwar wannan parlour ma ɓata lokaci ne but kuyi assuming a ranku yadda zai kasance, bayan haɗawa irin ta parlourn, wani sihirtaccen ƙamshi ne da kuma sanyin AC ke tashi, nan da nan jikin Zahrah ma yayi sanyi.

Zaunar da ita yayi a parlourn ganin Hajjaty bata nan yasa shima ya zauna ɗin jiran fitowar ta, don kuwa ƙa'idar su ce haka in dai Hajjaty bata parlour sai dai ka tafi ko kuma ka jira ta, ko kaɗan ba sa so a takura wa tsohuwar.

Fitowar Laraba daga kitchen ne yasa ya miƙa kallon shi ga hanyar kitchen ɗin, sunkuyar da kai Laraba tayi saboda girmamawa, gashi dai gulma na cin ta ganin wannan dirty creature ɗin gefen Alhaji Umar kuma wai a parlourn Hajjaty tunani take wai dama Hajjaty suna da dangi talakawa ne?

Katse mata tunani yayi yace “Ki kawo mata refreshments, Babu musu Laraba ta juya ta kwaso snacks da drinks a kan tray, gaban Zahrah ta ajiye har zata wuce taji Muryar sa
“ki ƙira Hajjaty in ba bacci take yi ba”
Kai ta gyaɗa sannan ta wuce wata hanya wacce zata sada ka da bedroom ɗin Hajjaty.
Ita kuwa Zahrah mamaki ne ya cika ta ganin har yanzu mutumin ko kyakkyawan kallo bai yi mata ba balle ya gano ita ɗin jinin sa ne ga kuma uban refreshments dake gaban ta wai duk ɗin ita aka kawo.

A hankali ta ɗauki cake da hannu bata ko bi takan spoon.s da knives ɗin da ke gaban ta ba. Ta gutsiri na farko taji wani daɗi ya ziyarce ta, tana kai na biyu taji takun mutum hakan yasa ta dakata da cin cake ɗin.

Hajjaty ce sai kuma Laraba a bayan ta, kyakkyawar tsohuwa ce fara sol da ita, tana da mulmulallen jiki irin na tsofin da ake ƙira *bakwa tsufa*, sanye take cikin shigar ta ta alfarma, riga da zani ne ɗas a jikin ta, tunda ta fito idon Zahrah ke akan ta! Abun mamaki kana ganin ta kaga Mamah zaka tabbatar daga jikin ta ta fito, kamar su ɗaya sak, tsufar ce kawai banbanci sai kuma Hajjaty da a yanzu ta fi Mamah hasken fata.

Sai da ta kusa ƙarasowa idon ta ya sauƙa akan ƴar matashiyar da ke gefen yaron ta Umar, ɗagowar Zahrah da ta sunkuyar da kai yasa suka haɗa ido da Hajjaty, lokaci ɗaya zukstsn su suka buga dummmmm, Hajjaty ce tayi ƙarfin halin zaro idanuwan ta tana furta

“Maaa..ma...dii...diiiiiiiiiii...diiiina...ceeee”
Daga haka ta faɗi sume.

ALHAMDULILLAH, NAN NA KAWO ƘARSHEN TAKUN FARKO NA LITTAFIN A BABBAN GIDA Takun farko, ina riƙon Allah ya bamu ikon amfana da abubuwa masu muhimmanci daga ciki ya kuma yafe mana kurakurai da na tafka ciki.
In Sha Allahu nan ba da jimawa ba zan sake muku littafi na biyu wanda shine ainihin cikin labarin.
Ku ci gaba da kasancewa da ni don jin yadda littafin zai kasance.
Na gode muku sosai Allah ya bar ƙauna.
FADIMATU ADAM HASSAN
DIAMOND BHATOOL
DIAMOND LADY
OUM ZAINAB duk nice.....ki ci gaba da BIBIYAR ALƘALAMIN DIAMOND LADY, na gode.
ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH WABARAKATOUH

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login