Showing 36001 words to 39000 words out of 41765 words
da already ta gama sayar da awarar tsoro ne ya hana ta shiga. Ba ita ta shiga ba sai around 12:00am lokacin har sun yi bacci, a hankali ta lallaɓa ta shige ɗaki bata ƙara fitowa ba coz lokacin da take shigowa da kayayyakin aikin ta taji motsi kuma ta san ba Kawu bane tunda Baba AMARYA ta riga ta haramta masa kwanan gida.
A ƙasa ta kwanta saboda Baba AMARYA ta sa an sayar da komai na ɗakin Mamah a cewar ta ai ba dawowa zata yi ba kayan gado ne. Kuɗin kuwa a cike aka bata dubu uku wai ta fara awarar a ƙofar gida kuma kullum ita take dafa awarar, ta yanka tun a gida a lissafa in ta kawo kuɗin da bai kai ba kuma taci uban ta da duka gashi ba wani isasshen abinci take ci ba shiyasa ta zama wata solo-solo kamar raƙuma.
Da yake kullum da asussuba take tashi in Bata tashi ba ma za'a zo a kwara mata ruwa. Tana cikin bacci taji ruwa a jikin ta....ba shiri ta miƙe, ko sallah ba'a barta tayi ba taji duka ta ko ina
Suna dukan ta suna tsine mata.
“shegiya karuwa jiya har da ƙin shigowa wato kin bi kwarton naki Koh!”
Tana ihu suna ƙara bugun ta sai da taji jiki suka barta. A wurin ta sume baba AMARYA ta lalume ta ta kwashe kuɗinta.
Ta kwashe kusan awa guda tana kwance babu wanda ya damu da sumar ta ballantana su watsa mata ruwa. Sai da lokacin ɗaura girki yayi Baba amarya ta watso mata ruwa.
Ajiyar zuciya Zahrah ta sauƙe yayin datake buɗe idanuwan ta da suka yi mata nauyi, gashi kuma bata jin ƙarfin jikin ta.
Ganin ta farfaɗo yasa Baba AMARYA taka ƙafafuwan ta, babu shiri ta saki ƙara.
“don ubanki waye zai yi girkin mayya kawai ki fito ki mana abinci”
Cikin rawar murya Zahrah tace
“ki....yi....haƙu...ƙi....ri...ba...nida.....lafiya....”
Wani sabon bugu baba AMARYA ta ke yiwa Zahrah ita kuwa bata da ko ƙarfin ihu daga ƙarshe ta ce lallai lallai ta fito tayi musu girki. Sai can da ƙyar Zahrah ta miƙa ta fito, ga wani irin jiri da take ji a haka tayi musu abincin.
Ko ɗanɗan ba'a bata ba wai tayi laifi kuma ta cinye kuɗin awara. Haka suka lamushe abun su.
A daddafe Zahrah ta koma ɗakin ta tunawa da awarar jiya da ta ɓoye kamar ta san ba zata samu abinci ba tayi. Ɗauko ta tayi taci ko ruwa bata iya sha ba ta kwanta ...sallah kuwa yau ko asuba bata yi ba gashi la'asar ta kusa.
Bayan la'asar haka ta fita tayi musu girki tayi awara wanda kawai ƙarfin hali ne ammah sun riga da sun nakasa ta.
Bayan tayi wanka da ƙyar ta iya ɗauko ƙanzon da ta kankare na awara ta cinye shi gaya kamar mayya. Tana kuka tana hawaye har ta ɗan ɓigire tana bacci, Baba AMARYA ce ta zo ta canke ta da ƙafa a zabure Zahrah ta miƙe
“don ubanki assrar waken zki min, ki fito ki fice da awarar” tana faɗin haka ta fice.
Zahrah bata samu fitowa ba don kuwa kanta wani irin juyawa yake....sai da ya ƙara wajen 40minutesa wajen, Baba AMARYA kuwa tunanin ta Zahrah ta fice da awarar don kuwa ta san bata mata magana biyu.
Lokaci ɗaya taji kanta ya yi wasai saboda haka ta fito sannan ta kwashi kayan suya.... Alhamdulillah yau da wuri ta sayar ta dawo gida tana bawa Baba AMARYA kuɗin zata juya taji tace
“akwai wankin kayan mu Ni da Bibalo yanzu ki zo ki wanke”
Marairaice fuska tayi ko Baba AMARYA zata ji tausayin ta tace
“don Allah Baba ki bari sai gobe da safe kinji, wallahi bani da lafiya”
A hasale Baba AMARYA tace
“mayya yau in asibiti ne kan ki sai kin yi wankin nan, shegiyar mai siffar aljanu.
Babu yadda ta iya ta juyo ga cikin ga sai ƙugi yake mata, yunwa kamar ta hallaka ta. Bayan Baba AMARYA ta shiga ciki Zahrah ta faki idon ta ta je wurin tukunyar da suka yi abinci. A hankali ta buɗe ta tsoma hannun ta, jin taliya ce yasa ta wawusa a baki kamar mayya, ta ƙara ciko hannun ta ta kai baki, sai da tacinye tass ta rufe a hankali ta zo ta haɗa ruwan wanki.
Tana cikin wanki Bibalo ta shigo, hara ta banka wa Zahrah yayin da ita kuma ta sunkuyar da kan ta ƙasa. Wankin ta take hankali kwance duk da kayan sun ci uban datti. Bibalo ce ta fito ta wullo mata pants ɗin ta wai ta wanke, a lokacin kuwa Zahrah bata san MEH ya faru da ita ba tace
“in na wanke miki shegiya nake” ta faɗa babu alamar tsoro a fuskar ta.
Bibalo ta jima tana mamaki saboda iya sanin ta Bulebule yace ba zata taɓa yi musu musu ba ya mallaka musu zuciyar ta sai yadda suka yi da ita. A tsorace ta koma ta sanar da baba AMARYA, babu shiri su biyu suka fito a ɗan tsorace, saboda kuwa Bulebule yace ina dai asirin kan Zahrah ya warke to uwar ta ma zata warke, kuma aikin ba zai ƙara yiyuwa ba sai Bibalo ta aure shi. Abun da baba AMARYA ba zata taɓa yarda ba.
Hankali tashe suka nufi ɗakin mamah coz Zahrah ta bar wankin ta koma ɗaki abun ta. Wani haushi kanta take ji ta yaya aka yi har suke dukan ta suke azabtar da ita haka....
Toh wallahi sai tayi maganin su.
Cikin ƙarfin hali da saddaƙarwa Baba AMARYA ta ce
“ke fito ki ƙarasa wankin nan”
Kallon da Zahrah ta aiko mata yasa ta zaro idanuwa ba shiri. Wani tsoron Zahrah ne ya ɗarsu cikin zuciyar ta. Babu shiri ta kamo hannun Bibalo suka taho ɗaki. Ita kanta Bibalo a tsorace take.
Ɓangaren Zahrah kuwa kuka ta saka bayan fitar su
“kun cuce ni iyakar cuta....kun azabtar da ni, kun ɓatar da mahaifiya ta yayin da kuka kulle min baki har na kasa faɗa wa masu ɗaukar min mataki.....kun shiga tsakani na da karatu na....tun hana Ni cikar buri na....billahil Azeem bazan zauna da ku ba, zan tafi na barku da halin ku daga ku har Kawu bazan yafe muku ba.....yau ba gobe ba zan tafi kun ƙuntata rayuwa ta na tsawon shekaru biyu....kun bautar da ni kooooooooo. Tunda knce Mamah ta ta mutu bazata dawo ba yasa kika sayar da kayayyakin ta shikenan, Allah mafi sani in da gaske ne bazan yafe ba in kuma tana nan zan ci gaba da addu'ar Allah ya haɗa Ni da ita.
Haka Zahrah tayi ta surutai daga ƙarshe ta tashi tayi wanka ta rama sallolin ta ta kwanta.
Safiya mai albarka Zahrah.
MUNA GAB DA SHIGA TAKUN ƘARSHE WANDA CIKIN SA NE LABARIN ZAI FARA, WANNAN DUK PROLOGUE NE!
SHAFI BASU FI BIYU BANE SUKA RAGE, IN KIN SAN KINA BIBIYAR ALƘALAMIN DIAMOND LADY TOH KI ƘARA HIMMA DA COMMENTS, IN BAKI BI TOH KI FARA KADA AYI BABBAN GIDA BABU KE... COMMENTS SECTION GROUP DUK WACCE BATA CIKI TA SHIGA IN NAGA BA A COMMENTS BA ZAN YI POSTING PART TWO BA KUMA ZAN MAYAR DA SHI NA KUƊI....What I need is ur comments saboda ƙarfafa guiwa.
DIAMOND LADY CE 💎
BHATOOL ADERM.
[08/10, 11:58 a.m.] 💎Diamond Bhatool 💎: ️______________★★★_______________
Typing 📲
🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡
_(All in a big family🏠)_
★TAKUN FARKO★
_[Labari/Rubutawa]_
*©Fadimatu Adamu Hassan*
*A.K.A DIAMOND BHATOOL*💎
️
_______________★★★________________
﷽
PROLOGUE
*PAGE* 1️⃣9️⃣
Dedicated to mah sister Shaheedah, I love u endlessly ƙanwa am.
*Masu Neman labarin daga farko, ku danna wannan link ɗin sannan kuyi following*
SHARE AND COMMENT PLEASE
_______________★★★______________
Ɓangaren Baba AMARYA da kuma Bibalo abun babu kanta kwana suka yi a zaune suna nemarwa kan su maslaha daga ƙarshe suka yanke tafiya gidan mata su bi ta kan Asabe ta raka su wurin wani bokan tunda Bulebule yace ina aikin ya ɓaci ba zai gyaru ba.
Asubar fari Bibalo ta ciro ƴan kuɗaɗen da take yafuta daga wurin Alhajin ta da sauran mazan da take mu'amala, daga nan basu tsaya ko ina sai gidan mata.
Ko da suka SANARWA Asabe batun su bata Musa ba tace akwai boka na kan dutse, zata raka su kuma za'a dace sai a lokacin Baba AMARYA ta samu nutsuwa da sawaba.
★★★★★★
Ɗauke da addu'ar bacci a bakin ta ta farka, miƙa tayi kafin tayi ƙoƙarin tashi, tuno da abun da ya faru yasa Zahrah ta miƙe tare da goge hawayen da yake zuba a fuskar ta, alwala tayi sannan tayi sallah, kayan ta da yanzu suke a zube a tsakar ɗakin ta fara dubawa, gaba ɗaya babu nata wanda ta sani, “kenan sun daɗe suna mulka ta” ta faɗa cikin ranta. Ɓarin zuciyar ta ne ta Musa mata hakan tace A'ah Zahrah a haka bane, can ta yamutsa fuska tace
“toh in ba haka bane yaya ne? Gashi duk kayan da Ammi ta bani duk da cewa sun daɗe ai ban kyautar su ba, toh ina suke?” ta ƙarasa tana birkito kayan.
Ganin hakan ba zai fisshe ta ba gashi har gari ya waye sai hargitsa kaya take yasa ta miƙe ta fito don nemar wa kanta abinci coz wata shegiyar yunwa take ji duk da cewa ta ci abinci ma jiya. Jin shiru a tsakar gidan yasa ta ɗan leƙa taga MEH shegun nan suke yi, zuwa dai-dai ɗakij Baba AMARYA tayi sai ta leƙa ammah bata ji motsi ba kuma babu alamun mutum, a hankali ta yi Bismillah tana takawa zuwa ɗakin....dube-dube ta fara can ta hango buhu da kuma waken suya, murmushi tayi tace
“shegiya Baba AMARYA wallahi bazan bar miki shi ba gwanda ayi asarar shi da na baki”
Barar da taji almajiri nayi yasa ta ƙwalla ƙiran
“ya ka”
Bayan Almajiri ya shigo taga kuma da girman shi yasa ta marairaice fuska tace
“don Allah ka taimake Ni ka taimaki rayuwar ummah na tana kwance babu lafiya bamu da halin kai ta asibiti saboda Baba na ya rasu kuma ita je ɗawainiya damu. Fuskar almajirin ta nuna tsantsar rashin fahimta ganin hakan yasa Zahrah tace
“ina so ka taimake Ni ne akwai waken suyar Umma mu siyar sai na kaita”
Yanda take marairaice fuska yasa tausayin ta ɗarsuwa cikin zuciyar sa, ba musu ya amince ya kwashi fiye da rabin buhu ita ma ta kwashe sauran suka fita, da yake lokacin awara na tashe yasa aka saye shi tas....kuɗin ya damƙa mata yace shi zai wuce ta shiga maƙwabta tasa su raka ummar tata kitso. Ɗari biyar ta bashi daga nan yayi mata sallama ta dawo. A lokacin da zata shiga gida ta tuna da jakar da Mamah ta bata ta barta gidan su Badi'a, gashi kuma ta riga ta yanke shawarar su ma ba zasu ƙara sanya ta cikin idanuwan su ba har sai ta nemo Mamah, coz in SUKA ganta duka da cewa an raba tsakanin su ba zasu bar ta ta tafi Abuja ba. Tana tunawa da cewa irin lokacin nan Ammi bacci take, Badi'a na school yasa ta dumfari gidan.
A hankali take takawa tamkar wata ɓarauniya har ta iso bakin part ɗin Ammi jin babu alamun motsi yasa ta ƙara lallaɓawa ta sanya kan ta ciki, tana shiga siɗif suɗif kamar ƙadangare haka take bin bango har ta isa ɗakin Badi'a.
Maimakon ta shiga ɗakin ta ɗauki abun da take so sai ta tsaya tana kallon curtains ɗin dake cikin ƙofar.
“Allah sarki Aminiya ta masoyiya ta, yanzu shikenan daga, duk rayuwar mu ta baya ta zama tarihi, ga Abba da ya kula da rayuwa ta na wani dogon lokaci ba tare da ya banbanta Ni da ƴar cikin sa ba, yayi wa rayuwa ta da ta mahaifiya ta hidima shima haka ya zama tarihi, Ammi, Allah sarki Ammi na...kin so ni fiye da yadda kika so ƴar cikin ki, ki kan bani zaɓi a kowanne lokaci kafin ki bawa ɗiyar ki.
Dole zan bar rayuwar ku bari na wani dogon lokaci har zuwa lokacin da Mamah ta zata bayyana, oh! Har zuwa lokacin da zan cika buri na.
Fata na da addu'a ta gare ku Allah ya saka muku da gidan aljanna, ya kula da ku fiye da yadda kuka kulani”
Shessheƙar kukan da Ammi taji yasa ta farka daga bacci, ƙoƙarin tashi ta fara yi coz ba lafiya gare ta ba kwanan nan, a hankali ta dumfaro parlour saboda tana son ta ɗan haɗa tea.
Motsin da Zahrah taji ne yasa tayi gaggawar ƙulewa ɗakin wanda yayi daidai da fitowar Ammi kuma taga wulgawar abu. A tsorace ta biyo direction na wurin da taga wulgawar abu. Zahrah kuwa tuni ta faɗa toilet ta, Bata yi ƙoƙarin locking ba ta maƙale can bayan ƙafa. Har ɗakin sau da Ammi ta shiga Bara fata kowa ba hakan yasa tayi la'akari da cewa idanuwan ta ke yi mata zato.
Jin ta fita yasa Zahrah sauƙe wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauƙe kafin tafito daga toilet, a hankali ta ɗauko sidedrawer ta ajiye sannan ta ɗale dogon wardrobe ɗin dake ɗakin, bata sha wahala ba ta janyo jakar.... hawayen fuskar ta ta goge sannan ta diro dummmmm kake ji. Jin sauti ya fito yasa tayi saurin miƙewa ta mayar da drawer tana ajiyewa ta koma toilet jin takun ƙafar da ta tabbatar Ammi ce kuma ƙarar nan ne ya sa tazo dubawa, stilll irin duban ɗazu tayi daga nan ta koma bedroom ɗin ta.
Sai da Zahrah ta tabbatar Ammi ta shiga room ɗin ta yasa ta fito a hankali tana leƙen Ammi ta jikin curtains, ganin Ammi Bara parlourn yasa Zahrah fitowa a hankali ta bar part ɗin, haka ta lallaɓa da sauri ta fice a gidan. Wata ajiyar zuciya ta sauƙe ganin ta haye wannan siraɗin.
Da sauri ta koma gida still su Baba AMARYA basa nan, ɗakin ta ta ƙara shiga tana bincike, ganin jakar ƴan gayu (Trolley) yasa ta juye kayan ciki a ƙasa taje ta jera nata, ta ƙara dawowa tana bincika wa har ta samu wasu kuɗaɗen ta kwashe tasss duk da ba masu yawa bane, har zata fita tayi tozali da kular abinci. A wurin ta zauna ta cinye shi tass daga nan ta fita.
Ko wanka bata yi ba ta ɗauki wani Coffee brown hijab ɗin ta wanda ya amshi kyakkyawar farar fuskar ta.
Janyo Trolleyn tayi yayin da gaban ta ke dukan tara-tara. Bata ɓata lokaci ba ta tari mai adaidaita har tasha ya kai ta daga nan ta shiga ta zauna, mutum biyun da suka rage suma shuka shiga daga nan na juyo dan ɗauko report kan su Baba AMARYA..
Sai da suka yi tafiya mai ɗan karen nisa cikin wannan dajin kafin su fara hango wani ɗan ginin ƙasa, kasancewar duk ƙwarin guiwar su a halin yanzu ya ta'allaka ne ƙara shirya wani tuggun yasa suka saki dariyar cin nasara a tare. Suna isa wurin ginin suka ƙule, kwane-kwane suka yi kafin su miƙe wata doguwar siririyar hanya. Sai da suka yi tafiya mai ɗan nisa suka dakata bisa umarnin da suka ji ba tare da ganin kowa ba.
“ku dakata da tafiya!” Muryar ta faɗa a kausashe. Kafin daga bisani suji ance
“kowacce ta rufe idanuwan ta!” da sauri kuwa suka rufe. Suna rufewa basu ƙara sanin inda suke ba saboda wata fitinanniyar guguwa mai ɗan banzan duhu da hargagi ta mamaye wurin.
“ku buɗe idanun ku!” wata murya apart from waccan ta faɗa. Suna buɗe ido suka yi arba da wanni mummunan mutum wanda bashi da daɗin gani kana ganin shi ka ga typical boka, ga wasu zungura-zunguran ƙahon shi guda biyu.
Dariya bakan ya kece da ita yana faɗin
“Tun da sassafe aka nuna min tahowar ku waje na ammah baku iso ba sai yanzu hhhhhhh.....hhhhh" zazzare idanuwa suka yi cike da tsoro, suna mamaki ashe duk hatsabibancin Bulebule bai kai na kan dutse ba
Katse musu tunanin yayi da faɗin
“ku daina mamaki, ke Saudatu kin zo ne saboda ɗiyar mijin ki wacce a halin yanzu shirin barin gidan take yi, na duba madubin tsafi ammah bai nuna min ainihin inda zata je ba ammah a halin yanzu asiri ba zai yi tasiri a jikin ta ba saboda shaiɗanun da ke kanta sun hasala ba zasu bari a cutar da ita ba”
Shiru Baba AMARYA tayi tana zaro idanuwa cikin ranta tace
“shikenan ta faru ta ƙare, yanzu mayyar yarinyar nan sai da ta ɓata aikin nan”
Asabe ce ta katse shirun da cewa
“toh mai girma na kan dutse ya batun uwar yarinyar kumah?”
“hhhh....hhhhhhh......wai Madinah kuke nufi?”
Kai suka gyaɗa, ƙara duba madubin tsafin shi yayi kafin ya ɗago ya kalle su yace
“hh...hhhhhhh......hhhhh Madina,” juyo da madubin tsafin yayi gaban su. Ido suka zuba kai tare da waro idon
Mamah ce zaune a wani hamshaƙin parlour ga kuma wata babbar mace a gefen ta dai wani dattijo a kujerar dake facing ɗin tasu. Fuskar ta a marairaice tana jijjiga kai alamun bata don abun da ake yi.
Ɗauke madubin tsafin yayi ya fuskance su, in a serious tone yace
“kuna ji koh, abun da kuka gani gaskiya ne...yanzu haka Madina tana can Kaduna gidan wasu mutane wanda suka kaɗe ta wata rana kan titi, da suka fahimci ba tada hankali yasa suka tafi da ita suna mata magani, sai dai babban sihiri aka yi mata, kuma makarin sa ɗaya”
Ƙara maida hankalinsu gare suka yi alamar suna son sani
“makarin ba komai bane face ƴar ta, tana haɗuwa da ita asirin zai karye ya rage naku ku san abun yi”
Yana faɗan haka ya murtuƙe fuska. Baba AMARYA ta marairaice fuska yana haɗa hannayen ta biyu
“ranka shi daɗe ka taimake ni bana don sihirin ya lalace ko dan saboda mijin da na aura, boka Bulebule yace da zarar asirin da aka yi wa matar ya karye to na jikin sa ma zai karye gashi dama can asiri nayi masa ya aure ni idan ya