Showing 6001 words to 7376 words out of 7376 words

Chapter 3 - UWAR MIJI A'ISHAH YAHAYA TANKO

10 Aug 2024

1589

kafin me miki kwalliya tazo nan da karfe uku jirginta zai sauka kuma zata taho miki da kayan da zaki amfani da su".

Kowa yai Mamakin Hajja har yaushe ta nemi me kwalliya duk faɗin garin nan na kano ace be isa ba har sai anje legos Tab! Babbar magana .

Bayan an kammala cin abincin ne Su Karime da Hanne suka kwashe kayan da aka bata suka kuma gyara wajen tsaf.

Aka fara shigo da kujeru ana jerasu a harabar gidan aka kuma shirya waje ya kyau sosai sannan Hajja tasa aka jajjera lemuka.

Sannan ta umarci isa direba da yaje filin jirgin sama zai taho mata da bakuwa ta kuma bashi number da zai kira idan ya karasa,ya amsa da to uwar dakin mu me rumbi alkairi ya nufi wajen da aka tanada don ajiye motaci ya zabi daya daga ciki ya shiga Nan da nan Bala ya wangale masa get ya fita da gudu .

Bala ya mai dashi ya rufe ya koma mazauninsa .

Shigar Hajja daki ke da wuya ta iske Auta na kwance tsakiyar gado tana waya.

Haba Auta kin duba lokaci kinga kuwa ai na dauka kinyi abinda nasaki ne ashe ke kina nan kinata faman waya to ki dakata da yinta saboda bose ta sauka yanzu haka anje taho da ita .

Ta kashe wayar tana turo baki ta kuma tsuke fuska tace.

" Nifa Hajja ki kyaleni na huta daga dawo wata zaki fara rusa min shirina kin san kwa da wanda nake waya".

To Auta na Dena amma dai ki tashi kije kiyi wanka kar tazo tana jira kinga Nima zatai min tamu ta manya ko.

Ta tashi tana zumburo baki ta nufin dakin ta .

A can bangaren su Amina kuwa tuni tana gaban madubi tana kwalliya cikin wani tsadadden less me ruwan goro Salim ya zuba mata ido yana kallonta ya magantu yace.

" wallahi Kanwata kin cinye kinga kuwa irin kyan da kikai sai kace yau ne ranar dinner dinmu ki tashi nai miki hoto tun kafin wani yai miki".

gaba daya sukai dariya.

Khadija ce tsaye jikin bangon falonta tana faman daukar selfe Adam ya fito daga wanka yana tsane ruwa tsayawa yai cak yana kallonta.

" Wow kinga kuwa yadda kayan suka amshi jikinki ya zama dole naiwa telan nan babbar kyauta saboda ya fito min da mata kefa zinariya kinfi kowa ya kamata nima na sa kaya ayi hoton dani baza'a barni a baya ba ke din ta da bance da Hajja ta rabani dake ai da tuni ta rasani kefa me kyauce nasan kafin na fada kin sha ji a bakin wasu".

Suka yi dariya a tare ta kuma fito masa da kayan da zai amfani dasu ta shirya shi tsaf ta feshe shi da turare iri da ban-daban.

A can kuma sashen Aminu kuwa suma sun sha adon su sanye suke da shiga iri daya shaddar ta amshi jikinsu ga wani kamshi daya ke tashi .


A can bangaren su Hajja kuwa tuni bose ta shrya su tsab ta kuma gyara Hajja idan ka kalli Hajja kasan naira tayi kuka anan .

Karfe biyar dai _dai kowa ya hallara awajen Mc ya fara gabatar da aikin sa ya kuma yiwa manya baki barka da zuwa tare da yi musu fatan alkairi ya kuma kara da cewa yana san babbar yarinya ta bayyana a nan filin ta nuna farin cikinta da Allah yasa ta dawo gida lfy.

haka kuwa akai ta fito cikin isa tai magana ta kuma koma inda ta fito me hoto da Dije kowa ya fara gabatar da abinda ya kawo shi gidan Marigayi Mudi Baba tun lokacin da Zahra ta fitone Najib ya kyalla idonsa akan Zahra ya kuma sawa ransa ya samu matar data dace dashi dama irinsu yake dan ita ce dai dai shi kuma sun dace da junansu


Duk inda Zahra ta gilma Najib yana binta da kallo tunaninta ya kunno masa kai ya kasa kai komai bakinsa ya mike ya nufo wajen mahaifiyarsa Hajiya Sa'a wadda tana ɗaya daga cikin Aminan Hajja Sarai ya rusuna a gabanta ya soma magana kamar zai fashe da kuka.

" Nifa Hajiya zuciyata ta kamu da san Zahra dan Allah ku kulla aure tsakanin mu ko dan zumuncin ku yafi dorewa na kamu da sosai".

Ta katse shi da cewa.

" bari idan munje gida sai mu san abinda daya dace kaga anan idon kowa yana kanmu kaji shalelena".

ya miƙe ba'a san ransa ba ya koma inda yake .


Bayan anci an sha kowa yayi kat .

Mc ya koma bakin aikin sa cikin murya me karfi yace ina san ganin Yaya Salim babban ɗa ga marigayi Mudi Baba ya fito ya bayyana kansa.

Yaya Salim ya fito cikin shigar alfarma ya fafada murmushinsa ya karbi abin magana ya soma da sallama sanan ya nuna jin dadinsa game da kammala karatun Zahra da kuma irin nasarorin data samo ya sa hannu cikin Aljihunsa ya zaro key din mota yace wannan itace gudunmarsa ga kanwar tasa sannan ya zaro kudi masu yawan gaske ya mikawa Mc.


Nan waje ya gauraye da ihu kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa.


Nagode fari me farar aniya bakai farin banza ba Allah ya jikan Marigayi Alhaji mudi Baba.

Yanzu ina san ganin Yaya Adam a wannan fili shima yazo ya nuna mana nashi farin cikin shima ya fito kowa dai ya fito ya nuna nasa farin cikin,bayan taro ya watse ne Hajiya fanna ta kebe da Hajja Sarai nan ta kara bayyana mata mummunan kudirinta akan surukanta .

Karki sake kiyi sake wasu can su mallake miki ya'ya' lokaci guda bayan ke kika sha wahalarsu kika kuma rainesu to dan haka bazaki zuba ido a rabaki da su ba sannan kar ki bari kuma a cika miki gida da yara ki dage kawata ba wasa.

"Kin san kuwa irin shirin dana yi bazaki gane ba dawowar Auta ne ya tsai dani amma yanzu zan dora inda aka tsaya ke dai ki zuba min ido kisha kallo na fada musu ba wani dangantaka tsakanina dasu sai ta uwar miji".


Suka tafa nasanki ba wasa Hajja sarai .

"Kin shirya komai ya shiryu duk ma'aikatan gidan nan sun fito tas dasu,ina autar ne ta fito muyi sallama direba yana can jirana".

Hajja tana can dakinta ita da kawayenta bari na kira miki ita.

Aa kyaleta zan ba da sako a ajiye mata kafin na wuce ta bude jakarta ta zaro wata karamar akwati wadda take dauke da Agogon gold ta mikawa Hajja Sarai ga tawa kyautar ki bata tana fada dai-dai lokacin da wayar tai kara, kinga ya gaji da jira sai munyi magana.

Ta rakato wajen da ya ajiye motar nan ma'akatan gidan suka dinga rusunawa Hajja suna gaida ita.


A can dakin Zahra kuwa tana zaune a katafaren gadonta suna hira da su kausar da Hibba wadanda kawayenta tun suna yara Hibba tace.

"Zahra nifa yanzu aure nake so nagaji da zama haka babu aure".

"tab! Haba hibba ana hira me dadi zaki kawo batun aure dududu yaushe muka kammala karatun da har za'ai maganar aure".

Zahra tace. "nida nayi alkawarin aure da wani dan kasar maroco amma naga Hajja ta nunan bata san nai nesa da ita ta kuma ce dole a bani office babba companyn mu".

Kuma na fara yadda da hakan kunsan wani har fa ya sanar da mahaifansa cewa ya sami matar aure yanzu bansan ta ina zan soma ba.

ai kuwa wannan me sauki ne zan tsara miki abinda zaki ce masa kawata.

Injin Kausar.


"Hmmmm kince kina kaunarsa har ta kai kunyi maganar aure yanzu kuma saboda wani dalikinki mara ma"ana ki canja masa lokaci guda kidai kara tunani kawata".

A can bangaren su Salma kuwa tun bayan dawowarta sashenta ta ke faman zabga kuka.

"Ashe bazaki iya jure komai a kaina ba ki sani bani nai miki ba kuma wadda tai muku uwace a wajen mu baki daya dole mu sawa kan mu hakuri da duk abinda taxo mana dashi ni nasan bazata cutar damu ba".

Ta mike tsaye ni bazan duba ido naga uwar miji tana san cutar da rayuwarta ba dan na auri dan'ta."

Ya saki baki yana dubanta kin san kuwa abinda bakinki yake furtawa .

Uwar miji fa kika ce tab!




```To jamma' a mu hadu a book 2 taku har kullum me san farin cikinku```



*AiSHA YAHAYA TANkO*

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login