Showing 3001 words to 6000 words out of 7376 words
to shima wannan dawowar ta akwai babban kalubale tana da iyayi gashi kuma duk abinda za'a mata baya burgeta hatta yan'uwanta basan zamanta agidan nan saboda rashin mutunci ga wulakanta mutane bata san darajar kowa ba, ke zata iya raga miki tunda kun hada jini da ita kuma kunyi wasa tare lamarin ba'a cewa komai.
Amina naji kince ko ina na gidan zagaye da camera amma naga kinai min bayani ba tare da fargaba ko jimami ba .
Ta daga kai ta dubi ko ina tace ai nan babu camera shi yasa na saki jikina yanzu me kike sha'awa Hajja taci .
Ni ina zan san abinda zata ci ki dai taimaka min muyi girkin tare bazan sakar miki ba.
Nan da nan kamshin ya cika gidan hatta hajja dake kashinhide a falonta ya cika mata hanci ta girgiza kai ta matsa remote din dake hannuta nan da nan Tv dake manne jikin bangon falon ta kawo hoto da sauti ta kwallawa hanne kira ta amsa cikin sauri ta gurfana gabanta gani ranki ya dade ko akwai abun da kike bukata ne.
Cikin isa take magana.
" inaso ya haɗa min kayan marmari yanzu san ki shirya mana wajen da zamu ci abinci ki kunna turaren wuta kiyi amfani dana wajen yar barno idan kin gama kije dakin auta ki kar kaɗe ko ina ki gyara mata shi tab ki mu kunna mata turaren wuta ki tabbata kinyi yadda ya kamata tashi kije".
To ranki ya dade duk abinda kikeso shi za'a yi na barki lafiya Uwar dakin mu me runbun alkairi taji dadin yadda Hanne tai mata saki murmushi.
An kammala komai an kuma jiresu a kinda ya kamata ne kowa ya hallara a falon Hajja hatta su Salim sun dawo gida da wuri yau abinci ne iri-iri Amina ta fara zubawa Hajja sannan ta zubawa Salim shima ta zubawa kanta,ta koma ta zauna.
Yanzu kuma ko wacce ta zubawa mijinta da kanta ita ta gama nata aikin na dare kuma Karime da Hanne su zasu dafa mana.
Nan fa Khadija da Salama suka fara ƙoƙarin aiwatar da abinda Hajja ta umarce su, wajen yayi tsit kowa da alama abincin Amina yayi daɗi ga kamshin ya turare da wajen yake kowa ci ya sha yayi kat bayan an kwashe kayan an Kuma gyara waje yayi tas kamar ba'a bata ba.
Hajja tace da Salim.
"Inaso ka kirawon Musa me hoto dan inaso zanyi hotuna da surukai da kuma ya'ya'na da kuma Autar Hajja kuma uwata ta kaina sannan inaso a haɗa mana walimar dawowar ta gida zan bawa ko wanneku damar ya gayyato mutane biyar dan suzo suci su sha su kuma taya Auta murnar kammala karatunta, sannan inaso idan ko wacce zata tafi a bata naira dubu 50 duk saboda murnar dawowar Zahra".
Kowa ya buɗe baki cike da Mamaki Salim yace.
" Gobe kike san ayi walimar ko yaya?".
Hajja cikin isa tace.
"Kar ka manta irin tarin dukiyar da muke da ita ya isa ace muyi amfani da ita a duk lokacin da muka ga dama bawai sai mun batawa kanmu lokaci ba duk na raba kwangilar abincin da za'a dafa,sannan kuma su Karime zasu soya kaji da kuma abinda ya sauwaka, ku kuma ku tashi kuje ku gayyaci mutanen da kuka ga dama sannan kuce musu karfe 5 zasu zo idan suka wuce ko basu karasa 5 ba to lallai baxasu shigo ba dan tuni ma na sanar da bala".
Dukan su suka tashi a tare ko wace mijinta ya bayanta Hajja ta dai bisu da kallo sannan taci gaba da latsa wayar dake hannunta ko wanne su ya kasance da matarsa yayin da yake bayyana rashin jin dadinsa akan dawowar kanwar tasa haka dai akai ta shigo da lemo na gwangwani da sauran kayayyaki .
Hajja tana zaune a gefen gadon dakin cikin shigar alfarma ta daga kai ta kalli agogan dake manne jikin bangon dakin nan zuciyarta ta fara sake-sake tai saurin kiran wayar dake gidan kiran farko Salim ya daga ya kuma amsa da cewa.
Yana zuwa".
haka ma Adam yai shi kuma Aminu sai da tai kira uku sannan ya daga ya kuma da cewa ta jira shi nan da minti 30 zai fito dan yanzu baze iya fitowa ba saboda wani dalili
Hakan ta hakura ta kuma kasa daukar mataki suka gurfana a gabanta sannan Aminu ya karaso ta dube shi tace Babana sarkin rigima wai yaushe zaka girma ka dena wannan halin naka kasan fa yanzu kayi aure dole sai ka rage wani abu
Ya sosa keya ya durkusa gabanta yace wallahi Hajja kaina ne yake min ciwo ne .
Ai sai kasha magani bawai kai ta zama da ciwo ba,yanzu dai ya maganar shagunan mu na dubai yanzu me ake ciki kuma kunce an sauke kaya amma ba wanda ya sake magana sannan kuma akwai wata oder da nayi dazu a paris wadda nake sa ran zamu samu alkairi acikinta sannan kuma inaso a kara dibar sababbin ma''aikata wadanda zasu bamu hadin kai sannan kuma inaso ko wanne ku ya tabbatar ya tanadin irin kyautar da zaiwa Mama,kun san gobe i yanzu muna tare da ita sannan kuma a samar mata office din daya dace a ita".
UWAR MIJI
PAGE 6 and 7
BY AISHA YAHAYA TANKO✍️
*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(Sarki da Sarauniya Writers)*
_We Rule the World of Writing_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100063945240173
SADAUKARWA GA FATIMA IBRAHIM MUHAMMAD ALLAH YA BATA LAFIYA DA DUKKAN MUSULMIN DUNIYA🥰
Gaba daya suka amsa da toh ta kara da cewa inaso ku jawa matayenku kunne akan Auta ta bana San bacin ranta ko yaya.
Karki damu Hajja in sha Allah babu wata matsala balle damuwa ai suma duk na gida ne babu bare acikinsu kuma sun San juna ko da an jima ba'a hadu ba amma zamu tunasar dasu.
"ina da Magana.
cikin sakin fuska to Babanah muna saurararka.
Kema Hajja ki tsawatar mata akan matayen mu kar daga zuwanta zata fasa Mana gida kin San halinta da gadara da izza ya kamata ma tayi kokarin fito da mijin aure itama ta tafi can gidan mijinta ta huta ba muma ta bar mu sake da matan mu cikin walwala
"Cewar Adam.
Wani dogon tsaki taja wanda sautinsa ya fito fili ta gyara zaman fuskar a murtuke ta kai hannu ta dauki robar ruwan dake gefanta ta kurba ta kuma ajiye ta dubi Adam wannnan itace hirar da kuka tattauna kai da ya'n uwanka shi yasa naga bakwa farin ciki da dawowarta gidan nan to ku sani dole ta dawo gidan nan saboda ba inda yafi mata nan kuma dole tayi abinda taga dama ko zan aurar da ita ba yanzu ba sai na da lokaci me tsawo duk ku tashi ku bar min waje bana San kara ganin anan sai na nemeku.
"Kiyi hakuri Hajja tuba muke tsautsayi ne yasa shi fadar haka amma baze kara ba ki duba girman Allah ki yafe masa .
"Ta daka musu tsawa nace ku tashi ku bani waje ko ni na bar muku wajen tunda ban isa ba.
Haka suka tashi jiki a sabule ta kau da kai gefe guda kamar ba su take kallo ba tana jin sun fice ta dauki wayarta ta danna number kiran farko aka daga.
A can bangaren.
"kuwa Hajiya fanna ce hakince a katafaren gadonta wanda ya mamaye dakin ga haske ta ko ina tamkar rana kamshi na tashi ta ko ina sanye take da shigar Alfarma jin karar wayar ne yasa ta dago kanta a hankali tana duban wayoyin dake gabanta idonta ya kai daya daga cikin wayoyin ganin sunan Aminiyar tata ne yasa taki wani guntun murmushi na manya mata tasa hannu ta dauka ta kuma kara a kunneta Hajja ya garin ya kuma Angoye fatan dai kowa lafiya yana ji muryarki haka ko wani abu ne .kiyi hakuri kinsan fa sha'anin yaran nan sai addu'a fa to Allah ya kaimu goben zamu taho dasu sadam in sha Allah.
Bayan sunyi sallama ne ta jiye wayar tace Hajja sarkin rigima.
Tun bayan wayarta da Hajiya fanna kuwa taji sanyi a cikin zuciyarta ta kuma tuna da gobe i yanzu tana tare da rabin ranta Autar mata wato zahra baby. tayi ajiyar zuciya ta kara da cewa Allah ya kawo min ke lafiya gudan jini na.
Sannan ta saurin kunna karamar na'urar dake manne jikin bangon wadda take iya ganin dukkan abinda take gudana acikin gidan me idonta zai gani ta kara murza shi ta tabbatar da su salim ne zaune a wani bangare na gidan ina suka tara matansu suna tattaunawa abin Mamaki Amina ce ta mike tsaye tana nuna salim da hannu kamar zata kai masa duka Nan da nan taji wani abu ya tokare mata kirji tai saurin kashewa tare da kifa kanta jikin kujera tana karanto addu'oin da suka zo bakinta .
Ta fada a fili shin me hakan yake nufi da sake bazan lamunta ba kuma ban haifo ragon da' ba zan sake shi ina kaunarku ya'ya'nah zan nunawa duniya ni uwar miji ce .haka hanne tazo ya shaida mata duk ta gama komai hatta wanke bandakin shima na kammala ko akwai abinda kike bukata yanzu
'Cikin isa bana bukatar komai sai dai ki dauko min magunguna Masha dan yau ko na safe ban sha ba ga kuma na dare.
Subhanallahi uwar dakin mu garin yaya haka ta faru ai kuwa yanzu sai kiyi kokara sha bari naje na dauko miki.Nan da nan ta tashi cikin sauri ta nufi wajen da ake ajiye maganin ta dauko ta kuma nufo wajen Hajja nan ta bude mata robar ruwan ta kuma bude mata maganin tana bata tana sha har ta shanye ta gyara mata wajen sukai sallama ta fice daga cikin dakin.
Tun Asuba gidan Marigayi mudi Baba ya dau haramin kamshi ta ko ina abinci iri-iri ake shiryawa kafin kace kwabo an gama komai an kuma fara shiryawa a babban falon gidan .
A can bangaren Hajjja kuwa tasha ado cikin shiga ta alfarma ta zuwa yan'kunne da sarka tasha as bin hannu na Gold sai walwali take ta ga wani kamshi da yake tashi ta mike ta nufo karamin falon ta zauna tana shan kamshi.
Tana jin muryar su Salim ta kara hade rai ta kau da fuskarta tai kamar tana kallon TV dake manne jikin bangon falon ta amsa sallamar ba tare da ta dubesu .
Wai Hajja har yanzun fushi kike ai kamata yai a wannan ranar ko me akai miki kiyi hakuri tunda yau rana ce ta farin ciki da walwala be kamata Auta ta dago ta ganki acikin wannan halin ba mun ari bakin Adam muna me kara baki hakuri dan Allah .
Tadan saki fuska kada'n ta kara da cewa na yadda amma jiya naga abin daya bani Mamaki akanka ta nuna Salim da hannu tace yaushe ka zama rago kai kuma lalacewar da matarka zata dinga daga maka murya tana nuna da hannu kamar zata mareka wannan abun jiya da shi na kwana shine dambe zaku yi ko kuma naku salon soyayyar ne haka ta dakata da yin maganr daidai lokacin da wayarta ta dau kara nan ta saki murmushi wanda ya tabbatar da cewa sanyin idonta autar ta ce ta kira gaba daya suka mai da dubansu wajen Hajja sannunku! Sannunku!! Sannunku!!! Auta ta kun sha hanya yanzu isa direna zaizo dauki to bakya san ya zo muna tare dasu bari gasu nan zuwa Ta ajiye wayar ta kuma sanar dasu dasu je filin jirgi su dauko zahra sun sauka yanzun nan suka tashi suka nufo wajen da aka tanada domin ajiye motoci Aminu ne yace Yaya salim mu hau waccen jib din can kasan Ac tana da karfi kuma kasan yarinyar akwai rainin hankali cewa zatai mun dauko ta a mota me zafi haka kuwa akai .
Adam ne yake tuka motar cikin nutsuwa yake tafiya can wayar Salim ta hau kara ya lalubata acikin Aljihunsa sunan Hajja ya bayyana a fuskar wayar yace to me Kuma ya faru bayan yanzu muka baro gida kai Hajja ta fiye rigima ya danna sannan ya kara a kunnensa muna fa hanya kinsan akwai nisa tsakinani mu amma in sha Allah nan da mintin biyar mun karasa.yana ajiyewa ya dubesu kunji wannan sangartacciyar yarinyar nan ce ta kirata wai ta fara gajia zafi yana damunta suka yi tsaki ba tare da sun bada amsa ba suka isa filin jirgi can suka hangota cikin shigar riga da wando ko dan kwali babu taci karin gashi har gadon baya ga dogon takalmi tsinsa kamar zai karye kayan sun manne da jikinta tana hangosu ta rugu da gudu ta rumgumesu tana murna jamma'ar da suke wajen suka bisu da kallo bayan sun shigar da kayanta ne duk shima cikin mota ya tayar suka dau hanya a nan take basu labarin tayi wani saurayi dan kasar maroco kuma sun daura alkawarin aure dashi.Adam yaja ya tsaya a gefan hanya suka ce lafiya ya kallesu yace ai dole na tsaya auta tazo da labari me dadin gaske zatai aure a kasar maroco inda mike dad wani katafen companyn zaitun ai kunga sai ta ci gaba da kula sashi.
Suka amsa da Eh ka kawo shawara.
Tab! Aini ba wahala naje ba zaman aure naje kunsan ni bazan iya aiwatar da aiki ba dama ku canja shawara ni dan Allah Yaya Adam kaja mota mu tafi wani wari ne yake dukan hanci.
Aminu ya tabe baki kaji ya'r rainin hankali ta ina zakiji warin bayan ko ina a rufe yake
UWAR MI JI🍁🍁*
*PAGE 8*
*BY AISHA YAHAYA TANKO✍️*
Ta tabe baki tace. "ai daman Yaya Aminu duk abinda nace baka yadda dashi ni wallahi na matsu naga Momcy nah".
"To koh za'a baki motar kija ne tunda kin fimu sauri daga dawowarki zaki farai mana iyayin banza da wofi".
Wai me yasa kuke haka ya kamata ku kame bakunan ku ku sani farin cikin Hajja baya wuce mu farantawa kanwar mu rai amma ku kin ki ganewa sai faman jan magana kukeyi.
Cewar Salim.
Shi yasa nake ji dakai Yaya salim kana nunan kauna sosai da ban nai ma taka tsarabar.
Acan bangaren gidan Mudi Baba kuwa kowa ya shirya tsab dan taryar Babbar bakuwa kuma autar Hajja.
Ji sukai an hon da sauri bala ya tashi ya wangale get Adam ya sako hancin motar be zame ko ina ba sai wajen da aka tanada
Hajja ta karaso wajen motar tana dogara sandanta Zahra ta bude murfin motar ta fito cikin sauri ta rumgume Hajja tana tsalle da murna duk wadanda suke wajen basu isheta kallo ba hajja na rike da hannunta suka karasa cikin daki.
Bala me gadi ya dinga shigo mata da akwatunan ta bayan ya gama ne ya rusuna yace sannun da zuwa Autar uwar dakin mu fatan kinzo lafiya .
Ta kalle shi a wulakance ta kuma toshe hanci tace.
"dan Allah Bala kaje kayi wanka baka ji yadda kake bugawa ba sai kace mushe nifa ba rayuwar Nijeria wannan bacin ran ne damuwata".
Hajja me ka tsayi yi ne ko baka ji abinda Auta tace ba ka fice min daga daki sai kai wanka zaka dawo kuma sai na nemeka .
Cikin sanyin jiki ya fice daga dakin zuciyarsa ba dadi ya jima yana surutai kafin ya koma mazauninsa.
Gefe daya Amina da Salma da Khadijah ne suna jimama abinda Zahra tai musu ji sukai kamar daga sama ana cewa sai kunyi hakuri tunda ta dawo,gida komai ya kara lalacewa.
Karime ce ta karaso wajensu dama nasan wannan ranar tana zuwa ta dubesu duk wannan baze sa ku sami ku sami mafita ba tafiya zaku yi dakin Uwar dakin mu kuce kunzo ku yiwa Auta sannu da zuwa haka kuwa aka yi suna isa sukai sallama nan suka iske Zahra kwance cinyar Hajja tana sangarta suka rusuna a gabanta suka ce.
"Dama zuwa mukai muyi miki murnar dawowar Zahra fatan tazo lafiya".
Ta saki ranta na gode sosai kuje ku huta idan auta ta huta zan nemeku kuzo muyi kari kafin lokacin walima yazo idan kun fita ku turo min mzajen ku.
Kwance take a cinyar Hajja latsa wayar hannunta hajja na tuna kince min su Yaya Adam sunyi aure koh Allah yasa
Zasu dinga biyayya a gareni dan ni bana san raini.
"kaje ana san ganinka a dakin Hajja yanzun nan".
Amina ke wannan maganar.
UWAR MIJI🍁🍁*
*PAGE 9 and 10*
*BY AISHA YAHAYA TANKO✍️*
*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
*(Sarki da sarauniya writers)*
Duk suka hallara a falon Hajja suna sauraron suji abinda zata ce musu shiru bata ce musu komai ba tama mai da hankalinta akan zahra tana bata labarin paris da kuma yadda tasha gwagwarmayar data sha akan karatun suka gangaro labarin saurayinta ɗan ƙasan Maraco da kuma alkawarin da suka kulla na aure.
Cikin girmamawa yace.
" kince kina san ganin mu ,kuma munzo amma kinyi burus dani hakan yana nuna har yanzu baki wuce ba ya kamata kiyi hakuri muyi abinda ya dace kin san yau muna da baki".
Ta d'an saki fuska hakane komai ya wuce yanzu kowa ya kira matar sa a waya zamu ci abincin rana tunda yau ko kari ba'ai a gidan nan ba duk dan zuwan Autar hajja .
Suka amsa da hakane Hajja suka faɗa suna kokarin mikewa tsaye .
Tai saurin dakatar dasu ta hanyar nuna su da hannu ta kurbi ruwan dake gefan ta ajiye tace.
" ina kuma zaku ko baku ji abinda nace ba"?.
Nan kowa ya amsa da munji suka zaro wayoyinsu suka fara kokarin abinda Hajja ta umarce su da su yi
Cikin lokaci kada'n Kowa ya hallara a wajen cin abinci .
Zahra cikin ya tsinar fuska take cin abincin kamar wadda akai mata dole .
"Nifa Hajja wannan abincin be min dadi ba sai kace na ƴan koyo naji ya fara samun ciwon ciki zanje restaurant naci abinda raina yake so".
tana fada tana kokarin mikewa tsaye.
"Haba Auta ba inda zaki je yau na shirya miki walima ta murnar dawo warki tashi zaki yi kije kiyi wanka