Showing 1 words to 3000 words out of 9074 words

Chapter 1 - LAIFIN WAYE by A'isha yahaya tanko

07 Aug 2024

1540

Laifin waye...?,

Laifin wayeeeeee


Godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai
Ya Allah ka bani iƙon fara wannan littafi
Lafiya in gama lafiya Allah ka ban iƙon
Rubuta dai-dai

da fatan da za'a ɗau darasin dake cikin
Wannan littafi domin ya haɗa komai
Inna CE komai ina nufin komai

Gargaɗi!!gargaɗi!!
Ban yarda wani ko wata ya canza min
Labari ba ko mai da min document
Ko masu YouTube channel su mai da
Min audio duk wanda yayi haka

Hmmm zai fuskanci fushin hukuma


Wannan labarin kirkirarre ne duk
duk wanda yaga yayi dai-dai to ya ɗauka
Arashine.......

*TSANANIN RAYUWA*









*NA MARUBUCIYA *A'ISHA YAHAYA TANKO*






_Wannan littafi yana ɗauke da abubuwan daban-daban na tausayi da Al'ajabi nasan idan ki/ka karanta sai ka zubar da hawaye😭😭_





Fatima da Sadiya ne zaune a ƙofar wani katafaren gida kallo ɗaya zakai musu kasan suna neman taimako.

Na taka burki ina ƙoƙarin fitowa daga cikin motar naji sautin muryar ɗaya daga cikin su tana cewa.

"Ke Sadiya mu gudu kar ya sace mu".

Turus nayi jikina a sanyaye na jingina a jikin murfin kofar,ina saƙa abubuwa a zuciyata har na dena kallonsu saboda irin gudun da suke yi.

_Wannan shine rashin sani wanda yafi dare duhu da kun tsaya zan taimake ku amma rashin sanin waye ni yasa kun yiwa kanku in sha Allah nayi alƙawarin zai taimake ku aduk inda kuke._

Inji Yusuf lokacin da yake furta wannan kalaman a cikin zuciyarsa.

Yana gama faɗa ya shigewarsa mota ya tada ya fara tafiya a nutse yake toƙi har ya isa cikin gida a falo ya tarar da Amina tana kwance tan

"Sannu sarauniyar mata,ana sana'anarne baki san bama nazo bare kizo ki tare ni ina yaran ne banji motsin su ba,ko basa nan ne?".


Ta ɗago kai cikin sauri tace.

"Sannu da zuwa Hubbi sun gama cin abinci sukai bacci nima kai nake jira to ya hanya ko duk gajiyar ce tasa na ganka haka ko yunwa ce?".

Inji Amina.

"Duk abinda kika faɗa akwai a tare dani yanzu inaso kafin ki kawo min abinci ki haɗa min ruwan dumi nayi wanka".

"To Hubby duk abinda kakeso yanzu za'ai maka shi".



Ga ci gaban Tsakanin Rayuwa


Ta karashe Maganar tare da mikewa tsaye ta nuni bayan gida tana kokarin haɗa masa ruwan.

Tunanin yaran nan ne ya dawo masa ji yai hankalinsa Yayi mutuƙar tashi saboda ganin karancin shekarunsa shin ta ina zai sami mafitar da abinda ya ƙudura acikin zuciyarsa ji yai an tsaya akansa ana magana da cewa.

"Dama ni nasan akwai wani abu dake shirin ɓoye min shi yanzu alamu sun fara nunawa tunda ɗazu na jima akanka amma baka sani ba,to bama wannan ba yanzu ka tashi muje na gama haɗama ruwan wankan".


Cewar Amina.


Tashi yayi a sanyeye ba tare da yace uffan ba bakinsa ya gaza cewa komai Toilet ya dosa cikin ƙankanin lokaci ya kammala komai.


Haka ya iske ta afalo ta haɗa masa abinci kala -kala nan ya kwasa.

A can riga kuwa Fatima ne da Sadiya zaune cikin yana yin damuwa.
Inna tace

"Nifa bana san irin wannan shirman naku ai gashi nan kun dawo baku samo mana ko kanzo ba ga kawunku tunda ya fice har yanzu ba'aji duriyarsa ba ko yana raye ko yana mace Allah ne masani mi dai zan tsunduma cikin burni don na samo mana mafita wannan rigar tamu ba'a taimakon mu sai mun fito a dinga zunbe mu wai harɗo ya tafi ya bar mu cikin kunci da wahala".


"Nifa Inna nayi alƙawarin a wannan lokacin zan samar miki da farin ciki amma inaso ki bari na dinga fita ni kaɗai saboda ki gane irin kwazo nah".


Inji Sadiya.

"Bana san rawar kai kinsan mutanen burni basu da kirki kar su sace ki kamar yanda suka sace kawunku harɗo ku dai yi haƙuri wata rana sai labari".

A can gidan Yusuf kuwa yana kwance a falon Amina ta fito daga cikin ɗaki wai ka fasa zuwa rigar ne.

"Cewar Amina.

"Zanje hutawa nake ne Musa ne nake jira ya fini sanin ta kan rigar.









Taku har kullum



*A'ISHA YAHAYA TANKO*

💱💱💱
LAIFIN WAYE
💱💱💱




*Story and Writing By*

*AISHA YAHYA TANKO*✍️




~Page~ 2






Dogon suma Hauwa'u ta sake yi cikin sauri Baba Sa'a ta fara kokarin yayyafa mata ruwa cikin kidimiwa umar wanda tuni ya jima da suma a tsaye ji sukai an turo kofar dakin da karfi wanda gaba gaba yasa suka bi kofar da kallo likitoci suka shigo a gigice jin karar Hauwa'u da sukai sun tsaya a bakin gadonta suna tambayar dalilin da yasa ta haka Baba Sa'a ta nuna Umar da hannun ta.


"Gashi nan shine yake so ya dawo muku da aiki naya tace bata san ganinsa a wannan wajen Amma yaki fita dan Allah ku fitar dashi daga cikin asibitin nan".

Tana gama fadar haka ta maida dubanta ga Hauwa'u wadda ta dan fara bude idonta a hankali tana bin kowa da kallo, likitocin da suka bi Umar da kallon mamaki daya daga cikin su yai masa nuni da hannu akan ya fita daga cikin dakin fita Umar yayi jiki a sanyaye.



Sannu Baba Sa'a ta shiga yiwa Hauwa'u fatana lafiyarki ta dore.

Likitan dake tsaye ya dubi Hauwa'u wadda take kwance akan gado yace.

"Ki rage damuwa karki fama ciwonki kinji, ki sani cewa a yadd kike din nan ba'a so ki kara shiga damuwa".

Yana gama fada ya juyo da kallonsa ga Baba Sa'a inaso ki biyoni office yanzu zan miki tambayoyi.

Ta amsa da toh suka fice daga cikin dakin tabi bayansu.

Acan office din Likita na zaune akan kujerarsa yana yiwa Baba Sa'a tambayoyi.

Baba Sa'a ta dan'nisa kadan' gaskiya laifina na shi wnnn mutumin dana ce ka Kora dazu shine wanda yai sanadiyar faruwar ciwon Hauwa'u dan'mijina ne tun Hauwa'u tana karama ya nuna yana santa, duk wasu abubuwa kala-kala na yara yake kawo mata duk abinda Hauwa'u take so shi zai mata tunda ni amana ce awajena yarinyar Kanwata ce tun da aka kawo ta yaye take hannuna har lokacin da Allah yasa ta kai shekaru 15 nan maza sukai nuna ra'ayinsu game da auren Hauwa'u ni kuma na tsaya tsayin daka akan naga ta amince da Umar ganin irin kulawarsa akanta ba yadda na gama komai na aurenta na shaidawa Mahaifinsa na tsaida ranar auren Umar da Hauwa'u.murna wajen Malam Sule ba'a cewa komai sai san barka ranar na kira Hauwa'u daki nai mata fada sosai akan ta bi mijinta shine aljannarta ta amince naji dadi nasa mata albarka muka kaita dakinta washe gari Umar ya shigo ya iskeni a tsakar gida na lura da fuskarsa ba kamar yand na saba gani ba muka dai gaisa a haka ya nufi wajen Mahaifinsa.

da ya fito ne nake tambayarsa ina Hauwa'u nan yace.
"Tana nan kalau".

"ka gaisheta".

Shine abinda na fada masa

Amsamin yayi a dakile ya fice daga gidan naci gaba da aiwatar da aikina amma zuciyata cike da zullumi a haka na gama gudanar da aikina na wunin ranar.



Aisha Yahya Tanko✍️

*AMAZING WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
®️🪄

_(Burinmu mu Fad'akar mu wa'azantar tare da Nishadantar da Al'Ummah)._

*🗻A•W•A🗻*
*KUNGIYA MAI ABUN MAMAKI🇳🇬*

~Idan Rana ta fito tafin hannu bai iya kareta🌞🌄.~



*NA MARUBUCIYA AISHA YAHYA TANKO✍🏻*



*PAGE* 3



```Rashin comment dinku yana sagar min da giwa, kodai book din baya muku dadi ne```






Na koma dakina na iske Malam Sule yana gabatar da sallah na sami waje na zauna daf da shi na jira ya idar yai addu'a muka shafa a tare yayi Jim kafin yayi magana na dan yi karfin hali nace.

"Malam lafiya kuwa naga Umar ya canja kamar ba shi ba.ko dai akwai matsala ne?".

Malam Sule yayi gyaran murya yace.


"nima na lura da hakan amma nasan baze wuce gajiar biki ba, kinsan yaran yanzu sun san garce da yawa basa san wahala sosai".


hakane malam.

shiru na lokacin kadan'ina share kwallar data cika min kuncina.

Likita ya zare glas din dake fuskarsa yana tsane gumi da hannusa zuciyarsa ta fara raya masa abubuwa da yawa Akan Hauwa' ya dubi Inda Baba Sa'a take tace.

"naji dukkan bayananki amma har yanzu ba'a zo abinda nakeso naji....".

Be karasa maganar ba wayarsa ta shiga ringing hankalinsa ya dawo kan wayarsa hannu yasa ya dauka ya kara a kunnensa ya fara magana.

"eh ina office subhanallhi ganin nan zuwa karku taba shi ku bari na kara so".

mikewa yai tsaye a gigice yana dudduba files da suke gabansa ya dubi Baba Sa'a ki koma wajen yarinyarki zan nemeki zuwa anjima kinji yanzu wani mara lafiya zan duba yana bukatar taimakon gaggawa.



Allah ya bashi lafiya bari na koma wajenta ko zata bukaci wani abu.

suka fito tare da Likita.

Hauwa'u ta isheni tana bacci ta gyara mata kwanciyarta ta zauna a gefan gadon tana dubanta fuskarta cike da tausayawa murda kofar dakin akai ana kokarin shigowa Nurse ce ta shigo sanye cikin uniform hannunta rike da tulun magunguna ta tsaya abakin gadon tana ya nutse fuska


" Haba baiwar Allah dama har yanzu ba'a gyarawa yarinyar nan jikinta ba ko so kike mu zamu gyarata to kiyi kokari ki gyara mata tun kafin ta doyi kina jina koh ga maganinta na kawo idan ta farka ki bata tasha amma ki tabbata sai taci abinci ta koshi".


Tana gama fada ta juya ta fita.


Godiya Baba Sa'a yi tana cewa insha Allah tana tashi zan gyarata bama sai an kara mgn ba.


Hauwa'u ce ta bude idonta a hankali ta dubi Baba Sa'a

"wai daman kina nan".

yawwa w ai gwanda da kika farka inaso na gyara miki jikinki yadda bazan fama miki ciwon ba kinga an fara mgn akan rashin gyaran da ban miki ba.



"Wallahi gaba daya jikina ciwo yake min kamar an min duka".

Shine abinda Hauwa'u ta fada tana yamutsa fuska, taci gaba da cewa.


"Dan Allah ki dena barin bakin kumurcin nan yana zuwa wajen a, na tsane shi zan ka she.....


Hannu Baba Sa'a tasa ta rufe bakinta tana mamakin maganar data fito daga bakin Hauwa'u.

"Haba Hauwa'u ' me yasa irin wadannan kalaman suke fitowa daga bakinki daga yanzu kar na sake jin kinyi maganar kisa wlh baki fini jin haushin abinda Umar yai miki ba ina jin abin a zuciyata tunda laifina ne, amma naga alamar nadama a fuskarsa kamata yayi muyi sama sassauci sannan mu roki Allah ya baki lafiya".

Tana gama fadin hakan ta rike hannun Hauwa' tana kokarin tashinta zaune.


Cikin shashshekar kuka tace.


"shikenan Baba duk abinda kikeso shi za'ai amma fa zuciyata tana shiga damuwa a duk lokacin danai tozali dashi na kanji kamar na shakeshi kowa ma ya huta ki duba kiga tunda muka Asibitin nan babu wanda yazo duba ni daga bangarensa hatta Malam dana daukeshi a matsayin mahaifina shima be zo ba to iri-iren wadannan abubuwan sune suke da muna, ace dan' cikinka yayi barna amma ka kasa cewa komai".

ki dai bar wnnn maganar idan sunzo lafiya zasu baki ko me duk ki ciresu daga ranki ki fuskanci abinda yake gabanki, ki tashi mu shiga bayan gida na wanke miki jikin ki.


Cije lebe Hauwa'u ta kama gadon tana yunkurin mikewa tsaye Baba ta taimaka mata suka shiga bayan gida.










~kuna ina masu sha'awar siyan cup cake, birthday cake kai duk irin cake din da kuke so, zaku iya samu mu ta wannan number~ 👇
08169495093





*Aisha Yahya Tanko*✍️

*TSANANIN RAYUWA*







*NA MARUBCIYA A'ISHA YAHAYA TANKO ❤️🌸🌷🪷*




*PAGE 4*



Haka ta daure zuciyarta ta shige cikin shagon saboda tsananin yunwar da ta addabeta amma ya zatai da kanta tunda ranta tunda sun rasa wadanda zasu taimaka musu, ko da abincin da zasu dinga ci acikin rigar su ko wanne yana ƙyashin yai musu komai duniya ina zaki damu ace mai hali ba ze taimaki marar hali ba,duk tana faɗin haka a ƙasan zuciyarta ji tai ana cewa.

" haba ƴan mata ke kuwa wani irin tunani kike tun dazu na kawo miki abinci amma baki san na ajiye mkki ba, inaso ki sani komai yai zafi maganinsa Allah don shine yake saukar da ciwo a duk lokacin da yaga dama sannan kuma ya kawo maka sauki a cikin lokaci ƙanƙani".

Cewar Matashi.

Hawaye naji suna kwarara daga ƙasan kuncina hannu nasa na share ban wani bata lokaci ba naja kwanan gabana kafin kace maye tuni na share abincin nan na kora da ruwa sannan naji nutsuwata ta fara dawowa jikina nace araina.
_Allah sarki ko su Inna da Fatima sun sami abincin da zasu ci dan ni daga nan zan ƙara nutsawa cikin birin har sai na cimma burina_

"Dan Allah inaso ki sanar dani sunanki, da kuma inda kika fito da kuma dalilin da yasa kika zaɓi barinki gida, nace miki ni har ga Allah zan taimake ki ne dan bana san rayuwarki ta shiga matsalar a yadda kike da ƙarancin shekaru kinji".

Cewar Matashi.

Wani irin ƙarfi naji ajikina da nace. "Ni wallahi na fito ne dan samar mana mafita nida Inna ta da kuma yar'uwata mun gaji da zaman yunwa acikin rigarmu,mun kasa samun wanda zai share mana hawaye tunda Babanmu ya gudu ya bar mu, gashi kuma an sace mana shanunmu balle mu siyar mu biyawa kan mu buƙata shine na yanke shawarar da zan faranta ran Innata".


Shiru Salisu yayi yana tunanin ta hanyar da zai ganar da Sadiya yadda zata koma gida ba tare da wani ya ɓata mata rayuwa ba, duniyar yanzu babu gaskiya a cikinta burin masu kuɗi su ɓata musu rayuwa sannan su taimakeka.


Salisu yace.
" Ni dai atawa shawarar ki koma gida yanzu nayi alƙawarin in sha Allah zan dunga kawo muku abincin da zaku dinga ci sau uku a rana idan kin amince dani ni dai Alkairi nake nufinki dashi ba sharri ba zan rufe shigo ki muje rigar taku muyi magana da Innarta taki kinji".

"To shikenan babu matsala amma dan Allah kar ka sace ni naji ance mutanen burni sata mutane suke yi, dan suyi kuɗi ni bana san kaima ka sace ni".

A ɓangaren su Yusuf kuwa yana zaune akan doguwar kujerar yayin da Amina take shigowa da ƙwaryar nonon,bakinta yaƙi rufuwa dan murna ta zauna kusa dashi tana cewa.
'Habibi kaji garɗn Nono nan kuwa ba alamar tsami ko ɗaya, kasha kaji sai kace madara aka zuba a cikinsa".

Yayi murmushi yace.
"Ki kwantar da hankalinki ko yanzu kika shanye nayi alƙawarin zan koma na siyo miki tunda kina so".

Cewar Yusuf.

Wata irin ƙara tasa kamar zata tashi sama.

" Da gaske kake Habibi na ai kuwa na gode sosai Allah ya bar kauna bari na dama ma fura kasha ka ƙoshi".

tashi tayi cikin sauri ta nufi kichen.

A bangaren gidan Alhaji me rumbun Allah ya isa kuwa yana zaune akan wata kujerarsa ya sa bakin glas yana karanta jarida yana lura da takun mutanen da suke wucewa da waɗanda suke neman taimakon sa amma yayi halin ko un kula dasu.

A kan hanyar su Salisu da Sadiya kuwa tuni ya fara nuna gajiawarsa ta nisan tafiyar da suke ga kaya a hannunsa ita ko Sadiya ko ajikinta tunda ta saba tafiyar bata jin komai a haka suka ƙarasa cikin rigar,shigarsu ke da wuya suka fara karo da mutanen rigar kowa yana binsu da kallon mamaki masu zunde nayi masu dariya nayi suna Isa ne nan suka iske Inna tana shara duk ta haɗa gumi, Fatima kuma tana kukan yunwa ta dafe cikinta Inna ce ta saki tsintsiyar dake hannunta tana bin su da kallo.

Taku har kullum.


*A'isha Yahaya Tanko.*

*LAIFIN WAYE*



*AMAZING WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
®️🪄

_(Burinmu mu Fad'akar mu wa'azantar tare da Nishadantar da Al'Ummah)._

*🗻A•W•A🗻*
*KUNGIYA MAI ABUN MAMAKI🇳🇬*

~Idan Rana ta fito tafin hannu bai iya kareta🌞🌄.~



*NA MARUBUCIYA AISHA YAHYA TANKO ✍🏻*



*PAGE* 5






*_______📖* Haka na k'araso cikin d'akin mu na iske Hauwa'u ta gaji da jirana har bacci ya d'auketa na sami waje na zauna a haka nima baccin yai awon gaba dani.




washe gari ne d'aya Likitan ta shigo d'akin mu, ta tadda Hauwa'u tana zaune a bakin gado taji dadin haka rike hannunta tai tana cewa Allah mun gode, d'iyata ta sami lafiya saura kiris muyi sallama.


ji sukai Hauwa'u tasa dariya wadda sautinta ya mamaye cikin d'akin gaba d'aya suka bita da kallo.


Baba Sa'a taja tsaki tace "sakar kawai ai daman burinki kenan kina damuna da rigimar sai mun koma gida naga ajiyar da kikai duk kin cika mana kunne".

Lkita ta dafa kafadarta Hauwa' ke yanzu idan kin koma gida ya zakiyi da ciwon naki wasa nake miki amma dai nasan nan da wata biyar ko shida zaki warware sosai daga nan ne zamu iya cewa ku koma gida".

Nan da nan Hauwa'u ta hade rai idanuwanta suka kawo kwalla.


bari na koma na duba naga ko ruwan dana sawa yaron nan ya kare tai musu sallama ta fice daga dakin.



Baba Sa'a ta kalli Hauwa'u ai ke koh bakya jin magana naga uwar da zaki ci idan kin koma gdn, kin dai ji abinda tace idan zaki sawa zuciyar ki hakuri kisa ba ranar sallama yanzu aka fara zama ko kukan jini zakiyi kiyi na dena rarrashinki.



"Wallahi Baba kun cuceni keda Umar kune sillar rugujewar rayuwata tunda kema kin bada gudun mawa Babbage".



Nan hankalin Baba Sa'a yai mutukar tashi da jin kalaman Hauwa'u

"Au sharri zaki yi min to na dauka, amma dan Allah ki bar maganar nan tun kafin wani ya shigo yaji abinda kike Fad'akar".

Ji sukai an turo kofar dakin tare da yin sallama Malam ne ya shigo dakin hannunsa rike da leda baka ya ajiye a kasa yana duban Hauwa'u wadda ta kura masa ido kamar bata taba ganinshi ba.



"sannu yarinyar kirki ya jikin naki".


da k'yar ta amsa masa.


"yau dai na sameki ido biyu dan Allah ki yafewa Umar kinji kuskure dai anyi shi".



" Allah ne ya kaddara hakan" .


Inji Baba Sa'a.


Nurse ce ta shigo cikin d'akin tana ya tsune fuska kamar kullum hankalinta ya kai wajen Hauwa'u ta saki fuska ganinta tsaf akan gado tace.

"ko kefa yau haka nakeso naganki kullum dama ke me kyauce kamar ke kikai kaki amma ake barinki da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login