Showing 1 words to 3000 words out of 9145 words

Chapter 1 - DU'A HAUSA NOVEL

26 Aug 2025

726

👄👄👄👄👄👄👄👄
*_DU'A_*
💋💋💋💋💋💋💋💋
By maman noorul _hudah_

_Jan kunnin_

Ban yarda wani ko wata ya canza min labari ba ta ko wace tsiga ba,a kiyaye

~Tsokaci~
Kagaggen labari ne banyi shi Dan cin zarafin kowa ba in yayi dadai da rayuwarka/ki akasi aka samu


1️⃣✅2️⃣

Shekarun goma sha Tara da suka wuce


Gidan alhaji Abbas Mairiga

Gidane Mai girman gaske Wanda Kalli daya zakawa gidan kasan mallallakin gidan me kudi ne da rufan asiri .

Da misalim 2:13am gidan tayi tsit kasancewar dare ne sai hasken wuyar daya kawata gidan sai ta Bada ma'ana me kyau


Wata mata ce ta fito bazata wuce shekaru talatin da biyu ba sai waige take tana juye juye Bata son wani ya ganta cikin Riga da wando sleeping dress da bedroom slippers

Wajen garden ta tafi da yike Nan ne kadai ba ayiwa interlock ba rike take da wani karamin kwando tana zuwa ta shige ciki shukar inda ko Maigadi ba zai hangota ba,saida ta fara fito da wani layoyi guda uku ta Kai bakinta cikin muryar da baza a jita ba ta fara Kiran sunan kishiyarta

Saratu!
Saratu !!
Saratu !!!
Ki Farka

_______________

Hajiya saratu tana kwance taji kamar ana kiranta ta Bude Ido

Wani abu taji a kanta da yasa ta mikewa a razane kanta na wani irin tsarawa ta zauna ta rike Kai jikinta na rawa

Murmushi hajiya hauwa tayi ta Kuma Kai lauyar bakinta tace"so Nike ki bar gari bana son wani ko wata naki ya Kara Jin labarinki

Tana gama fadin haka ta binne layar ta koma gefe ta fara tone wani rami bayan ta gama ta dauko layar da ya rage guda biyu ta dau d'aya ta Kai Baki tana cewa"Fahad daga Rana irin ta yau Ina son rayuwarka ta lalace ka zama mara amfani kayi ta dauko magana kaine sata,ta'adanci,shaye shaye,ya taso mara amfani a aluma"tana fadin hakan ta binne layar

D'ayan da ya rage ta Kai Baki Allah yasan ta tsani yar Nan Du'a wallahi duk duniya ta tsani Du'a tunda uwarta ta haihota ta tsaneta

Tace"Ina son ta taso abin kyama da bakin ciki,Ina son Du'a ta taso tana fitsari a jiki Maza na gudunta Ina son ta kasa rike fitsari tayi ta Yinsa a jiki samari su kyamaceta

A zuciyata nace



Maman nur

👄👄👄👄👄👄👄👄
*_DU'A_*
💋💋💋💋💋💋💋💋
By maman noorul _hudah_


3️⃣✅4️⃣

This is awkward wavan wani irin bakar mugunta to ne ya' mace ayi mata wanan bakar asiri

Cigaba tayi da haka ramin tace"Ina so da ita da karatu suyi hanun Riga Ina son ta girma a jahila alhaji ya tsane ta ya Kuma muzguna mata na tsamesu

Tana gamawa shima ta binne

Ta Bude wanan basket din ta dau kurciyar dake ciki ta kira sunan

Saratu!
Saratu!!
Saratu !!!

Ki tashi kiyi tafiyarki kamar inda zan saki wanan kurciya kema haka Nike son ki bar garin Nan

Tana fadin haka ta sakesa yayi sama ta koma tana tafiya cikin sad'an tana Bude kofar zat shiga ciki sai ga Mami watoh hajiya saratu ta budo Kofa sukayi karo

Tunkude ta Mami tayi har ta Fadi Amma ko ta kanta Mami Bata bi ba ta tafi ko waigowa Batayi ba

Abin mamaki Maigadi na cikin d'akinsa Amma tana tab'a gate ya Bude ta bar gidan

Mummy ta mike dukda ta ji zafi Amma be hanata yin murmushi ba ta shige ciki zuwa d'akinta ta kwanta


Alhaji (Abba )

Yana bacci ya ji kukan Du'a ya Bude Ido kafin ya Mike yana mamaki agogo ya kalla ya gan 4:15 ya saka takalmi yayi d'akin Mami

Abin mamaki ya tarar da Fahad d'an shekara bakwai kwance a falonta,ya shiga cikin bedroom din ya gan Du'a na kuka da mamaki yace"hajiya Kina Ina kika bar yariya na kuka "

Shiru yaji ya sake kiranta kusan so biyar ya leka bayi Bata ciki

Yana kokarin daukar Du'a har ya mika mata hanun Du'a yar shekara uku ta fara Mika masa hanun ya dauketa

Wani irin muguwar zarni yaji ba shiri ya





Maman nur

👄👄👄👄👄👄👄👄
*_DU'A_*
💋💋💋💋💋💋💋💋
By maman noorul _hudah_


🅿️5️⃣✅6️⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim

Ya sake ta,ta Fadi har ta bugi kanta da gefen gado

Wani irin tsanar yariyar yaji ya taso masa da basan kansa ba yayi tsaki ya fita


Duk wanan abin da ya faru a idon hajiya ya faru Dan tana labe tana kallonsu Yana fita ta shigo d'akin tana murmushi tace"aiki yayi kyau daga yau da Kai da tsinanniyar yariyar Nan Mai tsufar mayu so Nike ku zama annabi da kafari


Komawa daki tayi ko kula Du'a Batayi ba

Gari na wayewa ta kira baaba watoh me aikin gidansu

Jiki na rawa baaba lami ta fito daga kicin Dan hajiya ba karamin tsoro take Bata ba muguwar ce number d'aya ga mugunta yanzu sai ta koreta a aiki,ita Kuma tana da marayun Ya'ya

Ba tare da ta kalleta ba idanunta na waya tana charting da kawarta saude

Tace"lami kina da mijine?"

Girgiza Kai babban tayi tace"ah'ah hajiya Allah ya masa rasuwa shekaru goma da suka wuce

. Tace"toh yayanki nawa?"


Ta girgiza Kai tace ban tab'a haihuwa ba"

Sai a lokacin ta d'aga Kai ta kalleta irin kallo na wulakanci sanan ta Kau da Kai tace"toh zaki dawo ki zauna Nan a wancan dakin na boysq"

Baaba tace"eh hajiya na ko gode*


Hajiya tace"toh gobe ki dawo Nan rokon Dua zai dawo hanunki

Da mamaki take kallonta saidai Bata ce komai ba

Hajiya tace tashi ki tafi

Mikewa tayi tana godiya itako hajiya ta cigaba da chart dinta cikin isa da nuna takama ita a dole matar me gidan

Ko da Abba ya fito be tambayi yayansa ba ya d'ibeta cikin so da kaunar dan yau ji yake kamar zai hadiyeta Dan so

Mikewa tayi cikin wani irin salo tana wani yauki taje tace"ka fito kenan

Jikinsa na rawa yace"eh hajiya na fito na fito

Dining suka je tana masa shagwab'a yace Ina yaran ?"

Sai da tayi faru da Ido tace"suna sama "

___________

Haka dai rokon Du'a ya koma hanun baaba lami Mai aiki da alamu alhaji ya mance ya tab'a auren wata mace saratu cin abinci suke suna Hira

Bayan kwana biyu da dawowar
Baaba ladi ta shiga damuwa Dan kuwa tun tana daukar lamarin fitsarin Dua yaranta ce har ta sallama domin har ta Kai shekaru goma fitsari take a jiki,ta so sata Boko Amma hajiya ta Hana tace Boko na yayanta ne haka ta taso cikin jahilci ba Boko ba islaniya abinda zai baka haushi da takaishi shine inda kwata kwata Bata iya rike fitsar da yike baaba ladin itama ba wani addini ne da ita ba sai abin yayi worst

Har kauye baaba ladi ta aita a Niko mata magani but yi ake madadin a samu sauki sai abin na worst

Dan ba minti guda Batayi fitsari a jiki ba ga kyau saidai da ka doso ta zaka ji wani mahaukacin zarni

Shiko Fahad duk inda ka b'oye abinka sai ya nima ya dauke b'arawo ne ba gaske

Yanzu shekarunsa ashirin da biyar itakuma ashirin da d'aya



_________

Cigaban labari




Maman nur

👄👄👄👄👄👄👄👄
*_DU'A_*
💋💋💋💋💋💋💋💋
By maman noorul _hudah_


7️⃣✅8️⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim

Rayuwa ce suke Yinsa ba dadi in ba ance maka Yayan me gidan bane saima ka Musa

Baaba girma ya kamata tsufa ya zo ga ciwon kafa ya kamata

Saidai duk wanan abu Dua dai fara ce sol ga Suma ga Kuma kyau hakan yasa hajiya Bata da zargin da takeyi kamar kiranta aljana haushinta take ji mussaman in ta duba inda Dua tafi Yayanta kyau ciki harda yar gaban goshinta ihsan

Ihsan kanta ta taso ne da tsanar Dua ta tsaneta kamar inda ta tsani mutuwarta

Yau ta kama Sunday ihsan ba makaranta ta na kwance a had'aden dakin ta da ya sha kayan more rayuwa

Kamar an tsikarata ta mike tana murmushi cikin wani Riga da wando ta fito tayi boys q

Zarni ne ya fara mata sallama ta toshe hanci tana shiga ta tarad da Dua tsaye ta gama nade kayan shimfud'arta zata Kai waje

Tunda ta shigo baaba taji gabanta ya Fadi da sauri tace"Ina yini hajiya

Ihsan tayi mata wani kallo tace"duk wari kuke ke


Jiki na rawa Dua ta uya Dan tana balain tsoronta ba kadan ba

Tace"zo Nan "

Jiki na b'ari fitsarin da Bata iya rikewa ne ya kufce mata hakan yasa ihsan ta wanka mata Mari tace"so nawa zan fad'a miki ki daina wanan shegen fitsarin naki a gabana

Rudu da firgici Hadi da tsoro yasa ta fara mammatse kafa duk inda taso rikewa saida ta saki fitsari a jiki

Wani irin naushi ihsan ta Kai Mata tace"Kai Ina na magana Dan iskanci kika Kuma yin fitsarin toh yau sai na baki mamaki Mai kama da mayu

Me Du'a zatayi in Banda kuka jikinta har b'ari yakeyi ihsan ta daka mata tsawa tace"ke zaki natsu ko sai na ci ubanki"

Da sauri ta Kam bakinta jikinta na b'ari Wanda a take sai da tayi fitsari yafi so biyar

Ihsan cike da kyama ta yatmusa fuska tace"aza kayan shimfid'a naki

Kallonta tayi dan fitsari har d'iga yake,jikin baaba yayi sanyi Dan ta lura da wulakanci ihsan ta tashi yau

Wani naushi ta Kai Mata da yasa Du'a sakin ihu tana Dan Allah kiyi hakuri

Tace"toh kwashe kayan shimfid'ar ki aza a kanki"tayi maganar cikin zare ido

Haka ta aza kayan shimfid'ar Leda ce da taburma sai wata yagaggiyar zanin gado

Tana azasu a Kai ihsan ta masa tace"yi gaba Dan ubanki


Gaban tayi ihsan na binta a baya baaba Bata iya tace komai ba saidai tausayin Du'a take Dan sai da tayi kwalla tasan wulakanta ta ihsan zatayi

Suna kawai gate din gidan ta tsaya tana kallon ihsan


Ihsan ta zare mata Ido tace"my friend move useless fellow dirty thing

Cikin marairaicewa da tashin hankali tace"Ina zamu je

Ihsan ta Kalli gefen ta ta Kuma juyowa ta Kalli gefen ta ta hango gorar masu gadi jingina da building dinsu take ta dauko

Tace"zaki fita ko sai na ci ubanki "

duk wanan abin da suke hajiya na daga sama tana kallonsu tana me Jin dadin abinda ihssan xatawa du'a dan rantsuwa tayi in har tana raye du'a sai tayi nauyi a kansa bazatayi aure ba

haka du'a naji na gani za a wulakantata ta fita da kayan fitssrin waje

tana fitowa ihssan ta



mamam nur

👄👄👄👄👄👄👄👄
*_DU'A_*
💋💋💋💋💋💋💋💋
By maman noorul _hudah_

This book is 500,vip 1k via 2378022567
Aisha Mohammed
Zeinith bnk


9️⃣✅1️⃣0️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Ta fara dukanta da saboda tana amalala Mai fitsarin kwance ta tsula ta Kuma tsulawa

Haka tayi tasa Du'a na tafiya tana binta a baya hakan ya ja attention din mutane da dama

Wasu suna mamaki,wasu Kuma suna ganin babba da ita ai iskancine a ce tana fitsarin kwance gwamma da akayi mata haka,wasu Kuma suna tausayinta

Wani matashin saurayine zaune a gate din wani gida Mai kyau

Ihsan na ganinsa ta d'an fara daidaita kanta tana sawa fuskarta murmushi shiko ya b'ata Rai saidai wani abin hankalinsa na kan Du'a

One thing with Du'a she attract people a kallo d'aya Dan kyaunta irin me hayaniya me Jan hankali mutane,Yana mamaki ne Dan be tab'a ganinta ba a layin

Jin ihsan da haushin kallon da yake mata yasa ta daka mata tsawa tace"muje katuwar banza me fitsarin kwance "

Sai a lokacin ya sake kallonta da kyau Aiko daidai fitsarin ya zo mata

Ya zare ido da mamaki besan Sanda ya maimaita fitsari ba with surprise dukda bawai ya lura da fitsarin bane kamar dai yayi magana kawai sai ya dauke Kai ya cigaba da latse waya

Dukda ba wata fita Du'a take VA zaku sha mamaki in na ce muku all this year's be fi fita biyar tayi ba which yanzu na tayi shekara uku Bata fita ba sai yau
Dan wanan Yana cikin sharrudan da boka ya sawa hajiya,ta jawa Mai gadi baaba lami kunnin akan hakan

Ihsan kallonta tayi tace kiyi ta tafiya sai kin Kai bakin hanya can junction

Kallonta tayi cike da tsoro da Kuma rashin sani
Cikin wani murya tace"Ina ne jakshan

Ihsan ta mata wani kallo tace"jahila banza tafi can babban titi

Cikin sanyi jiki jikinta na kyarma tace"toh "

Ta cigaba da tafiya

Ihsaan ta fara gyara fuskarta rigar bacci ne jikinta Riga da wando jikinta ta d'an kamata sai hula tayi kyau ba laifi

Ta dubi direction dinshi tayi murmushi ta Dade tana sonsa har sawa tayi aka binciko mata wajen shi

Ta karasa inda yake zaune cikin yanga da wani irin yauki da nuna ita din wata ce tace"Ina kwana"

Be dago ba ya amsa da lafiya a takaice
Ta saki murmushi tare da ajiyar zuciya kafin ta Mika masa hannun

Tace"sunana ihsan ga gidan mu Nan"

Still be d'ago ba Kuma be ce komai ba ta ji ba dadi ta Maida hanunta tace"wulakanci be da kyau ga musulmi nasan ka sani"

Sai yanzu ya d'ago ba yabo ba fallasa yace"sanin addinin ne yasa bazan yi musabaha da mace ba nasan tunda kin San addini ya Hana wulakanci ya kamata ki San wanan

Taji kunya ainun Amma ta dake ta tare da wayancewa tana murmushi ta zauna kusa dashi da dariya fuskarta

Tace"my bad sorry ai nayi kuskuren ban fahimci Kai uztaz babe

Ya Maida fuskarsa kan waya
Ta cigaba da surutu tace"Amma bakuyi shekara da zuwa anguwan Nan ba da nasan ba ku bane ciki,Siya kukayi ne?"

Ya girgiza Kai yace"satowa mukayi "

Tayi yar dariya me cike da ka Raina min hankali tace"please let be friends kana birgeni "

Ya jinjina Kai yace



Maman nur

👄👄👄👄👄👄👄👄
*_DU'A_*
💋💋💋💋💋💋💋💋
By maman noorul _hudah_


1️⃣1️⃣💋1️⃣2️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Yace"are we enemy now"

Cikin turancinta Mai kyau tace"not really I mean I want us to he close *

Yace"no problem "

Cike da Jin dadi tace"toh miye sunanka?"

Yayi murmushi da ya kusan suman da ita yace"mahmud "

Tace"nice name I will just be calling you handsome "

Yayi murmushi yace"you are pretty too "
Ta dafa kirjinta cike da Jin dadi tace"wayyo dadi zan mutu ni ihsan yace iam pretty dadi kasheni

Yace"ke miye haka tace"bari in yi murna please "

Sai ta bashi dariya

Da yike Du'a shashasha ce maimaikon ta nimi wuri ta b'oye sai taci gaba da tafiya abinda zai Baku haushi shine inda tayi ta wakar amalala wa kanta saidai Kuma abinda sai Baku tausayi Dua Bata San how life is ba Bata San inda zata tsallake titi ba Bata San rayuwa ba tafiya kawai take

Tuki yake Yana sauri sashi kotu Dan ya makara Sabar tashin sauri da gudu yake tuki


Jiiiiiiii kake ya kusan kwasheta da mota thank God ya tsaya itako ta firgita garin guduwa kafarta daya ya shige karafin culvert ta saki ihuuuu me razanarwa

Hankalinsa ya tashi ya fito a mota ya karasa Dan shi mutum ne Mai tausayi da jinkaji

Yace"sorry meyasa Baki duban titi


Kallonsa tayi dukda tana cikin azaba,suna Ido biyu dashi ta saki wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login