Showing 222001 words to 225000 words out of 296092 words

Chapter 75 - GABA DA GABANTA COMPLETE HAUSA NOVEL

21 Jul 2025

9539

bata dawo ba.
Daddy ya shirya zai ɗan fita, Amina na falo, tana ɗan cin abinci, hakan yayi daidai da shigowar Fadila falon daga makaranta.
Tana ganin Amina a zaune a falo, ta kalli Amina, ta ja wani uban tsaki, da ba tayi ma tsammanin ganin Aminan ba, dan basu san da daowarsu yau ba.

"Ke Fadila" taji Muryar Daddy ya kira sunanta.

Tsayawa tayi cak ta waiwayo, Daddy ya kalleta ya ce "Wa kike yiwa tsaki?"

Fadila tayi shiru ba tace komai ba.

"Da ke nake wa kike yiwa tsaki?" Yayi maganar a kausashe.

Ta ɗan razana ta ce "Daddy ba kowa"

"Ai naga abin da kika yi, me tayi miki? Kawai kin shigo kin tarar da ita a zaune, ke baki mata sannu da zuwa ba kawai kin yi mata tsaki. Fadila ki kiyayeni fa, idan kika wulaƙanta Amina tamkar ni kika wulaƙanta, tunda ni na aureta na ajiyeta, ba ita ta ajiye kanta ba, dan haka ki kiyayeni, bata haƙuri" wani abu ne ya soki ƙirjin Fadila, wannan 'yar yarinyar ƙanwar ƙanwar bayanta za a kalla ace ta bata haƙuri?.

"Ba magana nake miki ba?"

"Kiyi haƙuri" Fadila ta faɗa a taƙaice.

"Allah ya ƙara nuna mini kin mata tsaki ko makamancin haka, idan ba zaki mutunta ba to ban lamunci ki shiga sabgarta ba, balle ki ci mata mutunci, na sani mahaifiyarki ke zigaki, amma idan na tattara na aurar da ke, na yiwa tufkar hanci, da sun kawo kuɗin Aure ni ba zan saka lokaci mai tsawo ba, na gaji da halinku"

Kasa ɗaga ƙafafuwanta Fadila tayi, jin yayi batun aurar da ita, ga kuma furucinsa na ƙarshe, wai ya gaji da halinsu, duk tarin soyayya da tattali na Daddy a garesu, yau a saboda yayi aure yake musu wannan cin kashin.
Da ƙyar ta ja ƙafarta, ta nufi sashinta tuni hawaye ya wanke mata fuska.

Amina kuwa cewa tayi, Baby a dawo lafiya.

"Yauwa Meenal, Allah ya sa"

Bayan fitar Daddy, ita ma sallar tayi, ta dawo ta ɗan kunna turaren wuta a falon.

Kamar daga sama sai ga Hajiya Zainab, kamar an korota, Amina ta ɗago kai ta kalli Hajiya Zainab, ta ɗauke kanta ta cigaba da ƙoƙarin kunna Tv.

"Baƙar munafuka, na kusa kawo ƙarshenki" Mamaki ne ya kama Amin, ba ko sallama kawai ta fara maganar zata kawo ƙarshenta"

"Ni bani da lokacinki, an barwa karnuka faɗa" Amina tayi maganar a hankali, tana cigaba da aikinta.

"Ni kike cewa karya?"

Ta miƙa hannu zata janyo Amina, Amina tayi maza ta kauce ta ce "Karki kuskura ki kai hannunki jikina, ba ruwanki da ni, ba fa tsoronki nake ji ba da nake yi miki shiru, wallahi kika dakeni sai na rama"

"Bari na dakekin, naga uban abin da zaki iya, 'yar matsiyata wadda basu gaji arziƙi ba"

Amina ta ce "Daɗinta dai mai faskare bai isa ya nunawa maigadi arziƙi ba, idan har maigadi matsiyaci ne ban san me za a kira mai faskare ba"

Kan Amina ta kuma yi a fusace, zata daketa Amina ta kuma sake ja da baya, sai surfa uwar ashariya take kamar bamagujiya.
Fadila ce ta fito, bata san Mummy ta dawo ba, sai ganinta tayi a falo tana zage zage tayi kan Amina.

Da sauri ta ƙarasa in da Mummy take ta riƙeta, tana faɗin "Mummy dan Allah ki bari"

"Ƙyaleni, ki rabu da ni in ci ubanta, ni zata kalla ta zagi ubana?"

"A'a fa, ni ban zageki ba, ba faskaren ne sana'ar babanki ba?"

Cikin tsawa Fadila ta ce "Ke Amina, karki kuskura ki zagar mini uwa, ki shiga hankalinki"

Amina ta ce "Babarki zaki gayawa ta iya kanta, kar ta kuma zagina, sannan ke kuma karki sake ɗaga mini murya"

Hajiya Zainab ta sake ƙuluwa, tana miƙa hannu zata daki Amina.

"Kai! Meye haka Zainab a gidana? Me kike yi haka?"

Waiwayowa tayi ta kalli in da Daddy ya ke ta ce "Sannu shugaban munafukai, dole kace haka mana, ka ɗauki yarinya kaje ka shafe kusan wata guda, ko ta kanmu baka bi, wallahi idan baka ji tsoron Allah ba sai ka wulaƙanta".

"A gaban 'yata kike ce mini munafuki ko? Yanzu abin da kike koya mata ita ma taje tayi nata gidan mijin kenan? Ke idan bance kiji tsoron Allah ni kya gaya mini haka? Kin haɗu ke da 'yarki zaku daki 'yar mutane saboda kawai ina aurenta, shikenan na san matakin da zan ɗauka"
Ya ture Hajiya Zainab ya janyo Amina, ya ce "Ina fatan ba abin da suka yi miki?"

Amina ta ɗaga masa kai alamar eh, ya janyeta suka bar falon.

Hajiya Zainab ta nemi wuri ta zauna, ta dafe kanta, gaba ɗaya tayi mamakin yadda gaba daya Asirin da take bai yi aiki ba.

A ɗaki kuwa Daddy, rarrashin Amina yake yi "Meenal kinga dalilin da ya sanya nace miki na raba muku gida kenan, ban san me Yasa Zainab ta kasa haƙuri ta karɓi ƙaddara ba"

"Daddy, bana son ka ware mini gida, ka gaza yi mini adalci, yanzu na san da anyi wa Fadila aure maybe a samu sassauci a wasu abubuwan"

Ya ce "Haka ne, zan san abin yi. Gobe in Allah ya kaimu kuma zan je gidan sirikan Khalil ni da Alhaji Iliyas, mubi shawararki ya ganta idan tayi masa"

Amina ta ce "Allah ya daidaita su"

Ya amsa da Amin.

Daddare duk da yana cikin zullumin tunani, a kan karɓar da Hajiya Zainab zata yi masa, haka ya tunkari sashenta.
Sai dai sam bata kula shi ba, balle ta saurareshi, yana zaune a falonta yana duba wayarsa, ta shige bedroom ɗinta, ta saka key ta bar shi ya kwana a falo.

Tun da suka dawo Hajiya Zainab ta saka su a gaba, da tashin hankali da rashin mutunci. Da Sassafe ko Amina bai yiwa sallama ba, ya shirya ya bar gidan.

Ɗaya gidan nasa yaje ya samu ya ɗan huta.
Shi da Alhaji Ilyasu suka je gidan su Hafsa, domin magana a kan shirin bikin su Khalil, suka je a kan su faɗi zaɓin da suke na furnitures, Maman Hafsa ta ce ba su da wani zaɓi, komai aka yi musu sun gode.

Kasancewar da biyu suka je, Alhaji Ilyasu yaga maman Hafsa tayi masa, gata nutsatsiya ba zaka ce ma ta haifi Hafsa ba.

Alhaji Ahmad ya ce wa Maman Hafsa karta damu kanta a kan shirin bikin nan, zasu ɗauke komai za ayi, karta damu.

Mama tayi ta musu godiya, tare da yi musu Adduoi su da magabatansu.

A hanya Alhaji Ilyas, ya dinga yaba Maman Hafsa, yana cewa Daddy shi dai tayi masa yana sonta.

Daddy ya ce masa "To ni dai tunda na kaika ka ganta, sai ka yiwa kanka sauran aikin" Alhaji Ilyas yayi masa godiya, sannan Daddy ya tafi gida.

Dama Daddy ko karyawa bai yi ba, ko zuwa gidan baya son yi, dan ya fara deciding ya koma Lagos, ya huta da tijarar Zainab.

Kasancewar a wurinta yake, ba shi da wani zaɓi da ya wuce ya fara zuwa wurin nata, idan ta ga dama ta bashi abinci, idan kuma ta hana shi, ya je ya ci a wurin Amina.

A falonta ya tarar da Khalil a zaune a gaban Hajiya Zainab, tana ta zuba masa faɗa ko haɗiyar yawu bata yi.

Alhaji Ahmad ya kalli Khalil ya ce "Kai meya dawo da kai?"

Khalil da idanunsa suka yi ja, ya ɗaga kai ya kalli Daddy ya ce "Mummy ce ta ce tana son ganina".

"Tashi ka je" ya kalli Hajiya Zainab da ta tsare shi da ido.

Daddy ya ce "Ka tashi ina yi maka magana"

Khalil ya tashi, yana yi yana kallon Hajiya Zainab ya fice daga falon.

Hajiya Zainab ta ce "Wallahi duk masifarka, ɗa dai nawa ne, kuma baka isa ka aura masa yarinyar matsiyata ba wadda bana so ba"

Alhaji Ahmad ya gazgata maganar Amina, na ya yiwa iyalinsa illa da ya bar ragamar gidansa a hajiya Zainab, bai taɓa tunanin fuskantar irin wannan zazzafar ƙiyayya daga gareta ba.

A haka ya lallaɓa yai kwanakinsa biyu a ɗakinta, sai dai a falo yake kwana, dan kulle bedroom ɗin ta take ta bar shi a falo.

Komawarsa wurin Amina ne, ya samu sauƙi dan tana ɗaukar lokaci da shi, tana rarrashinsa tana tattalinsa da kwantar masa da hankali.

Dama can Hajiya Zainab ba tambayarsa take ba, idan zata fita amma yanzu abin nata ya ƙazanta sai ta wuni bata gida, ba tare da ya san inda ta tafi ba.
Ta gama wuninta bata gida, ta dawo suna falon sashinta ita da Fadila suna tattaunawa.

Daddy ya shiga da sallama, hannunsa riƙe da leda, Fadila ce kawai ta amsa sallamar a ciki.

Ya ƙarasa gaban Hajiya Zainab, ya ajiye mata ya saka hannu a aljihunsa, ya ɗauko kuɗi bandir ɗaya ya ce "Na rage lokacin bikin Khalil, ga invitation ne mun gama komai, nan da sati biyu ne bikin, idan da wani shirye shirye da zakiyi ne shikenan kya sanar da ni. Nayi magana da iyayen wancan yaron, sun zo ɗazu ga kuɗin auren 'yarki nan, dubu ɗari na tsayar da Magana wata biyu kawai na saka!!!

AYSHERCOOL
08081012143LITTAFIN NAN NA KUƊI NE, KU TUNTUƁENI TA LAMBAR WAYATA KUYI PAYMENT.



69

Gaban Fadila ne yayi wata irin mummunar faɗuwa jin ance wai an karɓi kuɗin aurenta, ita fa gaba ɗaya wannan Salim ɗin bai yi mata ba, bata son shi, kuma dan cin mutunci da ƙasƙanci, wai dubu ɗari aka kawo kuɗin aurenta.
Wani irin gumi ne ya shigo tsatstsafo mata, ji take ina ma mafarki take yi, wannan wane irin abu ne haka, dama da gaske Daddy yake yi, da ya ce zai aurar da ita ya huta, wato ya gaji da ganinta kenan ya daina sonta, saboda yayi aure?.

Hajiya Zainab ta miƙe tsaye, ta watsawa Alhaji Ahmad invitations ɗin a jikinsa "Ka kwashi tsiyarka Ahmad, kaje can dama kai ka nema masa auren, kaje ku ƙarata, ba da yawuna ba wallahi"

A sanyaye Fadila ta ce "Mummy dan Allah ki bari, Daddy ne fa"

"Dalla can rabu da ni, idan ke ubanki ne ni ubana ne? Da ni kake zancen mu zuba mu gani, shege ka fasa tsakanin ni da kai"

Girgiza kai kawai yayi, ya fito daga sashinta, ta biyo shi tana cigaba da surfa masa bala'i, Amina kuwa kulolin Abinci ne a hannunta da zata kai dining.
Kawai taga Daddy ya fito, Hajiya Zainab ta biyo shi tana watsa masa sauran invitations ɗin.

Idanunsa sun yi jawur, tamkar ya zubda hawaye saboda baƙinciki, a gaban 'yarsa take masa wannan tijarar.

Da taga watsa masa invitations ɗin bai isheta ba, ta shiga jan rigarsa tana cigaba da gaya masa duk maganar da ta ga dama.

Zare babbar rigar yayi, ya bar mata a hannunta yayi gaba, aikuwa ta kuma cukuikuye rigar ta jefe shi da ita, dafe kansa yayi da yaji yayi masa nauyi yayi waje.
Ajiye kulolin hannunta Amina tayi, tabi bayansa tana kuka.
Tabbas kowane rai akwai irin jarrabwarsa, amma yana daga cikin babbar jarabtar da Allah zai maka, ya haɗaka da abokin zama wanda bana gari ba.

"Daddy, Daddy" Amina ta bishi tana kiran sunansa, ta ƙarasa da sauri in da yake, tana zubar da hawaye ta ce "Daddy dan Allah kayi haƙuri"

Murmushin ƙarfin hali yayi ya ce "Me kika yi mini kike bani haƙuri"

"Daddy abubuwan da suke faruwa a gidan nan basa yi mini daɗi, zuciyata bata jin daɗin abin da ake maka, Daddy ko ka haƙura da ni, idan har hakan zai dawo muku da farinciki a cikin gidan nan"

Ajiyar zuciya yayi ya ce "A da ɗin ma ba a cikin farin ciki nake ba, zuwanki ne ya samar mini da shi, ina ga Albarkacin biyayyar da na yiwa mahaifiyata na aureta ne ya sanya, ya kawo mini ke cikin rayuwata, komai zai faru ba zan rabu da ke ba, sai dai mutuwa ta rabamu, ina sonki sosai kuma ni ba abin da kika yi mini, muna tare in sha Allah"

"To kazo mu koma cikin gidan, kar ka fita a haka dan Allah"

"Bakomai ki bari, zanje na huta ne"

Amina ta ce "Ni dai ban yadda ba, kazo mu koma" tayi maganar cikin marairaicewa.

Amina ta ja hannunsa suka koma, sashinta tayi masa wurin zama a kan kujerun falonta, ta ɗebo ruwa ta miƙa masa, ya karɓa ya sha ya ɗan lumshe idanunsa zuciyarsa na cigaba da jin zafin abin da matarsa ke masa.

Cikin sanyin murya ta ce "Babyna, akwai mutane da yawa da suke amfana da kai, mussman ma'aikatanka, gani ga 'ya'yanka da 'yan uwanka, duk muna sonka muna son lafiyarka, ba zan hanaka son matarka ta fari ba, amma dan Allah kar ka saka damuwarta a ranka ka cutar mana da kanka, muna sonka dan Allah ka mayar da komai ba komai ba, ka ga da taimakon Allah na samu jininka ya daina hawa, amma yanzu idan a'kasa damuwa a ranka aiki zai koma mana baya, mu mayar da hankali a kan shirin bikin da ke gabanmu, da sauran al'amuran rayuwarmu, please ka daina damuwa"

Daddy ji yake kamar ya zubar da hawaye, ya kalli Amina da tuni ita tata fuskar ta jiƙe da hawaye, ya janyota jikinsa, ya kwantar da ita, ya lumshe idonsa, hawaye suka zubo daga idonsa, kusan shekaru talatin ba ɗaya yana dakon baƙin cikin da Zainab ke ƙunsa masa, wani an sani wani ba a sani ba, daga shi sai ita da Allan da yayi su, ko tayi masa laifi ya tuna wasiyyar mahaifiyarsa sai ya ƙyaleta kawai, hakan ha sa ta cigaba da cin karenta babu babbaka. Babban abin da yake ci masa tuwo a ƙwarya yadda take nuna masa shi ba komai bane ba a gaban 'ya'yansa.
Cikin hikima ya goge hawayen ba tare da Amina ta sani ba, yayi ƙasa da murya ya ce "Amryata"

"Na'am Daddy"

"Ahmad yana sonki sosai, Allah ya sa mu kasance tare har Aljanna"

Ta shafa kansa ta ce "Amin masoyi, ka dinga saka uwargidan ka a addu'a Allah ya shiryeta, ka cigaba da haƙuri"

"Shikenan Meenalina, Allah ya ƙara mini haƙuri"

Ta ɗago daga jikinsa ta ce "Amin, ko a haka Alhamdilillah mutum ne kai mai haƙurin gaske"

Yayi murmushi ya ce "Nayi magana da Hajiya Maryam, na cika mata kuɗin abin da Khalil bai saya ba, za a turo da kayan lefen sai a kai musu"

Amina tayi murmushi ta ce "Alhamdilillah, sai a yiwa 'yan Dutse waya, su zo su gani sai a kai"

Ya ce "Ok shikenan, sai ayi hakan, kin san Alhaji Ilyas ya koma wurin maman Yarinyar nan fa"

Waro ido Amina tayi ta ce "Haba dai, ya aka yi?"

Daddy ya ce "Haka ya ce mini, kuma har sun daidaita ma, ina ga rana ɗaya za a ɗaura shi da na su Khalil"
Murna Amina ta dinga yi, tana tsalle tana faɗin Alhamdilillah.

Murmushi Daddy yayi ganin yadda, Aminan ke ta tsalle tana murna.

Da haka da haka, Daddy ya manta da batun Hajiya Zainab.

'yan uwan Daddy sun yi murna sosai da sosai, da jin batun Khalil zai yi Aure, har an nemi suje suga lefe, kuma sune zasu kai ma lefen.


Fadila fa abin duniya ya isheta, ta rasa in da zata sanya ranta, saboda yadda ta tsani Salim ɗin nan, wulaƙanci kala kala ba irin wanda ba ta yiwa Salim.
Tana kwance a ɗakinta, taga Salim yayi wani status, ta duba taga hotunansa ne ya ɗora, gaba ɗaya bai yi mata ba, bata taɓa saurayi mai muninsa ba, sai iyayin banza da ƙaryar turanci, gashi sam baaya jin haushin wulaƙancin da take yi masa.

Ita kanta Mummy taji haushin kuɗin da aka kawowa Fadila, amma saboda ƙawancen da ke tsakaninta da Hajiya Salma ya sanya bata nuna mata ba, suka cigaba shirye shiryen yadda bikin Fadila zai kasance.
Fadila ta kasa gayawa kowa damuwarta, dan ko Yusra bata gayaaa an kawo mata kuɗin aure ba, saboda yadda ta tsani Salim.

Khalil kuwa ba zama, sai shiga da fita da yake, yana shirin aurensa, amma ƙasan zuciyarsa babu daɗi, saboda yadda duk abin da yake yi babu hannun mahaifiyarsa a ciki, abin yana damunsa sosai da sosai.

Gidansu Hafsa ma ba laifi, Mama nata ɗan nata shirin, sai dai batun nata auren, ta so a bari sai an yi na Hafsa tukuna, amma Alhaji Ilyas ya ce ai ba haramun bane ba. Can wurin wani ƙanin kakanta a ƙauye aka je neman auren Maman, saboda danginta duk sun ƙare sun rasu. Ita da fari ma bata Amince da batun auren ba, Hafsa ce ta dinga lallaɓata tana cewa "Mama, ni idan nayi aure zamanki ke kaɗai ba zai yiwu ba, wa zai dinga kula mini da  ke, a muna tare ma kalli sharrin da ake mana, dan Allah Mama ki daure ki amince" Da ƙyar dai ta samu Maman ta amince ita ma. Sai dai lokacin da Daddy yaje musu da batun sauko da bikin, Mama taga abin yayi gaggawa da yawa, amma dai tayi shiru bata son yawan yin jayayya.

Hajiya Maryam da kanta ta kawo lefen Khalil gidan Alhaji Ahmad, kuma ba a kai su ko ina ba sai sashen Amina. Ba ƙarya Hajiya Maryam ƙwararriya ce wurin iya zaɓen abin da ya dace.
Akwatuna shida ne, babban set, ba ta cika su da tarkace ba, sai kaya masu kyau da tsada, dan babu atamfar ƙasa da naira dubu goma a kayan nan, abin dai sai wanda ya gani.
Shi kansa Khalil da ya ga kayan yayi murna sosai, saboda yadda suka haɗu, ji yake kamar ya kwasa yaje ya kaiwa Hafsa da kansa.

Kasancewar Mummy bata gidan lokacin da Hajiya Maryam ta zo, ya sanya bayan ta dawo, Khalil yaje ya sameta ya sanar da ita.
"Mummy ga kayan lefe can a kawo, na kawo miki nan ki gani ne?"

"Kar ka soma kawo mini kayan tsiyarka gabana, bana gaya naka ka nemi wata uwar ba? Kaje can waccan abar da ubanka ya aura ta zame maka uwa, ai ni na yafe ka a matsayin ɗa, 'ya ta ɗaya ni a duniya ka tashi ka bani wuri kan nayi maka mugun baki ka ƙarasa lalacewa, dan tuni ka riga ka gama lalacewa, sai abin da yayi saura"
Ire-iren abubuwan da Mummy take yiwa Khalil ne, yake sake karyawa Fadila zuciya, ba dan haka ba da ita ma bore za tayi ta ce bata son wannan mutumin da ake ƙoƙarin haɗata da shi.

Sai cigaba da damunta da lamarin yake yi, ya zamana ko Abincin kirki ba ta iya ci, sai dai ta ɓuya tayi kuka.

Hankali kwance Amina take shirin auren Khalil, dan mussaman ta buga nata invitation ɗin. Tana yada habaici a falo, tana faɗin "Abu namu na yaran talakawa sai in da ƙarfinmu ya ƙare, dole muyi shiri tunda mun samu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login