Showing 1 words to 1309 words out of 1309 words
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA PART 9
adalcinsa, kuma suka ce su daga yau sun zama Musulmi.
Sarki ya yarda aka ba su masauki, suka zama masu tsananin biyayya ga Sarki ta yadda ba dama a shirya makarkashiya da su.
Ni kuma nan take aka nada ni Waziri. Mutane suka yi ta murna, aka yi kwana da kwanaki ana shagali, kuma Sarki ya amince da ni a cikin gidansa. Aka fitar da iyalan tsohon Waziri daga gidan hukuma aka ba ni.
Na ci gaba da zuwa wurin malamina daukar ilmi, kuma soyayya ta yi karfi tsakanina da Fa'izah 'yar Sarki har kowa ya sani, kuma na yi sa'a Sarki da mutanen gari kowa ya amince. Sarki ya sa aka yi ta koya mini dabarun yaki daban-daban, na shahara har ya zama da wahala a sami jarumin da zai iya fuskantata gaba-da-gaba. Kai ba alfahari ba, ko ta baya mutum zai bullo mini sai ya shirya.
Aka shirya tsaf za a daura mana aure ni da 'yar Sarki, aka kawata kowane gefe na gari cikin shirye-shiryen tarbar baki da fuskantar shagulgulan biki da ke tafe.
Abin da kawai ya rage yanzu shi ne daura aure, sai wani abu ya zo ya sungume yarinyar nan tana cikin 'yan mata kawayenta suna wanka. Aka dai tabbatar wannan aikin aljani ne, saboda haka sai muka yanke
shawara ni da Sarki a kan cewa duk inda wannan yarinya ta ke a duniyar nan, matukar dai tana da rai, to ko a hannun aljanu ta ke sai mun samo ta, shi ne muka debi askarawa dubu uku da malamai guda dari muka zuba a cikin jiragen ruwa guda biyu muka shiga duniya har Allah ya hada mu da kai a wannan teku. Wannan shi ne labarina ya kai dan'uwana Idrisu.'
99
Shi ma Idrisu sai ya labarta masa yadda ta kasance a gare shi tun daga rabuwarsu har zuwa yanzu. A karshe dai duk suka amince cewa Sarkin aljanu Sham'una da ke satar 'yan mata ne babu ko shakka ya sace wannan yarinya da su Habu da Sarkinsa suka fito nema.
Saboda haka sai Waziri da dan'uwansa Idrisu suka dunguma suka je wurin Sarki suka sake jaddada masa labarin Sarkin aljanu da kuma irin mugun halinsa na kama 'ya'yan mutane, da kuma labarin Idrisu da irin niyyarsa ta zuwa don yakar wannan mugun maridi.
Cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa Sarki ya ce, "Ya kai Idrisu, na yi matukar farin ciki da jin wannan labari, kuma ina rokon Allah Ya ba ka nasara a kan wannan aljani, kuma na kara farin ciki da ya ke Wazirina Habu dan'uwanka ne.
Zan tambaye ka, shin wane irin taimako kake so daga garemu? Kana so in ba ka jirgi daya da askarawa su raka ka? Ko kuwa kana so mu tafi dukkan mu? Duk abin da kake so ko mene ne ka sanar da mu.
99
Sai Idrisu ya ce, "Ran Sarki ya dade na gode, duk abin da nake bukata ina tare da shi, ina da dokina da takobi da mashi da darduma, wadannan sun ishe ni. Kuma wannan tafiya tawa ba ta mutane da yawa ba ce, don akwai hadari mai yawa a cikinta. Abin da kawai nake bukata daga wurinku shi ne ku kai ni gabar teku, ku sauke ni sannan ku koma gida kuna ta addu'a tare da saurare.
99
Sarki ya ce, "Wannan mai sauki ne." Amma duk da haka sai da ya kawo karin guzuri ya kuma tursasawa jarumin karɓa.
Da gari ya waye Sarki ya ba da umurni jirage suka mika a cikin teku, daga wannan lokaci aka ci gaba da tafiya ba dare ba rana, sai da suka kwana goma sha tara sannan suka isa gabar teku a cikin tsakiyar dare. Da gari ya waye, sai aka shirya liyafa aka huta na kwanaki uku kowa ya koma cikin hayyacinsa.
Daga nan aka yi sallama, Idrisu ya rataya takobinsa, ya rike mashinsa ya yi tsalle ya haye dokinsa, ya daga musu hannu.
Ko waiwaye bai sake ba, ya zaburi dokinsa a guje zuwa cikin duniya. Shi kuma Waziri da Sarkinsa sai. suka juya jiragensu suka nufi garinsu cike da tunanin jarumi Idrisu dan Hamidu. ba a manta ba, Yahaya, wato dan'uwan su Idrisu da Waziri Habu, Yamma ya nufa bayan fitowarsu daga gida. To shi ma haka ya nutsa da tafiya ba dare ba rana har sai da ya isa wani katon lambu wanda babu abin da babu a ciki na kayan marmari.
Rashin sa'arsa na lokacin shi ne bai tarar da kowa da zai agaza masa game da yunwa da tun tuni ta sa shi gaba ba. Wannan dalili ne ya sa idanunsa ko kadan ba su sami wani tsaiko ba wurin hango wata gwanda katuwa kuma nunanniya a sama.
A gigice ya je ya dauko wata doguwar sanda ya zunguro ta ta fado, ya dauka zai yanka amma sai ya yi tunani cewa, "In na ci wannan gwanda ai na ci wa kaina haram, don kuwa mai ita bai ba ni ba... amma bari in dan dakata, in ya zo in tambaye shi, in kuma bai zo ba, to gaskiya a kan lalura zan yanka in sha. Ya jingina a jikin wata bishiya don amfana da irin inuwar da take saukarwa, hannunsa kuma rike da gwanda, ai kuwa sai barci ya kwashe shi. A haka mai lambun ya zo ya tarar da shi. Ya duba itaciyar gwandarsa kuma tabbatar da abin da ya ke tsoro,
ya
wato ita ce dai yaron nan ya zunguro, alhali dalilin zamanta tun tuni ba a shanye ta ba shi ne Sarkin garin aka ajiyewa.
Shi dai mai lambu mamaki ne kawai ya rufe shi irin yadda har za a yi wani mutum ya shigo cikin wannan lambu ya yi sata, sannan kuma don tsananin karfin hali, ya zauna a zo a same shi.
Ya tsaya a kan Yahaya wanda ke ta sharar barci. Zuciyarsa ta fara saka masa abin da ya fi kamata ya aikata don hukunta wannan yaro. Shin ko zai cire takobi ne kawai ya dauke masa kai, ko kuwa ya sami sanda ya lakaɗa masa dukan tsiya. Sai kuma wani tunani ya zo masa, to ai shi wannan kyakkyawan saurayi da a ce barawo ne, to lallai da kwando zai dauko daga cikin kwandunan da ke ajiye a gefe ya cika kayan marmarin ya kara gaba abinsa. To amma kuma bai aikata hakan ba, hasali ma gwandar da ya zunguro, bai sha ba kuma bai tafi ba. Kai lallai akwai wani dalili.
Sai ya sa gindin takobi ya zunguri Yahaya, ya tashi firgigi, sai ya ga mutum kato mai saje da gemu, fuska a murtuke tsaye a kansa da takobi tsirara a hannu.
Nan take a cikin zuciyarsa ya yi addu'a, "Allah Ka kiyaye ni daga sharrin wannan mutum.
99
Cikin ladabi ya gai da mutumin, kuma lallai mai lambu ya ji dadin irin wannan gaisuwar girmamawa da ya yi masa.
Mai lambu ya ce, "Wane dan Sarki ko Waziri ko kuwa wane dan mai arzikin ne kai? Ko kuwa kai dan wani gawurtaccen malamin ne? Mene ne labarinka? Me ya sa ka sata kana saurayi kyakkyawa kamar ka? Babban abin da ya sa tun kana barci ban cire maka kai ba shi ne don na ga alamar mutunci a cikin fuskarka, kuma na yi tunanin ban san asalinka ba kada in kashe ka in jawo wa kaina jangwam. To amma kuma in kana ma da wata daraja ko wani asali, yaya za a yi ka yi sata? To yanzu na yanke shawarar ba zan kashe ka ba, zan bari sai Sarki ya zo zan sanar da shi cewa gwandar da ya ke ta tsimi ka zo ka cire." Ya kara tambaya cewa, "Mene ne labarinka ya kai barawo?"
Sai Yahaya ya ce, "Ya kai mai lambu, babu shakka ni ne na ciro wannan gwanda, dalili kuwa shi ne ni bako ne wanda yunwa ta nemi zautawa. A cikin irin wannan halin ne na ciro gwandar sai kuma hankalina ya dawo jikina na tuna cewa haram ce zan ci