Showing 1 words to 2272 words out of 2272 words

Chapter 1 - YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAN’UNA PART6

15 Dec 2024

771

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA PART 6











cewa ga lambun nan ya shiryu. Sarkin aljanu ya cewa
'yan mata su leka ga lambunsu can an gama, suka tashi tare da chi suka je taga suna lekawa, sai ga lambu an ajiye shi a gefe shirim, kuma abin mamaki shi ne babu abin da babu irin na lambu a ciki.
Shi wannan lambu dai da bakin karfe aka yi shi, daga baya kuma aka cika shi da wani irin rairavi mai launi iri-iri. Itatuwa kuwa har da irin wadanda ba su sani ba akwai. Kai daga gani ka san aikin alian sai dai kallo kawai.
Suka yi ta mamaki don ba su taba gain haka ba.
Sarkin aljanu ya yi tambaya, "Ko wannan lambun ya
' yi?»
Nan da nan suka ce, "Kwarai kuwa ya yi, fiye da yadda muke zaton zai iya yiwuwa."
Ya umurci aljanu su dauki lambu tare da yarinya Nur a ciki don ta nuna musu inda take so a ajiye. Kafin Riftawa suka yi sama har cikin sararin samaniya, suka iso wannan daji, suka yi ta zagayawa kasa-Rasa har sai da ta hango wadannan dakuna biyu sannan ta ce a ajiye mata lambun kusa da dakunan, amma koramar ta raba tsakani."
Shaihin malami Ibrahim ya ci gaba da yi wa saurayi
Idrisu bayani cewa,
"Ina daga nan ciki sai na ji diririm,
in leka sai ga lambu shirim, na komo cikin dakina cike

da ta' ajjubi mara misaltuwa.
Bayan an sauke lambu kuma ya zauna sosai, sai yarinya ta shige cikin dakin nan na tsakiyar lambu ta umurci cewa a dauke ta a cikin sa a maida ta wurin sauran 'yan'uwanta, can inda Sarkin aljanu ya ke.
Da komawarsu sai Sarkin alianu ya umurci aljanu uku da umurnin cewa a kullum dare su rika zuwa suna daukar 'yan matan nan suna kai su, in sun gama wasanninsu sun shiga cikin daki a dauko su a dawo da su. Kuma kamar yadda 'yan matan suka bukata, Sarki ya ba da umurnin cewa duk in an kai su, to aljanun su rika nisantar su sai kamar bayan sa'o'i biyu sannan su dawo inda suke, don su rika samun cikakkiyar damar sakewa da walawa ba tare da sa ido ba, a matsayin su na
'yan mata.
Haka aka ci gaba da yi, a kullum in dare ya fara shiga sai aljanun nan su zo su kawo su wannan lambu. Su yi wasanni da kade-kadensu, har sai in sun kusa kammalawa sai 'yata Nur ta zo ta gaishe ni.
Ka ii dalilin wannan lambu ke nan, wannan yarinya da kake gani tauraruwar cikin su kuma ita ce Nur din, wato 'yata. Har yanzu suna nan a wancan gida da aljanin nan ya gina, kuma duk wannan shirye-shirye da muke yi har yanzu Sarkin aljanu bai sani ba." Dattijo ya dauki ruwa ya kurba sannan ya ci gaba da

cewa, "Muna nan muna ta fatan Allah Ya kawo wani wanda zai iya fuskantar wanna kalubale na ceto
'ya'yan jama'a, kwatsam sai ga ka, kuma wani abin sha'awa da burgewa na gan ka tare da wannan shahararren doki, kuma ga ka saurayi kakkarfa kuma kyakkyawa, sannan kuma ga shi kana da son yin ilmi.
Shi ya sa na hakikancewa kaina cewa kai ne za ka karya wannan aljani barawon 'ya'yan mutane.
Da farko da ka zo idan ba ka manta ba na dan jarraba ka, na ce kada ka yarda ka makara, to dalili shi ne ba a son namiji ya cika barci da yawa. Haka nan kuma lokacin da kake jin wakokin 'yan matan nan, in ka tashi za ka tsallaka zuwa cikin wancan lambu amma ka ji haniniyar dokinka hankalinka kan dawo maka ka juyo, to da a ce ka biye wa zuciyarka ka tsallaka ba ka ji shawararsa ba, to da kuwa kai da shi dokin naka kun rabu ke nan, amma sai ka yi sa'a ka hankalta da ishararsa.
Ya kai dana, yaki kuma da nake koya maka don ka san hiloli ne da dabaru irin na yakin tare da kuma juriya, kuma ga shi kana da doki wanda babu mai irin sa, kuma ga shi za ka sami takobi da mashi da kuma darduma, duk kayayyakin ban mamaki.
Ya kai Idrisu, yau shekara daya ke nan kana zaune a wurina. A nan ka karu da yawa na daga abin da Allah

Ya ba ni, ka yi ilmi mai yawa da sanin hikimomin rayuwa. Ina son in sanar da kai cewa gobe da Asuba, takobi da mashi da sirdi da darduma za su fito daga cikin wannan rijiya, kuma daga daren yau 'yata ba za ta sake zuwa wannan wuri ba, ni kuma zan koma garinmu ba zan sake gain ta ba sai lokacin da kamar yadda muke fata, ka sami nasara a kan Sarkin aljanu ka ceto su, sai dai kuma zan ci gaba da samun labarinta daga wurin dalibata aliana Dailanu, don kowace Asabar takan je wurinsu.
Mai yiwuwa tambaya ko tunani ya iya zuwa maka a cikin zuciva cewa ni da na san duk wannan sirri me zai hana ni zuwa da kaina? To ya kai Idrisu lallai ya kamata ka san cewa wannan ba aikin tsoho iri na ba ne, a'a, wannan aikin yaro ne mai jini a jika. Kuma ina kyautata zaton kai ne Allah Ya nufa da dacewa da wannan falalar.
Saboda haka sai ka shirya, don kuwa gobe za mu rabu, sai kuma Allah Ya sake hada mu. Ka je ka kwanta don yanzu dare ya yi."
Saurayi Idrisu ya koma dakinsa yana mamakin irin wannan labari.
Ya yi rigingine, ya tsunduma cikin tunani, shi da ya fito neman ilmi amma kuma ga shi zai kare masa da gwagwarmaya. Ya yi tunanin ko ya tafi abin sa ne kafin

wayewar gari, sai kuma ya tuna da karamcin malaminsa dattijo Ibrahim, kuma ya tuna da yarinya Nur, 'yar malaminsa da ke ciki kangin Sarkin aljanu, ya kuma tuna irin kyau da cikar halittarta tare da tabbatar wa kansa cewa matukar ya tafi ba ya gain ta, to tabbas rayuwarsa za ta kare ne cikin bege da da-na-sani.
Yana cikin tunanin yadda zai fuskanci duniya, sai ya ji wakar yarinyar nan ta iso, ita da sauran tawagarta suna rera waka mai dadin ban mamaki. Idrisu ya fito waje ya zauna kusa da dokinsa Jagora yana wasa da gashin wuyansa.
Yanzu kam Idrisu ya fahimci bakin zaren, saboda haka wakar da suka sa ta bankwana, nan da nan ya fahimci abin da take nufi, wato ba za su sake dawowa wurin ba daga wannan dare. Can sai yarinya Nur ta sauya salon wakar tana kiran sunan sauravi Idrisu tana yi masa sai wata rana, sai sun hadu. Ta dago hannunta tana yi masa sai wata rana shi ma yana mayar mata.
Bayan duk sun kammala, sai 'yan matan gaba daya suka shige cikin dakin lambu, shi ma Idrisu sai ya tashi ya shige cikin nasa dakin, ya haye gadonsa yana ci gaba da tunani.
To ashe 'yan matan ba tafiya za su vi ba, a'a, don kuwa bayan wani lokaci sai suka fito daga cikin wannan daki suka nufi dakin dattijo Ibrahim, suka gaishe shi kuma

suka yi sallama da shi, suka rabu suna kuka. Malam ya yi musu du'a'i, kuma ya tabbatar musu cewa in Allah Ya so Zai bai wa Idrisu nasara a kan Sarkin aljanu. A haka suka yi sallama, ko da yake kafin nan sai da Nur ta bai wa mahaifinta takarda zuwa ga Idrisu.
Lokacin da suka nufi lambu, sai dattijo Ibrahim ya fito ya tsaya yana kallon su har sai da suka isa cikin harabar lambun nasu sai suka tsaya, wato yau ba su shiga cikin dakin lambun ba, kuma kasancewar a daren akwai hasken wata sosai ana iya hangosu sosai. Idrisu yana cikin dakinsa sai ya ji rugumniya, nan da nan ya fito don gain ko mene ne, sai ya ga lambun su Nur a cikin sararin samaniya yana tafiya, kuma ga 'yan matan nan suna dago musu hannu shi da malaminsa, can kuma kafin 'van matan su bace sai varinya Nur ta sako wa Idrisu adikonta, nan da nan ya yi iyakacin kokarinsa ya ruga kafin adikon ya fadi kasa ya cafe shi ya dora a wuyansa, ya sake dubawa ko zai gan ta ko da sau daya ne amma ina!
Bayan 'yan mata sun bace tare da lambu, sai Idrisu da malaminsa suka ci gaba da kallon sama gefen da lambun ya yi, suna zubar da hawaye saboda irin wannan rabuwa, wato rabuwar da babu wanda ya san lokacin da za a sake haduwa sai Allah, in ma za a hadu din. Dattijo ya yi kuka kamar ransa zai fita ta yadda sai

da Idrisu ya tashi tsaye sosai wurin rarrashin sa tare da alkawarin cewa in Allah Ya yarda sai ya dawo masa da
'yarsa ko da kuwa wurin kokarin haka zai rasa ransa ne.
Da gari ya waye, sai malam ya cewa Idrisu, "Zo mu je wurin rijiyar nan, ko sakonmu ya iso." Ya wuce gaba Idrisu yana biye. Suna isa kuwa sai suka ga rijiya ta ciko har baki, ruwa ya dago sirdi da darduma da takobi da mashi.
Suna gain haka sai murna ta kama su tare da farin ciki mai yawa. Dattijo ya ce, "Je ka dauko, naka ne."
Nan da nan Idrisu ya nufi rijiya ya sa hannu ya kwashe wadannan kayayyaki, kuma wani abin mamaki shi ne yana dauke na karshe sai kawai rijiyar nan ta hadiye ruwanta kamar ba a taba yi ba.
Suka koma dakin malam suna ta duba wadannan kayayyaki suna mamakin su. Ya cewa Idrisu, "Na yi farin ciki da Allah Ya sada mu da kai, bayan mun yi zama na shekara daya tare ga shi za mu rabu, kuma rabuwa ta mutunci. Ina so ka sani ya kai Idrisu cewa za ka yi tafiya mai nisa, za ka shiga gwagwarmaya mai yawa, to amma kada ka damu, in Allah Ya yarda kana tare da nasara. Kai dai ka ji tsoron Allah.
Ina fata za ka zama namii mai juriya da dauriya, kuma ka zama mai yawan gaskiya da rikon amana.
Kada ka yi zalunci, kada ka yi girman kai, kada ka yarda

a cuce ka, kai kuma kada ka cuci kowa. Ka zama kana
mai neman ilmi har zuwa karshen rayuwarka, kuma
kada ka kuskura ka yi wasa da addininka."
Bayan ya gama yi wa Idrisu gargadi, sai ya mika masa wata takarda ya ce masa, "Nur ce ta ce in ba ka." Nan da
nan Idrisu ya sa hannu ya karba. Yana budewa sai
¡danunsa suka ci karo da rubutun yarinya 'yar Shehin
malaminsa,
"Daga Nur 'yar Ibrahim, zuwa ga kyakkyawan
saurayi Idrisu, gaisuwa zuwa ga wanda raina ya ratayu da so da kauna da kuma bege. Ina sanar da kai, ko da yake ba mu taba magana ba, cewa
ina godewa Allah da kuma matukar murna da
alfaharin cewa kana nan tsundum cikin kogin
soyayya musamman saboda abubuwan da na lura da su. Ni fa irin nawa imani da fahimtar ke han. Ko ba haka ba ne?
Ya kai wanda nake so tun ranar da na fara
hango ka a wannan daji, duk lokacin da na yi
tunanin ka sai in ji nishadi saboda tsananin so da
nake yi maka. Kai ne kadai mutumin da a doron
duniyar nan na taba jin cewa na kamu da son sa.
Sai dai kash!... Jin dadin soyayyar tamu ba na
yanzu ba ne, saboda mugun aljanin nan.

Na san cewa malaminka, wato mahaifina, ya ba ka labarin komai, kuma babu wani dalili na maimatawa. Ya kai farin cikin ganina ina yi maka addu'a zuwa ga nasara, kuma ina so ka yi kokari matuka wurin karya wanna makiyi na Allah.
Wannan fama za ka yi ne saboda abubuwa masu dama. Daga ciki na farko in ka sami nasara, to ka taimaki 'ya'yan mutane da wannan aljani ya sace har mu hamsin da dori wanda har yanzu maganar nan da ake yi, akwai yiwuwar in ya ga wata mai kyau ya karo. Na biyu malaminka zai kara farin ciki da murna da kai har abada. Sannan kuma sai na uku, wato soyayyar da nake zato a tsakani. Ko da yake duk wadannan kadan ne in an auna da irin tasirin da wannan yunkuri naka zai iya samarwa dunbin al'umma.
Ya kai ldrisu, zan yi maka wani alkawari, in Allah Ya ba ka nasara a kan wannan aljanikuma ka jicewa ba ka so na ko kuma ban yi maka ba, to na yi maka alwashin kowacce kake so daga cikin 'yan matan nan daga daya har hudu, in kuma duk ciki babu wadda ta yi maka, to zan ba ka kawata aliana Dailanu. Kai na tabbata dole

ne ma a cikin 'yan matan nan ka sami wadda ta
yi maka, don dukkan su zababbu ne a
garuruwansu a fagen kyau da natsuwa ko kuma har da ilmi, shi ya sa ma na hada da ce maka
'dole'. Amma kafin lokacin, za mu rika samun
labarin juna a warin Dailanu.
Ka huta lafiya, ya wanda nake so Idrisu.
Taka, har abada, Nur'yar Ibrahim."
Bayan Idrisu ya kammala karanta wasika sai murna
da dadi suka lullube shi, ya yi kamar ya yi tsuntsu ya bi
ta, kuma tun a wannan lokaci sai ya rika jin cewa da a ce
za su hadu da Sarkin aljanu Sham'una, to lallai da sun
kara, can kuma sai Idrisu ya kanne fuska, zuciyarsa ta
baci don a cikin wasikar Nur ta ce wai in ya ji ba ya son
ta za ta ba shi wata daga cikin kawayenta.
Sai ya cewa malaminsa Shaihi Ibrahim, "Allah Ya
gafarta malam, duk irin abin da ka fada mini na dauka kuma na amince, tare da murna gami da godiya zuwa gare ka a game da duk abubuwan da ka yi mini. Ina
rokon Allah Ya yi maka sakayya da alheri, kuma ina
shaida maka ya malamin malamai cewa, ko da babu
wani tallafi na kayan aiki wato makami da muka rika,
to ina jin in na ga aljanin nan, zan iya taren sa gaba da
gaba, kuma ko don wadda nake dimaucewa a kan ta,


1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login