Showing 3001 words to 3295 words out of 3295 words

Chapter 2 - GORAN DUMA BOOK 1 PART 1 HAUSA NOVEL

09 Nov 2024

2080

Ralau, ya halarci taron karawa juna sani a Lagos, sai libi zai dawo ranar da zaki tafi ke nan, kila ki dan jira 'shi ko? Tunda na san
¡da safiya zai dawo"
Da sauri Rumaisa'u ta ce.
"Ai na fasa kwana biyun, gobe da safe zan koma.."
•Nan' ma sai momi ta bita da kallon nazari, amma sai ta kasa cigaba da yi mata kawaici.
"Rumaisa'u kina are da wata matsala ne?"
A dan gigice Rumaisa u ta fara girgiza kai.
"A'a Momi, me kika gani?"
Kai tsaye Momi ta amsa.
"Fuskarki, na' nuna babu nutsuwa a cikinta, yakenki na nuna karfin halinki kawai, Hajiya ta sanar min kwana biyu kika ce mata zaki yi, yanzu kina dira kin ce da sanyin safiyar gobe za ki tafi, me ya kawo wannan sauye-sauyen, ko kina fuskantar wata barazana'ne?"
Rumaisa'u ta daddage ta bayyanar da Karfin

halinta a fuskarta da muryarta, ta ce.
"Babu komai Momi, wani aikin ne zai mayar da ni Kano a goben, wanda ban san da shi ba sai da na zo yau".
Momi ta rausaya kai gefe cikin saduda ba tare da rai ya so ba ta ce.
"Ai shikenan, idan haka ne wannan aikin ba karami ba ne kamar yadda kika fada mana kafin fara shi, in dai kuwa ojan-ojan din tafiye-tafiye za su dinga fadowa cikinsa ai ya fi karfin Karami Rumaisa'u...
Rumaisa'u ta tare Innarta da dariya mai
sauti
"Momi bai canja ba daga yadda na fada muku, ni dai ku ci gaba da yi min addu ar fatan alkhairi a dukkan al'amurana"
A sanyaye Momi ta ce.
"Shikenan, Allah Ya yi miki albarka, Ya yi miki katanga da kuncin duniya da na alkiyama"
Cikin murna da farin ciki ta amsa.
"Amin, na gode".
Momin ta ce da ita.
"To, dauketa ta ji duminki mana, watakila ma kewar ganinta ya kawo ki...
Rumaisa°u ta sa hannu ta dauki Hamida tana dariya, ta ce.

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login