Showing 1 words to 3000 words out of 3295 words

Chapter 1 - GORAN DUMA BOOK 1 PART 1 HAUSA NOVEL

09 Nov 2024

2079

GORAN DUMA BOOK 1 PART 1




Rumaisau wankan-tarwadar, mace
Mai matsakaiciyar tsawo da Kiba, fuskarta
na da alamun hakuri da sanyin hali a wajen wanda ya karanci mata, 'amma mai rashin matsaya ga mutumin da ya cikawa kansa zargi a cikin mutane" saboda rashin son maganarta da Karancin fara'arta. „Tana zaune a matsakaicin: falon gidansu a tsakiyar falon bisa Kafet ta yi kaca-kaca da
takardu.
Ga' wayoyinta da na'urar kwamfuta"(laptop) dake gefenta, ga kuma robar ruwa' da" kwalin lemo a gefe
Wannan yasa ba sai an fadi ayyuka ke cajan gabbanta ba wanda fuskarta da gabban suka kasa nuna gajiya, Watákila dan juriya da son aikin har zuci.
Can daya daga cikin Wayoyinta da ké zube tasaki wata siririyar Kara, amma abun mamaki duk da haka sai data firgitata. Ta dubi wayar da sauri" kúma a tsorace Zuciyarta na bugawa, duk da haka ta latsa sakon ya fito.
A' fili cikinta ya bayar da Wani kuu.
har sai data dan rankwafa na alamar ba a karar ya tsaya ba har da haifar mata ciwo.
Ga abin. da ke rubuce a allon wayar.

Rumaisan

Yaushe ne kika shirya barin numfashina ya huta? Duk vadda kike jin aiki da dawainiya a rayuwa b.r na tsammanin kin kama Kafata, amma kin san wani abu? Mamakin yadda kike share al'amurana ma wani tafkeken babi ne a kundin da na ware miki, wanda ko wannan babin aka barni da shi ya isa abin Wahalar da zuciya. Rumaisam bayyana min sirriki wanda ya rike ni na kasa amfani da Karfi wajen maganinku ke da zuciyata!
Ware min ko. sakan goma ne daga lokuttan ayyukanki ki yi min wannan aikin Rumaisa.
MAHAUKACIN MASOYI.
Ta yi wurgi da wayar kamar wadda ta galla mata cizo bayan ta kammala karanta sakon, tana satar kallon wayar, sannan ta koma satar bin falon da kallo, musamman jikin labulaye, harshenta fal ambaton Hashunallahu wa nilmal wakil Ta dora da fadin.
"À'uzu bi kalimatullahi tammat min sharri makhalak".
Duk illahirin gabobinta sun yi sakayau, babu nauvi tamkar idan an yanketa lini ba zai bullo ba saboda tsoro da wasi-wasi.
Tsawon fiye da sati hudfu ke nan tana fama
da sakonnin wanda ke
kiran kansa

MAHAUKACIN MASOYI, mutumin da a yanzu ta fara shakkar mutum ne ma ko aljan, mutum da aljan din na zahiri ne ko kuma ifiritai ne (hackers) suka hauro layukan wayoyi kamar yadda akan
'same su a yanar gizo-gizo?
Cikin zarginta uku kowanne ta canka babu dama a cikinsa, in mutum ne ta wanne bututun yake hango halin da ta ke ciki a lokacin da yake turo mata sako? Kamar yanzu da ya yi maganar cakudewar ayyuka.
Idan aljani ne ma wani bakin tashin hankalin ne dan babu ta inda aka gwamutsa
I mu'amalar mutane da ta aljanu bare har a gayyato musu batun soyewa irin haka.
Zargin 'hackers' din ne ma mai dan saufi wai idan ta kawar da kai ga rashin yawan bayyanarsu a layukan waya ta wanna sigar, ko kuma lissafin nemo manufarsu a kanta da suka dame ta ita kadai..
Wata dattijuwar mace fara mai tsawo da
Riba, ta yi sallama ta shigo falon. Da sauri Rumaisa'u ta gyara sahu ta hadiye maitarta ta amsa sallamar matar, fuskarta da gabobinta suka nuna ladabi, tana murmushi ta amsa. sallamar, matar mai alamun zafin nama ta dubeta ta ce.
"Rumaisa'u ki saki aikin nan ki huta haka.

Ga fura mai kyau can Alhaji ya shigo da ita, ki je
• ki dama ki sha..
vi Rumaisa'u ta' yi kokarin tattare tashin hankalin da ta Ke ciki ta ba wa cikinta ajiyarsa, ta tare matar da rawar muryar da ke Kokarin komai ya zama ba komai ba.
"Oh, Abba ya shigo Hajiya?"
mi" Hajiya ta yi murmushi, ta amsa mata..
•"Tun da Hamida ta bar mu gic an ya zame mana kamar hurumi, kiri-kiri Alhaji k • nuna fifiko tsakaninmu, ni kaina sai na zage nake sanin shiga da fitarsa".
Rumaisa't ta
bi wayarta
da kallo tana
murmushin hadawa® zuciyarta ayyuka biyu, tunania gudan jininta Hamida, da kuma tausayinta a matsayinta na mace mai rauni, wadda kuma zata taso kila cikin rayuwar da ta fi tata wadda ta ke tafiya cikinta a yanzu muni, sai kawai ta ji hawaye na son cika mata ido, amma ta dage ta hadiye, ta cewa Hajiya.
'"To Hajiya wannan dai tsakaninku ne".
Hajiya ta bar amsawa Rumaisa'u maganarta ta bi ruwa,
• saboda damun kanta da nazarin
Rumaisa'un da take son yi, wadda fuskarta ke son karyata abin da zuciyarta ke kokarin boyewa, amma da ta hada nazarin nata da wasu daban sai ta

•yi saurin sharewa gudun batawa kai lokaci, ta jima da sanin Rumaisa'u duk inda ake neman mutum mai kawaici ta cika mizani, mawuyacin abu ne ka ji Korafi a bakinta duk yadda ka kai ga kwarewa hilarsa wani ya. amayar da abin da zuciyarsa ta boye.
"Ba ki da bukata ko ta neman addu'a ce daga gare ni?"
Hajiya ta sami kanta da furta wa Rumaisau cikin tsura mata ido, sai Rumaisa'un ta dan diririce saboda fargabar ko ta yi wani abu da ya dago halin matsin da take ciki, ta hau hace takardu tana
cewa.
"'Hajiya ki yi min izinin gobe na kai rubutur nan Abuja na yi submitting".
Hajiya ta ci gaba da kallonta, kallo mai cike da tuhuma.
"Rumaisa'u kwananki nawa da zuwa Abuja, kuma tunda kike rubutun nan kin ta6a kai shi takanas? Ji nake ta E-mail kike tura musu?"
A ladabce Rumaisa'u ta shiga kokarin kare
kanta.
"'Akwai matsala ne Hajiya, kinga ban gama bugawa ba, kuma a ka'ida gobe laraba dole ne zan yi submitting, saboda ranar' litinin mujallar ke fitowa. Ba wai lallai ya zama sai nakai din ba,

amina dai ina neman alfarmar zuwan Hajiya saboda muhimmancin rubutun"
Hajiya ta yi siririyar dariya, tana ci gaba da yi mata wani kallo, wanda Rumaisa u ta kasa daurewa har sai da Hajiya ta cigaba.
Jai, alkunyarki ke son gazawa, ba zaki
iya rashin Hamida ba ko? Ni dai abin da zuciyata ta karantar da ni ke nan.
Da sauri Rumaisa' u ta tareta cikin zaro idon bijirewa batun Hajiyar, ta ce.
"Ah! Hajiya to na fasa zuwa tunda kin zargi hakan... Wallahi ko kadan ba dan Hamida zanje ba Hajiya.
Nan da nan Hajiya ta tareta.
"Na varda da ke Rumaisa'&, zan kuma sanar wa Alhaji, amma da sharadin za ki tashi yanzu ki nemi wani abu ki sa a cikinki"
Cike da jin dadin kulawar da Hajiya ta ke mata ta yalwata fuskarta da murmushi ta ce.
"Ai na bari tini?
Tun bayan fitar Hajiya ta janyo wayarta a gajiye tamkar wadda ta yi gudun shekara ta kasheta, ta jefa akan kuiera sannan ta fice debo furar da
Hajiya ke mata tayi.
Ta kori hayaniya da rudin wanna duniyar ta

tilastawa kanta shan furar sosai, har ta gamsar da ita.
Ta yi wanka ta sallaci isha'i, sannan ta zauna azkar din yammaci da ba ta sami damar yinsa da akan lokaci ba, sai ta yi shi a yanzu tana mai nutsuwa da kaskantar da kai ga mahalicci.
• Abin da ya Karfafa mata gwiwar isa gadon baccinta da wuri tare da tsammanin zata yi barci a nutse shi ne, azacin da ta yi na kashe waya tare da yunkurin barin Kano a gobe, dan gain gudun ruwan MAHAUKACIN MASOYI, wayar da yake kiran nata ta kashe, garin Kano idan ma kyamarar sirri (CCTB) ya makala a garin to ta bar shi, cikin kwana biyu kuma sai ta gani ta ina zai leko ya rikitata?
ABUJA
Karfe biyu da rabi na rana ta fito ofishin jaridar Aminiya dake Jabi da komawa masaukinta wajen Innarta a unguwar Wuse.
Duk a rikice take, tun saukarta Abuja tai wata bala' in rashin nutsuwa ya mamaye ranta, har yake bayyana a gabbanta, wato ayyukanta.
Misali, tana sauka bus din da ta kawota garin a matsayinta na wadda ta taho Abuja a gaggauce, dan zuwa ofis maimakon ta dauki shatar motar da zata kai ta Jabi kawai sai ta bige da daukar wadda zata kai ta gidansu Wuse cikin wasi-wasi.
A cikin tadi din ne ta budo naurarta mai

Kwalwa ta lalubo rubutunta tana nazari da sawarta tura shi kawai ta E-mail din ta wuce gidan ta kwanta.
Anan kuma" ta lalubo Modem dinta' cikin jakar. Sai ta tarar ta baro shi a Kano. Nan takc ta yanke shawarar tsayawa
iwani katafaren kantin
harkokin sadarwa da ke nan tilin da zai sada ta da Wuse daga: Utaho kawai, ta tsaya a nan ta tura rubutun.
9810
Ana isowa Annur, ta yiwa dircba umarnin ya.
tsaya a nan ta shiga ta fito.
I Ta kwashi lap-top ta yi ciki, katafaren waje ne mai kamar komai
" da ruwanka a
Sangaren.
sadarwa, wayoyin hannu, layukan waya, katin waya, kwafuta da sauran tarkacen da suka dangance ta, Modem din da ta. baro a gida ma wancan zuwan nata ta saye shi a nan.
15.
Haka dai gurin ya ke bangare-bangare, ko ina da abubuwan da ya kunsa.
Yau tana shiga bangaren"
"cafe ta tunkara,
amma kamar wadda ta zo daga' kauye duk Rafarta rawa ta ke, sai sassarfa take har ta isa inda ta nufa.
Ba wani abu no ya janyo hakan ba,
, sai garin
yadda kamar kowa a wajen ya zuba mata ido ne. Da yake yawancin katangar dake tsakanin bangarorin ta gilas ce, kamar duk ma'aikatan waien sun doro hankalinsu a kanta.
A gajiye ta karasa waien ta zube a° kujera

tana numfarfashi tamkar wadda ta yi gudun famfalaki, ta yar da jakar naurar gefe ta zube wayoyinta akan tebur.
Mai kula da Gangaren ya dago kansa daga printer da yake zaro wasu takardu ya yi mata wani kallo sanwa shi ya Kara tsinkc tunaninta. Ta shiga zargin ko wani mummunan abu no a jikinta da (mutane ke binta da kallo haka?
"A dabarance ta fara nazarin shigarta. Tana sanye ne da bakar after dress mai shoki da adon shudayen Kananan duwatsu kalar riga da siket din material dinta na ciki, kanta ta nade shi da mayafin rigar kuma da yake ba zata ya fitowa haka ba, sai ta
¡Kara da nade kafadarta da lallausan mayafi mai matsakaicin girma shi ma shudi, jakarta da takalminta duk shudaye, idonta sanye da siririn farin gilas.
"A zatonta ko ba gain idonta ba, gain idon kowa ma babu kauyanci ko digo cikin shigarta.
Duk da haka ba ta gamsu ba, sai ta saci ido ta bude jaka da sunan lalube ta kalle fuskarta tsab ta cikin jakar, komai fos hatta hodar fuskarta da man lebe (wetlips) babu abin da ya gigita su.
Ta zuge jaka tana sauke ajiyar zuciya, cikin (sananin tashin hankali, wanda ya karu lokacin da ta lura mai wajen ya kafa mata ido, kamar barauniyar da ta zo ta vi masa sata jiya, yau ma ta dawo.

Sai bakinsu ya hau rawa shi da ita.
"Madam... Madam me kike bukata?"
Ita kuma tana rawar bakin cewa.
"Don Allah... zan tura wani aiki...
"ta na 'urar
kwamfuta, ta me zan tura..
Bai iya amsa mata ba, sai gyada kai kawai yake kamar kadangare yana kallonta kai tsaye, hannunta sai karkarwa yake ta farke jakar system dinta, shi kuma da sauri ya Karaso ya tura mata foot. stool wai ko zata dora kafa.
Da wasa ba zata dorar da abin da ta yi a na 'urar kwamfuta ba, musamman da shi mai wajen ya dauki waya yana magana da wani harshe da ba ta sanshi ba alamunsa kuma na nuna hankalinsa na kanta.
•Ba a dauki ko cikakken minti daya ba, sai ga wani matashi ya shigo, mai matsakaicin tsawo da kaurin jiki, fuskarsa na da alamun fara'a amma a halin yanzu kai tsaye ba za a yi masa fassara ba, ya nemi guri ya zauna bayan sun, gaisa da mai kula da wajen, sai ya nemi kujerar da ke fuskantarta ya zauna yana satar kallonta tana latso-latse keyboard.
• Can ta yi namijin Kokarin dagowa suka dubi juna ido cikin ido, shi ya kawar kamar a razane, ita kuma ta hade fuska, ta nuna masa T. V' Plasma da ke makale a sama, ta cc.
Bawan Allah ka ga abin kallon can.

Ya yi firgigit ya dubi talabijin din, sannan ya dube ta muryarsa na rawa ya ce
"Ina... fatan dai ba tsarguwa kika yi ba?"
Ta mayar da kanta rai a Sace tana matsawa siririn hancinta hura iska, alamar dai haushin ta ji, amma bata tanka ba
Shi ma ya kawar da kai yana cewa.
"Batawa kai lokaci ne ka yi abin kallo ka.ce ba za a kalle ka ba".
Ta dago da sauri ta dube shi, amma ba ita yake kallo ba, balle ko a fuskarsa ta karanci abin da yake nufi. Ta Kokarta ta ce.
"Ko?"
•Ya juyo cikin kada kai
"Haka na cc, saboda haka kallon naki ya fi kallon wannan akwatin da kike nuna min Kaye..
Yanayin yadda yake magana
duk
kwakwalwarta ta kasa gane inda ya dosa, sam fuskarsa babu walwala bare a yi zargin irin mazan nan ne masu latse-latsen 'yanmata.
Tsam! Sai ta tattara kwamfutarta ta mayar a jaka, ta zuge jaka tana cewa.
"Bari na bar muku wurin ko? Kila ku yi abin da 7a amfanc ku, dan kallona babu ma'anar da zai ba
• ku... Malam nawa ne kudina?"
Ta mike rataye da jaka tana duban mai wajen.
Ya girgiza kai kamar a darare.

"Mc kika yi na kudi? Ki je kawai"
Ba ta ko tanka ba ta juya ta fice, kafarta na hardewa, kowa na damuwa da kallonta har ta fice cikin sassarfa.
Ba ta sami dirban da la bari cikin mota ba, sai kawai ta rungume hannu ta jingina da motar cikin. rudani tana zuba idon ta inda zai billo. Can sai ga shi da mujalla a hannu, cikin zafin nama ya bude motar yana neman afuwarta. Ta hango wanna gajeran mutumin da ya ce kallonta ya fi talabijin Kaye ya doso inda suke.
A hanzarce ta cewa direba.
"Sauri mu bar wajen nan".
Cikin direba ya dauki wani Rug da ya sa shi kasa bin umarminta, yanayin yadda ta yi maganar ya sa ya yi zargin babu gaskiya a tare da ita. Tsoro ya ke ko wani abin ta sato ta sa shi taka sawun Garawo, ya kai ta ya sauke lambar motarsa kuma ta shiga kundin masu laifuka. Saboda haka kawai sai ya yi suguri har gajeren mutumin ya Karaso ya mika mata.
wayoyinta ta windon motar.
"Madam sanyin A.C wajenmu ya sabbaba:
'miki mantuwa?"
Ta karba tana mayar masa da raddi
"Haka ne, musamman da yake daga Kaugen mahudar rana na fito".
Ya juya ya koma da karamin murmushi a

fuskarsa.
"Allah Ya ba ki hakuri idan gaskiyar tawa zafi ta vi miki"
•Direba ya yi ajiyar zuciya ya tashi motar yana ccwa.
"Kinga gata ma da muka tsaya".
Ko kala ba ta cc masa ba, har suka han titi, sannan ta yi masa umarnin ya kai ta ofishin jaridar
Aminiya kai tsaye ta gyara shirmen da ta yi.
RIG
A can kuma, ta watsar da dimuwarta ta yi abin da ya kamata. Karfe biyu da rabin nan ta fito da dokin zuwa gida don samun nutsuwar zuciya, amma dai ta san yaudarar kai no don gula daya a tsarge ta ke, sai kissifawa kanta ta kc wani na biye da ita.
Ba ta jima bakin titi ba ta sami mota, kuma da yake tsakiyar rana nc titin babu cunkoson ababen hawa, sai nan da nan tafiyar ta yi musu sauri, suna kan Berger flover kiran Innarta ya shigo wayarta da ke kunnc. Ta daga cikin muryar ladabi ta ce.
"Momi ina hanya na kusa isowa

Tana sauke wayar sai ta bi ta da kallo, a nan ta ci karo da envelop din da ke nuni da sabon sako.
Hankalinta kwance ta budo shi,
dan
a
amintacciyar wayarta sakon yake, wayar da ba ta
-taba hadata da gigitaccen sakon Mahaukacin Masoyi ba, saboda haka da karsashinta ta fara karantawa.

Rumaisa u.
Garin Abuja ni imtaccen gari ne ma'abocin dauke kewa da gadar da nutsuwa. tamkar yadda salihar fuskarki ta kc, amma yau na shiga rudani da nake gain fuskarki da ayyukanki a gigice.
Kila kin halarci Abuja ne bisa radin kanki ban kuma cire tsammanin dan ki samarwa kanki nutsuwa ba ne, amma ya ya kika hana zuciyarki da gangar jikinki hakan Rumaisa?
Laifin me daya wayarki ta yi kika kasheta?
Ina jiran amsa.
Naki, Mahaukacin Masoyi.
"A 'uzu bi kalimatullahi tammat min sharri ma khalak"
Wanan addu' ar ta karanto tana juya wayar duk da kuwa ta vi mata nauyi a hannu. A yau kam ta ji a ranta ba bil'adama ba ne Mahaukacin Masoyi, kuma ba 'hackers' ba ne, duk yadda ake yi yana daga shaidanun aljannu da zata tashi tsaye neman tsarin Allah da shi.
Har ta shiga gida cikin wanna rudanin biyu take na Malaukacin Masoyi, da kuma na son canko dalilin da ya sa ta zama madubin mutane a уац. Rakinta da
Ayatul Kursiyyu har da

Wattaba'u ta shiga gidan, Innarta ce kadai a falon tana mata marhabin, amma sai ta wayance da
matsuwar shiga toilet, inda ta ajiye jaka a falo
cikin sauri ta shige bandaki
Tayi tsaye gaban katon madubi tana kallon
kanta daga sama har Rasa, iyakar ganinta da
kwakwar juya bayanta ta kalla ba ta ga abi kushe
ko abin kayen da za a damu halittarta da kallo
haka ba. Wannan ya sa ta ji tausayin kanta ya
mamayeta, duniyar nan kamar ba ta karbeta ba,
duk inda ta shiga sai rayuwa ta zame mata kwado, ta rasa abin da ta ke so ko kubucewarsa in ta samu,
ko kuma fuskantar kiyayya daga wanda rayuwa ta yarda su rayu tare.
Da kyar ta rarrashi kanta yayin da zucivarta
ami dan wani sarari sakamakon jiyo kawar
Jiyarta Hamida.
Ta yi alwalar sallar la'asar ta fito falon
Innarta, da mai aikinta dauke da kyakkyawa
Hamida 'yar kimanin shekara biyu da rabi.
Sa'a mai aiki ta dire Hamida da sauri tana
cewa.
"Yauwa tafi da gudu ki yiwa momi oyoyo"*
Kamar Hamida ta gane manufarta ta taho a
guje ta tari Rumaisa'u, wadda kunyar idon tata
uwar ya hanata tarar Hamidan, sai ta dige da rike

mata hannu kawai, idonta akan Sa'a ta ce.
"Sa'a dama kuna cikin gidan?"
Sa'a ta amsa.
"Muna ciki uwar dakina, daga wasa goyo
Hamida ta yi bacci, kawai sai na kwantar da ita wajena"
Suka karasa kujera Rumaisa' u ta zauna tana
'yar dariya.
"Yanzu wannan katuwar yarinyar kike goyawa Sa'a?"
Sa' a ta yi dariya ta ce.
"Ai shi yasa na ce miki wasan goyo"
•Duk suka yi dariya har da Innar Rumaisa'u wadda hankalinta ke kanta, tana yi mata wani irin kallon tausayi.
Sa'a ta mike tana cewa.
"Dan Allah ki dora 'yar nan a cinyarki ta ji sanyi, kin kama kin wani rike mata hannu kamar
'yar awo, wanne abinci zan kawo miki?"
"Ba ni ruwan zafi kawai"
Wato ta share korafin
Sa'a a farkon
maganarta.
"Momi ina wuni, mun same ku lafiya?"
Momi ta yi murmushi irin na manya masu son karantawa kai korafi, ta ce.
"Lafiya Kalau Rumaisa'u, ya ya ayyuka?"

Ta. Ri duban Momi kai tsaye saboda itsarguwa da taiyi da kalion da Momin take mata,
ta amsa.
"Alhamdu lillahi Momi, ya ya Abba yana
"lafiya?"
Momi ta amsa..
90
"Lafiyarsa

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login