Showing 1 words to 2090 words out of 2090 words

Chapter 1 - YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA PART 4

08 Nov 2024

944

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA PART 4





taba jin irin sa ba a wurin tare da waka mai sanyaya rai daga cikin irin wakokin da sukan yi, can sai suka ga hayaki mai ban sha'awa da launi iri-iri, bayan wani lokaci ya Bace, sai ga aljanar ta zo cike da farin ciki don wannan zuwan ta yi shi ne don kawance ba mugunta ba.
Kai irin kayan adon ma sai wanda ya gani,
Tana bayyana sai sula tarbe ta da murna da farin ciki da nuna kauna, bayan sun gaisa ta kawo 'yan ciye-ciye masu dadi ta ba su. Da suka natsa sai suka shaida mata yadda ta kasance tsakanin su da Sarkin alianu da kuma irin yadda ya saki jikinsa da su, har ma da yadda ya tambaye su labarin yana jin wani kanshi na daban, da yadda suka shashantar da tambayarsa, har da yadda ya yi kwalla.
Bayan sun gama shaida mata sai ta ce musu, "Ai dama na gaya muku cewa shi wannan aljani fa duk cikin aljanu da wahala a sami wanda ya fi shi jarunta da saurin fahimtar abubuwa. Sai dai kuma namiji komai jaruntarsa mace ce maganin sa."
Suka ci gaba da gudanar da nishadinsu kamar yadda suka saba. Can zuwa La'asariyya sai suka shiga wani lambu da ke cikin gidan suna zagayawa suna tsinkar
'ya'yan itatuwa. Nur ce ta yi wa aljana magana, "Ya ke wannan kyakkyawar kawa tamu, ga shi mun zama kawaye kuma mun yarda da junanmu, mun bai wa juna

amana da aminci, amma abin mamaki har yanzu ba mu san sunanki ba, saboda haka yanzu muna son sanin sunanki, amma fa in kin yarda."
Da aljana ta ji zancen yarinya Nur, sai ta yi dariya mai daukar hankalin wanda ya ga hakoranta, sai ta ce, "Ya ke Nur, ke da kawayenki babu shakka kun san yanzu ina son 'van Adam. Na rantse da rana, a da mu aljanu ba mu da abokan gaba kamar ku mutane, don muna zaton ku miyagu ne, shi ma ya karfafa mini guiwa wurin kashe-kashen da na yi ta yi, ashe ba haka ba ne.
Yanzu na fi son ku fiye da 'van'uwa aljanu, kuma yanzu zan iya sadaukar da kaina domin ku. Sunana Dailanu
'yar Kailanu. Shi mahaifin Sham'una wato Damsalu shi ne yayan mahaifina."
Sai wata daga cikin 'yan matan nan ta tambaya,
"Ashe Sarkin alianu dan'uwanki ne na kusa?"
Dailanu ta ce, "Kwarai kuwa."
Da yamma ta yi sai Dailanu ta ce musu za ta koma sai ranar Asabar. Ta ce, "Kuma na yi muku alkawari zan zo muku da littafin da asirin kurwar Sarki Sham'una ke ciki. Littafin yana nan a wurin kakarmu Bakayalu kuma babu wanda ya isa ya shiga ma'ajiyarta sai ni.
In tana nan babu wanda zai tunkari wannan littafi. Ni ma abin da ya sa zan sami damar dauko shi don za ta yi wata 'yar tafiya ne, kuma ni ce kawai a dakinta, saboda

haka in akwai wadda ta iya karatu da rubutu daga cikin ku sai ta juyi bayanin ciki don in koma da shi. Ko kadan babu dama wannan littafi ya kwana a waje.
Kull Wannan littafi ya kwana a nan, to kuwa kwananku ya kare, ni kuma na shiga ukuba har abada." Sai yarinya 'yata Nur ta ce, "Babu shakka, akwai
wadanda suka iya karatu da rubutu. Na tabbata za mu iya juye shi cikin lokaci komai yawan shafukansa kuwa."
A haka suka tsayar da shawara. Lokacin da Dailanu za ta tafi sai Nur ta ciro wani warwaro na zinare daga hannunta ta sa mata. Aljana ta yi murna mai tarin yawa, a karshe dai ta koma tana been wadannan kawaye nata.
Bayan tafiyarta sai suka zauna suna kewar ta, suna ambaton kyan halinta tare da labarin irin kyau da cikar halitta da Allah Ya yi mata, tare kuma da tausayawa game da wulakancin da Sarkin aljanu Sham'una ya yi mata.
Washegari Sarki Sham'una ya zo, su kuma 'yan mata suka ci gaba da abubuwan da suka saba. Da suka natsa sai ya kalli yarinya Nur ya ce mata, "Ya ke kyakkyawa, ranar Juma'a na ji kin ce wani abu game da tsoron da kike yi game da rayuwata." Sai ya yi murmushi sannan ya kalli sauran 'yan matan yana mai ci gaba da bayani,

"Ya ku wadannan 'yan mata, ina so in sanar da ku cewa, tun can shekaru masu yawa da suka shude na gagari mazajen jarumai na aljanu. An dade aljanu suna shiri suna kawo mini hari ina wargaza rundunoninsu.
A haka sai da na zo na gagari dukkan tarayyar aljanu.
A cikin shahararrun alianun da muka fafata sai wani
Sarkin aljanu daga Yamma ne kawai ya dan wahalar da ni cikin shekarun da kasashenmu suka rika bugawa.
Yanzu haka yana nan a cikin battar karfe a kulle, ita kuma battar tana can karkashin tekun nan da babu wanda ke zuwa.
To ai ni Bata lokaci ne tunanin mutuwa a gare ni, don kuwa babu wanda ya san sirrin rayuwata sai wata tsohuwar kakata wadda ta san duk salon mugunta sannan kuma tana da tsananin mugun fushi, ko da mafarki babu wanda ke son ya kusanceta, kai in takaice muku labari ba wanda ya isa ya je wurinta daga ni sai wata yarinya 'yar' uwata sunanta Dailanu.
Ita wannan tsohuwa ita ce shugaba a wurin bautarmu, kuma a wurinta ne asirin rayuwata ya ke, kun san kuwa raina yana cikin garkuwa mai wuyar karyawa.
Wannan shi ne kadan daga cikin labarina, don dazan tsaya ba ku labarin yake-yaken da na buga ne, to da sai mu yi shekara ba mu gama ba."
Bayan Sarkin aljanu ya kammala wannan labari nasa

sai Nur ta ce, "Ya kai wannan Sarki mai tsananin karfi, lallai babu shakka ranka yana cikin katanga, katangar kuwa mai tsabagen karfi, saboda haka yanzu hankalina ya kwanta kuma na yi murna mai yawan gaske."
Tana gama fada masa haka cikin murna sai ta barke da waka, tana yi tana hadawa da sunansa sauran suna amsawa.
Yamma ta yi, wato lokacin tafiyarsa, sai ya yi sallama da su ya koma kamar kullum cike da farin ciki. Bayan Bacewarsa sai suka zauna suna. ta labari gami da tunani.
Ran nan dai 'yan matan nan cikin bakin ciki suka kwana, saboda jin irin kariyar da ran wannan mugun aljani ke ciki, amma kuma daga baya suka tattara lamarinsu zuwa ga Allah, suka ci gaba da rokon Sa da
Ya kwace su.
Sarkin aljanu Sham'una ya ci gaba da zuwa har ranar Juma'a. A ranar Asabar wasu daga cikin Musulmin
'van matan nan suna zaune suna karanta wata sura daga cikin Alkur'ani mai girma, sai ga aljana Dailanu. Tana isowa ta ji karatun nan sai hankalinta ya tashi, ta rude jikinta ya yi sanyi, ta ji ba abin da take so kamar karatun, saboda haka sai ta sami wuri ta koma gefe a zauna har sai da suka gama. Kafin su kammala sai ga aljana tana hawaye saboda irin firgicin da karatun ya jefa mata.
Suna gamawa sai suka ga Dailanu ba kamar kullum

ba, don hankalinta a tashe ya ke har yadda su ma sai da suka ji toro, suna zaton ko wani abu ya far ne.
Yarinya Nur ta tambaye ta, "Ya ke wannan kyakkyawar yarinya, yau mene ne lamarinki muka gan ki cikin wani irin hali da ba mu tada gain ki a cikin irin sa ba, kuma na bacin rai. Ko kuwa mun bata miki rai ne? To a gaskiya ba da niyyarmu ba ne, sai ki yafe mu Sarauniyar matan aljanu.
, »
Da aljana ta ji zancen kawarta Nur sai ta rungume ta, tana hawaye ta ce, "Ya ke Nur, babu wani abu da kuka yi mini na baci, wato abin da ya sa ni cikin damuwa shi ne lokacin da na iso nan na ji kuna wani abu kamar waka amma kuma na tabbatar ba waka ba ce, na ji a cikin jikina cewa lallai gargadi ne mai ban mamaki, shi ne na ji na dimauce, hankalina na ji ba wani abu da nake so kamar wannan abin da kuke yi."
Sai Nur ta ce mata, "Ya ke Dailanu, wannan abu da kika zo kika tarar muna yi shine muke kira karatun Alkur'ani, kuma shine addininmu, addinin gaskiya.
Ya ke Dailanu, wannan Alkur'ani da muke karantawa babu abin da babu a cikin sa na shiriya, amma fa sai wanda Allah Ya shiryar ne kawai zai yarda da shi. Na ji rannan kina yin rantsuwa da rana, to rana ita kanta baiwa ce ta Allah, ba ta da ikon kanta har sai an ba ta umurni, haka nan wata da taurari, wuta da ruwa,

duwatsu da mu kanmu mutane har da ku aljanu, duk muna Karkashin ikon Allah din ne wanda Ya samar da mu tun asali."
Bayan ta kammala yi mata wanna bayani da wasu bayanan masu karfafa na farko sai ta ce mata, "Ina ba ki shawarar ki shigo cikin addinin Musulunci, ki bar bautar rana."
Ba tare da bata wani lokaci ba aljana Dailanu ta karbi kalmar shahada ta musulunta, amma ta ce ba za ta taba yarda kakarta Bakayalu ta sani ba, don in har ta sani, to ta shiga uku ke nan.
Aljana Dailanu ta ce, "To ni ma ina so in koyi wannan karatu."
Sai Nur ta ba ta amsa da cewa, "Ai dama yin wannan karatu ga Musulmi dole ne, don in babu karatun ai babu yadda za ki san addinin naki sosai."
Daga nan sai Dailanu ta bude wani dan karamin bakin akwati ta dauko wani bakin kundi ta cewa su Nur, «Wanna shi ne littafin da labarin ran Sarkin alianu Sham'una ke ciki. Ina so ku juyi abin da ke ciki gaba daya don in zan koma in tafi da shi.
Sai dai ku yi hakuri ina tsoron kada wata ta taba shi da tafin hannunta, kuma ni na san dalilin da ya sa na ce haka, saboda haka zan rika dago muku shafukansa daya bayan daya kuna juyewa, in kun lura ma littafin ba

shi da yawan shafuka, ko mutum biyu ma kadai za su iya."
Nan da nan wasu daga cikin 'yan matan suka dauko takardu da alkaluma, suka juye shi kaf! Dailanu ta mayar da shi ta hada cif? Sannan ta sa shi cikin akwatinsa.
Lokacin tafiyarta ya yi suka yi sallama a kan cewa in ta zo makon gobe, za su shawarta a kan yadda za su bullo wa bayanin da ke cikin kundin.

TAFIYAR aljana Dailanu ke da wuya, sai 'yan matan nan suka shirya shafukan da suka juye tsaf! Daga nan sai Nur ta dukufa wurin
nazarin bayanan da aka rubuta don suna da sarkakiya da wahalar fahimta, amma saboda irin zurfin ilminta bayan wani lokaci sai ta fara yi musu bayanin abin da ta iya ganewa. Ta ce,
"Muddin ana so a kashe Sham'una, to da farko sai an kashe kakarsa mai rayuka biyu, wato bayan an kashe ran farko na cikin jikinta sai kuma an kashe na biyu dake matsayin wata irin hatsabibiyar macijiya mai mazauni a wani kogon dutsen da ke cikin wasu manyan duwatsu a bayan duniya. Kuma an nuna cewa kuskure ne babba yin kisa na biyu ba a cikin kogon dutsen ba.
Bayan samun nasara a kan wanna sannan sai a fafata da shi kansa Sham'una, in an sami nasara a kashe shi.
In ba a aikata haka ba, to aljani Sham'una dan Damsalu ba zai taba halaka ba.

Dole sai an bi ta hanyar da aka tsara sannan za a iya yin nasara, in kuwa aka bi ta wata hanya, to kuwa tabbas za a halaka."
Nur ta gyara zama sannan ta ci gaba da bayani, "Dole ne wanda zai dauki wanna kasada ya sami abubuwa biyar masu ban mamaki. Na farko da na biyu kuwa su ne shahararren takobin nan da kuma mashi wadanda babu mai iya daga su sai mai su, na uku sirdin zinare, na hudu darduma mai tashi sama. Cikon na biyar din kuwa shine dole mai irin wanna kalubale a gabansa ya san cewa ba ya yiwuwa a kan gama-garin doki, a'a, dole sai an sami zakakuri kuma ingarman doki.
Yadda za a iya samun wadancan abubuwa hudu kuwa shi ne sai an shiga cikin duniyar mutane, a tsakiyar wani Kungurmin daji da ake kira Surkukin-gagara wanda ba a taba samun mutumin da ya ratsa ta cikin sa ya fito da ransa ba. A cikin dajin akwai wata rijiya wadda a cikinta wadannan kayayyaki na ban mamaki suke. Yadda za a sami wadannan kaya daga cikin rijiyar kuwa shi ne, akwai wani dan karamin rafi a kusa da ita, a kullum za a debi ruwan cikin sa tulu goma daidai ana zubawa a cikin rijiyar har na tsawon kwanakin shekara.
A ranar da aka kammala ne rijiyar za ta cika har baki ta yiwo ambaliya. Ruwa zai dago da sirdin doki na zinare da darduma a kan sirdin, nannade cikin

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login