Showing 1 words to 2362 words out of 2362 words

Chapter 1 - YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA PART 3

02 Nov 2024

830

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA PART 3






daya. Bayan sa sai suka ga wani irin hayaki ya turnuke, siffarsa kamar bakan gizo, yana da launin shudi, ruwan goro, kore, ja da algashi. Can bayan wanna hayaki ya baje, sai suka ji muryar wata mace tana cewa, "Yau kwananku sun kare. Sai dai wasu ba ku ba."
Suna jin haka sai hankalinsu ya tashi suka dimauce suka sakankance da mutuwa, amma duk da haka sai suka ci gaba da yin addu'o' in neman tsari, kowacce tana yi da irin abin da ya zo bakinta ko kuma ta yi imani da shi.
Allah cikin ikonSa Ya amshi addu'arsu, Ya ba 'yata karfin hali ta ce, "Ko wane ne ke son halaka mu ya kamata ya fito fili mu gan shi tukuna, kuma ya fada mana dalilin halakawar, in muna da ta cewa sai mu ce.
Amma in wanda ke son halaka mu din ya aikata haka ba tare da mun gan shi ba, to kuwa lallai yana daga cikin azzalumai."
Suka sake gain hayakin ya murtuke jajawur, sai ya bace, sai ga wata mace wadda ta dan dara su shekaru ta bayyana. Babu shakka wanna mace Allah Ya yi mata kyau, kai da gain ta ka san ba mutum ba ce. Irin adon üikinta kurum ba su taba mafarkin gain irin sa ba.
Suka ga fuskarta a daure babu annashuwa ko kadan.
Lallai da gani ta shiryo sharri a ranta.
Aljana ta ce, "Yau kwananku sun kare, mugaye,

mazinata! Babu mai ceton ku, babu mai kare ku don kuwa lallai yau za ku bakunci barzahu."
Furta haka ke da wuya sai wadannan 'yan mata suka firgita, firgici mai tsanani tare da kara sakankancewa da mutuwa. 'Yata ce ta yi karfin hali ta yi saurin amsa
mata.
"Abin kuwa da mamaki, irin yadda kyakkyawar mace wadda ga dukkan alamu kyan ba na jiki ba ne kawai har zuci... a gaskiya bacewar basira ce kawai za ta sa kyakkyawa kamar ki ki aikata mugun hali. Me muka yi miki da kike son hallaka mu?"
Sai suka ga fuskarta ta yi haske har ta dan murmusa sannan ta cewa 'yata, "Ashe ina da kan da har ke kike yabawa? To gaskiya a da na zo da sharri ne amma yanzu na ji zuciyata ta yi sanvi. Yanzu kuma zan ba ku dalilin da ya sa nake son halaka ku.
Na dade ina kashe mata da yawa ba don komai ba sai kishi.
Ina daya daga cikin kyawawan matan aljanu, kuma . shi wannan Sarkin alianu da ya kawo ku nan dan'uwana ne. Tun yana saurayi soyayya ta shiga tsakanin mu.
Muna cikin kogin soyayya, haka kurum wata rana sai ya shiga soyayya da wata mace 'yar. Adam, , ya yi mini wulakanci mai yawa, ya karya alkawari, kuma -a

al'adarmu in Sarki ya taba neman mace, to ita wannan aljana babu wanda zai sake neman ta har abada.
Wannan yana daga cikin dalilan da kan sa ku ga wasu matan al janu suna auren wasu mazaien na mutane."
Aljanar ta Kara da cewa, "Bayan wannan aljani ya yi mini wulakanci, sai na vi yunkurin tavar masa da kayar-baya amma sai ya sa aka kulle ni a cikin wani daki har na tsawon shekara ashirin. Daga baya kakarmu ta roke shi ya sa aka sake ni. Ni kuma na vi alkawarin in dai zan gan shi da mace 'yar Adam, to babu shakka zan halaka ta. Na kashe 'yan matan mutane sun fi a kirga a dalilin wannan mugu.
Yanzu ma abin da ya sa ya kawo ku wannan tsibiri shi ne don babu aljanin da zai iya zuwa nan sai wanda ke da jinin sarautar gidanmu a jikinsa. Kuma ya kawo ku nan din ne don kada wani abu ya taba ku. Niyyata ita ce in kashe ku in ya so duk abin da zai faru ya faru, amma da ya ke kuna da sauran shan ruwa, sai kika yi mini magana, kuma a cikin maganarki na ji kin ce mini kyakkyawa, to mu kuma matan aljanu babu girmamawar da ta fi ki cewa aljana tana da kyau. Duk wadda kika ce wa haka, to kin gama da ita."
Shaihu Ibrahim dai ya ci gaba da ba Idrisu labari cewa, da 'varsa ta ji jawabin aljanar nan sai ta sami makama, don irin dabiar dan Adam na dogon tunani. Sai ta ce

wa aljanar, "Ko kadan babu wasa ko yaudara cewa ke kyakkyawa ce, duk hassadar mai hassada sai dai ya yi a game da wani abin amma ba game da tantamar kyanki ba, don ni na tabbata irin ki a wanna duniyar sai an
tona.
Abin da nake so ki gane shine, ganin mu da kika yi a nan ba a son ranmu ba ne, a'a, dole aka yi mana don fin karfi da kuma kasancewar babu yadda za mu yi. Ke kanki idan kin yi tunani za ki fahimci cewa babu abin da ya hada aliani da mutum.
Shi wannan dan'uwa naki ba shi da imani, ki duba zuwa yau din nan mu hamsin da daya ne a nan, kuma har gobe in ta kama kawowa ya ke yi, garuruwa da kasashenmu kowacce daban ne, wasu 'ya'yan sarakuna ne, wasu na malamai, wasu kuma 'ya'yan talakawa ne da masu dukiya, duk an kamo mu ba a son ranmu ba, aka raba mu da iyayenmu da 'van'uwanmu da samarinmu, kin ga an raba mu da jin dadi ke nan.
To ke inda kika yi kuskure ke nan, ki ka rika kashe
'ya'yan mutane ba tare da hakkinsu ba. Kin ga wannan ba laifinsu ba ne don babu yadda za su iya da shi, laifin dan'uwanki ne, in ma halakawa ne shi ya kamata ki kashe. Saboda haka ya ke kyakkyawar yarinyar aljanu, muna fata ki yi tunani mu zama kawayenki ba abokan gababa.

Da aljana ta ji jawabin 'yata, sai ta fara kwalla shar-shar. Bayan ta nisa sai ta ce, "Lallai kuna da gaskiya, babu shakka na cuci 'ya'yan mutane, na halaka su ba a kan hakkinsu ba, duk a dalilin wanna mugun aljanin, amma babu komai, kwanansa sun kusa karewa."
Suna jin haka sai suka ce mata, "Ai yakan yi barci a nan, muna iya taruwa mu yi ta soka masa wula har sai
ya mutu.
Aljanar nan ta kyalkyace da dariya sannan ta ce, "Ku dai 'yan Adam ba ku rabuwa da almara, ai shi wannan aljani in duk aljanu sun taru da mutane ba za su iya i masa ba. Nice zan taimake ku, kuma daga yau kun zama kawayena, ke kuma ke ce babbar kawata. Ni dai na vi muku al kawari duk ranar Asabar
da ya ke ba ya zuwa nan zan rika zuwa. Kuma na dauki alkawarin ba zan sake kashe wata mace ba saboda wannan mugun aliani."
Bayan ta gama zayyana musu duk wadannan bayanai, sai kuma ta ce musu, "Zan yi iyakacin kokarina in sato wani littafi da asirin rayuwarsa ke ciki. Shi ma kansa wannan aliani dan' uwana bai taba gain wannan littafi ba, don kuwa yana nan wurin wata kakarmu mai shekaru sama da dubu hudu.
Kada ku vi mamaki na ce dubu hudu na shekaru, to ko kadan babu mamaki don mu aljanu ba mu mutuwa

sauri kamarku mutane."
Daga nan fa sai ta shiga cikin 'yan matan nan suka sha kade-kade da rave-ravensu. In ka ga aljanar nan a cikinsu lallai za ka ga yadda Allah Ya viikonsa.
Daidai goshin Magriba ta ce musu za ta koma, suka rabu suna kuka kamar sun yi shekaru tare, amma kafin ta tafi sai da ta gargade su da cewa kada ko da da wasa su kuskura su fada wa Sarkin alianu cewa ta 2o.
Kafin ta tafi sai ta daga hannunta sama, sai ga wata Ratuwar kwalbar turare, ta bude ta fesa duk a cikin gidan, sannan ta ce musu, "Abin da ya sa ni fesa wannan turare shine, don in ban fesa ba, yana zuwa zai ji kanshin jikina. In kuma ya gane na zo, to ni na shiga ukuke nan."
Tana kammalawa sai ta yi dariya, kafin ta rufe baki sai hayaki ya turnuke ya tashi sama ya fita ta taga, ta tafi ke nan sai ranar Asabar. Wannan shine lamarin aliana.
Amma lamarin 'vata da sauran 'yan mata bayan tafiyar aljana sai suka ci gaba da hirarsu, dare ya yi suka kwanta. Bayan waywar gari da kuma daidaitar lokacin zuwan aljani, sai suka fara wake-wake da raye-raye.
Can kuwa sai ga shi ya iso.
Yana gain su cikin wannan hali na farin ciki da walwala, sai murna ta kama shi, su kuma 'van matan sai suka zagaye shi suna yi masa marhaban-lale, sannan

suka ci gaba da wakokinsu. Bayan sun gaji sai suka dakata, aka yi ciye-ciye da tande-tande, aka sha 'ya'yan itatuwa masu dadi. Babu shakka Sarkin aljanun nan yana cike da farin ciki, kuma ga 'yata kusa da shi, komai ya ce nan da nan sai su tashi su vi masa. Wasu 'yan matan kuma na tausa masa jikinsa.
Duk suna yi masa haka ne don hila irin tasu ta mata, ba wai don suna son sa ba, don ka san su mata su ma kansu aljanun kansu ne. To bayan aljanin ya natsu, can sai ya cewa 'yata, "Ni fa ina jin wani kanshi ne kamar na aljani."
' Sai ta ce masa,
""Wace irin magana kake yi haka?
Ka tara mu har hamsin da dori, sannan ka ce ba za ka ji Ranshi daban-daban ba? Kuma ka san mu mutane kowa kanshin jikinsa daban ne."
Sarkin aljanu ya amsa mata cewa, "E lallai kam kin yi gaskiya. Ni ma kuskure na vi."
A wannan rana ma kamar kullum, Sarkin aljanu ya yi murna da farin ciki mai tarin yawa. Da yamma lokacin tafiyarsa sai suka rera masa wata waka mai dan karen dadi har ya rude ya tafi yana begen su a cikin ransa.
Bayan tafiyarsa sai suka taru wuri daya suna cewa,
"Babu shakka za mu kama wanna mugun aljani a hannu, in ya san wata ai bai san wata ba, in shi aljani ne, to mu mutane ne, za mu ga wanda ya fi wani."
A haka har Juma'a ta kewayo, za su yi sallama da shi

sai ranar Lahadi ke nan don ba zai zo ranar Asabar ba.
Kafin su rabu duk sai 'van matan nan suka fara 'yan koke-koke wai ba zai zo gobe ba, shi kuma da ya ga haka sai ya rude vana rarrashin su, can sai 'yata ta tashi ta ce masa, "Ya kai rabin raina, wanda na fi so a cikin rayuwata, wai ku aljanu haka soyayyarku take ne? Ana ta buga soyayya babu sanin suna? Ko ni ban isa in san sunanka ba don ni ba aljana ba ce 'yar'uwarku?"
To su aljanu a irin tasu al'adar, in mace ta tambayi namiji sunansa, to wanna mata babu wanda take so a rayuwarta kamarsa. Da Sarkin aljanu ya ji yarinya ta tambaye shi sunansa sai ya sake dimaucewa, hankalinsa ya tashi, ya rude ya rasa halin da ya ke ciki don dadi, sai ya nisa ya ce mata,
"Ya ke hasken
rayuwata, ya ke abar kaunata, sunana Sarki Sham'una dan Sarkin aljanu Damsalu."
Yarinyar nan tana jin haka sai nan take ta rera waka da sunansa, tana hadawa da sunanta sauran 'yan matan suna amsawa. Sunan wannan 'ya tawa Nur.
Da Sarkin aljanu ya jì sunansa a cikin waka sai kwalla shar-shar saboda mura. Ya daga hannunsa sama sai ga lu'ulu'u yana zuba kamar ruwan sama. Ya ce, "Ga kyauta nan irin tamu ta aljanu.
Nur ta ce, "Godiya muke ya Sarkin duniya. Amma ya kai wannan Sarki mene ne dalilin yin hawayenka?"

Sarkin aljanu ya ce, "Ya ke rabin raina Nur, kin san mu aljanu ba ruwanmu da lissafin shekaru irin yadda ku mutane ku ke yi, amma da yake ni masani ne na irin wannan lissafin saboda irin gagarata sai in ce yau kimanin shekara dari hudu da hamsin da bakwai da wata biyar ke nan ban yi hawaye ba sai yau, ga shi kuwa na yi karo da mazaje da yawa a filayen yake-yake mabambanta, na kashe mazaje shahararru, naga farin ciki da bakin ciki amma ba su taba sa ni kwalla ba sai yau, dalili kuwa don tsananin son da nake yi miki."
Sai Nur ta ce, "Ya kai wanna kyakkyawan Sarki, babu shakka ina da abin da ke damu na."
Sarkin aljanu ya tambayeta, "Ke kuwa mene ke damun ki a wanna duniya alhali ina kusa da ke? Kan mutum nawa kike so? Ko kuwa kan aljan nawa kike so yanzu-yanzu a kawo su nan?"
Nur ta ce, "A'a, ba kawunan aljanu ko mutane ke damu na ba, ni abin da ke damu na shi ne rayuwarka, don ka ce mini kana yake-yake da yawa. Ni kuwa kaicona ranar da za a kashe ka, ni ma ranar ba zan kwana da rai ba."
Sarkin alianu Sham'una yana jin zancen yarinya Nur sai ya kece da dariya har yana kyakyatawa. Bayan ya gama dariyarsa sai ya ce mata, "Kai, ku dai mutane kuna da ban dariya, shi ya sa kullum na 2o nan sai na
koma cikin farin ciki, shi ya sa yanzu talakawana ke matukar jin dadina. Tun daga lokacin da kika zo nan har yanzu ban sa an yi wa wani aljani ukuba ba, don ina komawa fadata ne cike da farin ciki daga nan wurinki." Ya ci gaba da cewa, "Ya ke kyakkyawa Nur, a yau lokaci ya kure, yanzu ana can an fara zama a fadata."
Yarinya Nur ta tambaye shi, "Y a kai masoyina yaushe ne ake maka fadancin? Ga shi kullum a nan kake yini sai yammaci kake komawa?"
Sai ya ce, "To ai mu aljanu ba ma fadanci da rana sai dai da dare, da rana kuma shiru. Ai kamar ku mutane ne da daddare shiru amma da rana ku vi ta hidima."
Sai ta ce, "E lallai gaskiyarka, ya kai Sarkin aljanu, lallai ya kamata ka tafi yanzu kada in rike wa talakawa Sarkinsu, don dole wani lokaci in rika adalci in rika tuna ceva ba ni kadai ce da kai ba.'
Ya yi murmushi, ya ce, "E wannan kuma daidai ne." Nan da nan ya yi sallama da su ya bace yana mai cike da annashuwa. Wannan shine lamarin 'yan mata da
Sarkin aljanu Sham'una.
Yana tafiya sai suka shiga hira suna yaba wa yarinya
Nur, saboda hikima da dabara da iya hilarta.
Ranar Asabar 'yan matan nan suka shirya suna ta nishadì suna sa ran zuwan kawarsu wato aljanar nan.
Can kuwa sai suka ji wani kanshin turare da ba su

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login