Showing 33001 words to 36000 words out of 41765 words

Chapter 12 - A BABBAN GIDA HAUSA NOVEL

13 Oct 2024

4115

je a nan zata ci gaba da zama zuwa a samu mahaifiyar ta”
Ba tare da Kawu ya damu da jin sai an samu mamar ta ba yace shi bai yadda ba.

Wasa wasa haka suka yi ta ɓata lokaci daga ƙarshe Abba ya ce zata koma ammah da sharaɗin zai kula da ita. Kawu ya amince saboda shi yanzu damuwar shi bai wuce ta koma ba don tsoron Baba amarya yake kamar mutuwa shiyasa tana cewa ya nemo ta ya zo nan ɗin.


Bayan ta sha kukan ta Ammi tayi mata nasiha daga haka ta wuce.

Tunda Zahrah ta koma Baba amarya ta saka ta gaba da faɗa har da duka, daga ƙarshe yace ita zata ke yin aikin gida gabaɗaya. Tsananin shakkar ta ya hana Zahrah cewa komai.
Bayan tayi girki baba AMARYA tace ai babu rabon ta a abincin. Haka daren Zahrah bata ci abinci ba.

Sassafiya ta tashi saboda ta yi ayyukan da aka gindaya mata cizon bata don makara.
Tana gama shara tayi wanke wanke ta ɗaura musu girki, abun da bata yi kullum Mamah ke girka musu ammah yau ita zata girkawa maƙiyar mahaifiyar ta.

Sai around 7:25am Baba amarya ta fito daga ɗaki tana hammah alamun ko salla bata yi ba. Ido ta ƙurawa Zahrah dake gaban wuta tana izawa. Yayin da zuciyar ta ke ƙara saƙa mata irin izayar da zata yi wa Zahrah, ba zata taɓa bari ta ji daɗi ba wallahi.
“ke don ubanki baki iya gaisuwa bane?”
Zahrah da bata san da fitowar Baba amarya ba ta sunkuyar da kanta ƙasa
“ina kwana”
Harara ta maka mata kafin tayi tsaki
“yo da ban kwana ba zaki ganni ne shegiya kawai mayya”

Ita dai Zahrah baki ya mutu bata ce komai ba, sai da Baba amarya ta kewaya taga Zahrah ta gama komai yasa takaici ya cika ta cikin ranta tace
“zaki ci ubanki ne, aikin zan ƙara yawan sa”

Taliya leda ɗaya baba amarya ta Bata bayan ta dafa ta soya manja da yaji ammah baiwar Allahn nan ta hana Zahrah. Ba tare da ta damu ba ta shirya a gaggauce sai dai lokacin already Badi'a ta wuce, Ammi sai da ta tambaye Zahrah ko taci abinci tace A'ah.
Kai kawai ta gyaɗa taje ta haɗa mata basket ɗin ta sannan ta kaita school da kan ta bayan ƙorafin da ta shigar kan makarar Zahrah. Daga nan ta wuce.

Zahrah kenan, gaba ɗaya bata jin daɗin rayuwar fatan ta Allah ya ɗauke ta ta huta ita ma, ina Mamah ta gudu ta bar ta ita bata sani ba gashi yanzu ta dawo ƙarƙashin kulawar Kawu, mutumin da tafi tsana, mutumin da sanadin shi ta tsani maza with the exception of Yaya Ishaq ɗin ta da Abba.
Bayan an tashi suna komawa Zahrah ta shige gida abun ta, tana shiga babu wata wata ta cire uniform tayi wanka, daga nan ta zo bakin ƙofar Baba amarya, ɗan rusunawa tayi saboda hango ta baje kan katifa da tayi.
“ina wuni Baba amarya”
Ai bata amsa ba ita kuwa Zahrah tayi tunanin ko bacci take yasa zata juya, bata ankara ba taji sauƙar dorinar Baba AMARYA a jikin ta.
“don ubanki shegiya mayya Gara na kashe ki na huta, gidan uban wa kika tafi ɗazun”
Cikin Muryar kuka da azabtuwa Zahrah tace
“makaranta naje kuma ai na gama aikin safe”

Ɗan dakatawa tayi tana bin Zahrah da matsiyacin kallo kafin tace
“toh kafiku uban karatu, kin fi ƙarfin tambaya ta to ba zaki ƙara zuwa makarantar ba”
Lafazin ta na ƙarshe yasa Zahrah ba shiri ta kamo ƙafafuwan ta tana kuka
“don Allah Baba AMARYA kar kiyi min iyaka da makaranta, zanyi miki duk abun da kike so amma kada ki zama shamaki tsakanina da....”

Wani banzan bugu Baba AMARYA ta kaiwa Zahrah tare da tura ta gefe, tuni ta faɗi ƙasa tana kuka, har ta wuce ɗaki ta dawo gaban Zahrah tace
“shegiya mayya kuma tashi yanzu ki girka min abinci duk kin bar Ni da yunwa”
Babu yadda ta iya ta tashi da ƙyar ta kaɗe ƙasar jikin ta sannan ta fara ƙoƙarin haɗa wuta.
Bayan ta gama kamar da safe Baba AMARYA bata bata abincin ba, hakan yasa ta koma ta kwanta kan gadon Mamah tana kuka.

“haba Mamah, MEH yasa? MEH yasa? MEH yasa zaki bar Zahrahn ki a wurin mugwagen nan?, Gashi yanzu ko makaranta an dakatar da Ni ammah wallahi ko meh zata yi sai naje” cikin zuciyar ta ta faɗi hakan daga nan ta miƙe tunawa da kayan abincin su da ba sosai suka yi amfani da shi ba coz tun da aka fara kawo abinci daga gidan Ammi Mamah ta daina girki sosai.
Cikin ranta tace
“Allah sarki yaya Ishaq ɗi na mai tausayi na! Kaima ka tafi kaƙi dawowa balle na ganka na faɗa maka halin Baba AMARYA da hukuncin da ta yanke game da karatu na!”
Goge hawayen da ya zubo mata tayi ta wuce ta zaro ledar taliya ɗaya, a hankali ta fito ta girka ta, thank God baba AMARYA bata fito ba har ta gama ta tattare komai.

Sai a lokacin ta samu ta juye abincin a cooler ta ɗiba taci da mai da yajin da ya rage musu.
Wanka ta ƙara yi tayi shirin islamiyya duk da cewa lokacin ta ya wuce, ta ƙara fiye da hour guda.
Still Bata tambaye Baba AMARYA ba ta kama hanyar ta ta fita.
Gidan Ammi da ta shiga ta tarar Badi'a kwance babu lafiya. Bata jima ba ta miƙe ta wuce islamiyya.

Bayan ta dawo gida ta wuce kai tsaye, sabon Bala'i ko kaya bata cire ba ta jiyomuryar Baba AMARYA. Bata san ita da waye ba ammah taji ana cewa
“sai ta dawo zata ci ubanta, ban san ina ta tafi ba shegiya wata ƙila wurin maza ta tafi kin san ƴaƴan yanzu haka suke. Yarinya ƙarama sai kiga ta san bin maza balle wannan da jikin ta ya kai na wata ƴar shekara 18yrs.”
Bata ji me ɗayar ta ce ba Baba AMARYA ta cafke
“bar shegiya tunda na wulaƙanta uwar ta har ta bar gidan saura ita, shegiya mai fuskar aljanu.”

Duk da cewa Zahrah ba babba bace ammah ai ta sanbata kula maza ita dai, kuma kenan Baba AMARYA ce ta kora Mamah?, Lallai kuwa zan sanar da Abba ya taimaka wajen nemo ta kuma a nema mata haƙƙin ta wurin baba AMARYA.
Ganin babu inda tunanin zai kai ta yasa ta fito don ta lallaɓa ta je gidan Ammi kwatsam suka haɗa ido da Baba AMARYA ta rako baƙuwar ta.

Cike da fargaba ta juya zata koma ɗaki sai dai bata kai ga ƙarara shiga ɗakin ba baƙuwar ta dakatar da ita.
“ke mai siffar Mayu baki iya gaisuwa bane ko Saudatu baki koya mata ba”
A sanyaye ta juyo tace
“ina wuni”
Ko amsa wa batayi ba suka wuce abun su, sai can Baba AMARYA ta dawo.
“ke mayyatu fito”
A guje Zahrah ta fito tace gani

Jawo ta Baba AMARYA tayi ta ɗurma mata dundu ta ja ta....har sai da suka je wajen bulalar ta ta janyo ta rinƙa tsulawa zahrah har sai da Muryar ta ta dishe ta tsaya.
Allah Sarki Zahrah abun tausayi.
“tashi ki je kiyi girki kuma mai daɗi zaki yi saboda yau ƴata zata zo, daga nan kuma in kin gama akwai wanki na da zaki yi min kinji ko?”

A hankali ta miƙa ta ɗaura musu girki har sai da ta gama Baba AMARYA tazo ta kwashe tas bata bar mata ba. Haka ta jibgo kayan ta Zahrah ta wanke.
Sai 8:45pmta kammala komai daga nan ta shiga ɗakin mamah ta ci taliyar da ta dafa.
Ɓigirewa tayi ta fara bacci babu tsammani taji an watsa mata ruwa. A gigice ta miƙe tsaya.
Wata ƴarinya ce da bata girmi Zahrah ɗin ba, da wani ƙaton hancin ta da ƙananun idanuwan ta.

“ke don buraubanki ki tashi ba ke babu bacci tunda na dawo”
Kan Zahrah ɗaure take kallon Bibalo da ke zaro mata ido. A zuciye ta janyo ta ta fara dukan ta tana ramawa daga ƙarshe Zahrah ta naushe Bibalo a ciki. Cike da munafurci ta ƙwalla ƙara. Da gudu Baba AMARYA ta fito tana zuwa, ta hau Zahrah da duka.

Bayan nan taja hannun Bibalo suka wuce, ita kuma Zahrah awurin bacci ya ɗauke ta.

Bayan Baba AMARYA ta shiga ɗaki ita da Bibalo, ta busawa Bibalo huɗubar irin azabar da zasu ganawa Zahrah.

★★★★★★

Some month later, Zahrah ta azabtu iya azabtuwa wurin Baba AMARYA da Bibalo, sun mayar da ita jakar su, wanki girki duk ita ce abun takaici in tayi girkin ma ba za'a bata ta ci ba and gidan Ammi yanzu ba zuwa take yi ba, duk ranar da ta saka ƙafa ta je gidan kuwa har Baba AMARYA ta fahimta to kashin ta ya bushe,Kawunzu ba abun da yake yi sai da izinin Baba AMARYA. Ashe ba banza ba su Ammi suka cire damuwar Zahrah a ran su ba sai dai ashe aikin Bulebule ne da baba AMARYA ta kai mishi.

Zahrah ta samu sauyi cikin rayuwar ta, duk hasken fata irin na Zahrah sai da ta disashe, ga kuma wata shegiyar rama da tayi, wuyan nan kamar mariƙar lema ƙasusuwa sun fito kamar wata skeleton, Abu ɗaya da bai sauyu ba jikin Zahrah shine tsantsan kyau da Ubangiji ya bata wanda wahala bata sa ya tafi ba.
Ƴan abubuwa kuwa sai dai in zahrah ta samu shiga school ƙawaye su tarkata su bata Ana cikin haka kuwa school ya gagari Zahrah, da ƙyar ta kammala ss1 nata daga nan ita ma ta cire rabon ci gaba da karatu.

Sannu sannu babu wuya a wurin Allah Zahrah ta kai shekaru goma sha biyar, ta fara menses sai dai babu wani mai kula da al'amarin ta, don ma bata manta wasu karatukan ta na islamiyya ba tana applying wurin tafiyar da rayuwar ta. duk irin ranar da ke jikin ta bai hana ainihin ƙirar jikin ta bayyana ba, tana da ƙirji ga kuma hips nata so Masha Allah kamar na wata babbar mace.

TEAM ZAHRAH WAI KUNA INA NE JARUMAR KU TA ZAMA ASARA A HANNUN BIBALO DA BABA AMARYA?
WHEN ZASU DAINA AZABTAR DA ITA?
KO INA RAI MAMAH TAKE? TA MUTU KO TANA RAYE?
All theses na a cikin littafin babban gida wanda yanzu ake dab da fara wasan
IN ALLAH YA KAI MU GOBE ZAN CI GABA kunga kwana biyu bana post saboda baku yi comments ne, at least in ma ba za'a yi comments ba ayi reacting hakan zai sa naji ƙarfin guiwa.
DIAMOND LADY CE 💎
[07/10, 7:16 a.m.] 💎Diamond Bhatool 💎: ️______________★★★_______________
Typing 📲
🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡
_(All in a big family🏠)_
★TAKUN FARKO★
_[Labari/Rubutawa]_
*©Fadimatu Adamu Hassan*
*A.K.A DIAMOND BHATOOL*💎

_______________★★★________________



PROLOGUE


*PAGE* 1️⃣8️⃣

Dedicated to mah sister Shaheedah, I love u endlessly ƙanwa am.

*Masu Neman labarin daga farko, kuyi following channel ɗin nan zaku samu*
https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X

*WhatsApp group*
https://chat.whatsapp.com/IWQW3ytbVc611XLon2sn66


SHARE AND COMMENT PLEASE
_______________★★★______________

AFTER FEW MONTHS....

Abakin wani makeken hotel motar tayi parking, na cikin basu fito ba for more than 10minutes, can wanda ke driving motar ya buɗe ya fito, wani ƙatoton shiregegen mutum ne wanda ya kai shekaru 45years a duniya. Maimakon ya shiga ciki ya zagaya ɗaya sure ɗin ya buɗe, a hankali ya miƙa ma na cikin hannu yayin da shima na cikin ya miƙo nasa sai naga hannun kamar mace.

Ɗago ta yayi ta miƙe still dai hannun shi riƙe da nata.
Wata fitinanniyar shiga ce da ko a ƙasar Turai ban jin ana yin ta. Wata lalatacciyar maroon gown ce a jikin ta wacce bata ɓoye komai nata ba. A haka suka shiga hotel ɗin har suka kai ɗaki room 48, ba tare da ta juyo ba suka shige ciki. Hour uku cikakku suka kwashe kafin suka fito kayan jikin mutumin duk sun yaƙushe..

Sau al lokacin na ƙarewa budurwar kallo Bibalon Baba AMARYA ce.
Tun daga nan na ja ƙafafuwa na na gudu kada Baba AMARYA tace ina sakawa ƴar ta ido.

On the other hand ✋

Ɗan gaba da majalisar su Kawu a nan ta kafa murhun da take soyawa Baba AMARYA awarar sayarwa. Hijabin jikin ta da yaji jiki ka ɗigo ɗigon maiƙo nasha nasha.
Wani saurayi da ake kira da Bubby ya zo ya tsaya kan ta ce
“yah Zahrah zubo min ta ɗari biyu gobe zan baki”

Saurayin da kana kallon shi kaga ɗan duniya ta ƙura wa big eyes nata, cikin ranta kuma tsoro take saboda har yanzu bata manta su waye maza ba musamman yadda Kawu ya wulaƙanta rayuwar ta.
“kaga Bubby in na baka Baba AMARYA ta ga babu ko ta biyar ne sai ta jibge ni, don Allah kayi haƙuri..”
Cikin kallo na baki isa ba yace
“zahrah yau ko uba amarya ne ba Baba amarya ba kwarangwatsa sai kin bani.”
Yana faɗa yaja matsamin da take zubawa ya fara ci...

Hawaye ne suka fara zubowa Zahrah don babu yadda ta iya gashi bata don Baba AMARYA ta yi ta bugun ta akan awarar nan ga kuma dukan Bibalo da zata ƙara mata wai ta yi wa uwar ta asara.
Sai da yaci kusan ta ɗari biyar ya tura abun gaban ta kafin ya miƙe yana cewa
“shegiya ba dai kin ƙi ki zo ɗaki na ba saboda tsantsar wayon ki?, Toh wallahi kullum sai naci iya ci na asawanyar taki ta kashe ki ƴar ɓakin ciki kawai"
Yana faɗar haka ya ja ƙafafuwan shi ya wuce, sunkuyar da kai Zahrah tayi ta fara kuka tun ma kafin ta isa gida.

Tana cikin wannan yanayin ne motar da na gani a hotel ɗin nan tayi parking, tare da mamakin motar Bibalo ta fito suna jerawa ammah kayan jikin ta yanzu atamfa ce. Sun tafe suna hira tamkar couples ɗin nan har suka zo gun awara....sai da ta tsaya ta yi tsaki tana tofa yawu a daidai jikin Zahrah. Zahrah da hankalin ta baya kan su jin sauƙar abu ruwa ruwa hannunta yasa ta juyo don ganin wa ya watso ruwa.....maida kanta ƙasa tayi ganin Bibalo ce.

Mutumin da suka zo da Bibalo, Alhaji Yunusa Budawa kenan, mutum ne mai kuɗi ba laifi amma ba can ba kuma yana da mata huɗu har da yaran shi kusan takwas ammah duk da haka basu ishe shi ba, bin matan banza kuwa kamar wanda aka saka shi.
Yau ina kin ganshi da wannan gobe kuma wata zaki ganshi da ita. Ya maida mata tamkar motar hawar sa amma yana kashe musu kuɗi in suna tare.

Sun haɗu da Bibalo ne a wajen wani Dije da aka yi bayan layin su, da yake Bibalo ƴar duma-dumar nan ne tuni ya ƙyaso ta...ita kuma don abin duniya da ya rufe mata ido gashi dama ita da bin maza kamar wata karya tun bata kai haka ba ta san maza.

Ɗan kaɗa kan sa yayi ya matso saitin kunnen Bibalo yace
“darling wannan kyakkyawar yarinyar fa?” ɗan haɗe fuska tayi haɗi da yamutsa ta kamar wata tsohuwa tace
“bebi mai aikin gidan mu ce, sam na tsane ta don Allah mu bar gurin warin jikin ta ya dame ni”
“toh kawai yace saboda shi ya riga ya hango abu kuma ko zasu rabu da Bibalo toh sai ya san yadda ya samu fine babe ɗin nan duk da cewa iya fuskar ta ya gani ammah har ya hasaso yadda yarinyar zata kasance.

Ganin bashi da niyyar tafiya gashi ya tsira wa Zahrah ido yasa Bibalo hasala, a lokacin ta cire takalmin ta ta buga wa Zahrah a ka
“shegiya mayya wai ke duk wanda ya kalle ki sai ya tsaya ne...toh wallahi ki sake shi don kuwa auren shi zanyi”
Ƙasa hana ta yayi saboda ya riga ya faɗa fa shikam.
Dukan da ta kai mishi a ƙeya ya dawo da shi hankalin shi nan da nan ya fara kame kame.
Babu kunya a bainan nasi Bibalo ta fizgo hannun shi, kamar wani raƙumi kuwa ya bi ta har sai da ta kai shi mota ta zaunar da shi ita ma ta shiga tayi ta surfa mishi Bala'i daga ƙarshe ta bar shi ya tafi.
Yana tafiya ta yi kan Zahrah da ke zuba wa wani awara a leda ta wanka mata mari har sau biyu left an right kafin tace
“zaki shigo ki same Ni mayya kawai” tana huci ta shige gidan.
Saurayin da take sallama ne ya bata haƙuri Saboda tun ba yau ba suka fuskanci yarinyar na cikin damuwa ga irin cin kashin da matar baban ta da ƴar ta suke gabza mata koda kuwa a wurin tallan awarar ta ne.
Ita sam ba damuwar ta dukan da Bibalo tayi mata bane sai dai uban Bala'in da zata tarar, ga Bibalo ga Baba AMARYA ma kuɗin da Bubby bai biya ba. Daga ƙarshe dai Zahrah yanke shawarar ƙin shiga da wuri tayi har sai sun kwanta.

Ɓangaren Bibalo tunda ta shiga ta fara kututtuma ashar wai ita ala dole mai kishi...mutumin da ko zata mutu bashi da niyyar auren irin ta ma infact Bata kai ba kawai dai yana rage zafi da hutawa da ita ne.

Baba AMARYA ce ta dakatar da ita da faɗin
“ke kuma fa Bibalo, ke da kika fita neman abun arziƙi kuma ya zaki dawo kina masifa? Ko dai bai biya ki ba ne?”
Hararar Baba AMARYA Bibalo tayi tace
“rabu da Ni kema, wannan ƴar abu ta kazar ubance mai ƙirar mayu....”
Nan ta kwashe komai ta faɗa wa Baba AMARYA
“shegiyar yarinya kinga irin kallon ta da yake yi?” ta faɗa tana ƙara banka harara kamar Zahrah na gaban ta.

Salallami Baba AMARYA ta fara
“innalillahi, Ni Saudatu ina ganin bariki yanzu duk irin rayuwar bariki da nayi yau sai da nayi mamaki, shegiyar yarinya bari ta shigo”
“si kuwa nimah cin uban ta zanyi Saudatu ” ta faɗi sunan gatsau babu ko girmamawa.

Shiru shiru Zahrah ta ƙi shigowa har wajen 10:00pm tana waje gaban murhun ta

15, January 2025
Ummee isah

R

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login