Showing 30001 words to 33000 words out of 41765 words

Chapter 11 - A BABBAN GIDA HAUSA NOVEL

13 Oct 2024

4118

da suka gaisa tare cikin mintuna marasa yawa yasa ya matso
“meh ya samu zahrah?" Badi'a da ta shiɗe tace
“Abbah Zahrah ta mutu, shikenan ta mutu kuma babu abun da aka yi mata”
A hankali Abba ya kai hannun shi ya riƙo hannun ta, jin akwai pulse yasa ya ɗago Zahrah da sauri.
“ku biyo baya na”

Cikin hanzari ya fita da Zahrah direct parking. Space ya nufa ya kwantar da ita, Ammi da Badi'a suka shiga.
Kai tsaye Northern Specialist hospital ya nufa da ita. Ba a ɓata lokaci ba aka karɓe ta saboda yanayin da aka zo da ita.

Cikin aƙalla 30minutes aka taro numfashin Zahrah da taimakon doctors da kuma Nurses. Daga nan aka saka mata line na N/A sannan aka yi mata antidepressants injection tuni bacci yayi awun gaba da ita.

Ganin doctors na fitowa yasa Ammi saurin nufar su
“ehm Please ta tashi ko? Zahrah bata mutu ba ko yauwah ku faɗa min meh ke damun zahrah”
Ganin yadda ta bi ta ruɗe yasa doctor murmusawa have
“she's Alright now, ammah tana buƙatar hutu, so zuwa jimawa za'a ɗauke ta daga nan a mayar da ita paediatric medical ward sai ku duba ta”
Jijjiga kai ammi tayi ba tare da ta fahimci dogon bayanin shi ba tunda yace she's alright.

Reception suka koma suka zauna suna ta addu'ar fatan sauƙi wa Zahrah. Sai a lokacin Ammi ta tuna basu bi sun sanar da Mamah ba can tace ba sai an sanar da ita ba kawai saboda kada a ɗaga mata hankali bayan ba cikakkiyar lafiya gare ta ba.

Har wajen azahar shiru hakan yasa Ammi komawa A&E wadda ɗin, karo suka ci da doctor ɗin da yayi mata bayani.
“ehm doctor Bata tashi ba har yanzu?”
“eh yanzu dai a je a nemo mata abun da zata ci zuwa jimawa zata iya farkawa anytime”
“ok” daga nan Ammi suka koma suka yi girki suka dawo.

Har yamma Zahrah bata tashi ba, hankalin su ba ƙaramin tashi yayi ba shine Mamah ta yanke hukuncin sanar da Mamah kada ta ji Zahrah shiru.
Abba na gida kawai ta ƙira shi tace ya aika yaro ya sanar da Mamah Zahrah na asibiti ammah ba sai ta zo ba da an sallamo ta zasu dawo.

Cikin sauri Mamah ta yi picking call ɗin da ke shigowa wayar ta.
“Eh ina ji”
Ta ɗaya ɓangaren kuma ban ji MEH aka ce ba. A zabure ta miƙe tsaye
“ban gane ba.....tooooh ko zaka sa a tambayi amaryar gidan ko tana kwance ba lafiya ne ita ma?.....ohk ina jira”

Daga haka ta dawo ta zauna.
Wasa wasa maghrib tayi kuma Zahrah dai bata farka ba, kuma Abba bai ƙira Ammi ba.
Yanke shawarar barin Badi'a tayi in yaso in Zahrah ta tashi kafin su dawo ma ita tana nan.

Tana isa bayan tayi girki ta nufi gidan Mamah, ɗakin Mamah ta nufa kai tsaye tare da sallama a bakin ta. Jin shiru babu amsa wa tasa ta shiga da sauri tunanin ta ko Mamah na bayan gida ne.
Shiga tayi ta ɗan zauna saboda ta jira ta. Jira shiru shiru Mamah bata fito ba gashi Ammi na son wucewa asibiti. Kai tsaye ta nufi hanyar banɗakin.
“da mutum ne a ciki?”
Sai da Ammi ta maimaita sau biyar ammah shiru ita ma nan da nan zuciyar ta buga wani irin tsoro ya kama ta.

Ganin jiran ba shi da amfani yasa Ammi ta shawarar tambayar baba amarya ko ta ga fitar ta.
Wani kallon banza Baba amarya ta wulla wa Ammi tare da jan tsaki ta koma ɗaki bayan jin ƙudirin Ammi.

Cikin ruɗu Ammi ta fice zuwa gida, ta sanar da abba kafin yace ta wuce babu damuwa wata ƙila Mamah gidan wasu ƴan uwan su ta tafi.

Har lokacin da Ammi ta koma ba'a sauyawa Zahrah waje ba saboda har lokacin bata farka ba.
Allah Sarki ƙauna Badi'a kam kasa cin komai tayi sai kuka ta ke yi

“kiyi haƙuri kiyi wa Zahrah addu'a idan kina kukan babu abun da zai miki sai dai kema ki fara ciwon kai.”
Kai ta gyaɗa tace
“toh mamah”
“oyah zo ki ci abinci” babu musu ta ƙarasa Mamah tayi serving nata, ta ɗauki spoon kenan zata kai loma tace
“Ammi baki bi kin yi wa Mamah magana ba ne?”
“eh tana kan hanya” haka kawai ta faɗa saboda kada ta tayar mata hankali.

Bayan Badi'a ta ci abinci ta ƙara barin reception ta nufi wurin A&E ta tsaya.
Tana cikin tsayuwar Dr. Ya fito. Ganin ɗazu ya ganta tare da Ammi yasa ya nufe ta.
“Baby ina mamar taku?”
“tana can reception” kallon ta yayi yace ta ƙura Maman su.
Da sauri ammi ta biyo bayan Badi'a suka taho.
Ganin irin tashin hankalin da Maman nasu ta shiga yasa Dr. Yin murmushi.

“Yauwah Hajiya ke ce kika kawo wannan yarinyar ko?”
“e...eeeh nice ta farka ne?”
“eh ta farka ammah bata cikin hayyacin ta, so yanzu za'a sauya mata ɗaki sai a bata abinci taci”
“tooh shikenan”

Bayan an sauya wa Zahrah ɗaki zuwa medical ward Ammi da Badi'a suka wuce. So da yake amenity suka kai ta ya sa duk su biyun suka shiga.

Lumshe idanuwan ta suke yayin da fuskar ta tayi pale, sai kamannin ta da Mamah ya ƙara bayyana.

Ƙarasawa wajen ta suka yi suna ambaton sunan ta.


MU HAƊU GOBE DON JIN YADDA ZATA KAYA HAƊU GOBE DON JIN YADDA ZATA KAYA

[05/10, 7:26 a.m.] 💎Diamond Bhatool 💎: ______________★★★_______________
Typing 📲
🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡
_(All in a big family🏠)_
★TAKUN FARKO★
_[Labari/Rubutawa]_
*©Fadimatu Adamu Hassan*
*A.K.A DIAMOND BHATOOL*💎

_______________★★★________________️






PROLOGUE


*PAGE* 1️⃣6️⃣

Dedicated to Aunty fateemah (oum sa'eem)

*Masu son labarin daga farko kuyi following channel ɗin nan:* https://whatsapp.com/channel/0029VanUFkw5kg7G2ci16o2X

SHARE AND COMMENT PLEASE
_______________★★★_________

A hankali Zahrah ke buɗe idanuwan ta yayin da suka buɗe ras sun sauƙa kan Ammi da Badi'a.
Juya idon tayi don gane a wani wuri take, ganin I.V line maƙale hannun ta ga kuma ruwan da ke zuba a hankali yasa ta fahimci a asibiti take. Ammah me ya kawo ta?
A hankali ta fara tuna last scene nata ta shiga duba Mamah gidan Ammi kuma bata ganta ba daga nan ta manta yadda take.

Katse mata tunani Ammi tayi ta hanyar zuba cips and fried egg da ta soyo mata a plate. Kujera ta na ta zauna yayin da ta miƙawa Badi'a plate ɗin wacce fuskar ta ke ɗauke da murmushi.
A hankali Ammi ta ɗago Zahrah bayan ta zaunar da ita da kyau ta amso plate ɗin hannun Badi'a ta fara feeding Zahrah, bata Musa ba ta buɗe baki ta naɗi child ɗin tas.

Bayan ta kammala ci Ammi ta dama mata tea Mai kauri ta Sha, daga nan nurse da ke duty ta shigo, ganin IV fluid ɗin ya ƙare yasa ta zare mata shi kada jini ya zuba. Daga nan ta turo doctor.
Dr. Yayi farin ciki sosai ganin ta ji sauƙi har ya jata da zance. Tuni ta ware kamar babu abun da ke damun ta.
Da zai fita ya kira Ammi zuwa office ɗin shi, a nan ta sanar da ita abun da ke damun Zahrah
“ba komai ke damun ta ba sai anxiety Wanda yayi sanadiyar faɗawar ta shock ammah abun bai yi nisa ba Alhamdulillah, sai dai yarinyar taki na buƙatar kulawa ta musamman in ba haka ba akwai matsala. So yanzu na rubuta drugs sai ku bi pharmacy ku amsa. Don Allah Hajiya a kula da ita kuma a nuna mata soyayya”

Daga nan Ammi tayi mishi godia ta koma ward ɗin cike da fargaban ina Maman Zahrah ta je yau kuma, sannan menene dalilin faɗuwar Zahrah.

Basu ɓata wani lokaci ba aka yi discharge nasu, bayan shawarwarin da nurse ɗin da ke duty ta Basu.
A gajiye suka wuce gidan Ammi. Ɗakin Badi'ah Ammi ta raka Zahrah, ta haɗa mata ruwa mai zafi ta sata tayi wanka. Bayan ta shiga wanka ta turo Badi'a wurin ta sannan ta koma gidan ko mamah ta dawo sai dai shaaaaam kamar yadda taga ɗakin Mamah yanzu haka yake.
A sukwane ta dawo gidan lokacin Zahrah tayi wankan ta ta saka light gown na Badi'a.

Ita dai Zahrah baki ƙimmm bata ce komai ba tunda suka shigo gidan, ganin haka yasa Ammi ta bar ta zuwa safiya suji meh yasa ta faɗi.
“daughter ki kwanta ki huta, sai da safe.”
Kaɗa kai Zahrah tayi daga nan suka kwanta ita da Badi'a.

Ɓangaren Ammi da Abba abun ya ɗaure musu kai. Abba tun bayan Ammi ta sanar da shi mamahn Zahrah fah Bata nan shima ya shiga halin mamaki.
Daga ƙarshe suka yanke shawarar neman ta gobe bayan sun ji damuwar Zahrah ɗin.


★★★★★★★

“gaskiya ƙawata aikin boka Bulebule kamar yankan wuƙa yake”
Tafawa suka yi ita da Asabe kafin Asabe tace
“ke dai ki bari yanzu bani labarin abun da ke faruwa manah, shegiyar ta mutu ne”
Kallon ta baba amarya tayi kafin tace
“ke har kin manta boka Bulebule baya kisa ne?,”
“ooooh haka fah” ta faɗa tana riƙe baki alamun ta tuna
Baba amarya ta Kamo hannun Asabe ta riƙe sannan tace
“ina baki labari, ban san yaushe shegiyar matar ta fita ba ammah dai zancen da nake miki an rasa ta....wataƙila yanzu kam ta riga ta kama bolar zama”
Ta faɗa suna sheƙewa da dariyar shaƙiyyanci.
“baki da dama ƙawa ta, toh ita ƴar tata fah?”
Ɗan zare ido tayi sannan tayi fari
“ohoooh Ni ban sani ba, ammah na sani babu makawa aikin boka ya yi ina jira ta dawo ta sane ni nan”

Girkin da take yi ta ƙarasa ta zuba musu shi duka a tray, suna ci suna magana kamar wasu mahaukata. Bayan sun cinye suka ji gaba da hirarrakin su.
Baba amarya ta dubi Asabe ta ce
“ƙawa ta yaushe ya dace na ɗauko Bibalo ne daga ƙauye don yanzu kam ita ma nan zata dawo NBmu zauna mu mulki ɗiyar shegiyar tare”
Dariya Asabe tayi tace
“ƙwarai ya kamata ki ɗauko mana Bibalo gashi kuma ba zata fi sa'ar ƴar kishiyar taki ba”
Jin kishiya yasa Baba amarya makawa Asabe harara. Da yake duk ƴan duniya ne tuni Asabe ta harbo jirgin ƙawar tata sannan tace
“Kaji uwar kishi, kin zo kin samu mata da ƴa gidan su ammah ke kike kishi ba ma ita ba”
“yo ai dole nayi kishi da ita, da ace irin banzayen nan ne ma tooooh, ammah baki ga matar ba ga kyau ga kamala ni wallahi bata yi min kama da ƴar talakawa daga gani ƴar babban gida ce”
“ai kuwa na lura da hakan, ammah ko ma ƴar jibgegen gida ne ba babban gida ba yanzu kam ai kin wulaƙanta ta ta zama kashi”

Tafawa suka yi suna dariya kafin Baba amarya tace
“yanzu dai gobe ki raka ni ƙauye mu ɗauko Bibalo mudawo nan saboda ina son mu gasawa shegiyar aljanar yarinyar nan aya a hannu, ta yadda zata daina rasar kunyar da ta zama mata jiki”
“Ai Ni ƴar nan tun ranar tariyar ki na ƙullace ta saboda abun da tayi ga kuma shegen kyau har ta so ta fi uwar fa”
Bana amarya ta ce
“hmm ke dai ki bari kawai, zamu ci uban ta ne ai”
Haka suka yi ta hirar su daga ƙarshe Asabe ta koma gidan mata da yake dama can ita a can take da zama.

★★★★★★

Asuba nayi Zahrah ta tashi a hankali tayi alwala tayi sallah bayan tayi ta tayar da Badi'a ma tayi.
Bayan sun yi sallah suka yi wanka saboda yau zasu koma makaranta bayan sun dawo daga Jos.
Basu shirya ba sai around 6:30am suka nufi kitchen don taya Ammi aiki sai dai Ammi ta kora Zahrah kan ta huta ai bata da lafiya ita kam.

Da wuri suka yi breakfast ganin akwai sauran lokaci mai ɗan yawa yasa Ammi tace
“zahrah” a hankali ta ɗago da kanta ta mayar da hankalin ta kan Ammi
“jiya MEH ya same ki bayan jin zo nan kika faɗi??”
Bata ɓoyewa Ammi komai ba daga baccin su da tashin ta daga bacci har zuwa rasa Mamah da tayi.

Rarrashin ta Ammi tayi tace mata kada ta damu Mamah za ta dawo coz Abba ya sa a nemo ta. Cike da farin ciki tayi a Ammi godiya sannan suka wuce school.

Har suka dawo babu wani labari da aka samu akan Mamah, hakan ya ƙara sanya Zahrah cikin halin damuwa duk da cewa Ammi da Badi'a har da Abba na ƙoƙarin kwantar wa Zahrah hankalin ta. A haka suka wuce islamiyya bayan sun dawo ammah Mamah shiru Babu it's Babu labarin ta.

★★★★★★

Kwanaki uku kenan da ɓatan Mamah ammah shiru babu labari, duk wani radiostation da aka sanar babu wani ci GABA. Gashi har TV stations an sanar harda picture ammah babu ko tari balle wani ya ganta.

Yau da safe Zahrah ta cewa Ammi zata je gida ta ɗauko wasu kayan ta. Tana fita Kai tsaye gida ta shiga, bata tsaya ko Ina ba ta ahiga ɗakin Mamah, cike da damuwa da ƙunci Zahrah ke kallon ɗakin Tana hawaye.

Ɗauko wanna bag din da Mamah ta Bata a daren da zata ɓata tayi tana manna shi a ƙirjin ta. Wani sanyi take ji tamkar Mamah tayi hugging.
“Allah sarki Mamah na, Ina matuƙar ƙaunar ki, Ina Kika tafi haka Kika bar ɗiyar ki ɗaya? Don Allah Mamah ki samu ki dawo kada ki bar ni Ni kadai a nan”
Tsagaitawa tayi da maganar sannan ta ci gaba tamkar Mamah take gani
“aah Mamah nafi so ko zan je gidan ku wurin su Hajjaty da Kika bani labari muje tare da ke tunda ke ce dolem su”

Haka zahatah tayi ta surutai wasa wasa sai da ta kwashe awa guda a wurin. Motsin da ta ji ne yasa ta miƙe ta waiwayo ko zata ga mamah ammah wayam, hakan yasa ta ɗauki bag din tare da haɗa wasu kayayyakin ta ta wuce gidan Ammi.

Baba AMARYA dake tsaye bakin ƙofar ɗakin ta ta Kama kunkumi sai wani jijjiga take tamkar wacce ta ke jiran abokiyar faɗa ta kawo mata dambe. Ashe tun shigar zahrah da taji motsi ta leƙo ganin shegiyar yarinyar da take jiran dawowar ta yasa ta tsaya Tana jiran ganin ko zata fito tace zata taho.

*Don't forget to react and share*
[06/10, 6:23 a.m.] 💎Diamond Bhatool 💎: ______________★★★_______________
Typing 📲
🏡 *A BABBAN GIDA* 🏡
_(All in a big family🏠)_
★TAKUN FARKO★
_[Labari/Rubutawa]_
*©Fadimatu Adamu Hassan*
*A.K.A DIAMOND BHATOOL*💎

_______________★★★________________️






PROLOGUE


*PAGE* 1️⃣7️⃣

Dedicated to mah sister saddeeqah. Much love dear
SHARE AND COMMENT PLEASE
_______________★★★_________

Fitowar Zahrah yayi daidai da matsowar Baba amarya bakin ɗakin Mamah. Babu zato babu tsammani ta fara zubowa Zahrah uban Bala'i
“yanzu ke dan uban ki ina kuka gudu ke da shegiyar uwar taki...”
Bata kai ga gama faɗa ba Zahrah ta kai mata duka jin ta zagi missing mamahn ta.
Baba amarya ta jawo Zahrah har sai da bag ɗin da ta ɗauko ya faɗi....

“don ubanki da shegiyar uwar ki Ni nafi ƙarfin ki har Ni zaki kaiwa bugu don ubanki, toh wallahi yau sai naga wanda ya tsaya miki a gidan nan...bari kiji babu inda zaki ƙara fita don uwarki shegiyar yarinyar mai siffar mayu”

Tana shirin kai mata bugu da bulalar da ta zaro daga bayan ta kwatsam Badi'a ta shigo don kiran Zahrah. Ganin Aminiyar ta hannun shegiyar babar ta yasa ta fita da sauri ta sanar da Ammi.
Da sauri ammi ta biyo ta suka dawo lokacin kuwa Baba amarya ta jibgi rabon ta. Ganin mata ƴar gayu da yarinyar da ke shigo da abinci kwanaki yasa ta tsayar da dukan tana cilla Zahrah gefe wacce ta faɗi ƙasa.

Kallon tuhuma Ammi ta maka mata sannan tace
“meh tayi miki kika duka ta?”
Daga haka ta ƙarasa ta ɗago Zahrah dake yashe.
“badia riƙe ta ku koma gida”
Caraf baba AMARYA tace “gidan uban wa?”
“gidan da za'a kula da ita”
Daga haka Ammi ta ɗauki bags ɗin Zahrah ta bi bayan su.

Cike da takaici suka koma gida Ammi ta sa Zahrah ta ƙara wanka, Badi'a kuma ta wuce school. Tunda Badi'a ta fita Zahrah bata furta uffan ba don yanzu mugun shakkar Baba amarya take yi. Kafin Badi'a ta dawo zahrah ta ɓoye bag ɗin da Mamah ta bata.

Bayan sun yi lunch Ammi take sanar da Abba abun da ya faru ɗazu.
“lallai matar nan ba ƙaramar muguwa bace, toh menene damuwar ta da yarinyar da ba kulata ma take yi ba?
“nimah abun ya ɗaure mun kai gaskiya, shiyasa nace ya kamata a samo wa Zahrah mafita tunda yanzu ba wata lafiya isasshiya gare ta ba”
“worry not dear, zan san abun yi, idan ma magana zanyi wa baban nata sai ya bar min ita a nan su zauna har zuwa lokacin da za'a samu mamar tata.”

Suna cikin zancen suka ji ana wani mahaukacin knocking da ake yi kamar za'a ɓalla gaye. Da Abba ya fita yana isa bakin gate ɗin bayan ya buɗe kawun Zahrah ne kamar wani mahaukaci.
Ƙure shi da ido Abba yayi kafin yace
“lafiya kake buga min ƙofa kamar wani mahaukaci”
“yoh ai dole na haukace bayan ka sace min yarinya toh wallahi ka fito da ita ko na ƙona gida” ya faɗa a hasale yana nuna wa Abba gallon na petrol dake hannun shi.
“toh ka ƙona ka gani, wallahi sai na sa an ɗaure ka har ka bar duniya a prison zaka zauna”

Jin abun da Abba ya faɗa yasa Baba rusuna yace
“shikenan bazan ƙona ba ammah ka bani yarinya ta na wuce”
“aah babu inda Zahrah zata

15, January 2025
Ummee isah

R

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login