Showing 9001 words to 10897 words out of 10897 words
na gaida ki ko bakya da lafiya ne? " Lafiya ta k'alau "Ohh iskanci ne kenan " k'ara turo baki gaba tayi, ya kalleta tare da girgiza kai, ya wuce khadija ta taso ta rakasa har bakin k'ofa sannan ta dawo
"Komai shafe_shafe munsan tsufa dan duk wanda ya shafa man dallah munsan shi" Khadija najin ta tayi kamar bata ji ba tayi d'aki,
tana nan zaune taji sallamar k'awarta safiya da gudu taje ta tarbo ta "Aah yau kece a gida nan"Wallahi kuwa yau allah yayi nazo kuma nazo miki da haja"Kice dai ita ta kawo ki "Aah wallahi daman inada k'udurin zuwa " To muje daga ciki"d'akin suka wuce, firar yaushe gamo suka d'an ta'ba daga nan safiya ta bud'e Jakarta tana fitowa da maganin mata " Amman wallahi naji dad'in zuwan nan naki kamar kinsan ina buk'atar su sai dai kuma banada kud'i a hannu" Ai kuwa ba bashi ba ne, kinga wannan, safiya ta fad'a tare da nuna ma balkisu wata kaulba " Eh nagansa" Hmmmmmmmm wannan shi ake kira da sa kishiya tagumi hana kishiya bacci " Ni kinsan irin wad'an nake so, so nake ki bani wanda ina yana samana har mak'ota sai sun ji ihun sa "Hehehehe idan wannan ne baki da matsala ai da kin kawo ga wannan magana ta k'are ke ba mak'ota ba layin nan naku gabaki d'aya sai anjiyo shi bare kuma muta nen cikin gida ai sai kun hanasu bacci kuma zai zazzage kimi aljihun sa ke da kinyi aiki dashi sau biyu to shikenan sai abinda kika ce a gidan nan kuma duk abinda kika tambayesa koda baya da shi sai yaje ya nemo miki shi" Shegiya k'awata kamar kinsan abun da nake so wallahi " Hmmmmmmm kedai kawai fito da kud'i ki siya kaya kiga aiki nasan sai kin godemin "Haba k'awata mu sasanta mana sai ki bani kinga gobe zan kar'bi aiki idan nayi aiki dashi na samu kud'in sai na baki kud'in ki har ma na miki kari
Tab baki shiryar siyaba bari idan kika samu kud'in sai na kawo miki dan gobe barin garin nan zanyi, kinga ko bazaiyi na bada kaya nn bashi ba "Kar muyi haka dake " To mezai hana ki ranto"To ni wazai rantamin ? "Idan kina so akwai wata mata da na sani mai dashe nan take ma cikin unguwar ku tana rantama mutane kud'i "To kina ganin ba matsala "Ba wata matsala "To bara nasa mayafina muje" To,
Tasa mayafin ta suka fito, suka wuce, gidan baya da wani jayawa daga gidan su, da suka je ma matar ta gane balkisu dan sunje ganin amarya, bayan ta basu waje suka zauna suka fad'a mata buk'atar da ta kawosu wajen ta matar ta numfasa tare da fad'in " To maganar gaskiya kud'i akwai su amman akwai wacce za'a kwaushe ma dashen ta jibi amman idan kunyi alk'awarin zaku kawo kafin lokacin sai na baku"Eh in Sha Allah kafin nan ma ta kawo dan gobe muke sa ran za'a samu kud'in" to shikenan dubu ashirin kuka ce ko amman dai kunsan talatin zaku mai suwa "Eh "To shikenan, ta tashi ta shiga d'aki ta irko musu kud'in ta Mik'a musu tare da fad'in"Dan Allah ku cika alk'awari "Karki damu in Sha Allah" suka amsa suka fito, safiya ta had'a mata kayan dubu goma, sannan balkisu ta bata dubu biyu kyauta, sukayi sallama ta wuce, kafin ta isa gida sai da ta kusa kashe dubu biyu ta siya awara da madara ta biya ta siyo kilishi sannan tayi gida
Koda ta shigo gidan, khadija na bakin murhu tana aiki, ta d'ago ta kalleta dan ita bata ma san bata nan ba " Fita kikayi? "Ai gashi na dawo " balkisu ta fad'a tare da shigewa d'aki, khadija ta mayarda hankalin ta ga aikin da take yi .............................................
Cikin d'aki ta shige ta koma gefen gadonta ta zauna a k'asa , ta bud'e k'afafuwanta tasaka ledar a tsakiya, tun kafin ta bud'e ledar yawu har sun fara taruwa a bakin ta, ledar kilishin ta bud'e ta fara ci, sauri_sauri ta rik'a cin sa kamar wacce ke aikata wani mugun abu batasan a kamata, haka ta rik'a ci, ta cinye ta janyo ta awara ita ma sai da ta cinye tass harda sa harshe ana lasar d'an bad'in da ya lak'e a ledar, zanen gadon ta janyo ta goge hannun ta dashi ledodin kuma ta tura k'ark'ashin gado, ta d'auki maganin tana kallo tare da yin wata irin dariya
" Hehehehe sadik ka kusa shigowa hannu sauran k'iris, zan juyaka yarda nake so na tatale dukiyarka koda yake yanzu baka da komai sai dai nasa ka rik'a ciwobashi kana kawo min naci dad'ina khadija taki ta k'are Hhhhhhhhh"
Khadija ta gama aikin ta, har tayi wanka ta had'e cikin wata doguwar riga, rigar kamar roba take duk ta kwanta a jikin ta duk yarda ta motsa sai jikin ta ya raya, sai k'amshi take zubawa ita da d'akin ta, abincin balkisu ta d'auko tazo ta kawo mata, tayi tsaye bak'in k'ofar tasa hannu ta k'wank'wasa k'ofar, balkisu dake zaune cikin d'aki tana lissafin abubuwan da zata yi, taji ana k'wank'wasa mata
" Wai lafiya? " Idan kika zo zaki gani"khadija ta bata amsa " To naga alkhairi"Shi muke fatan gani a koda yaushe" Uhmm, tana fitowa khadija ba tare da ta sake cewa da ita komai ba ta Mik'a mata kular ta juya, da kallo balkisu tabi bayan ta har ta shige d'akinta, taja tsaki ita ma tashige d'aki tare da fad'in" sai wani kuri da take da d'uwawu sai aka ce mata muma bamada su mtsssww to allah dai yasa kowa nada d'uwawun nan sai dai kawai ace na wani yafi na wani to muma munada namu ehheeeeeee"
Khadija ko tana komawa d'akinta ta d'auko had'in da tayima kanta tayi zaune tana Sha..............
Gogan naku koda yadawo cin abincin ganin khadija cikin wannan shigar ba k'aramin tayar masa da hankali tayi ba, ai kuwa yace bazai koma kasuwa ba dak'yar khadija ta lalla'basa ya koma
Yau ma kamar jiya koma nace fiye da jiyan, khadija ganin abun nasa yayi yawa za'a iya jiyo su yasa ta dakatar dashi, ta hanyar janye jikin ta daga gareshi ta koma gefe, a hauka ce ya d'ago yana kallan ta yana haki, kamar wanda ya sha gudu, kallan ta yake itama shi take kallo, bakin sa na matsi alamar magana yake son yi amman ya kasa, dak'yar ya iya furta kalmar " Miye hakan ? " Ba mu kad'ai bane a gidan nan ba fa za'a iya jiyo mu " Wani kallo ya watsa mata tare da fad'in"To sai me dan an jiyo mu ba mata da miji bane mu har kike jin kunyar ajiyomu muna raya sunnar ma'aiki( S A W)" Ya fad'a cikin 'bacin rai
Khadija ganin kamar maganar ta 'bata masa rai yasa ta dawo wajen sa tare da shigewa cikin sa tana shafa jikin sa a hankali ta furta" yi hak'uri ba haka nake nufi ba "ta fad'a tare da d'agowa tana kallan face d'in sa " To ya kike nufi ? " Sorry zuma na yi hak'uri ka gafarce ni bisa furucin da nayi" zai sake yin magana tayi saurin had'e bakin su waje d'aya, daga nan suka ci gaba da faran tawa junan su................
*'bangaren balkisu*
Ko yau ta jiyo su ta tashi tayi zaune tana kitstsima abubuwa a ranta, har bacci yayi awon gaba da ita
* Washe gari*
Bayan ya dawo sallahr asuba sai da ya sake nemanta dan yasan yau ba a d'akin ta zai kwana ba, ai kuwa ta makara wajen had'a karin kumallo, balkisu ta fito tayi zaune minti d'aya minti biyu tayi tsaki, ganin tsakin yayi yawa yasa khadija ta d'ago ta kalleta tare da fad'in "Balkisu lafiya kuwa? " Ita ta kawo hakan " To allah ya kyauta"Amin mtssww
Balkisu allah_allah ake dare yayi tun kafin ayi sallahr magrib ta je tayi wanka, ta kakkamta komai, ta d'auko maganin ta shanye rabi sai d'ayan ta cusa a gabanta ango kawai take jira
Sadik koda ya dawo matse take da ya shigo d'akin, ta matsu taga komai ya kankama, al'adarsa ce inda ya dawo sai ya je ya gaida Mahaifiyar sa yayi masa sai da safe sannan idan bake ke aiki ba zai shiga ya miki sai da safe, da yaje d'akin khadija ya d'an jima a can sannan yayi d'akin ta,
Abinci ta kawo masa yaci, yana gama ci ya haye gadon yayi kwanciyarsa, tashi tayi ta cire komai na jikinta ta fad'a saman gadon ta kwanta saman sa, bacci har ya fara d'aukar sa yaji ta saman sa, juyowar da zaiyi yakai hancin sa saman kashin kanta, warin kan ta yayi wufff sai cikin hancin sa, ba shiri ya zabura ya tashi zaune, ganin yarda ya tashi yasa ta biyo shi tana fad'in "Lafiya"Girgiza mata kai kawai yayi alamar eh dan yama kasa bud'ar baki, k'ara matsawa tayi cikin sa tana goga masa jikin ta,
Khadija kwance tana juyi saman gado, bacci ya kasa d'aukan ta juyi kawai take yi, zuwa can ta tashi zaune tare da jingina bayan ta da gadon,tana tuna moment d'in su na jiya ita da sadik, wasu hawaye masu zafi taji suna zubo mata, tayi saurin sa bayan hannunta tana gogewa tare da furta " Sadik yanzu ba nawa bane ni kad'ai mijin mace biyu ne " Ta k'arshe maganar tare da fashewa da kuka mai ta'ba zuciya " Allah ka zamo gatan mu duniya da lahira" kuka take sosai har bacci yayi gaba da ita,
K'ara goga masa jikin ta take Shi kuma idan aka zo wannan fanni ba juriya ce da shi ba, dan haka ya bada kai bori ya hau, balkisu ta baza kunnuwa taji sambatu amman shuru takeji maimakon ma shi yayi sai ita ce ke yi, 'bangaren sadik kuwa haryanzu ya kasa sama ma kansa kamsuwa a wajen ta, Jin ta yake salaf_salaf sai tsakin da yake ja a k'asan ran sa, balkisu ita kad'ai ke jin dad'in wannan harka, har ya sauka a kanta bai samu wata gamsuwa daga wajen ta ba,
Balkisu anyi baje_baje an ware k'afafuwa, sadik ya kalleta tare da jan tsaki a ransa a fili ya furta " Tashi muje muyi wanka" Ya tsina fuska tayi tare da fad'in "Wallahi nagaji sosai sai da safe zanyi" Wankan? Ya fad'a cikin jin mamaki da furucin ta "Eh " kad'a kai kawai yayi ya fita dan tsarkake jikin sa,
Yana fita tayi zumbur ta Mik'e zaune sai yanzu ta tuna da wani zancen maganin da ta sha " Ah ah nafa sha maganin na to amman banga aikin da yayi ba to kodai ban shasa yarda ake Sha bane ko kuma sai goben idan na sake amfani da shi zai fara aiki, kai haka ne ma inaga sai an shanye baga d'aya zaiyi aikin Hhhhhhhhh allah ya kaimu gobe " Ta koma tayi kwanta sai bacci, koda ya dawo tayi bacci ya kwanta daga gefe, ya runtse idanuwansa, moment d'in su na jiya tare da khadija ya rik'a tunawa, murmushi ya rik'a saki shi kad'ai, a k'asan zuciyar sa yana ta suburbud'a mata ruwan albarka da haka har yayi bacci..........................................