Showing 6001 words to 9000 words out of 10897 words
ta d'auko jaka ta Mik'e mata naira dubu tace "gashi a siyo kayan miya da kayan ciki tun da akwai sauran kaya kayan miya ne kawai babu" kar'ba tayi ta fita taje mak'otansu ta samu wani yaro ta aike sa ta dawo takai redar shinkafar, nan tayin su
Tun daga lokacin suka shirya, muddin khadija na aiki to balkisu sai tazo ta tayata itama hakan take, sai dai abu d'aya wanda khadija ta lura dashi shi ne, balkisu nada shegen kwaud'ayi, sannan idan taga anata zuwa siyan kaya wajen khadija sai taga tana wani ciccin magani, alamar hassada
Sadik ne ya shigo gidan, d'akin khadija ya shiga yaga bata nan, d'akin balkisu ya shiga, yatsina fuska ya rik'a yi tare da bin d'akin da kallo, wai d'aki kamar ba mutum a ciki ya fara k'ura ga wani hanamin bashi_bashin da yake tasowa, ga kaunukan da akaci abinci nan zube tsakar d'aki har sun bushe, balkisu na kwance tana sharar baccin ta, girgiza kai yayi tare da jan tsaki mtsww ya fito daga d'akin, yana fitowa sai ga khadija, kallan ta yayi daga sama har k'asa sanye take da hijab har k'asa
Daga ina kike na duba ban ganki ba? " Daga wajen mama"okay, muje ki zubamin abinci " ka manta ba fa girkina bane " ina sane nidai muje " Bata nan ne? " Wani kallo yayi mata bata sake cewa komai ba ta wuce ya biyo bayanta, tana shiga d'aki ta kau'be hijab d'in ta, sanye take da riga da wando, Wandon ya matseta sosai sai rigar y'ar guntuwa idan ta d'aga hannun ta ana ganin cibiyarta, rigar kawai ce a jikin ta ko bre bata saka ba, wasu irin yawu sadik ya had'a, ya kasa jurewa sai da ya taso ya rungumota ta baya tare da zura hannayensa gaba ya d'ora akan na shanunta yana..................... juyowa tayi suna fuskantar juna, ta d'ora hannun ta a kafad'arsa tare da zagayowa, shi kuma hannayensa na kan k'ugunta, gira ta d'aga masa tare da fad'in " Yane nayi kyau" Sosai sosai kayan nan sun miki kyau" ya fad'a yana shin_shinan daddad'an k'amshin dake fitowa a wuyan ta, bakin su ya had'e waye d'aya ya shiga tsotsa ita ma ta biye masa sun d'au yan minutes a haka, ganin yanan san cire rigar da ke jikin ta yasa ta kaunce kanta daga gare shi tare da dai_dai ta natsuwar ta tace" Zauna na kawo ma abincin" wayyoooooooooo sadik ba haka yaso ba.................................
*ZUWA GARE KU MATA ✍*
Kishin da bazai qara miki..........................
martaba da kima a idon miji ba, kishin da bai sa kin samu qarin kusanci a wajen miji ba, kishin da ba zai sa ki qoqarin gyara da kyautata dabi'un ki ba, kishin da ba zai sa ki qara kusantar miji da mahaliccin ki ba, kishin da zai sa kimar ki ya zube, miji ya nisance ki ko ki nisanci miji da mahaliccin ki ko ki koma bibiyar 'yan tsubbu
Tabbas wannan ba kishi bane rashin hankali, rashin sanin daraja da mutuncin kai da qarancin tsoron Allah da son zuciya ne, muddin kika biyema irin wannan kishin tabbas zai kai ya baro ki duniya da lahira ko kiyi asarar duniya da lahirar ki.
*🤲YaAllah sa mu gane gaskiya ya bamu ikon binta*
_-_Perfectly Pen's_-_~*✊ 2024
*~_-_Perfectly Pen's_-_~*🤟
*Team One.*
*🌹 perfectly Pen's together with five Talented's ✍️✊*
*Our Ongoing Book's...✍️*
*1_PRINCE ASAD.*
*Free Book. BY: Zieey Dodo.*
*2_SHIRYAYYIYAR ƘADDARA.*
*paid 500*
*Season one Free. BY: Queen Kainaat.*
*3_TSANTSAN SO.*
*Paid,500. BY: Nainarh KD Nkd's.*
*4_MU ZUBA MU GANI.*
*Paid,300. BY: Oum Yasmeen.*
*Mun Shirya tsaf domin kawo muku daɗaɗan littattafan mu masu cike da ilmantar wa faɗakarwa tunatar wa wa'azantar wa har ma da Nishaɗantar wa.💝*
*🔥Kada ki bari wannan tafiyar ya kasance ba tare dake ba. Don't Miss It Dearest sisters 🔥
Abincin ta kawo masa yaci ya k'oshi, Sannan ya tashi ya koma kasuwa duk da ba ciniki, daya fito ko d'akin balkisu bai sake lek'awaba ya wuce, har yanzu ko tana nan tana sharar baccin ta,
Koda ta tashi daga baccin taga lokacin zuwan sa cin abincin harya wuce ta Mik'e ta fito khadija ta zaune tana gyaran waken suya " Aunty sadik bai dawo cin abinci ba ne? " Ya dawo mana ai har yaci ya koma" Okay shine bai tashe ni ba" To kinsan ba dad'i mutum na bacci a tadasa" Uhmmmmmm" ta fad'a ta koma d'aki, bud'e kulolin abincin tayi taga ba abinda aka ta'ba a ciki, ta sake fitowa " Aunty " Naam " kin ce ya dawo yaci abinci? " Eh " To ai ni banga anci komai ba cikin abincin " Eh dayake ba anan yaci ba wajena yaci " Bangane ba" balkisu ta fad'a a tsatstsaye " Kamarya kenan? Khadija ta fad'a tare da ajiye waken da ke hannun ta " Ahh to naga dai bake ke aiki ba taya zai je wajenki yaci abinci ai wannan salon munafurci ne " Yau ga ikon allah shin yazo kina bacci kuma yunwa yakeji yace nazo na saka masa abinci shikenan sai nace masa aah ko tunda ba girkina ba ne sai nabar mijina da yunwa bayan Kuma ina da abincin to wallahi ki sani koda bani da shi yazo wajena yace na saka masa sai naje na nemo masa rainin wayon banza kawai " Ah ah naga kina wani zazzaburomin sai kace wani abun na fad'a bancin kuma gaskiya na fad'a ke idan girkin ki ne namiki hakan zakiji dad'i? " Me zai Hana wallahi dan kinyi haka bazan ga laifin ki ba daga ma kin taimaka min kin basa wallahi ni nace balkisu muddin yazo gidan nan ranar girkina ya tarar da ina bacci wallahi jashi d'akin ki ki basa abinci ke har ruwan wanka kai masa abu d'aya kawai nasan bazan lamunce ba ranar girki na yace ya kwanta dake, bare nasan bazai aikata hakan ba dan yasan haramun ne bancin wannan wallahi ni ba abinda zai damuna " To nidai ban lamunce ba ehhheeeeeeeeeeee kowa yayi aikin sa ranar girkin sa " Ke balkisu wai ma da kika zo kika tasani gaba ni nace kije kiyi bacci sannan ki bari shi wanda ya aika tan idan ya dawo sai ki tasasa a gaba kiyi masa fad'a kar ya sake yin haka " Ai ni bashi yamin laifi ba bare kice na masa fad'a" Ohh wato ni ce nayi laifin ko" khadija ta fad'a tare da Mik'e wa tsaye" Ke naga kina son gayamin magana to wallahi bazan d'auka ba dan mai maganin ki ce a wajen nan ina san muzauna lafiya gidan nan amman daga alamun ke bakyada buk'atar haka muje a hakan duk yada ki ka zo nima dai_dai nake da ke a gidan nan " Magana dai ceee na fad'a ba uban da ya isa ya hanani fad'an abinda nayi niyya" To tsaya daga nan dan bana jurar zagin iyayena idan ba haka ba wallahi yanzu na ma mutum hailar baki " Hmmmmm wai hailar baki" To idan tantama ki ke kiyi ki gani wallahi bakin ki sai ya cika da jini " Balkisu ta bud'e baki ta sake magana khadija ta fere hannun ta wanka mata mari sai da ta fad'i, ta taso tayi cikin khadija, khadija ta samu taja k'afafuwan ta sai k'asa, balkisu ta fad'i khadija ta haye Samanta ta shiga dukan ta, da taji azaba ta fara ihu na neman taimako,
Mama da taji ihun balkisu yayi yawa yasa ta taso tayo wajen su, khadija ta gani ta kai balkisu k'asa ta haye sai dukan ta take da sauri ta k'arasa tare da fad'in " Subhanallah! Subhanallah khadija meyake faruwa ne? " Dak'yar mama ta samu ta raba su, balkisu ta koma gefe hawaye da majina sai ambaliya suke a fuskarta " Dan Allah gobe ki k'ara"khadija ta fad'a " Wai meya had'a ku ne ? Mama ta tambaya" Mama wai................................................. khadija ta zayyano mata duk abinda ya faru " Gaskiya balkisu bakya gaskiya ai dan ma abun bai miki dad'i ba ba ita ya dace ki yima magana ba shi zakiyi ma maga cikin hikima amman gashinan yanzu wa gari ya waya bakin ki harya fashe " Eh ina ruwan ki bak'ar muna fuka ai daman nasan goyon bayan ta zakiyi" khadija da mama suka Kalli juna mama ta girgiza kai, khadija tasa hannu zata janyo ta tayi saurin rugawa tayi d'aki tare da rufewa " Ai da kin tsaya k'aramar mara kunya kawai" khadija ta fad'a tare da juyowa tana bama mama hak'uri akan abinda balkisu ta fad'a
" Karki damu, amman kema ya kamata ki rik'a hak'uri ki rik'a sassauta zuciyar ki " To mama in Sha Allah...........................
Washe gari
Balkisu zatayi girkin rana, khadija ta kar'bi girki, gashi sadik bai bata komai na girki ba, da ya riga da ya rabar da khadija zata bayar dan yanzu bayada k'arfin da zai iya ciyar da gidan khadija ke ciyar dasu gabaki d'aya, dan haka yana tashi yayi tafiyar sa, zaune take bakin k'ofar ta tana maganar zuci, Hmmmmm gashi mun samu sa'bani jiya bani da daman da zance naje na kar'bo shinkafa na dafa to ya zanyi mtsssssssww kowa ya ci da kansa to koda ma ance haka ita me zata ci?
Ita dai khadija na nan na faman aikin tarbon miji ana had'a kayan gyara ( Kayan mata) bayan ta gama ta aika aka siyo mata cuscus da kayan ciki, tazo ta kashe girki mai rai da lafiya, ta had'a kunun ayar ta Wanda yaji kayan Had'i, su dabino, kwaukwa, kaninfari, minannas, mazark'aula, madara......................................... balkisu ana zaune sai had'iyar yawu ake ( Hhhhhhhh abun ka ga mai kwaud'ayi )..............................
Wannan page d'in sadaukarwa ne a gareku masoya na nakusa da na nesa much love for you fisabillilah ♥️♥️♥️ ♥️ ♥️ 🌹 🥰🥰🥰😍 🌹 🌹🫶💝, ina jin dad'in comment d'in ku i really appreciated, dan hk ku k'ara k'aimi wajen comment nima zan k'ara muku tsawon update 💃💃💃💃💃kun ji a taimakawa mar'atussaliha🧕💔💔♥️ comment d'in ku shine k'arfin guiwarmu😍 love you fisabillilah
Bayan ta kammala ta zuba ma mama taje ta kai mata, ta dawo takai sauran d'akin ta, ta fito tayi shimfid'ar ta waje ta zauna, anata zuwa siyan kaya,
Balkisu an gaji da zama ta shige d'aki ta kwanta, sadik koda ya dawo ya tarar da khadija tayi shimfid'a waje tana zauna, ya samu waje ya zauna kusa da ita, tayi masa sannu da zuwa tare da fad'in "Ya kasuwa? " Hmmmmmmmmmmm to alhamdulillah za'a ce dan yau an d'an siya abu, ya fad'a tare da sa hannu a aljihu ya ciro d'ari biyu " kingan ta wallahi tun safe ita kad'ai aka yi, ya fad'a tare da nuna mata kud'in" Ohh subhanallah allah ya kyauta hak'uri zaka ci gaba dayi in Sha Allah komai zai dawo dai_dai "Hmmmmmmm to allah yasa khadee ki duba kiga yanzu fa ko gidan nan bana iya ciyar da ku, ya fad'a cikin raunanniyar murya " Ga sauran hak'k'inku da ya rataya akaina amman duka yanzu bana iya sauke ko d'aya allah ka kawo muna mafita"
Khadija ta matso kusa da shi ta d'ora kanta a kafad'arsa tare da fad'in"Amin ya rabbi dear kar ka damu muddin ina da shi to kaima kana da komai nawa naka ne duk abinda kake so ka tambaya indai bai fi k'arfi na ba zan baka "Nagode sosai matata ko wannan d'awainiyar da kike damu ta isa bana buk'atar komai allah ya miki albarka yasa albarka a cikin sana'ar ki "Amin ya Allah, ta kai bakin ta dai_dai kunnesa tana magana " Dagaske? ya d'ago yana kallan ta, gira ta d'aga masa tare da kanne ido d'aya" Ki ce yau akwai shagali " Sosai ma" ta fad'a tana dariya na zuboma abinci? " To lallai kam"okay "
Tashi tayi taje ta kawo masa tare da kunun ayar da tayi ya d'au sanyi, yana ci yana zuba mata albarka, ita kuma tana gefen sa tana masa fifita, bayan ya gama zai koma kasuwa ta basa dubu bakwai, tace, anjima idan zai dawo ya biyo musu da kaji
Balkisu koda ta tashi daga bacci bata tsaya bincikar sadik ya dawo ba ko bai dawo ba dan ko yunwar da take ji kad'ai ta isheta, cikin ta har k'ugi yake, zama tayi bakin k'ofar d'aki sai rabon ido take, khadija na lura da ita, tasan yunwa take ji " Hmmmmm ni dai bazan d'auko nace Miki gashi ba amman idan kika zo da kanki kika nema bazan hana ki ba " khadija ke wannan maganar a zuci,
sake Mik'ewa tayi ta shige d'aki tayi tsaye, tana waige_waige cikin d'akin ko zata samu abinda zata saka ma cikin ta, tsaki taja mtsssww tare da fad'in "Kai gwaunda kawai naje wajen ta ko zan samu haka ma za'a yi, ta fad'a tare da fitowa daga d'aki kai tsaye wajen khadija ta nufa tare da zama " Aunty khadija iska ake sha haka"Eh, ta bata amsa a tak'aice " Ko akwai aikin da za'a miki ne " Babu" To aunty khadija daman nace dan allah, tana Fad'a tana sosa kai kamar wata tsohuwar muna fuka, dan allah idan kina da abinci ki sammin wallahi yunwa nakeji sosai " Okay kawo filet" da sauri balkisu ta Mik'e taje ta kawo filet, khadija ta kar'ba ta sako mata, kar'ba tayi tana godiya
Khadija ta tashi ta gyara murhu, dan d'aura abincin dare, tuwon d'anyar shinkafa ce zatayi da miyar ganye, cikin k'ank'anin lokaci ta kammala girkin, miyar taji kayan Had'i sai k'amshi take zubawa hmmmmmm khadija badai iya girki ba, k'arfe takwas da rabi sadik ya dawo da gasassaun kaji manya guda biyu, ya Mik'a ma khadija, ta raba d'ayar biyu tace d'aya mama d'aya balkisu d'aya kazar kuma ni da kai, ya d'auki na mama yaje ya kai mata ya dawo ya d'auki na balkisu, koda je d'akin ta har tayi bacci tsaki yaja mtssssww "ita wannan wai bata gajiya da baccin na ne Haba" ledar kaza ya jefa mata, tayi firgita ta farka tana murza ido " Sannu da zuwa"Yawwa ga naki nan " Miye a ciki? " Idan kika bud'e zaki gani, yana gama fad'in haka ya juya ya fita
K'amshin da taji yana bugun hancin ta yasa ta saurin Kai hannu ta d'auko ledar ta bud'e, idanuwan ta sukayi arba da kazar ta saki wani lallausan murmushi tare da lashe la'b'banta kamar tsohuwar mayya "Shege ashe dai yana da kud'i " (🙆🙆🙆🙆wai miji ake cema shege balkisu kinga ta kanki hhhhhhh)
Tuwo ta kawo masa sai da yaci ya k'oshi, dan yana son tuwon d'anyar shinkafa gashi kuma ta samu lafiyayyar miya, ta kawo masa kazar bai wani ci da yawa ba dan ya k'oshi, ita ma bata ci da yawa ba tasa sauran cikin fridge harda da safe sai ta dumama masa, daga nan suka wuce cikin d'aki suka fara gudanar da ibadar aure,
Balkisu an cinye har an fara bacci, kamar wacce aka tsikara cikin baccin ta, ta rik'a jiyo ihun sadik, ta tashi tayi zaune can ta sake jiyo shi, yana sambatu saman khadija tashi daga falo tayi taci cikin d'aki, bangon d'akin su d'aya da khadija taje ta tara kunnen ta kamar wacce za'a fad'a ma magana a kunne, hawaye taji na yawa a saman kumatun da dan abinda kunnuwan ta suka ji baki bazai iya fad'an su ba, ganin idan ta tsaya nan har abinda yafi kuka zata iya yi yasa ta koma falo ta zauna "Babu munafukin Allah kamar wannan mutumen wato ni in yana d'akin nan bayamin irin wannan sambatu nidama nake amarya amman sai wannan wacce ta kwana dubu hmmmmmmmmmmm to wallahi bazata sa'bu ba..........................................
_-_Perfectly Pen's_-_~*✊ 2024
*~_-_Perfectly Pen's_-_~*🤟
*Team One.*
*🌹 perfectly Pen's together with five Talented's ✍️✊*
*Our Ongoing Book's...✍️*
*1_PRINCE ASAD.*
*Free Book. BY: Zieey Dodo.*
*2_SHIRYAYYIYAR ƘADDARA.*
*paid 500*
*Season one Free. BY: Queen Kainaat.*
*3_TSANTSAN SO.*
*Paid,500. BY: Nainarh KD Nkd's.*
*4_MU ZUBA MU GANI.*
*Paid,300. BY: Oum Yasmeen.*
*Mun Shirya tsaf domin kawo muku daɗaɗan littattafan mu masu cike da ilmantar wa faɗakarwa tunatar wa wa'azantar wa har ma da Nishaɗantar wa.💝*
*🔥Kada ki bari wannan tafiyar ya kasance ba tare dake ba. Don't Miss It Dearest sisters 🔥*
Balkisu ta jima zaune taci kukanta sosai, zuciyarta kamar zata fito, da haka har bacci 'barawo yayi awon gaba da ita,
*'Bangaren su khadija*
Yau ta kashe sadik da dad'i, ga styles d'in da ta rik'a masa kala_kala wad'an da suka k'ara zautar da shi, ya rik'a mata sambatun dad'i, sun jima suna abu d'aya sannan ya barta suka fito suka yi wanka tare da tsarkake jikin su, suka koma d'aki, khadija kwance saman jikin sa, suna kallan junan su, murmushi ta sakar masa tare da fad'in " Wannan kallan fa? Sai da yaja numfashi kafin yace " Wai daman kin iya irin wad'an nan styles d'in ko koya miki akayi " Sai da tayi dariya sannan tace " Uhmmmm na iya mana ba wanda ya koyamin "Amman shi ne baki ta'ba min ba to daga yau ina expected d'in su gare ki"Kar ka damu dear gobe ma akwai sabbin styles wad'an da na tanadar maka"Dagaske honey ? d'aga masa kai tayi alamar eh " Wayyoooooo allah na shiyasa nake k'ara son ki matata kice gobe zan k'ara Sha dad'ina" ya fad'a tare da kai ta'b'bansa ya d'aura a sana yashiga tsotsa ita ma ta tayasa yaja musu bargo ya rufe su
*Washe gari*
Bayan ta gama had'a musu breakfast ta dumama kazar jiya, ta bama sadik, balkisu ta fito duk haushin su take ji anyi tsinin da baki kamar ya ta'bo sama, tana lura da khadija da sadik ta zarar sun had'a ido sakarma junan su murmushi wanda ta rasa gane ko na miye, nan take ta k'ara k'uluwa, ko ina kwana batama sadik ba bare kuma khadija,
Har ya gama karin sa, yayi shirin fita ganin bata gaidasa ba yasa sa zuwa wajen ta tare da fad'in "Kin tashi lafiya? Tun da ke bazaki iya gaidani ba ni bara