Showing 18001 words to 21000 words out of 29604 words
auren aneesa da ishaq.
dayake makirace duk kwarewarka wajen bin diddigin abunda ke kunshe aranta bazaka taba ganewa ba.don azahiri kam tana nuna tsantsar kaunar zahra abinda kenan yake karamata kima acikin idanun ishaq dr.rukayya kai harma dasu umma inka dauke anty lubnah dake kallonta kar!.
ranar asabar wanda yayi dai-dai da zamowa sati biyu cif da kwanciyar zahra asiviti dr.rukayya dakanta tabasu sallama don dai amarya zahra ta warware tas bakace tataba samun wata matsala a tattare da itaba.
dama ta'kosa abasu sallama don jinta take kamar a prison,musamman dasu ummilolo sukazo gaisheta suke bata labarin gulmarta da lami takeyi wai ance ta haukace.
kaii ranar zahra tadanna mula-mulan zagi takuma ba ummilolo sallahun cewa tayima lami brush da kashin kaji kafin a sallamota.
ummilolo ta'amsa da to,
dayake lokacin dakin bakowa sunje sallah ,sukabar ummilolo ganin zata taya zahra zama.
ranar dasuka dawo gida ishaq jiyake kamar yayi kuka don ba karamin shakuwa yayi da zahra ba.
mummy yasama idanunnan sun canja kala tanan kawai zaka fahimci damuwarshi,
kallonshi take cikin kulawa yanda ya langwabe kai,ahankali ta rike hannunshi tace"akwai damuwane ishaq?"
tayi tambayar bayan ta tattara dukkan hankalimta gareshi
sauke numfashi yayi yana shafa sumar kanshi a hankali,sai da yadan samu natsuwa yace"mummy shikenan yanzu idan zahra takoma gida sai yaushe?"
kafeshi da idanu tayi kafin tace"sai randa mahaifanta suka nememu mana."
dasauri ya kalleta saikuma yakoma kalar tausayi dafadin"haba mum pls kisaka baki kawai awuce da ita dakinta ".
baki sake dr.rukayya take kallonshi tana fadin"eh meko zaihana ayi hakan tunda nice kakar mashirmanta ba."
rike hannunta yayi yana rokonta"pls mum,banaso yarinyar nan tana nisa dani pls"
yakarasa maganar kamar zai saka mata kuka;
yunkurawa tayi danufin tashi"kaga sakemun hannu nisam ba'ahaka dani."
"kayi hkr idan takara samun karfin jikinta dakansu zasu nememu,ai sunada hankali ba yara bane."
tana gama fadin haka tayi gaba abinta batare datako sake waiwayar inda yake ba.
kifa kanshi yayi akan karamin teburin ofis din,Allah ne kawai yasan meyakeji dangane da zahranshi.
itako zahra murna hada tsalle aranta tana kissima saitaci uwar dije tabbas don ita bata barin kota kwana.
har suka gama shirinsu tsaf bataga gilmin ishaq ba,saikuma duk taji babu dad'i,takasa daurewa. takamo hannun dr.rukayya dake yima umma bayanin wasu magunguna.
juyowa dr.rkyn tayi,ganin zahra tasaki murmushi tace"yadai d'iyata zahra?"
zahra takasa daurewa idanunta sunyi kwalkwal da hawaye tace "mummy ina yake?"
dr.rky ta kalleta da rashin fahimta tace"wakenan?"
zahra ta amsa"wannan d'an gayunnan wanda yake bani chocolate da ice-cream;baki sanshi ba?"
tayi tmbyr tana kallonta"dariya dr.rky tayi tace"sunanshi yaya ishaq kinji haka zakike kiranshi".
gyada kai tayi,alamar gamsuwa saikuma tasake maimaita question dinta"to yana ina?"
dr.rky tace kiyi hakuri zaizo kinji ko?
gyda kai tayi kawai takoma tazauna jiki ba kwari sam.
har suka isa bakin mota ishaq baizoba dr.rky ta kira number dinshi.
da sanyin jiki ya daga calling dinta tace"toka fito zasu wuce....
manage for this.
*mum meenat*✍????
[12/7, 1:02 PM] +234 703 895 3431: *MIJIN 'KWAILA*????????♀
chapter 21.
*written by maman meenat*????
*edited aysha abdullahu,*
(umman faruq).
*MODERN HAUSA NOVELS*
*MIJIN KWAILA FANS*
*M.MEENAT NOVELS*
*WANNAN SHAFI KYAUTANE GAREKU SISTERS"*????
*Wallahi dashi ake samun natsuwa,yawaita yinshi yana kara imani,yana sanyaya zuciya.*
*wallahi kika/ka lazumceshi bakada kaico!wlh muddin ka lazumceshi zaibaka farin jini natsuwar ruhi,kwarjinin fuska ,zaisaka yawaitar arziqi duniya da lahira...*
*BAKOMAI BANE FACE SALATIN ANNABI(SALLALLAHU'ALAIHI WA SALLAM.)*????????
"Toka fito zasu wuce"
maganarta ta doki dodon kunnenshi,
"to"kawai ya'iya furtawa,saikuma yaji wani kwarin gwuiwa ya ziyarceshi.
mikewa yayi saida ya rufe mata office din yanufo harabar asubitin,
akoridon dazai sadashi da farfajiyar asibitin yacikaro da aneesa wadda ta tsuke cikin riga da sket nawani jan material,
asamansu tad'ora siririn gyale kalar flowers din kayan.
fuskarnan with full make up.
bayaga katon sun-glass daya mamaye rqbin fuskar tata,
tun daga nesa kamshin turarenta yagama bud'e hancin ishaq.
kallo d'aya yamata yasake tsuke fuska,tatako tamkar tarwada yanda take kada jiki.
gilashin fuskarta tacire ta kafe ishaq da shu'uman idanunta datake wana maza dasu,ganin yasake hade rai yasakata sakin karamin smile tare da tare hanyar dayake kokarin ratsewa ya wuce.
karyar da wuya tayi,cikin salonta namatan dasuka kwankwadi karatun yahudu tace"hada ya ishaq don allah yanzu da gaske saika wuceni bako gaisuwa"?
yanda tayi maganar a shagwabene yasakashi kallonta.
sarqa idanunta tayi cikin nashi kafin tace"waito miyene laifine,kawai donnace inasonka?": "haba ishaq,wlh inaji kamar bazan iya rayuwa ba idanna rasa ka."
tayi shiru don tuni muryarta tafara rawa,
ganin bai tankaba yatsareta da gold eyes dinshi yakara sakar mata da jijiyoyin jiki.
jitake kamar takamashi da karfin tsiya tayi hugging nashi,duk idan ta kalleshi takanyi imagining yanda zatayi luf a faffadan kiejinshi.
"ishaq,"
takirashi dai-dai lokacin data rungume hannayenta akan kirjinta.
kallon daya batane yasakata hadiye miyau bata shiryaba.
idanunta suka kawo ruwa cikin taushin murya tace"don Allah na rokeka katsakurarmun koda kankanin gurbine axikin zuciyarka.nasan kasan menene so,babu bukatar saina fayyacemaka menake ji dangane dakai.sonka azuxiyata natabbata jarabane don nakasa samun matsayi daga gareka.
jiyayi tabashi tausayi,amma daya tuna zahra saiyaji sam bama zaifara kwatanta sonta dana wata ya mace ba.
ya runtse idanu lokacin dayake tunano kalaman late zahranshi’’ _ya ishaq kasani zahra takace kai kad'ai inason kaima ka'ajiye aranka cewar kai kadaine na Azahra don banajin zan iya sharing dinka dakowace mace.ina tsananin kishinka yayanah_.
sauke ajiyar zuciya yayi,yad'ora da fadin"kiyi hakuri aneesa natabbatar kinada masoya da yawa kibama wani dama acikinsu.ni amatsayin kanwata na daukeki."
kallonshi take kasa-kasa,acikin zuciyarta tana ayyana ishaq amatsayin mutum mara tausayi dakuma sanin darajar soyayya.
sam batayi auneba ta hangoshi ya wuce abinshi
bin bayanshi tayi da kallo;lokaci guda tajingina da vango don jirin datakeji yana barazanar kayar da ita.
juyawa tayi da sauri ta nufi ofis din aysherh wadda take zaune tana duba patients, cikin shagwaba da sangarta aneesa tafada ofiz din batare da tunani ko daukar izini ba.
bata damu da ganin mara lfyr da aysrh ke dubawa ba tafada kan cinyarta gami da sakin kuka me tsuma rai,harga Allah tanama ishaq so mai zafin gaske.
adaburce ayshen tagama duba mara lafiyan da bada iznin kada wanda yakuma shigowa tanada uzuri,
rungume aneesa tayi tanadan bubbuga bayanta ahankali tace"meyake faruwa ne baby?"
anee cikin muryar kuka take magana"haba mum sai yaushene zaki tabbatarma duniya cewa ishaq nawane? sai yaushene zaki nunama duniya cewar dani ishaq yafi dacewa, yaushene sunanshi na *mijin kwaila* zai dusashe yazamo mallakina",pls.mum inajin kamar lokacin mutuwa tane yazo muddin narasa ishaq,bqna zaton sake farin ciki arayuwata madamar bana tare da ishaq mum pls help..."
kuka yaci karfinta takifa akan teburin ofis din tana tsiyayar da hawaye sosai.
dr.aysher tamike tasoma zagaye ofis din cike da tashin hankali;saqawa take tana warwarewa dolene tacikama anee burinta koda shine abuna karshe dazata aikata aduniya, kai koda duk abinda ta mallaka zai kare saita nunma dr.rukayya karshenta don tasan inda rukayya ta'amince da auren ishaq da anee toda bai isa ya bijire ba.
komawa tayi ta zauna ahankali gami da dafa kan diyar tata xike da rarrashi.
: zahra kam harta shiga mota tana waiwayen ta'inda ishaq zai bullo,
can ta hangoshi yana doso motar dasuke.
dasaurinta ta balle marfin tafita kaitsaye runguneshi tayi,tsayinta baikokai a kirjin ishaq ba.
cikin dariya take fadin"shine kaje ka 'boye ko? hmm damunyi tafiyarmu bazaka sakeee ganina ba."
tafada tana sakarmashi murmyshi,
kama hannayenta yayu,yasaita tsawonshi danata tahanyar durkusawa yace"kalleni zahra".
qura mashi idanu tayi batako kyafta ba.
ya sauke numfashi ahankali yace"i love yhu,i love yhu with all my hrt zahra, ican't life without you zahra,"
zahra ta kwashe da dariyarta da fad'in "hu'umn,kainifa ban iya turanci ba.mudai anty dinmu tana mana karatun reader ne kawai,barima kaji a father and his son...."
bata karasa ba ishaq yasake matse hannayenta yace"zahra kiyimun alkawari zaki rayu dani rayuwa ta har abada.zaki kasance abarin damana aduk matsayin dana kasance bazaki gujeni ba?"
zahra kwalalo idanuwa tayi saikuma tama'ke kafada tace"amma inka yarda zaka dinga goyani yanda ummana takeyimun da banida lafiya?"
tafada hadi da tafa hannayenta dakuma birkicesu tahada gaban hannun da bayan,yanda yara sukeyi idan abu ya kayatar dasu.
ishaq dariya tabashi ya lakace hancinta dafadin"zangoyaki abayana zahra,zanmaki dukkan abinda kike bukata dangane dani,zan maki koda wankane da wank...."
bai karasa ba zahra ta katseshi ta hanyar cewa"kuma zamu dinga hawa bene inka yarda,"
ya gyada kai.
"hardama kwamfutar wasa zan siya maki."
yadai lura akan zahra babu komai sai tulin kuruxiya.
tsalle.tayi tadare bayanshi.
dai-dai lokaxinne anee da dr.ayaherh suka karaso wajen.
wani kallo aneesa ta watsama zahra mecike da zallar kishi da tsana....
*maman meenat*✍????
[10:36AM, 11/25/2017] maman meenat????: *MIJIN 'KWAILA*????????♀
Chapter 22.
*written by maman meenat*
*edited aysha abdullahi* (umman faruq)
*Hakika kalaman baki basu isa furta matsayi da girman kimarki a idanuna ba,aysha umman faruq kedin ta dabance.matsayinki da kwazonki gareni hakika sune suka taka muhimmiyar rawa wajen bani kwarin gwuiwar himmatuwa akan rubuta wannan labarin,kin nunama maman meenat kaunar da bazata taba mantawa dake ba.Allah yaraya maki yaranki yaahirya su ubangiji yabarki da abban hyidar aci gaba da soyewa*
*wolla sister ina kaunarki,wujiga-wujiga*????????.
*Anty hajjaris mtn*
*Anty badiyya*
*kuna ina?, this page is dedicated for u sisters.tnks for ur luv and care am really appreciate.*????
wani kallo aneesa ta watsama zahra me cike da zallar kishi da tsana.
jitake kamar tamakure zahra don takaici,
kallo daya zaka mata ka tabbatar da ainahin abinda ke zuciyarta.
itadai umma ganin abinda zahra tayi yasata juya kaida sauri donkunyace ta rufeta.
dr.rukayya kam dariyq sosai take musamman ganin datayi damnata yashiga nishadi cikin kankanen lokaci.
hango dr. aysher datayine yasakata tsagaita dariya takarasa wajenta da sauri,kama hannun aneesa tayi wadda ke.kauda kai cikin daure fuska,duk da sanin da dr.rukayya tayi cewar tatsuniyar gizo bata wuce koki bai hanata sake tambayar aneesa damuwarta ba.
anee kam gani take dr.rukayya tama raina hankalinta don haka saita kauda kai gefe amma har lokacin tanajin zafin yanda zahra tawani dane bayan ishaq saitake ganin kamar da gayya.zahran ta aikata haka,itadai zahra ko ajikinta wai antsikari kakkausa.
dr.aysher da dabara tatake yatsun kafar anee dana hararta kasa-kasa,
daga bisani tasaki dariyar dabatakai ciki ba tana kallon rukayya"hm mummy kibar aneesa da rikici wai tana fushine na hanata zuwa abuja,nace tayi hakuri sainan gaba."
tayi maganar tana sake kyaftama aneesa ido,
aneesa kam gefe ta harara gami da kwace hannunta cikinna dr.rukayya tayi gaba abinta.
zata iya barkewa da kuka muddin zataci gaba da kallon salon tacewar da ishaq yakeyi da zahra agaban idanunta.
azuciye tagifta ishaq wanda baimasan tanayi ba,hankalinshi nakan zahra dake zubamashi surutu.
dr.rukayya kam bayan anee tabi da kallo,saikuma tasauke ajiyar zuciya tana kallon dr.aysher da idonta yasauya kala don tausayin tilon diyarta da Allah ya jarabta da *son maso wani*
[11:50AM, 11/25/2017] maman meenat????: sauke ajiyar zuciya tayi,kafin tasakala hannunta cikinna rukayya tace"bazan sake maimaita kalmar rokona akan cewar ishaq ya auri aneesa agareki ba,amma zanyi kuka mai yawa dakuma rataya alhakin hakan akanki duk ranar da'akace yau gashi wata lalura takama aneesa akan son ishaq.
zankuma dora alhakin rasa aneesa akanki matukar tarasa ranta tadalilin ishaq."
tasharce hawayen dayake fita idanunta tadora dafadin"natabbata duk nagartar dan adam yanada makusa rukayya,taki makusar itace babu abinda kike fifitawa fiye da kanki.
kinason kanki dayawa,kinkasa nunamun cewar aneesa diyace awajenki,farin cikin ishaq yafi rayuwar aneesa muhimmanci agareki.
tadan tsaigaita kafin tadora dafadin"kitaimakeni kitallafi rayuwar tilon diyata aneesa, bana burin rasata kamar yanda narasa yan'uwanta kinsan komai rukayya."
tausayinta yacika zuciyar dr.rukayya tasake makale hannunta cikinna aysher tace"tursasa ishaq ya auri aneesa bashine zai kawo maslaha acikin lamarin ba.aneesa tasamu kwanciyar hankali agidan aurenta shine abu mafi girma daya kamata ki tunkara,bana zato ko tunanin idanna matsa ishaq ya auri aneesa tahakanne kawai zai kwantar da hankalinta."
jaye hannunta aysher tayi tana fadin"kizauna kiyi tunani yazakiji da'ace iyayen zahra sun hana ishaq aurenta,?
wanne kunci zakiji acikin zuciyrki,?
ki kwatanta hakan akan kaina,na tabbata zaki gane menake nufi."
tana kaiwa nan tayi gaba abinta batare datasake koda waiwayar inda dr.rukayya take ba,
mota tashiga inda aneesa take zaune takifa kai tsakanin cinyoyinta tana gunjin kuka,zafi sosai zuciyarta kemata.
watakila damarta ta karshe zatayi amfani da ita akan zahra,irin dai damar datayi amfani da ita akan late zahra.
tasauke ajiyar zuciya jin andafa bayanta kobata waigoba tasan kowacec;
dago jajayen idanunta tayi tadora akan fuskar mahaifiyar tata tace,"dole zan mai-maita abinda na aikata abaya mummy,duk da alkawarin danayi akan natuba bazan sake ba,amma kisani bazan yarda ingama niqa wata takwashen gari ba.
naso ishaq tunkafin insan menene so,
mezesa insake rasashi akaro na biyu?
bana zato ko tsammanin zan'iya hakan mum ican't."
tafada har lokacin idanunta basu bar zubar hawaye ba.
"bazamu sake maimaita kuskuren mu ba aneesa, cewar dr.aysherh.
"amma kisani damata takarshe da itane kawai zanyi amfani;."
gyada kai anee tayi,lokaci guda tabi motar su zahra data giftasu da idanuwa,ahankali tasaki gajeren murmushin daya fito tare da guntun hawaye ita kadai tasan abinda ta kudurta acikin zuxiyarta.
*****************
Kwanci tashi asarar me rai,ahaka muketa cinye lokacin mu,guzurin mu nadada 'karewa yayinda tafiyar take dad'a nisa.
gaduk mai hankali idan yadubi yanda lokaci yake gangarawa yanzu zaigane lallai tabbas duniya tana gudu.
acikin murginawar lokacin muka tsinci kqnmu asati nabiyu cif da sallamo zahra daga asibiti,
abunfa saidai hamdala don zahra kam tayi natsuwar dole,to tadolece mana tunda umma tasakamata takunkumin bashiga ba fita.
akoda yaushe dai tana makale gida tana kamama umma wasu ayyukan gida.
duk da harga Allah jitake tamkar tana prison ne musamman idan tajiyo zazzakar muryar ummilolo tana rera wakensu dasukeyi idan za'ayi wasa"liyoooo y'an wargi liyoooo,ya wasan dare darana yake,ke uwande kizo muna kira,ke dije kizo muna kira,ke zahra kizo muna kira inkinqi kisha bugun jiya......"
ai tunkafin ummilolo tadasa aya jikin zahra zaifara kyarma,so dayawa takanyi attempting fita amma dataje zaure saitaga ansakama gidan sakata, wannan yasa tadena fita kwata-kwata takanjiyo su ummilolo suna buga gidan amma sai umma taleka ta wargadesu aguje zatajisu ridididi sun ruga.
akan zauna wani lokacin tamike kafafu tayita barza kuka,amma umma saitaba banza ajiyarta.
saukinta daya dayake ishaq koda yaushe yakan zo musamman idan yatashi aiki da wuri,wannan tasa tarage kewa don zaunawa yake yabiyemata suyita tafka shirme.
ahaka bakaramin sabo tayi dashi ba.
itama umma sosai take nata bakin kokarin wajen jawo zahra ajiki tanakara nuna mata abinda yadace dakuma yimata nasiha musamman akan yawan jarabar fadanta.
todai kusan nasihar umma zamuce wata tana samun shiga watakan tanabi tanan????????tafita tanan din dai????????????...
Kwana biyu da dawowar alhj saifullahi mahaifin ishaq daga cairo ya tuntubi rukkayya da maganar tarewar zahra,
itadai cewa tayi batasan komai akai ba.
iyayen zahran basuce komai ba,
alhj saifullahi dakanshi ya tuntubi ishaq akan yakamata zahra tatare tunda ta warware,
ishaq jiyai kamar anmashi bushara da Aljanna don haka yabar wuka da nama a hannun dady din.
Dadare kuwa dady yasamu abba agida bayan sallar isha'i kamar yanda ya alkawarta.
Abba yaji dadin yanda suka nunamashi kulawarsu akan zahra don haka yace"Ai alhj da zahra da ishaq duka nakane don haka kayanke duk lokacin dakaga yakamata in Allah yaso zata tare."
Alhj saifullahi bakaramin dadi yaji ba yace"totunda abun yqzama haka nasaka nan da sati guda,aiba wani dogon sha'ani za'atsaya yiba."
Abba yace"kwaraima kuwa,kuma kasan aure yafi albarka idan aka takaita almubazzaranci aciki."
dady ya gyada kai yadora dafadin"duk meke kawo wannan fituntunun idan ba saka riya acikin aureba,kaga masu kudi basu kira malamai sunyi wa'azi a auremsu ba amma sunkira mawaka fiye da ashirin.da'anyi magana ace ai zamanine."
dariya abba yayi yace"to'ai gashi tun ba'aje ko'inaba anbama shedan lasisin zama na dundundun agidan ma'auratan karshe saikaga auren tun ba'aje ko'inaba anata samun matsala."
musamman dama angama shashanci awaje to abu kadan saikaga zargi yana shiga tsakanin ma'aurata.
tun ba'aje ko'inaba saikaga anfara marin juna dq nuna ma juna yatsa."
dady yayi tsaki yace"barta nunama juna yatsa yanzu gashi har anfara kisa,amma abin haushi mutanenmu sunma maida abun abun wasa da tsokalar juna dashi."
Allah ya kyauta"
cewar abba dayake mama kin abun.
(nimadai nace amin)
koda abba yadawo yasanar da umma yanda sukayi da dady fatan alheri tayi,sannan taroki abba daya sanarma sauran yayun zahra zuwa da safe.
hakan kuwa akai ranar juma'a takama ranar zahra zata tare but umma tahanata gayyar kawaye.
*mum meenat*✍????
*for any corrections;comments or complain about this buk you should contact me as 07014709470.pls wtsapp only*...????
[8:02PM, 11/27/2017] maman meenat????: MIJIN 'KWAILA????????♀
chapter 23.
written by maman meenat????
Awannan ranar kam inkaga zahra sam bazaka shaidata ba don kyawon datayi,
donma matsalar duk yanda su anty lubnah suka dage akan tabari sumata kwalliya mekyau amma fir zahra kin amicewa tayi.
shigewa daki tayi abinta tajawo tarkacen kwalliyar tazauna bakin gado tasoma dankarama fuskar tata foundation yakama fuskar yayi shanana dashi don bawai tayi blending dinshi bane.
powder ta dauko no 1.memakon number 3,matsayinta na baqa tadora saiya kasance kalar powder din yafita davan da kalar foundation.
kwallima data shafa hawayen masoyi tayi;wato tajawoshi har gefen kunnenta.
asannan tasoma tsara eyebrow dinta,dafarko tafarashi kamar abin arziki sai-dai mamadin tayi using eyepen wajen yin brow din saita dauki kwalli kajal tasoma zanawa akan girar tata data kasance mefadice datsayi bayaga yalwar gashi da Allah ya yalwanta mata.
Agaban giran tayishi mefadi sosai yazarce kima saikuma tayi tsakiyan dan siriri dashi karshen girarma sai tayishi kwalele,don haka shape din yafita kamar tabarya.
ja sosai na lipstick tasakama lips nata masu taushi,
bayan tagama zageye bakinnata da bakin kwalli
tsuke bakin tayi tana karkata fuska aganinta babu yana biyunta wajen kyau.
dankareren leshin jikinta dayasha dinkin riga da sket yamatukar amsarta.
kalar flwers na less din shine kalar siririn mayafinta hakanan takalminta duk kala dayane cikas dinta kawai kwalliyar.
yanda tafito tana takawa das-das yajawo hankalin matan gidan,duk da kasancewar umma batayi gayya ba illa yan uwanta dana abba hakan baihana gidan xika da yan ganin kwakwaf ba.
wata daga cikin abokanan wasan zahrance ta rangada guda lokaxin da idonta yasauka akan zahra metahowa cikin tafiyar yanga.
sahura ta sake rangada guda dafadin"tofa ga amarya agidan ishaq nan tafito,barka dazuwa sarauniyar isiyaku.,"
zahra ta farfara mata idanu dazummar wucewa,amma sahura donta tsokaleta tace"wai wannan kwalloya haka saikace wata ba'indiya zahra."
zahra ta juya manyan idanunta dafadin"aidai nayi kyau ko?."
sahura tace kwarae ma kuwa,don wannan da angon zaiganki wata kila tun daga yau ali zaiga ali."
sauran mata suka kwashe da dariya,
wata daga cikinsu tace"aifa lallai,yaganta tu'bul-bul yazata wata gara zai kwasa;Allah sarki inama inzama sauro inmakale insha kallon gwagwarmaya."
sahura tacafe,"yo ni amaryar banmayi zaton tasan harkar ba ai."
umma tafito daga daki tanama sahura dakuwa tace"kinci gidanku sahura,yazaki sakamun yar auta agabane wai eye."
sahura tana dariya tace"allah umman zahra kibani ita insakata daki
inmata yar nasihar nan tamu ta manya watakila ashawo kanta.
umma gaba tayi"kyaji dashi dai."
su anty hafsa ne suka shigarma zahra akayita caccakar juna.
hakan yabama zahra damar sulalewa tafita babu wanda yasani.
akofar gida tayi kacibis dasu ummilolo anrasa gwanin dazai ahiga gidansu zahra kowa yana tsoron unma.
dasauri zahra takarasa ta basu hannu suka kashe tadubi uwande datasaki baki tana kallonta tace"dalla lafiya kike kallona,konaci ban biya ba."
uwande ta washe hakora tace"uhm ganinai kinzama yar gayu wlh."
dariya zahra tasaka kafin tace"yara kuma bakuda wayo kuce aimuku aure irinnawa,yara gidan bene zankoma inta kwana acan."
ummilolo tadanyi sakale,saikuma tasaki dariya"su zahra yan gayu za'asha dadin bene."
zahra ta kyalkyale da dariyar jin dadi,
ummilolo tace"dama ace nice zahra yaseen indinga hayewa kan bene inayin sululu.indinga shan dadina."
sauran yaran suka dinga dariya dafadin"ahegiya zahra za'asha dadi????.
zahra jin ana zugata hadacewa"aidama d'arewa zanyi