Showing 426001 words to 427912 words out of 427912 words
yasa ta miqe da sauri tana dube dube, hancinta ya shaqo mata warin wani abu kamar fetur, bata qarasa tunanin ba ta miqe da qarfin gaske ta bude qofa saboda hango Abida da tayi tsaye a jikin window da Ashana a hannunta tana qoqarin qyastawa tana fita daga dakin kuwa ta cilla Ashanar taje wuta ta kama dakin balbal ko ina. Yanda kasan wadda aka jonawa lantarki haka jikinta ya ringa rawa ta fice daga falon sukaci karo da Abidar na shigowa ita kuma
"Au baki qone ba? Yanzu kuwa zan qarasa ki wlh dan nayi alqawarin sena kasheki sannan shima ya dawo nabi dare na qona shi" ta fada tana qoqarin kama Umaimah ta maida ita dakin, qarfin da bata san ina ta samoshi ba ta tattara ta hankadeta gefe babu batun mayafi balle aje ga takalmi ta fita daga gidan da gudun tsiya tana kuka. Tundaga daga cikin Darmanawa seda taje round about din cout road a qasa kafin ta shiga tare Adaidaita dakyar ta samu wani ya dauketa dan dallon mahaukaciya suka ringa mata ganin yanayin data fito.
Su Mama na tsakar gida ana tattara kayan Gara da za'a kai mata da yamma ta fada musu kamar jifa suka miqe gaba daya a rikice suna tambayarta lafiya? Kuka ta fasa ta gagara cewa komai, yanayinta da rawar da jikinta yake ya saka Mama cewa au rabu da ita tukunna, Anty tace
"Nifa warin fetur nakeji ku duba ko inji ne yake zuba"
Cikin kuka tace
"Nice nake warin fetur, matarsa ce zata qonani, tana can ta kunnawa dakin ma wuta" ta sake rushewa da kuka, yau kam taga masifa qarara harda bala'i. To ashe ita qaramar yar jagaliya ce manyanta na inda suka.
Bayan Isha Kabir yaje gidan saboda kiran da Abba ya masa, dama yana kasuwa maqocinsa ya kirashi akan gidansa ya kama da wuta ya taho hankali a tashe Allah yasa an kashe wutar kuma da yake gini zamani ne iya dakin ta ci babu abinda aka fitar a ciki komai ya zama toka. A bakin yan unguwar yaji sunga fitar Umaimah da gudu Abida kuma ta fita a mota daga baya ya ringa sauke ajiyar zuciya tunda Allah yasa babu kowa a cikinsu amma tabbas ko sama da qass zata hade babu abinda ze hanashi cin kan uwar Abida dan ya tabbatar ita ta kunna masa wuta.
Abba beja doguwar magana ba yace masa ayi haquri kawai da auran nan ya sawwaqe mata tunda ga yanda Al'amira suka fara kasancewa, kamar yanda ta fada badan Allah ya farkar da ita ba da yanzu qata magana ake ta daban dan haka kafin azo ana batacciya kowa ya haqura kawai.
Tsabar iya makirci harda kuka yana durqusawa a qasa akan shi yana sonta baze iya sakinta ba Abida kuma ze dauki mataki akanta bazata qara kwatanta abinda tayi ba Abba yace shi duk wannan be shafeshi ba ya sakar masa yarsa kawai, aka kada aka raya yace shifa besan zance ba daga qarshe ma ya tashi ya bar musu gidan yana jaddada wlh baze sake taba zama da ita yanzu ya fara dan ta masa yanda yake so. Haka taci gaba da zama a gida cikin tsammanin ze aiko mata da takardarta dan har iyayensa Abba ya samu sukace su basu da ta cewa shine ma'auri tunda yana son matarsa ayi haquri kawai a koma tunda yace zeyiwa tufkar hanci.
Watanta daya a gidan daga zazzabi, ciwon kai se Amai ana zuwa Asibiti ciki, hankalin Umaimah idan yayi dubu ya tashi ta ringa kuka tana tumami Mama kanta batayi farin ciki da wannan ciki ba a halin da ake nema a yakice ubansa Abba ko ya ringa ce musu kun gani ko duk abinda kaga ya faru da dalili yanzu ina za'a kai wannan rabon. Da kansa ya kira Kabir din ya gaya masa ya ringa murna a ranar se gashi a gidan, Umaimah na kwance tasha kuka ta godewa Allah se ganinsa tayi kawai a dakin ta tashi dakyar ya ringa mata murmushi yana cewa
"Sannu Baby, kinga yanda kika rame kuwa da kina gidana da tare zamuyi rainon cikin nan ai" ya ringa mata soki burutsu har ya gaji ya tafi, shikenan ya maida gidan kullum se yaje baya kunyar kowa yake zuba musu iskanci son ransa shi yakeyi Umaimah kejin takaici a haka Abba yace ta haqura ta koma kawai kodan wannan rabon bayan sun zauna anyi yarjejeniya ya kuma yarda ze raba musu mahalli ita zata koma sama gaba daya kamar yanda daman tsarin gidan yake. Wannan yasa ta samu yar nutsuwa amma ba gaba daya ba tunda dai Abida na gidan bayan ubanta ya biya kudin Asarar da tayi masa dan hatta gadon daya qone seda suka biya yace shi be gaji Asara ba kuma baze sake taba itama bata nemi sakin ba dan son abinta take a hakan suke zaune kamar auran Bariki ana doke doke da zage zage.
Umaimah ta koma gidan Kabir taci gaba da rainon ciki ga bala'in sa da kullum cikin neman sauqi a gurin Allah take. Dan Kutumar uban data dade tana laqawa Khalil ta aura kuma tana ganinta ganin idonta. Ya hanata aiki, kasuwancin ma badai a shigo gidansa a siya ba dan baqi ko yan uwanta ne zasu zo se an sanar masa idan ba haka ba ranar babu zaman lafiya haka itama ba zata fita ba seda kwakwkwaran dalili kuma shi ze kaita ko ya hadata da Driver, kudi kuwa idan ya bata seya bi diddigin komai yaji yanda akayi dasu kuma kamar yanda ya fada be gaji asara ba ko abinci kika dafa yayi yawa se kinsan yanda zakiyi dashi kika bata masa abu kuw abiya zakiyi babu abinda ya shalleshi, bala'in Kabir da Jarabar Matarsa da bata da buri sena ayi tashin hankali suka hadu suka tasota a gaba ga ciki me dan banzan laulayi a wata shida da auran idan ka ganta se ta baka tausayi. Dole ta haqura ta saki ranta da irin rayuwar da ta tsinci kanta a ciki ta nemi hanyoyin samar wa kanta farin ciki da nutsuwa ta hanyar lazumtar Karatun Alqur'ani, istigfari da kallon shirye shirye da zasu ringa debe mata kewa wani lokacin takan taba karatun littattafan hausa Wanda bayan farawarta ta samu darussa sosai a ciki, ta samu hanyoyin warware matsaloli da yawa tsakanin ta da Kabir dan ta karanta blabaran hutsayen mutane irinsa da yanda ake tafiyar dasu kuma Alhamdulillah idan ta gwada dabarun tana ganin ci gaba dukda me hali baya fasawa amma darajar son da yake mata da kulawar da take qoqarin bashi tasa abubuwa da yawa sun sauqaqa tana iyakar qoqari gurin kiyaye duk abinda ze kawo sabani har yayi mata tijarar tasa musamman daman abinda yafi hado su batun Yammatansa da yake waya dasu cikin gidan duk sanda yaga dama tana ganin ai cin fuska ne idan tayi magana ranar ko cin mutunci se wanda ya manta dole ta tattara shi ta watsar ta fuskanci rayuwar ta, duk abinda yafi qarfinta kuma seta barwa Allah taci gaba da kai masa kokenta.
Seda ta haihu sannan yaranta sukaje gidan ta samu Muhammad Sabir kayan barka Tuli Humaira da sukaje tare ta kai mata da kudi kuma wai inaji Dadynsu ta ringa kallon Humairan da baka buqatar a gaya maka irin kwanciyar hankali da walwalar da take ciki wanda ribar haquri ya kawo mata. Bata san Khalil ne ya kawo su ba seda zasu tafi ta rako su har qasa, Humairan na Murmushi tace mata
"Ko nayi masa magana ya leqo ku gaisa tunda kin sakko?" Gabanta ya fadi, amma ta daure tace mata toh. Ta fita babu jimawa suka shiga tare da Khalil daya qara zama wani Hamshaqi dashi suka gaisa ya sakeyi mata barka bata ga wani abu bayan qaunar matarsa dake gabansa a tattare dashi ba. Har a ranta taji dadi kuma tayi masa fatan Alkhairi, ta tabbata da ita dashi kowa ya samu kalar sakamakon daya dace da rayuwarsa.
Kwananta Arba'in da biyar da haihuwar Sabir Allah yayiwa Abbansu rasuwa cikin dare sugar sa ya tashi da hawan jini duk lokaci daya, kafin ma su isa Asibiti a mota rai yayi halinsa. Fadar kalar tashin hankalin da suka tsinci kansu a ciki bata baki ne, abinda kawai take tunawa kwana uku kenan dataje gidan yawon arba'in, irin hirar da sukayi da maganganun daya ringa gaya mata se da akace ya rasu ta gane wasiyyace yake mata. Ya ringa jaddada mata cewar tayi haquri da rayuwa a duk yanda ta zo mata a sannan yake ce mata
"Kinga ko yanzu na mutu zan kwanta lafiya saboda nasan cewar babu wata fitina da tayi saura a cikin ahalina Alhamdulillahi ko ba yanda aka so ba amma kowannen ku ya samu rayuwa me kyau daidai da yanda Allah ya nufa ze samu. Kinga Kabir din nan idan kika yi haquri kika jure wata rana zakiyi farin ciki da auransa koda yake ma gashi har kin fara tunda yau mun zauna kusan minti nawa baki ce Kabir yayi ko Kabir yace ba"
"Kawai haquri nakeyi Abba amma ko yanzu da zamu fito seda muka haura" ta fada tana yar dariya shima yayi dariyar yace mata
"To kici gaba da haqurin kinji ki riqe auranki karki bari shaidan ya sake samun damar da zeyi rawa cikin al'amuranki kici gaba da Addu'a ita ce babban makami in sha Allahu komai ze daidaitar miki wata rana ko cewa akayi yayi miki fada ma bazeyi ba". Suka ringa hira yana tuno mata da abubuwan baya, harda hotunanta na yarinta ya debo mata ya bata da yake ta ajiye dasu Mama na tayi masa tsiya wai soyayyar ce ta motsa kenan da yar gaban goshi yace mata Eh se Bayan Sallar Isha Kabir ya dauketa bayan Abba ya sake hadasu yayi musu nasiha tare suka tafi gida ashe ganin qarshe tayi masa.
Haka rayuwa taci gaba da garawa rasuwar Abba tasa suka qara hada kansu dukda daman a hade suke amma suka qara dunqulewa ya zamana komai zasuyi se sun shawarci juna ba duk abinda ya shige mata duhu su zata nema su warware mata, har yanzun kuma Kabir be barta aiki ba seta qara qarfafa kasuwancinta na turaren wuta daga baya ma da kansa yace ta ringa kaiwa Kasuwa ana zuba mata a shagunansa se gashi kuwa sun karbu kasuwa ta qara bude mata kuna babu mugunta ze bata kudinta daidai idan an siyar ta sake hada wasu ta kai shiyasa rashin sake mata hannu da wani tsantseninsa baya damunta tunda tana samun na kanta ba kuma ta da wata hidima akanta dan tun Sabir bata sake haihuwa ba su Mu'ayyda kuwa sedai tayi musu abu kawai a matsayinta na mahifiyarsu badan suna da buqata ba, tsakaninta da Ahalin Khalil kuwa abin se sambarka. Yaran su na zuwar mata dukda basa kwana sukanzo su wuni tareda sauran qannensu wani lokacin Humaira da kanta take kai su wani lokacin Driver ita dai batada qarfin guiwar da zata iya sake taka qafarta a cikin gidansu.
Bata sakeyin qawa ba a yanzu idan ka cire Rumasa'u ita kadai ce qawarta se Hadiza. Ta samu labarin Safina wai ta tafi Libiya neman kudi bayan da itama auranta ya mutu watanni kadan bayan na Umaimahn kusan shekararta biyar acan se gata an dawo da ita babu yanda take ciwo an rasa kalarsa suka hadu da Mshaifiyarta da itama take jinya duk an rasa kan abinda yake damunsu ita dai data ji labarin tayi mata addu'ar samun sauqi a gurin ubangiji dan bata fatan ko a lahira Allah ya sake hada fuskokinsu.
QARSHE