Showing 171001 words to 174000 words out of 241374 words

Chapter 58 - HALYSAAH HAUSA NOVEL

19 Jan 2026

1024

wallahi, ko ma ina za a kai ta a kai ta ni na amince ta je, ai ita tasan tarbiyyar da muka yi mata in ma ta gantalar da tarbiyar ita da Allah, kuma gobe gobe zan sa a kira min ba?ar kawar tata ta zo in gaya mata uban Khaleesah ya amince koma waye zai dau nauyinta ya dauka, taje can ta ci gaba da karatun ta, ai gwara tayi nesa da mu ko bakin cikin dake damunta a rai zai ragu, mu kanmu in tana ganinmu takaici da bakin ciki take don ba mu da wani babanci da Awdul a wajenta tunda mu muka ja mata komai, gwara ta koma ta gama karatunta ta dawo da kwalinta don bazata tashi a tutar babu ba, shi kansa Awdul din yana samun labari an samu wanda ya maidata Amurka ta ci gaba da karatu sai bakin ciki ya kusa kashe shegen, a nan kuma zai san ba a banza Khaleesah take ba farin jininta ya shahara" Nenne na huci ta juya ta kalli Umma tace "Ke kuma Zahra'u halan tallan alalen ki ke da niyyar dora mata da kike mata bakin cikin komawa ta karasa karatun? To kamar yanda kike takama kina da iko da ita nima haka tunda ni na haifi ubanta, ban ga shegen da ya isa yace bazata koma ta karasa karatun ta ba" Ita dai Umma bata ce ma Nenne komai ba, Malam Ali dai na tsaye rike da buta a hannunsa yana kallon uwarsa, can dai yace "Amma dai Nenne sam babu tsari ace mun sake barin yarinyar nan ta bar kasar nan da sunan wani zai dau nauyinta bayan duk abinda ya faru, me kike son jama'an gari su ce a kaina? Sannan nace duk sanda na samu kudi zan nema mata Jami'ar garin nan tayi, ba wasu shekaru gareta ba balle ace lokaci zai kure mata" Nenne ta kallesa da sauri tace "A gidan uban wa zaka samu kudin? Mutanen garin in sun fasa fadin abinda za su fada a kanka Allah ya tsine masu albarka, kai bari kaji Ali bana bukatar ra'ayinka ko shawararka a yanxu saboda kai ma sanda ka bi ra'ayinka ka yarje ma Awdul ya kai ta kasar waje babu wanda ka saurara ko kaji shawaransa, don haka ni ma yanzu wallahi bazan saurare ka ba Amurka ne sai Khaleesat ta koma ta karasa abinda ta fara in sha Allahu, in kuma nuna ma duniya zaka yi ni er banza ce a gareka to Bismillah" Kofar gida kawai Malam Ali ya fita da butansa a hannu, Nenne ta kalli Khaleesat tace "Maza ki hada akwatinki ki tsaya cikin shiri, in sun biya maki kudin jirgin ki kama gabanki kije kiyi abinda zai taimaki rayuwarki, zama gidan nan kadai ya ishi mutum ya fada cikin mummunan damuwa, gida kamar na 'yan sansanin gudun hijira, ga lafta laftan mata suna yawo suna doyi a cikinsa, ai ko mutum matsiyaci ne ya kasance dai yana da tsaftarsa dai dai gwargwado, amma gidan nan ga talauci ga kazanta, ina bawa zai iya rayuwa a nan idan ba dole ba" Nenne na kai wa nan ta kama hanya tayi tafiyarta, Khaleesat ta daga kai ta kalli Umma da ta bi Nenne da kallo, Mama Shatu ta mike tana kallon Umma tace "Muddin kika ce baza ki bude baki kiyi magana ba to kina ji kina gani za a mayar maki da er ki karuwa Zahra'u, wata birkitacciyar tsohuwa can kamar Nenne ce zata yanke ma er da kika haifa hukuncin abinda ya shafi rayuwarta? Ita ta tsugunna ta haifar maki er? Mu meyasa ba a mana iko akan namu yaran ba? Saboda an san baza mu dauka ba mu ba yan iska bane, to kuwa wallahi Nenne na dab da kai ki ta baro ki, mata me tabin ?wa?walwa zaki yarda ta yanke hukunci akan 'er ki? ai in ita Khaleesar ta bude baki tace bazata je ba babu uban da zai tilastata ta je wallahi, waye bai san Nenne da kwadayi da son abun duniya ba kamar tayi sata?" Muryar Nenne suka ji ashe tana makale bata tafi ba tana jiran jin abinda za a ce, Nenne ta dinga kwalo ma Malam Ali kira, sai gashi ya shigo da sauri yana kallonta yace "Lafiya Nenne? Ai magana ta wuce yanda kika ce haka za ayi" Mama Shatu tayi wuri wuri da ido daga inda take tsaye, Mama Zubaida ta mike ta lallaba ta dau kwandon kwanon wanke wankenta ta shige daki ta sako labule, Nenne ta rushe da matsanancin kuka tana kallon Malam Ali tace "Ali yau sai dai ka zaba ko ni ko Shatu a gidan nan, kawai ka zaba ko ni ko ita, ni Shatu zata kalla ta kira me tabin ?wa?walwa wato mahaukaciya er macukule? Ni zata ce ma me kwadayi da son abun duniya? Tunda nake me na taSa zuwa gun almajirin ubanta dake bara a bakin danja nace ya bani? Me na taSa rokon uwarta me shanyayyen kafa? Bata san ina labe ban tafi ba duk ina jin abinda take cewa, cin mutunci da zagi sai wanda ta manta ne bata min ba Ali, har tana gaya ma Zahra'u ni na haifar mata er da zan yanke mata hukunci akan ta? Me nayi ma Shatu da har zata yi mugayen kalamai haka a kai na? Naga dai kullum ci gabanka da na iyalan ka shi ne burina, fadi tashi babu wanda bana yi akan kai da iyalinka, amma daga karshe sai zagi da cin mutunci ya biyo baya, tsofe tsofe da ni Shatu tace min me son abun duniya?" Kuka sosai Nenne take tana share idonta da gyalen jikinta, Malam Ali na kallon Mama Shatu da tayi tsuru tsuru yace "Shatu ki tafi gida, sai na neme ki" Mama Shatu ta gwalo ido tace "Ban gane in tafi gida ba Malam, wani gidan zan tafi?" Malam Ali yace "Gidan iyayenki, ki je na sake ki" Mama Shatu ta zabura tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ka sake ni fa kace Malam, na shiga uku na lalace" Labibah ta mike tana huci tace "Gaskiya Baba sai dai mu bi Baabarmu mu ma" Nenne tace "Shegiya ku bi ta mana, yunwar cikin ku kadai ma ya isheku ai" Malam Ali na kallon Mama Shatu dake rusa kuka yace "Kar in dawo in sameki a gidan nan" Daga haka ya fice daga gidan, Nenne ta bi bayansa tana goge idonta ita ma ta fita, sai a sannan Mama Zubaida ta fito tana salati tana kallon Mama Shatu dake kuka wiwi, Umma tsabar yanda jikinta yayi sanyi ta ma kasa cewa komai daga inda take zaune, Mama Zubaida na kallon Umma tace "Ke kam kinyi asara wallahi Zahra'u, ko wani bala'i ta dalilin ke da tsinannun 'ya yan ki yake faruwa a gidan nan, gashi yau saboda ke da er ki an saki Shatu, sam babu alkhairi a tare dake da zuri'ar ki Zahra'u" Umma ta juya tana kallon Mama Zubaida sai dai bata ce komai ba, Khaleesat ma ta daga kai tana kallonta, Mama Shatu na kuka sosai tace "Kuma in sha Allahu asirin da kike yi zai kare maki a gidan nan Zahra'u, yanda kika yi sanadiyyar tsinkewar igiyar aurena daya ke da er ki wallahi sai nayi sanadin naki igiyar kema, ko tsirara zan yi yawo kuwa, Ni saki daya aka min ke ukun gaba daya za a maki, kuma kamar Ali ya maida ni ne don yanxu na fara auren sa wallahi" Don mamaki Umma ta ma rasa abun ce masu ganin yanda suka juya zancen lokaci daya, yau ga fadan karfin hali tana gani kiri kiri, biyesu ma bata lokaci ne kawai a wajenta ga makota na jin su, tsam ta mike tayi shigewarta daki, Khaleesat ta mike ta bi bayanta. Washegari da sassafe Umma da Aunty Farida suka fito tsakar gida suka tarar da Mama Zubaida da Mama Shatu a tsaye suna jiran fitowarsu za a je ba Nenne hakuri, ko wanne da Hijab dinsa har kasa don sanyi ake sosai, duk abinda suka yi ma Umma jiya hakan bai sa tace bazata bi su zuwa gidan Nenne ba, Su ma din sun san ta dalilin Umman sai Nenne ta iya hakura ta sa Malam Ali ya maida Mama Shatu shi yasa Mama Zubaida da kanta ta samu Umma ko kunya babu tayi mata magana wajen karfe biyar din asuba, Mama Shatu dama a makota ta kwana ranan don sae da Nenne ta dawo ta korata har da watsi da en tsummokaran ta, sae kusan hudun asuba Shatu ta dawo gidan daga inda ta kwana, a haka duk suka kama hanya zuwa gidan Nenne da asuban. Ranan Thursday da safe Khaleesat na zaune dakin Umma tana kallon Aunty Farida dake ta jera mata kayanta da aka amso wajen guga a cikin akwati, ita dai Khaleesat har sannan ta rasa gane me take ji a ranta, farin ciki take ko akasin haka duk ta kasa ganewa, babban damuwarta yanxu bata san da idon da zata kalli Housemate dinta ba idan ta koma America, sannan gani take kamar babban burden kawai zata zame masa a can din tunda ita ba komai gare iyayenta da za su tallafa mata da shi ba idan ta koma, Wan kudin dake account dinta ba wani kudin kirki bane kuma da shi ta siya sabon waya with new sim card, sai few abubuwan da tasan zata bukata a can kasar, sauran kudin dake account dinta ko dubu dari da hamsin bai karasa ba, duk wannan tunanin yasa take damuwa sosai a ranta, Aunty Farida ta daga kai tana kallonta kafin ta rufe zip din jakar tace "Baki manta komai ba dai ko?" Khaleesat ta gyada mata kai kawai, Aunty Farida tace "A Airport din za ku hadu da Safiyyah goben?" A hankali Khaleesat tace "Eh" Aunty Farida ta kulle zip din tace "Gwara ki saki ranki kiyi abinda ke gaban ki Khaleesat, ki cire duk wani damuwar dake ranki kar ki je ki samu matsala a karatun ki, shi kuma Jawwad Allah ya saka masa da mafificin alkhairi...." Khaleesat ta sauke idonta bata ce komai ba, lkci daya taji hawaye ya cika idonta, Aunty Farida ta mike ta dauko daya akwatin don hada few foodstuffs din da suka siyo mata da Umma wanda zata iya shiga Amurka da shi, a hankali Khaleesat tace "Toh Aunty ta yaya za a maida masa kudinsa dake account dina?" Aunty Farida ta daga kai ta kalleta, can tace "Kudin wa? Ko Abdul?" Khaleesat ta gyada mata kai, Aunty Farida ta saki baki, can tace "Wai dama har yanxu kudaden nan nasa na account din ki?" Khaleesat ta gyada mata kai, shiru Aunty Farida tayi kamar me nazari, after a while tace "Ki ci gaba da ajiye kudin kawai Khaleesat, duk sanda ya dawo ya bukaci kayansa sai a basa, ko Umma kar kiyi ma maganar kudin for now, bana son a samu delay a tafiyarki don yanxu sai su iya cewa sai an maida masa kudadensa, kuma hakan zai iya ja maki delay...." Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, Aunty Farida ta ci gaba da hada foodstuff din da take a akwati.
[7/1, 1:11 PM] khaleesat Haiydar =???
'?: Wajen karfe uku na yamma Khaleesat na zaune bakin kofar dakin Umma Aunty Farida na combing din mata dogon gashinta bayan ta wanke mata shi da Shampoo da Conditioner, har wani sheki ba?in gashin nata yake yi bayan Aunty Farida ta shafa mata man gashi, tun daga wajen wanke gashin Aunty Farida ke ta mata fadan ta bar gashinta ya kakkarye saboda banzan da tayi da shi ta dena kula da shi, ita dai Khaleesat bata ce mata komai ba don har sannan basu san irin zaman da tayi a gidan Abdul ba, don ma abun ya tsaya iya kakkaryewan gashi, har bata son tuna experience dinta a gidan Abdul hakan yana traumatizing dinta, su Mama Zubaida da Mama Shatu dai na bakin murhu suna girka abincin siyarwansu na yamma, suna yi suna kuskus a bakin murhun, lkci lkci sai su kalli direction din su Khaleesat, ita dai Aunty Farida dama ko kallo basa isanta a gidan, a da dai ta biye su har dambe sun sha yi amma yanxu bata da wannan time din, kallon stark illiterates kawai take masu, wasu mata biyu ne suka shigo gidan babu ko sallama, sun yi shiga ta alfarma sun sha gwala-gwalai suna taku cikin isa, at the same time suna bin ko ina na gidan da kallo cike da kyama gashi dama su Mama Zubaida sun yi gaje gaje da ruwa a tsakar gidan ranan, Khaleesat ta dinga kallonsu haka Aunty Farida da ta ajiye comb din hannunta, Mama Zubaida ta mike tace "Sannun ku da zuwa ko dai batan hanya ku ka yi ne, in gidan Hajiya Samira matar Alhaji Bala ku ke nema can karshen layi za ku karasa sai ku yi tambaya a nuna maku gidan, amma ba nan bane" Momy ce ta shigo gidan tana tafiya gansan gansan da Drebanta a bayanta yana biye da ita, mayafin nata ma ko yafa shi bata yi ba, gashi ta sha wani tsadadden ba?in glass no respect, Khaleesat ta dinga kallonta babu ko kiftawa, lkci daya taji gabanta ya fadi sosai, ta juya ta kalli Aunty Farida, sai ga Meemah ita ma ta shigo gidan tana yatsine fuska, ita ko mayafin ma babu a hannunta, Aunty Farida ta dake tace "Bayin Allah lafiya? Daga ina haka, babu ko sallama" Daya daga matan da suka shigo da farko tana ma Aunty Farida wani matsiyacin kallo tace "Ba shi ya kawo mu ba, a irin wannan bolan za ayi maku sallama?" Umma ta fito daga dakinta don tana jin duk abinda ake cewa, tsaye tayi bakin kofa tana kallonsu, Mama Shatu da Mama Zubaida dai sai zazzare ido suke kamar wa enda suka yi ma sarki karya, Momy ta karaso har tsakiyar compound din tana tafiya cikin isa da gadara, fuskar nan nata babu ko digon mutunci tace "Zuwa nayi in ji ko shegiyar er ku tana da gadon Abdul ne, Ko kuma shi ma satan da ku ka yi ma ubansa kuke da niyyar za ku yi masa, in kuwa babu gado to yanxun nan ba sai anjima ba a maido mana kudadensa dake account din er ku..." Umma ta kalli Khaleesat nan da nan hankalin Umma ya tashi sosai, Aunty Farida tace "Ikon Allah, shi ne sai anyi wannan zuga haka kamar za ayi yaki?" Meemah ta matso har gaban Aunty Farida tana mata matsiyacin kallo tace "Yakin ne ai, ko kin ga alamar da sassauci muka zo? sanin halin familyn na ku na sata wanda ku ka gado a gun Malam me dattin hula ya sa mu ka yo tattaki a mayar mana da kudaden mu tun wuri, ai kowa yasan sata da cin amana shi ne tambarin gidan nan, don haka tun wuri ba a jiyo kan mu ba a maido mana Miliyan goman Abdul, kun zata bulus za ku ci ga banza ta fadi ko? To Sponsoring din matsiyaciyar er ku da ya dinga yi da kudinsa ma ai ba yafewa yayi ba sai kun biyasa a lahira wallahi, kawai babban farin cikin dake saka ni nishadi idan na tuno shi ne karewar da zata yi as dropout din John Hopkins university, don ko kaf zuri'arku za ku siyar baza ku samu kudin biya mata ta ci gaba da karatun a kasar Amurka ba, da yau ta gama John Hopkins sai bakin ciki ya kasheni, amma Alhamdulillah a dropout zata kare, Abdul kuma ya yar da kwallon mangwaro ya huta" A fusace Momy tace "Ke Meemah tsayuwa cikin kangon bolan nan ne ke burge ki da baza kiyi abinda ya kawo mu mu fita ba, ko so kike Cholera ya kama mu? Ina ke ina cacar baki a irin wannan gida" Aunty Farida tayi wani murmushi tana kallon Meemah tace "Sai dai kuwa bakin cikin nan ya kashe ki don kina ji kina gani Khaleesat zata gama karatu a makarantar da kike fada, Allah ya ji ?an ki in Advance" Cikin tsawa Meemah tace "Keee, ki iya bakin ki, kar ki gan ni tsaye a wannan bolan gidan a gabanki kiyi zata ni sa'ar yin ki ce, don wallahi inda na bi da kafata ma baki isa ki bi ba har duniya ta nade, ni ba sa'ar ki bace ta ko wani angle, banda Abdul yayi downgrading dinmu ya kaskantar da darajan da Allah yayi mana ina mu ina hada hanya da matsiyata talakawa irin ku balle har aje ga auratayya? Ke ki duba irin wajen da ku ke rayuwa wanda ko karen gidanmu baza mu bari yayi rayuwa a cikin wannan hali ba, To wallahi ki iya bakin ki ni ba sa'ar yin ki bace, ba karamin aikina bane in sa a shafe babin ki a duniya" Tun kan Aunty Farida ta mayar ma da Meemah amsa Umma ta hanata, cikin fushi Aunty Farida tace "Kamar yaya in yi shiru Umma, gidanmu fa suka zo suka same mu kuma ki ce inyi shiru? ashe ma karyar arziki suke in don saboda miliyan goma za su yi wannan uban zugan kamar masu bibiyan miliyan 50 har su tsaya suna kumfar baki suna tada jijiyoyin wuya akan 10M, uban wani ya saka ya tura mata kudin a account dinta da har za su zo nan suna gaya ma mutane maganar banza, ko kuma rokonsa tayi ya saka mata kudin, su arzikin ma wallahi da gani taka haye suka yi, da can su ma matsiyata ne" Meemah ta mika ma Momy handbag dinta tana huci zata cakumo Aunty Farida, Momy ta dakatar da ita tace "Ke me ya kai ki, ki taSa ta ki ce kin taSa wa? Salon ta goga maki ?ashin tsiyarsu kike kokarin dambe da ita? Yanzu wannan har Class din damben ki ce in ba rashin wayo irin naki ba Meemah? Ai ba a dambe da talaka matsiyaci" Umma ta kalli Khaleesat tace "Ta yaya za ki fiddo kudaden a account din ki Khaleesat?" Khaleesat

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login