Showing 18001 words to 18924 words out of 18924 words
wannan Itace Amaryar taka,"
Mik'ewa itama Azma tayi ganin Naina sambatayi tsanmanin sakeganin Naina Cikin Rayuwarta ba Lalle ko anyanka tatashi,
Zubawa juna Ido Sukayi cikeda tsantsar tsanar juna Had'id'a tuhuma ko Wanne da Abunda kecikin ransa
"Waimeke faruwane kinsantane Naina," cewar Ummeenta
Wani mugun kallo sukebin junadashi, takawa Naina tayi taje gafda Azma cikin k'asada murya tace"Yau k'aryarki tak'are,"
Hannu Azma tad'aga daniyar wanke Naina damari Cikin sauri tarik'e hannunta "kinyi wannan kuskuren daga farko amma Yanzu bazaki Samu damar sake aikatasaba"
Gyaran murya Maimartaba yayi yace"jikata kizauna kifad'amana meke faruwa Kuma inakikasanta,"
Zama tayi kusadashi"nasanta a Istanbul ne kuma Lokacinda Muka fita nida Shareef Acan mukaganta hotel tareda saurayinta idan zaka zagada photon ta kaf makarantar mu bawanda baisantaba tantiriyace Mara kunya batada k'awa macce Saidai Namiji kuma bawanda baisan Rashin kamun kantaba nayi mamakin yarda ace waikaine Adeel zaka k'are da Auran wannan abar,"
"Kunga nifa bazan saurare cinmutuncinku ba danhaka duk Abunda Zakuyi Bismillah,"
"Abunda zamuyi ai afili yake Kai Adeel Yanzu basai Anjima Inason kafad'a Gaban kowa kasaketa kuma sakinda baida gyara,"
"Koda bakanemi nayi hakanba zanyi domin koyanzu Auran nawa baihanata shek'e ayarba nasan Komai, dan haka kije Azma ni Adeel nasakeki saki Uku,"
"And so what's, mtswww matsiyata Kawai," tafice tabar Gidan
Nasiha Maimartaba yayiwa Daddy Sosai domin shine silar samun wannan marar kunyar cikin Ahlinsu,
"Abunda yasa nataraku anan shine nayanke hukuncin had'a Auran Abid dakuma Naina,"
Zabura Naina tayi Cikin rawar murya tace"Aure kuma kaka nida ya Abid,"?
"K'warai kuwa Naina na Isa daku shiyasa nayanke wannan Hukuncin nanbada jimawaba Za'a d'aura Kuma bawanda zaijada Hukuncina,"
"Amma kaka inada Wanda,..."
"Wayekikeso samadani d'an uwanki Naina? Mezaibaki Wanda Ni zankasa baki, wllahi Inasonki Naina fiyedashi,"
"Ya Abid yaushe kafara sona? Nidai a'a Gaskiya a'a abari nayi zab'ina dakaina ni banason Auran zumunci ko Had'i Gaskiya Ni a'a," tamik'e tana gunguni
"Naina kiyarda dani tawa Soyayyar ba irinta Adeel bace bazan tab'a watsamiki k'asa a'idona harcikin *ZUCIYATA* nakesonki wllahi idanbansamekiba komai zai iya faruwa dani dama *ZUCIYA* ta Naina kisaurareni dan Allah,"
Wucewarta tayi yabibayanta saurayin Shiga Gabanta yayi yad'auka gabanta yace"tinda Aka haifeki nake k'aunarki nayi iya k'ok'arina wurin b'oye tawa Soyayyar ne saboda kince Adeel kikeso dukanku Ina k'aunarku shiyasa bazan iya Fad'ar sirrin *ZUCIYA* taba gamedake amma nashiga wahala maiwuyar fassara, idan zaki tina Wanda yake yawan miki text da b'oyayyar number bakowa bane faceni,"
Saurin kallonsa tayi"k'warai kuwa nine Naina kiyarda dani" fidda Wayarsa yayi yakira Aikuwa saiga number tabayyana
Murmushi tasaki Had'id'a Godiya ga Allah daya batamai k'aunar harhaka Kuma Cikin ahlinta,
"Katashifa da mutane a palourn tafad'a tana k'asa k'asa da murya"
"Saboda Samun k'aunarki bazanji kunyar duk'amikiba Koda akasuwane haryanzu baki ansaminba kinasona,"?
"Eh inasonka ya Abid"
"Dagaske,"?
"K'warai kuwa"
"Yakai Wanda kikama Adeel," yafad'a yana kwab'e fuska Alamar kishi
Dariya tasaki"oh ya Abid rigima nifa yanzu nafahimce bana wani k'aunar Adeel Kawai haukan KURUCIYA ne"
"Kintabbata"
"Sosai inadakai ai magana tak'are Kuma my soul mate"
"I like this name"
"Me too,"
"To sarakunan Rashin Kunya" Cewar Hajiya mama
Guduwa Naina tayi sukuwa suka saka dariya...
BAYAN SHEKARA D'AYA
Anyi Auren Naina da Abid soyayya sukebugawa sosai Yanzu haka tanada cikinsa, inda Khairy kuwa yaranta biyu,
Daddy nagani Cikin tashin hankali domin kuwa Kud'insa masu yawan gaske danashi Dana jama'a dayak'arb'o dominyin canji duka dollars d'in sukab'ata, Koda zai'a Saida komai nasa korabin biyan bashin mutane bazasuyi ba tashin hankali yasashi fad'uwa yasuma akawuce dashi Asibiti masu Kud'i kuwa suntabbatar sai Anbiyasu Kuma baida Hanyar Samun Kud'in hakan yasa ciwonsa tsananta,
Tafiya bawan Allan keyi ga yunwa ga Rana gazafi kwatsam saiya hangi jaka gefen hanya yajuya ko Ina bakowa zuwa inda jakar mutumin yayi yaduba ganin Manyan Kud'ine Saida yatsorata domin Arayuwarsa baitab'a ganin dollars ba d'auka yayi yanufe gidansa baifad'awa kowaba dama gidan shine Kawai matarsa batanan cikeda tsoro da zulmi yayi bacci zuwa safiya yashirya yatafi Gidan redi'o mafi kusa yace asaka cigiya idan ansamu maisu Afad'amasa nanma suke fad'amasa Ankawo sanarwar neman Kud'in nawani Alhaji ne, tare Suka rankaya zuwa Asibiti dankaisa yaga Alhajin ,
Kodasuka Isa Asibitin har afitoda daddy police sunsashi gaba domin Ansaka k'ararsa Kan Kud'in Sauran Ahlinsa kuka Kawai suke, Mom kuwa nangaban kowa tatakemasa gidan wuta kanbazata zauna dashiba tinda yanzu talaucine zaibisa haka yanaji yanagani yabata saki domin shak'e wuyansa tayi kandole saiya saketa,
Harza'a sashi mota mutumin yace"Adakata ga Kud'in natsinta Kuma nadawo makadasu,"
Sake baki Daddy yayi ganin shigar mutumin Koda ba'a fad'aba kaga talaka talakanma matsiyaci amma shine yadawo masa daduka Kud'in, dubawa Akayi Kuma duka Kud'in ne, Kama Hannunsa Daddy Yayi yasaki kuka yana Godiya Rana tafarko da daddy yayi nadamar aibata talaka, yanzu Kam yaga ranar talaka kuma yaji kunyar Abunda yafad'a gameda talaka Masu Kud'in dayake tink'aho dasu saigashi duka sungujesa Harda mom amma TALAKA shine yadawo masa dadukan farincikinsa,
Alkairai dayawa mutumin yasamu Kuma Daddy yamaidasa kamar d'an uwa, duniya juyin K'osai Wai yau Daddy ne da k'aunar talaka harda samun y'artalakawa ya Aura
Hunmmm lalle duniya tafi bagaruwa Jima maishirya d'an Adam Dan dole..
Mom Kuwa Abunda take tak'ama tatara tahad'u da yandafara Suka cinye,
Azma kuwa karayar Arziki tasami mahaifinta itakuwa tasami HIV garin yawonta Abu Yama Abba yawa kusan maikud'i Idan yarasa Kud'i daga K'arshedai Abba yahad'e *ZUCIYA* yamutu bajimawa itama matarsa tabisa Azma tashiga duniya..
D'ayan familyn kuwa rayuwa suke cikin farinciki da Jindad'i yanzu dai Daddy Yana k'aunar talaka Sadaka kuwa ba'a Magana saiya yazauna Cikin talakawa suyita fira ba kyama........
ALHAMDULILLAH
ANAN NAKAWO K'ARSHEN WANNAN LITTFIN NAWA MAITAKEN *ZUCIYA* ALLAH YA K'ARA SHIRYAR DAMU, SAIMUN SAKE HAD'EWA A SABON LITTAFINA MAIZUWA NANBADA JIMAWA BA IN SHA ALLAH.......................
TAKU HARKULLUM MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 QUEEN OF WRITER 📝 HAUSA NOVELS 📚 (MRS_MLM)
_BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_
WhatsApp number 07064904617
OR 07031012948
THURSDAY 18/4/2024 APRIL