Showing 1 words to 3000 words out of 7941 words
[6/8, 11:51 AM] ~Siyama.♥️:
©®2023-K_shitu🦋
Khadija Muhammad Shitu
Arewabooks: Kshitu
Hikaya: Kshitu
Wattpad: Kshitu
K_shitu Multimedia.
*SIHIRTACCEN IKO!*
(Al’ajab).
📕K _ S H I T U
*Page 1&2*
Bismillahir Rahmanir Rahim.
Mafarin Ƙaddarar ya fara ne tun sanda Kakata ta ɗauki tulun ta fasa! tun daga wannan lokacin ba mu sake samun salamar Rayuwa ba, Shaiɗanu ke bibiyar Rayuwarmu.
Sihirtaccen Iko! Ya zame mana fitina a rayuwarmu, Sheɗanu sun yi nasarar Hallaka Kakata amma har yau babu tabbacin tana raye ko ta mutu, sannan mahaifiyata itama an samu nasarar hallakata ta bar wannan duniyar ke nan har abada.
A hankali na sauke Ajiyar zuciya mai ƙarfi, na mayar da idanuwana kan Ruwan da muke tafiya saman shi daga inda nake ina iya hango yanda ƙananun kifaye ke shawagi hankali kwance.
Na zurfafa sosai cikin duniyar tunani, ina ta saƙe-saƙe da maganganu cikin Raina, Har ban san lokacin da muka ƙaraso Yankinmu ba, mutane har sun fara fita, amma ni na yi shiru, na yi zaune.
Kiran sunana da na ji an yi ne har cikin ƙwaƙwalwata, ya dawo da ni daga duniyar tunanin da na tafi.
Har lokacin Idanuna a rufe suke ban buɗe su ba, Kamar a mafarki na kuma jin An kira sunan nawa,
"Zoya! Zoya.!!" A ɗan firgice na buɗe idanuwana.
Rungume juna muka yi ni da Ariya cike da murna da kewar juna, Sakina ta yi tana ƙare min kallo tana ƴar dariya "Zoya kina nan dai yanda kike baki ƙara komai ba, sai fari da kika yi amma kina nan ƴar siririya." dariya na yi ina hararta na ce,
"Na dawo ke nan zaki fara samin ido, ko ina Kaka da Anum, har da baba aka zo tarba ta?"
Jan hannuna tayi, tare da faɗin, "Oho! ke fa kin iya tambayoyi, idan kinje kya gani da idonki."
Harar ta na yi, sanna na biyo bayanta muke fice daga cikin jirgin ruwan, Tsaitsaye na gansu alamun ni da Ariya suke jira. Da gudu na nufi Kaka ina murnar ganinta zan rungumeta.
Saurin kaucewa tayi tana dariya, har na kusa faɗuwa Baba ya riƙo ni yana murmushi, "Wato Kaka kaɗai kika gani ko Zoya ni bak..". ban bari ya ƙarasa zancensa ba na rungume shi ina dariya, na ce "Baba yi haƙuri na so na fara zuwa gurinka amma Tsohuwa ta ɗauke min hankali."
Mun daɗe muna gaggaisawa da Ahalina, cikin farin ciki, da walwala, Kafin Baba ya ce mu tafi gida haka nan, Amalanken shanu muka shiga guda biyu, muka kama hanyar gida, Babban gidanmu muka ƙaraso mai kyau wanda kallo ɗaya zaka masa kasan ko a ɗan garin Muna da wadata sosai da Arziƙi.
Tun da na fito na tura gate ɗin gidanmu na shiga nake aikin ƙwalawa Kawu kira, "Kawu, Kawu! ka fito yau na dawo na dinga takura ka, me ma yasa baka zo tarbata ba, Kana ina kawu ka fito mana Zoyarka ta dawo..". haka nayi ta surutu ina ƙwala masa kira, Daga ɗakinsa ya amsa min "Ke Zoya kin dawo ke nana! shi ke nan ba zan sake samun sukuni ba zaki yi ta haddasa min ciwon kai."
Fitowa ya yi daga ɗakin yana kallona, "Barka da dawowa Zoya, yanzu dai ya kamata ki je ki ci abinci da kuma wanka".
Sauran ƴan'uwana dake parlourn suka shiga hidima da ni, tare da tambayata ya na baro yayana, ni kuma ina ta amsa musu da lafiya lau, shi ma yace yana nan tafe.
Agogon Hannuna na kalla tare da, Miƙewa na ce "Ƴan'uwa zan shiga na yi wanka, na ɗan huta, idan na gama zan fito."
Akwatin kayana Ariya ta biyo ni dashi, tana aje min itama ta fice dan ta bani guri na huta.
Mintuna Sha biyar tsakanin shiga ta wanka da fitowa ta, nayi wanka na fito na shirya cikin doguwar riga Blue da mayafinta fari, sannan na jawo Akwatin kayana na janyo na fara fito da su ina jerawa, inda muke ajiye kaya nida da Ariya, Wani littafina ɗauka Na SIHIRTACCEN IKO! na ajiye bisa gadon, sannan na ci gaba da kimtsawa, sai da na gama duk abin da ya dace sannan na hau gadon na janyo littafin na buɗe shafi na farko na fara karantawa.
Abin da na fara gani a farkon shafin ya sanya ni natsuwa sosai da son karantawa, dan fahimtar komai da kyau.
Shafain farko abin da na ga an rubuta Shi ne SIHIRTACCEN IKO! da wani jan rubutu kamar jini, kafin na ci gaba da karantawa na soma ƙarewa bangon littafin kallon ba wani hoto bane a jiki ko adon wani abu, littafin ƙarami ne mai baƙin bango, sai wani jan abu wanda yafi kama da jini a farkon littafin, daga ƙasa wani rubutu ne wanda ban san da wane yare aka yi shi ba, ban kuma iya karantawa ba, bayan ma Rubutun ne dai.
Tunani na fara akan tsohon da ya mallaka min da littafin, Chan kuma na soma magana a bayyane, "Anya shi ɗin ya kasance jinsin mutum kamar ni? ko dai na yi kuskure a bisa karɓar wannan littafin, to me yasa ƙwayar idanunshi fara idanun kuma suka kasance baƙaƙe ƙwayar idon kawai ce fara Anya kuwa ban yi kuskuren yi masa kyautar zinare mai daraja sannan kuma ai tun a ranar da abin ya faru har ya mallaka min littafin ban sake ganinsa a jirgin da muke tafiya. kuma na san babu inda muka tsaya, taya kuma ya san sunan kakata da mahaifiyata? sannan ya ce a duk sanda na buƙaci ganinsa na buɗe littafin akwai hodar Sirrin da zan gano shi da ita mu gana! Anya kuwa zoya ba ki yi wauta ba?"
Ajiyar zuciya na sauke wannan karon tsoro ya fara shigata, amma na daure na janyo littafin na fara karanta bayanin.
SIHIRTACCEN IKO! Abun da aka rubuta shi ne; Sihirtaccen Iko! ya kasance ƙwaya ɗaya tak amma yana da sassa uku na iko, wato mahaɗinsa, Ɓarin ikunan sun kasance ƙwaya uku, duk wanda ya yi nasarar mallakarsu zai samu ƙarfin sihirin da babu mai shi kaf faɗin duniyoyin da muke da su.
Duk Wanda ya yi nasarar Mallakar Sihirtaccen iko! zai iya mulkar duniyoyin manyan matsafa da aheɗanu har abada, zai zama shugaba ga kowa da kuma ko wane jinsi da halittun da ke akwai a duniya!
Ɓarin Sihirtaccen ikona farko, ya kasance Wani Narkakken Ruwan lu'u-lu'u ne, mai cike da sihiri marar misaltuwa wanda zai iya shafe tarihin duniyar mutane. Sannan ya kasance ba ko wane jinsin halittu zai iya taɓa ɗan tulun da yake ciki.
Numfashi na sauke da ƙarfi sannan, na buɗe shafi na gaba.
Cikakken bayani da kuma mamallakin Ɓarin Sihirtaccen Iko har sauri na ke wajen jefa ƙwayar idona kan rubutun da yake ƙasan bayanin, amma abin takaicin wannan rubutun ne da na gani a ƙasan bangon littafin wanda ban san ko da wane yare aka yi amfani wajen rubuta shi.
Takaici ne ya sanya ni buɗe Ma'adanar kayayyakinmu na saka littafin, tare da miƙewa na fice daga ɗakin bakiɗaya.
Ɗakin kaka na nufa dan ina kyautata zaton Ariya na chan.
Kwance na same ta tayi ɗaiɗaya bisa gadon Kaka tana cin Gyaɗa, faɗawa na yi nima bisa gadon ina faɗin, "Ash na gaji Riya!" Dariya ta yi ta ce "Yanzu fa nake son zuwa na tashe ki kin huta da kika kawo kanki."
Hannu na sa na ɗibi gyaɗar na murza sannan na watsa a baki ina taunawa a hanakali, "Wai ina tsohuwa ne?" na tambaye Riya ina sake bajewa bisa gadon.
"bata ma jima da tafiya kasuwa ba, ta ce tana son yin siyayy ne ta miki girki mai daɗi.
Ɗibar gyaɗar na yi na murza da dukkanin hannayena ina faɗin "Zan ci girkin tsohuwa mai daɗi."
Na ƙarasa faɗa ina watsa gyadar a bakina.
Wani irin na ji ɗanɗanon gyad'ar ga kuma kaina da ya sara lokaci guda kuma na soma jin zufa na tsiyayo min daga cikin gashin kaina zuwa gadon bayana.
Ni kuwa bam sani ba, ashe na yi mummunan kuskure na cin wani abu ba tare da na wanke hannayena da ruwa mai tsarki na taɓa littafin Sihirtaccen iko.
Idanuna na ji sun min nauyi ba na jin surutun da Ariya ke min, kawai idanuna suka lumshe, jikina ya sake na soma barci....
**PaidBook 300 Vip500 2329557913 UBA Evidence of Payment via 09117440993.*
(Ina godiya sosai wa masoyana, Littafin kuɗi ne na yi muku sauƙi no complain 300N masu son VIP 500)
09117440993
[6/8, 12:10 PM] ~Siyama.♥️:
*SIHIRTACCEN IKO!*
Arewabook@Kshitu.
*Page 3&4*
Tun da na fara barci ban farka ba saida duhu ya fara sannan Anum ta soma tashi na, da ƙyar na iya buɗe idanuwana na sauke su kanta, "Zoya ki tashi wannan barci haka tun wajajen safe, yanzu fa duhu ya fara." firgit na miƙe ina waro idanuna waje na ce, "Kai Anum shi ne babu wanda ya tashe ni?"
Dariya ta yi, tare da faɗin, "Wace ni? yanzun ma fakaitar idon Kaka na yi, dan ta ce kar wanda ya tashe ki"
Miƙewa na yi ina hamma, da ƙananan ƙunƙuni, sannan na fito daga ɗakin na tunkaro parlor ƙamshi ke dakar min hanci na girkin Kaka, da gudu na faɗa madafar na mamayeta na rungumo ta baya ina dariya da faɗin,
"Yanzu Kaka duk ni kika shiryawa wannan?" Sai da ta saki ajiyar zuciya sannan ta ɗan wurgo min harara tare da faɗin, "Ke fa matsalarki ke nan! yanzu har kin tsorata ni." Turo bakina na yi na ce, "Shi ke nan, tun da ba dan ni, kika yi ba, na tafi ɗaki kuma kar wanda ya neme n...," Bata bari na ƙarasa ba ta hau lallashina, "Haba jikalleta, duk dan ke fa nayi duk wannan ɗin, kar ki bari aji kanmu fa, kije kiyi wanka ki zo kici mai isarki."
Murmushi na yi, sannan na fice na nufi ɗakinmu.
Banɗaki na shiga, na ɗebi ruwa daga cikin Roba, sannan na zuba a bokiti na shiga cikin kwamin na fara wanka, Ina ta wankan ina jin jikina yana sauyamin sosai, amma haka na gama na ɗaura Tawul, sannan na tsaya gaban madubi ina sharce gashin kaina.
Kallon kaina na yi ta cikin madubin, Ai ban san lokacin da na saki matajin gashin ba na ƙwalla razananniyar ƙara, mai ƙarfin gaske wacce nake da tabbacin cewa duk mutan gidan sun ji ta.
Abin mamaki daga inda na yanke jiki na faɗi, haske ya ɗauke bakiɗaya babu wani haske ko dai-dai da ƙwayar zarra, duhu ya mamaye ko ina.
Kukan tsuntsaye na fara ji cikin kunnuwana, da sautin dariya mai rikitarwa, abin da ya daɗa dagula mini lissafi Kin kamar wani na hura ni da iska, haka na dinga jin jikina da kuma motsi ta gefene, da iface-iface da ke tashi na mutane kunnuwana.
Cikin ƙanƙanin lokaci na soma bin umarnin da gangar jikina da zuciyata ke mini, ɗaga madubin da ke manne jikin bango na yi na fasa shi, ji jake tas! Haske da sheƙin ƙwayar idona su suke nuna min komai tamkar a mijigi.
Gabaɗaya jin jikina nake tamkar an musanya min shi, wani bala'itaccen ƙarfi ya zomin cikin sa'o'i kaɗan.
Ɗaga ƙafata na yi, na iso inda Robar ruwanmu ke girke, na sanya hannuna ɗaya na ɗaga robar, na buga ta da ƙasa ta tarwatse, ruwan suka malale, Ɗaga ƙafata na yi, tare da yin wani tsalle na dawo, take ƙasan gurin ya soma tsatstsagewa yana rugujewa, ga ruwa da ya fara kawo min har wuyana.
Ina cikin hayyacina, kuma ina sane akan abin da nake aikatawa sai dai ba ni ce, nake sarrafa kaina ba, tunanina bai yanke ba saida ruwa ya kawo har kaina, na kuwa yanke jiki na faɗi.
Da tari na farka daga doguwar sumar da nayi, da ƙyar tarin ya lafa na miƙe daga bisa gado ina ƙarewa ɗakin kallo, a lokacin da wadataccen haske.
A hankali na soma tariyo abubuwan da suka faru cikin mintunan da na san basu wuce 60 ba wato awa ɗaya.
A take mamaki da tsoro suka dirar min lokaci ɗaya na soma tunanin anya ban yi mummanan kuskuren karɓar littafin ba domin gabaɗaya akalar tunanina tana ga wannan littafin da na ɗauka na karanta Alwashi na daukar wa kaina ba zan sake bi ta kan littafin ba.
Tashi na yi cikin sauri-sauri na kimtsasannan na zura jallabiya na nufo Parlour.
Kiciɓus muka yi ni da Ariya, "Yauwa! dama yanzu Tsohuwa ta turo ni na gano mana lafiyarki, wannan wanka naki haka?"
Abin da ta faɗi ke nan cike da shaƙiyanci, ban kula ta ba, ni dai na ce,
"Ki shafa min lafiya Riya, ki bari idan na ɗan samu wani abu ya zauna a cikina, na maido miki martanin tsokanarki."
Dariya ta yi ta min, na ƙyale ta har muka isa, wani wuri gefe cikin parlourn inda Ahalinmu suka ware dan cin Abinci.
Guri na samu na, zauna na fara gaishe da mutanen da ke zaune, kaf Ahalinmu ƙwanmu da ƙwarƙatarmu mu Goma sha ɗaya ne.
Yayana, Mahish, sai matarsa Yaya lailah, sai kawu Yahiz, da Anum(Mama) wato ƙanwar mahaifiyata mai suna Azla, sai baba Rahul, sai ni Zoya, da kuma kaka Milha, ƙanin mamata Kawu Raihan, sai kuma ɗiyar kawu Raihan Aziya, da kuma Ariya ɗiyar Anum, sai matar Kawu raihan Ruksha, sai mamata da ta mutu, Nasrin, kakata kuma, Lailah. gabaɗaya ban da su Mama da kakata mu tara ne, sai kuma Yaya mahish da yay lailah da ba a nan suke zaune ba.
Kusa da kaka na matso, ina wani marairaice fuska, "Kaka ina nawa, ba a dai cinye ba ko?" taɓe baki tay ta ce "Ke kika jawa kanki, wani wankan jaraba mutum tun da haske haske har dare yayi yana wanka, je ki ɗauko cikin faranti na ɗibar miki komai, suna madafa."
Maganarta ta ƙarshe ce ta ɗan sanyaya min raina, na miƙe cikin azama na miƙe na je na ɗauko, na dawo na zauna.
Tun kafin na kai abincin bakina, ƙamshinsa yake dakar hancina, miyauna ya kai ƙololuwar tsinkewa.
Lomar farko da nayi, saida na lumshe idanuna na buɗe, sosai ɗanɗanon girkin ya tafi da ni, ya min daɗi sosai.
Ba tare da na farga ba, na cinye abincin da ke gabana tas, duk da haka ban ƙoshi ba.
Haka kaka ta ƙara mata, amma bata ƙoshi ba, haka nan ta daure ta ce ya ishe ta.
Bayan an gama cin Abinci kowa ya tafi makwancinsa.
Tun da Muka nufi namu ɗakin ni da Ariya ta yi kwanciyarta ta fara barci
Yayin da nima na kwanta bisan gadon, ban da juyi babu abin da nake gabaɗaya na kasa barci, so nake na bi umurnin zuciyata, na ɗauko littafin SIHIRTACCEN IKO! na karanta amma fargabar abin da zai sake aukuwa ya hanani.
Rufe idanuwana na yi da zummar fara barcin amma na fara jin maganganu cikin kunnuwana.,
"Zoya! Tun da kika fara taɓa littafin ikunan Sharri, zaki yi aiki ne dole, kin fara aikinki, babu makawa ke ce zaki ƙarasa shi, babu wani mahaluƙi da ya isa ya dakatar da faruwar hakan...,Je ki, ki je ki ƙarasa bincike akan SIHIRTACCEN IKO! zan taimake ki, ina so ki ɗauki fansa akan ikon SHARRI...Daga nan zuwa daren murnar tunowar Kafuwar SIHIRTACCEN IKON SHARRI, Rayuwar ahalinki zata kasance cikin haɗari, ke ce zaki zame musu garkuwa kuma waraka, ki je Zoya ki aikata komai daidai ina miki fatan nasara!. Ki cire tsoro da fargaba a zuciyarki, ki tari kasada! ki zamo silar kawo ƙarshen wannan Ikon sharrin, kar ki karaya... Kar ki bari su samu nasarar mulkar DUNIYA! kar ki bari su salwantar da rayukan al'umma, Zai kasance ƘADDARAR IKON SHARRIN SIHIRTACCEN IKO! zasu fara bibiyar Rayuwarki, ki kasance jaruma karki bari suci galaba akan ki!"
Da ƙarfi ƙirjina ya buga zuciyata shiga harbawa da sauri sauri, gabaɗaya gumi ya wanke min fuskata...
*PaidBook 300,VIP,500. 2329557913 UBA Bank. Evidence of Payment via 0911440993.*
*SIHIRTACCEN IKO!*
Kshitu@Wattpad & Arewabook.
*Page 5&6*
Da safe muka tashi domin gudanar da adu'a kamar yadda muka saba a kowace safiyar Alhamis da Talata, Matan muna sanye ne da Dogayen riguna farare masu ratsin ja da mayafi fari. Muna addu'ar ido rufe hannayemu waje guda domin nuna girmamawar mu wa Abin bauta.
Wata irin ƙara na soma ji da ƙaraji da ƙarfi cikin kunnuwana ban san lokacin da na buɗe idona ina toshe kunnuwana ba wani kalan nake ji cikin jikina tsigan jikina na miƙewa na sunkuyar goshina ƙasa da ƙarfi ina jin wani an ambatar sunana da wata murya me kaushi.
Tulun dake rataye da ruwa me tsarki ya faɗo saman kaina ya fashe, Wani iri ihu na fara ina toshe bakina da son daidata yanayi amman na kasa sarrafa kaina.
Tamkar ana kartamin jikina nake ji, kawu ne ya fara nufo ni yana kiran sunana daga nan ban sake sanin abinda ya faru ba.
House of Late Sultaan of Liansa.
"Baka da Hankali Amaan!" mommy tace "Amaan wai meke damunka ko baka san hatsarin tafiyar ba idan kai baka son rayuwarka mu muna so nd i'm surprised zaku yi tafiya da wata mace ku biyu ne maza kana son janyo mana surutan mutane ka son jiran gidan nan ake"
"Whatever Allah ya sani, ku yi adu'a gobe ne tafiyan we have to go nd searc.." Aunty sarina ta katse shi "ko ma miye don Allah mommy ku ƙyale shi kun manta shi a rayuwanshi ba abinda yafi so irin fitina tun yaushe kuke magana akan abu ɗaya shi ne zai tafi ba wani ba ku bar shi mana na ga fa aiki ne zai kai su ba wani abun ba"
Abbu ya rufe maganan da faɗin "i trust my Maan wish all the best becareful nd respect your self where ever you're aikin sa ne ayi masa adu'a"
Ba wanda ya sake jan maganan da tsayi.
Meera ce ta haɗa masa kayan da zai tafi da su.
Yana ta murmushi be ce komai ba Liner ta sake cewa "i'm talking to you Maan" ya gyara kwanciyarsa da ƙer yace "Ke ɗaya za ki if not kuma kema ba sai kin je ba, Better get out of my place idan wani ya same ki anan kome aka miki i won't say anything"
Rai ɓace ta bar ɗakinsa ta gate ɗin baya ta fice daga gidan.
Numfashi Parook ya sauke cike da mamakin abin ya kawo Liner gidan su da dare haka, Dake shi ba mutum me saka