Showing 1 words to 1079 words out of 1079 words
GWARZON SADAUKI PART 5
itama ta farka daga barcin ta dube shi cikin alamun damuwa a lokacin da tuni ya sauko daga kan gado yafara sa kayansa.
Ta ce,Wane mai rabon mutuwar ne kuma yake kokarin guduwa daga gidan nan a wannan
daren?"Gadaraz ya ce "Ni ma abin da nake mamaki kenan. Mutum biyu ne kacal daga cikin fursunoni za su iya
yunkurin guduwa daga gidan nan, wato Insam da Barsad kuma suna kulle cikin dakin horo babu yadda za su iya fita bare har su yi kokarin gudu. Bari dai na je na ganewa
idanuna."Ilaila na jin haka sai ita ma ta yi wuf ta mike tsaye ta fara sa kayanta ta ce "Ai kuwa ni ma ina son na ga ko waye wannan mai tsautsayin wanda ya gaji da rayuwarsa a duniya."Shi dai Gadaraz ko kallonta bai yi ba, sai ya ci gaba da shiri, ya debi dukkanin makamansa na yaki, ya sa a jikinsa, sannan ya fice daga cikin dakin.
Nan da nan ita ma Ilaila ta sa tufafinta da takalmanta, ko da ta nufi kofar fita daga dakin sai ta ga layar tsafin mijin nata a ajiye a kan tebur.
Al'amarin da ya yi matukar ba ta mamaki ke nan, ta tsaya cak tana kallon layar tana tunani da wasu-wasi. Ita dai Ilaila a saninta da
Gadaraz dare da rana baya rabo da wannan laya face sai idan zai kwanta barci da daddare sannan yake cireta daga wuyansa ya dora ta a kan wannan tebur kuma da zarar alfijir ya keto yake farkawa daga barci ya dauki abar sa ya mai da ita wuyansa.
Ko sau daya a tsawon shekaru biyu da ta aure shi ba ta taba ganin ya mance da wannan laya ba, sai yau. Lallai akwai ayar tambaya a cikin wannan al'amari. Gama ayyana hakan ke da wuya sai Ilaila ta yi sauri ta fice daga cikin dakin, ta janyo kofa, ta rufe da mukulli, sannan ta falfala da gudu izuwa cikin kurkukun.
Duk fadin cikin wannan kurkuku
Ilaila ce kadai 'ya mace wacce babu wani fursuna da ya isa ya yi mata ko da kyakkyawan kallo saboda
tsananin tsoron mijinta da ake yi.
Ilaila ta kasance kyakkyawar mace a bar kwatance amma shekarunta za su kai talatin da biyu zuwa da uku. Ba komai ne ya sa
Gadaraz ya auri Ilaila ba face
kyawunta da kuma jarumtakarta domin ta kasance mace mai kamar maza, sannan matsalarsu a rayuwa iri daya ce.
Gadaraz ya hadu da Ilaila ne a can kurkukun birnin Misira a lokacin da shi ne shugaban dakaru masu tsaron kurkukun wanda ya kasance nà mata ne zalla. A tarihin wannan kurkuku na birnin Misira wanda aka gina shi sama da shekaru dari da doriya baya ba a taba samun fursunar da ta sami damar guduwa daga cikinsa ba sai Ilaila kuma sau
- biyu tana guduwa da kyar da sidin goshi Gadaraz ke iya bin bayanta ya kamota ya dawo da ita, amma sai bayan sun yi mugun artabu ya sha bakar wahala domin sai sun yi wa juna rauni saboda karfin damtsenta na sadaukantakar da Allah ya ba ta.
Kawai da karfin sihiri ne ya ke samun lagonta, har ya sami nasarar kamata.
Ba wani laifi Ilaila ta yi ba face shiga gidan Sarkin Misira domin ta dauki fansar mutuwar mahaifinta wanda ya kasnace Bafaden Sarkin.
Saida ta sami nasarar shiga har cikin turakar sarkin amma da yake yana da karfin sihiri ba ta gan shi ba alhalin ga shi kwance a kan gado yana ta faman sharar barcinsa.
Nan fa ta kama dube-dube a cikin turakar, ashe wadansu kuyangi dake kwance a kasa masu taya sarki barci ba barci suke ba, sun ji motsin shigowarta. Har sai da ta tsallakesu ta nausa can cikin turakar sarkin sannan daya daga cikinsu ta mike tsaye cikin sanda ta je, ta dauki wata gudumar katako ta doka a kan wani faifan karfe. Nan take karar faifan ta cika gidan sarautar gabadaya. Nan da nan sai ga dakaru da yawa ta ko'ina suna bullowa a guje rike da makamai.
Kafin Ilaila ta ankara tuni dakaru sama da guda arba'in sun kewayeta a tsakiyar turakar sarkin.Karar wannan faifan karfen ce ta tashi sarki Marhat daga barci.
Koda ya mike zaune ya ga bakuwar mace a tsakiyar turakarsa ga dakaru sun kewayeta ta yi shigar yaki sai ya kura mata idanu da kyau ya ga bai santa ba, bai taba ganinta ba a birninsa gabadaya. Har dakaru sun yunkura za su afka mata sai sarki Marhat ya daka musu tsawa suka ja da baya, sannan ya sauko daga kan gadonsa ya dubeta cikin murmushi,
ya се.Ke'yanmata wace ce ke, kuma wane gangancin ne ya kawo ki har cikin turakata domin ki yi min sata" Ko da jin wannan batu sai Ilaila ta murtuke fuskarta ta dubi Sarki Marhat cikin harara mai nuna tsananin kiyayya ta ce, "In da sata na zo yi ba nan zan shigo ba cikin turakarka, da can baitul mali zan je inda kake boye dinare da lu'u-lu'u.
Zuwa na yi na dau ranka."Da jin wannan batu sai sarki Marhat ya dubi dakarunsa da dukkanin hadiman dake wajen ya kyalkyale da dariyar mugunta, sannan ya dubi Ilaila ya ce. "Laifin me na yi miki kike son ki Kashe ni? Haila ta ce "Ka kashe mutum daya jal wanda shi kadai ya rage mini a duniya Barde Amzad. Ni yarsa ce" don haka yau dole ne takobina tá sha jihinka." Sarki Marhät na jin wannan batu sai ya sake kura mata idanu da kyau, kuma ya bushe da dariya a karo na uku ya ce Tábbas ni ne na kashe mahiafinki ba don komai "ba sai saboda shi ne kadài ya san sirrina na dukiyata, da kuma sirrin tsarón rayuwata. Ina tsoron kada wata rana ya ci amanata ya hada baki dã wasu a raba ni da rayuwata ko dukiyata.
Dama"na" sami labarin yana dà 'ya guda daya, wacce tun tana da shekaru bakwai ya dauketa daga nan cikin birnin Misra ya kai ta can birnin Askandariya wajen wani gawurtaccen mayaki ana ba ta horo na jarumta. Babu irin neman da ban yi miki ba, ke da mayakin da ya ba ki horo amma ban ganku ba. Akwai wani littafi wanda ke dauke da sirrin inda na boye dukiyata da kuma inda sihirin tsaro na rayuwata yake a hannun mahaifinki. Har na kashe shi ban san inda littafin yake ba, kuma bincike ya tabbatar mini da cewa ke ma baya hannunki sai dai babu mamaki kin san a inda yake. Kina da zabi guda biyu, zabi na farko shi ne ki sanar da ni inda wannan littafi