Showing 1 words to 2234 words out of 2234 words

Chapter 1 - YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA PART 8

28 Mar 2025

570

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA PART 8






junanmu. Muka yi sallama da ita ta ce mini sai gobe da dare amma da safe lallai in je wurin malam in dauki karatu, sannan kuma ta ce in saki jikina in dauka cewa ni dan gida ne, kada wani abu ya dame ni, na ce mata, "To."
Da safe aka kawo mini kalaci na ci na yi kat, sannan na je dakin malam na gaishe shi ya amsa mini da irin murmushin nan na malamai. Ba tare da bata lokaci ba muka shiga karatu har zuwa hantsi, na yi sallama da shi na koma dakina.
A takaice dai ya kasance sai dai in wanke goma in tsoma biyar kawai.
Bayan cin abincin dare sai na wuce wurin malam, na kuma lura yana murna da ni, don ya fahimci ina da sha'awa game da koyon ilmi, kuma daidai gwargwado ina fahimta. Muna cikin karatu sai ga yarinya ta iso, ta gai da shi sannan ta juyo ta yi mini irin murmushin nan da kan sa zuciyar masoyi narkewa. Muka yi karatu muka gama kamar kullum, muka bar wurin malam, na dauko karatuna ina bita, inda na yi kuskure ta gyara mini, don ta yi ilmi fiye da ni. Daga baya muka yi sallama ta koma. i sm
Sai da muka shafe wata shida a haka, to ashe abin da ya faru ita wannan yarinya Fa'izah 'yar Sarkin wannan garin ne ni ban sani ba, kuma wannan
malami da muke karatu a wurinsa kawunta ne, a wurinsa ta girma.
Mahaifinta Sarki Zulkiflu yana da wani Waziri, wanda Sarkin ya amince wa, kuma ya yarda da shi. ke yi masa ya sa ya sakar masa Saboda son da ya
komai.
Duk abin da Sarkin nan ke yi, Waziri Jatau ba ya kaunar sa ko miskala-zarratin. Ya shirya makarkashiyar da zai kawo wa Sarki bakin jini wurin jama'a ba a san iyaka ba, amma kuma duk Allah Yana kiyayewa, don kuwa alherin Sarkin yana da matukar yawa. Yana son talakawansa, ga tawakkali da sanin ya kamata. Wannan ya sa su ma talakawan ke matukar son sa kamar su lashe.
Wani abin mamaki shi ne, ko Sarki Zulkiflu ya gane munafuncin da Waziri Jatau ke shiryawa sai ya kyale shi ya yi kamar bai fahimta ba.
Da Waziri ya ga ya kasa dugunzuma ran Sarki, sai kawai ya yanke shawarar halaka wani abu wanda Sarkin ke matukar kauna, saboda haka sai kawai ya yanke shawara a kan cewa zai sa a sace Fa'izah wadda kuma ita ke nan abar da Sarki ya taba haihuwa a rayuwarsa, don ya sa a halaka ta. Ya tabbata cewa in aka yi haka, to zuciyar Sarki za ta sami tsananin kunci yadda mai yiwuwa ma ciwon zuciya ko
tsananin damuwa su zautar da shi ko kuma ma su yi sanadin halaka shi kowa ya huta. In ya so sai shi Wazirin ya ci sarauta.
Shi ne dalilin gayyato wadancan mahayan majusai su shida don su cika masa wannan babban kudiri nasa. Allah Ya yi sauran kwananta na gaba muka hadu da ita da yardar Allah kuma na cece ta.
Ashe lokacin da muka shigo cikin garin nan da dare Sarki ba ya nan, ya shiga cikin duniya neman ta, kuma Waziri shi ne ya ke rike da gari. Da muka zo sai ta kawo ni wurin malami kuma kawunta. Ta shiga gidansu babu wanda ya sani don kada Waziri ya sake shirya mata wata makarkashiyar. Duk garin babu wanda ya san ta dawo, daga malam sai mahaifiyarta.
Bayan wata shida sai ga Sarki ya dawo don sake sabon shirin fita, duk ya rame ya fita kamanninsa, saboda tsananin kawazucin 'yarsa. Ya shiga gida mutanen gari suna ta murna, ana ta kade-kade da bushe-bushe saboda murnar dawowarsa. Matan gida, barori da bayi suka shiga hada-hadar da suka saba in Sarki yana gari.
Lokacin da kowa ya bar shi don ya huta, abin mamaki sai ga 'yarsa da ya je nema ta zo ta rungume shi.
Mai martaba ya ji kamar mafarki ya ke yi. Sai da ya

dauki ruwa ya wanke idanunsa sannan ya tabbatar cewa ba mafarki ba ne. Ya zura mata idanu yana hawaye saboda tsananin murna da kauna da ya ke yi mata. Yana hawaye ita ma tana yi, a dalilin irin shakuwar da suka yi da kuma tausaya wa irin halin da ta ga ya shiga a dalilin rashinta.
Yarinya ta kwashe labari kaf ta shaida masa. Da ya ji labarin, sai ya sake fashewa da kuka saboda takaicin Waziri.miguh nilio side RV RO Sy sd phe?
99
Ya yi tunani wai shin ko ya taba saba wa Waziri ne? Amma dai ya kasa tuna ko da rana daya da hakan ta taba faruwa, sai ya cewa 'yar tasa, "Lallai sha'anin dan Adam yana da ban tsoro." stam syide Ya sa aka yi yekuwa cewa yana son kowa ya hallara a kofar fada gobe don yana da jawabi. Nan da nan masu shela suka bi kwararo-kwararo suna cewa, "Sarki ya gaishe ku, bayan gaisuwa Sarki ya ce a sanar da ku cewa, yana da jawabi, saboda haka kowa ya hallara a kofar fada da hantsin gobe." raud-sdaud ponDa daddare Sarki ya fito fada, Waziri ya zo ya yi gaisuwa Sarki ya amsa kamar yadda ya saba. Sarki ya tambaye shi labarin gari, sai ya ce, "Ranka ya dade ai gari lafiya lau sai dai alheri. Babu wata matsala da ta wuce kewar ka da ta gallabe mu. Kai da Gimbiyarmu"Sarki ya ce, "To madalla, na gode. Allah dai Ya bar zumunci.
Waziri ya tambaya, "Allah Ya taimake ka ko an yi nasara wurin nemo yarinyar nan?"
M
Sarki ya ce, "Waziri ai watakila wannan yarinya fa ba ta da rai.'
""
Waziri yana jin haka sai ya barke da kuka wai yana taya Sarki bakin ciki.
wan
Da Sarki ya lura da halin da Waziri ke ciki da kuma irin makircinsa sai haushi ya kama shi don ya ga kiri- kiri an mayar da shi wawa za a raina masa hankali. Saboda haka sai ya ce ya gaji zai shiga ciki sai gobe. Ita kuwa 'yar Sarki ran nan ma sai da ta zo muka yi Karatu kamar kunum a w karatu kamar kullum a wurin malam. Bayan mun
ta
gama ta kawo wasu irin riguna na alfarma ta ba nit ce gobe in malam zai tafi amsa kiran da Sarki ya yi wa jama'ar gari in sa mu je tare, ni dai na ce mata to, kuma ban tambaya ba.
A kullum mamakin ta nake ta yi, ina tunani a zuciyata cewa duk yadda aka yi dai wannan yarinya daga babban gida ta fito, kuma ga ladabi da ladaig kyakkyawar dabi'a.
nob Wayewar gari ke da wuya muka karya kumallo, malam na alarma, ni ya yi shigar kaya irin ma na shige cikin nawa, kai in ka gan ni sai ka dauka wani dan Sarkin yanka ne. Malam ya yi umurni barorinsa suka kawo dawakai biyu, su ma dawakan da irin tasu kwalliyar ta alfarma.
Muka hau ni da malamin, ban fada maka sunansa ba, sunansa malam Abdulkadir, muka tunkari fada, kowace kusurwa ka duba jama'a kake gani suna fitowa kamar za a je Idi, duk kowa ya amsa kiran Sarki.
Isarmu fada sai aka kama dawakanmu aka kewaya da su, sai na ga an nufi kujerun da ke kusa da Sarki an zaunar da mu a kan wasu na mutunci. Fada ta cika makil, ko ina ka waiga babu abin da za ka gani sai kan mutane. Can sai ga Waziri ya iso.
Tambura suka fara tashi wanda hakan ke alamta fitowar Sarki, kowa ya mike don girmamawa, da Sarki ya zauna sai kowa ya zauna. Daga nan sai mai martaba ya mike don yin bayani.
Ya fara da gai da jama'a, kuma ya yi musu godiya saboda irin kauna da kuma addu'o'in da suka yi ta yi masa lokacin da ya shiga cikin tashin hankali, ya kara gode musu irin yadda suka zauna lafiya bayan ba ya nan. Daga nan sai ya jefo wata tambaya, ya ce, "Ya ku mutanena, ina rokon ku ku gaya mini gaskiya don girman mulkin Allah kada ku boye mini komai. Don Allah kuna jin dadin mulkina ko kuwa ina zaluntar ku? Don Allah idan ina zaluntar ku, to ku fada mini yanzun nan in cire wannan rawanin, ku zabi wanda kuke da kyakkyawan zato a kan adalcinsa ni kuma na yi muku alkawarin cewa ni zan fara yi masa mubaya'a.
99
Kafin a bari Sarki ya kammala sai wuri ya dauka, "A'a muna son ka! Muna son ka! Allah Ya ja zamaninka."
nob
Bayan sowa ta lafa, sai Sarki ya ci gaba da jawabi, "Ya kujama'ar wannan kasa mai albarka ku sani cewa na riki Wazirina kamar dana, ina son sa kamar yadda mahaifiya take son danta, na amince masa, kuma na tabbata ban taba saba masa ba, hasali ma babu abin da bai sani ba game da sirrina don tsananin amincewa." Sai ya juya gefen Waziri ya ce masa, "Waziri ko ba haka ba ne?"
abied
99
Waziri ya ce, "Haka ne Allah Ya ba ka nasara. Tunaninsa ko Sarki ya yanke shawarar sauka ya dora shi gadon sarautar ne don mayar da hankalinsa wurin neman 'yarsa.
Ana cikin haka sai ga keken doki ya kawo 'yar Sarki. Da mutane suka gan ta sai sowa, wajen kamar zai tsage don tsananin murna suna cewa, "Sarki ya samo Gimbiya, lallai tafiya ta yi nasara, mun gode wa Allah 'yar Sarkinmu Fa'izah da ta bata ta dawo." Bayan sowa ta lafa sai 'yar Sarki ta gaisa da jama'a cikin girmamawa da ladabi, sannan ta zauna kusa da mahaifinta.
احتياج
Waziri kuwa kirjinsa sai bugawa ya ke ta yi don tsoro da bakin ciki, ga kuma mamaki.
Vadum
Bayan Sarki ya ga mutane sun natsu sai ya ce, "Ya ku jama'ata masu girma akwai abin mamaki, amma kuma dai ba za ku ji daga bakina ba, don an ce waka a bakin mai ita ta fi dadi. Yarinyar nan za ta ba ku labari da kanta"
'Yar Sarki ta sa aka kawo mutanen nan guda biyu a daure, ashe ranar da muka iso ta damka su ne a hannun wasu amintattun bayinta don a tsare su har zuwa dawowar Sarki. Ta sa aka kwance su daga daurin da aka yi musu, sannan ta ce musu, "Ina so ku shaida wa Sarki da sauran jama'a abin da ya faru."
$
Sai suka nuna Waziri Jatau suka ce, "Shi ne ya ba mu kudi jaka hamsin-hamsin kowannen mu, mu shida ne, muka je muka sace 'yar Sarki, ya ce mu je can nesa mu kashe ta.
Mu dai ba mutanen wannan kasa ba ne. Bayan mun yi tafiyar kwana da kwanaki da ita ne muka isa wurin wani rafi inda gardama ta sarke a tsakaninmu a kan shin a kashe ta ko kuwa a sayar da ita a kara samun wasu kudaden? Kuma kasancewar muna cikin mayen giya ne ya sa fada ya kaure tsakaninmu da wadanda ke son a kashe ta bayan sun zare takobi sun nufe ta za su kashe, shi ne dai muka yi nasara a kan su muka kashe su, sannan muka koma shan giyarmu har barci ya kwashemu. Can sai muka ji ana ta bugun mu har sai da muka yi lilis sannan suka daure mu, suka dora mu a kan doki, wato 'yar Sarki da wancan saurayin." Sai suka nuno ni, ai duk sai idon mutane ya juyo kaina.
Bayan wadannan barayi sun kammala ba da labarinsu, sai yarinya ta waiwayo ta dube ni ta ce, "Ya kai masoyina tashi ka shaida wa jama'a yadda abin ya faru" Na tashi na ba da labarin abin da na sani tun daga farko har karshe. d Edib Mutane kowa ka duba sai ka ga yana kwalla saboda takaici, sai Sarki ya tambayi barayin 'yarsa, "Shin ku kowane irin dalili ne Waziri Jatau ya ba ku na abin da ya sa ya ke so a halaka mini 'ya?”
Sai suka ce, "Ya ce mana ne wai so ya ke yi bakin ciki ya taru ya kashe ka, don in ba ita aka sace ba, to babu abin da zai iya jefa maka babban bakin ciki." Sai Sarki ya cewa jama'a, "To kun ji abin da Waziri"
yayi mana.m
Nan take wuri ya hargitse, kowa yana fadin albarkacin bakinsa, "A tsire Waziri! A tsire maciyin amana! A hada su a tsire! A yanka shi! A miko mana shi nan mu yagalgala shi danye!" Kowa dai yana ta fadin albarkacin bakinsa.
Can sai Sarki ya yi magana ya ce, "Ya ku jama'ata, ku sani cewa ni na dade da Waziri, kuma ni ba zan iya yi masa komai ba sai dai in bar shi da Allah. Amma daga yau na fitar da shi daga wazirci, kuma na ba shi sa'a hudu ya bar mini kasata.
Jin wannan jawabi sai wata sabuwar hayaniya ta tashi, mutane suna ganin lallai dole sai an halaka Waziri sannan hankalinsu zai kwanta, shi kuma Waziri ya yi shiru kamar wanda ruwa ya ci, sai ya yi wuf ya jawo wata sharbebiyar wuka daga kuibinsa ya daba a cikin sa, bayan wuka ta shiga sai ya farke cikin, nan take sai ga 'yan hanjinsa a waje, ya yi 'yan shure- shurensa ya mutu, mutane suka ce, "Ya yanke wa kansa hukunci. Da ma karshen maciyin amana kenan.
Sai Sarki ya cewa mutanen da suka sace 'yarsa lallai yanzun nan su bar masa kasarsa, ya sa askarawa su raka su.
Mutanen suka ce suna da magana. Aka amince musu. Sai suka ce suna neman a yafe musu, kuma suna son in Sarki ya yarda suna son zama tare da shi a cikin fadawansa ba don komai ba, sai don irin

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login