Showing 1 words to 1903 words out of 1903 words

Chapter 1 - TAKOBIN DAUKAKA CHAPTER 2.txt

26 Jan 2025

580

TAKOBIN DAUKAKA CHAPTER 2




Tsawon dakika arba'in bai ce uffan ba sai daga bisani ne ya dubi lasmirat yayi gyaran murya yace" ya sarauniyar kyawawan duniya kiyi sani cewa hakika kin zomini da al'amari mai girman gaske
Hakika bakaramar hikima kikayi ba da kika bayyana bukatar a gareni domin shi ilimin tsafi kogi ne komai nutson ka a cikin sa baza ka kwashe Abinda ke ciki ba,
Kuma kinsan masu iya magana na cewa Abin da Babba ya hango yaro ko ya taka tsani bazai hango ba, abin da bincike ya tabbatar mini ga me da bayanin ki shi ne.
Matsawar kina son ki fi kowa ne sarki dadewa abisa karagar mulki kuma ki auri mijin da yafi kowanne kudi a duniya to yazama wajibi ki mallaki abubuwa guda uku domin ki samu nasarar samun ruwan koramar matsafil
Daryalu
Da farko za,a nemo ruwan kogin ma'ul-hayatu, Sannan wadansu zobunan tsafi dake ajiye a kogon fatalwa a can yankin kasashen Larabawa a wani daji da ake yiwa lakabi da Husumul-kadar
Abu na karshe shi ne kubar miftahul-daryal,
Shi dai wancan ruwa zamu yi amfani dashi ne a lokacin da zamu shiga wani daji kafin mu isa inda koramar boka
•Daryalu takr, ruwan zai bamu kariya ne daga wadansu musifu dake dajin,
Su kuwa wadancan zobuna zamuyi amfani da su ne a lokacin da zamu shiga gidan boka Daryalu rukuni na farko wajen sanya su a hannayen mu,

Domin babu yadda za,ayi mutum ya shiga gidan face ya na dauke da wadannan zobunan sihirin,
Kubar miftahul-daryal kuwa zamu yi amfani da ita ne wajen bude gidan boka Daryalu
Dazarar mun samu nasarar debo ruwan koramar kinsha to shi kenan bazaki auri wanda yafi kowa talauci a duniya ba,
Lokacin
da boka Dayyubul-Barmas yazo dai dai nan azancen sa sai hankalin sarauniyar lasmirat ya dugunzuma ainun
Ta dube sa cikin alamun tsantsar damuwa tace" ya Sarkin bokaye shin taya ya zan mallaki wadannan abubuwa kafin ajali ya riskeni
Koda jin wannan tambaya sai Dayyubul-Barmas ya bushe da dariya sannan ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa
Sannan daga bisani kuma ya fashe da kuka.
Al'amarin da yayi Matukar bawa sarauniyar lasmirat mamaki kenan kuma ya daure mata kai ta dube sa ta ce"
• yà uban bokaye shin ina dalilin wannan dariya,da kuka naka?
Da jin wannan tambaya sai Dayyubul-Barmas ya share hawayen dake sannan ya budi baki yace ya shugaba ta abinda ya sanya dariya shi ne bincike ya tabbatar mini dacewa a wannan zamani nine bokan da zan samu daukaka fiye da kowa ne matsafi domin ya cika burin

Abinda Ya sa ni kuka kuwa shi wani bakon jarumi zai rushe wannan daukaka tawa ta yadda ko tarihina bata sake tunawa a duniya ba
Kuma wannan jarumi ba wani bane face namiji da zaki aura har ki samu Haihuwa wanda yafi kowa talauci a duniya
Sai dai iyakar bincike ne na kasa gano ainahin a nahiyar da saurayin yake,
Domin jarumin yana yana dauke da wadansu sirrika masu basa kariya.
Lokacin da boka Dayyubul-Barmas yazo dai -dai
nan a jawabin sa, sai hawaye suka sake zubo masa, Nan take Sarauniya lasmirat taji ta kamu da matukar tausayin sa
Dayyubul-Barmas ya cigaba da cewa ya sarauniyar kyawawa kiyi sani cewa bazaki taa fin kowane sarki dadewa abisa karagar mulki ba face kin mallaki wata takobin da ake yi wa lakabi da TAKOBIN DAUKAKA,
A salin' TAKOBIN DAUKAKA ta wani
gagurtaccen mayaki ne ma'abocin addanin musulune, Bayan shudewar jarumi Hilal ne wani mashahurin matsafin aljani ya sace takobin ya shiga halarar tsafi ta tsawon shekaru arba'in yana sana'anta takobin da sirrikan tsafi
An kira takobin da suna TAKOBIN DAUKAKA ne saboda duk jarumin da ya mallake ta zai samu daukaka a duniya

Lokacin da aljani Sautul-Hidar ya kammala halwar sa sai yaga wani Al amari da ya firgita sa kuma ya dimauta sa, Abinda ya gani shi ne bazai taba samun amfani da TAKOBIN DAUKAKA ba ajali zai riske sa,
Wani jarumi wanda bai kasance kowan kowa ba shi ne zai mallaki takobin ya lalata sirrikan tsafin dake jikin ta kuma ya daukaka a duniya,
Lokacin da aljani Sautul-Hidar ya ga wannan al'amari sai ya cika da bakin ciki
Kawai sai aljani Sautul-Hidar ya dauki. TAKOBIN DAUKAKA ya caka a kirjinsa a saitin kahon zuyar sa, Faruwar hakan ke da wuya sai numfashin sa ya dauke komai na jikin sa ya daina motsi ya sandare,take gangar jikin sa ta zagwanye ta zama wani irin bakin ruwa mai yauki,
Daga bisani sai ruwan ya rikida izuwa wadansu irin gabza
-gabzan samudawan aljanu dukkanin suna shirye cikin wata irin gagarúmar shigar yaki mai matukar kwarjini da ban tsoro a hannayen sa 'rike da wadansu irin makaman yaki masu barazana ga duk wata halitta mai numfashi, Koda bayyanar aljanun sai wani daga cikin su wanda da alama shi ne shugaban su ya dauki TAKOBIN DAUKAKA ya sanya ta acikin wata akwatu ta farin gilashi ya dauki akwatin da takobin ke ciki ya shiga sanya ta acikin wadansu akwatin har guda dubu,
Sannan ka sa dakarun aljanun izuwa kowace kusurwa ta gidan domin tabbatar da cikekken tsaro ga takobin

Tun daga wannan rana wadannan aljanun suke gadin gidan boka Sautul-Hidar dake kan tsaunin lauhul- azwar
Binciken bokaye da matsafa ya tabbatar da cewa duk daya daga cikin wadannan aljanun yana iya kayar bil'adama guda miliyan daya
Ke nan hakan ya nuna cewa aljanun zasu iya yakar duniya baki daya
Tabbas a halin yanzu tunkarar gidan aljani Sautul-Hidar dai dai yake da mutum ya bude taskar ANNOBA DARI
Lokacin da boka Dayyubul-Barmas yazo daidai
nan ajawabin sa.
sai idanun sarauniya lasmirat suka zazzaro kuma tsoro ya kamata, ta shiga damuwa ainun kamar tacewa boka
Dayyubul-Barmas ta janye bukatar ta,
Amma sai ta dube sa cikin karfin hali da ki fadi irin nasu na sarakuna tace" ya uban bokaye shin. yanzu yaushe zamu yi wannan gagarumar tafiya ta dauko TAKOBIN DAUKAKA?
Dayyubul-Barmas ya gyada kai yace"ya
sarauniyar
kyawawa ai komai ya na hannun ki duk lokacin da kika shirya tafiya a shirye nake,
Koda jin batu sai sarauniya lasmirat tayi godiya a gare sa ta debo dukiya mai mai yawa ta basa
Wannan shi ne cikekken tarihin sarauniya lasmirat.

Koda samun wannan gagarumar nasara sai kyakkyawan saurayin ya sakarwa sarauniya lasmirat dake kwance a kasa wani tattausar murmushi.
Har saurayin ya juya da nufin da nufin ya cigaba da tafiya a cikin kasuwar, sai yaji alamar motsin tafiya a bayan sa. Koda ya waiga sai yayi arba da ita fuskar cike da annuri ba wata ba ce face sarauniyar lasmirat,
lasmirat ta dube sa tace" yakai wannan kyakkyawan saurayi ma'abocin sadaukantaka idan baza ka damu ba ina bukatar nayi maka wadansu tambayoyi, kuma ina neman wata alfarma guda daya a wajen ka,
Koda jin wannan batu sai saurayin ya yi murmushi har fararen hakoran sa suka bayyana ya dubi lasmirat yace" yake wannan sarauniya fadi duk abinda kike son tambaya ni kuwa zan baki amsar ta dai dai abinda na sani,
Lasmirat ta dubi saurayin da wani irin kallo mai dauke da alamar tambaya sannan tace
"Yakai wannan saurayi shin mene ne sunan ka da ma
Abinda Ya Kawo izuwa wannan birni nawa'
Alfarmar da nake nema a wajen ka ina so ka biyo ni izuwa gidan sarauta
domin ina so mu tattaunawa
wata
muhimmiyar magana
Yakai wannan jarumi kayi sani cewa kai ne jarumi na farko a rayuwa ta dana taba fafata yaki da shi har ya samu nasarar kai ni kasa

Sa'adda sarauniya lasmirat ta zo nan a tambayar ta sai saurayin ya dube ta yace
" Ni dai da farko suna na yaslir ibn Hulzal na fito ne daga wata nahiya da ake yiwa lakabi da Nashmir
Game da Alfarma da kika nema a waje na kuwa bazan amince da ita ba
Sai kin yarda kuma kinyi mini alkawarin cewa zaki dunga daraja kowane dan adam,
Ma'ana za ki dai na azabtar da mutane da zaluntarsu, ›
Sa'adda saurayi yaslir ibn Hulzal yazo nan a zancen sa sai sarauniya lasmirat ta zurfafa izuwa kogin tunani
Sa,adda talakawa da sauran jama'ar kasuwar suka ga yadda sarauniya lasmirat ta kaskanta kanta a gaban saurayin sai suka cika da matukar mamaki da al,ajabi domin fiye da shekaru masu yawa hakan bai taba faruwa tunda lasmirat ta hau bisa karagar mulki]
Daga can sai ta dago da kanta da dubi saurayi yaslir tace"na amince da wannan sharadi naka yakai wannan jarumi,
Koda gama fadin hakan sai sarauniyar lasmirat ta yiwa wani badakare inkiya da hannu kamar badakaren yasan abinda take nufi sai kawai ya janyo wadansu fafaren dawakai ya iso gaban ta ya risina ya rike ta linzamin dokin daya,ta kama ta hau,
Ta na mai yiwa yaslir nuni da yau bisa dayan dokin take ya kama dokin ya hau

A lokaci guda suka sakarwa dawakan linzami sauran tsirarun dakarun suka mara musu baya a ka cigaba da tafiya,
Jama'a suka bisu da kallo cike da tsananin mamaki
*****
A can kololuwar sararin samaniya inda Allah (s,w,t) yayiwa halittu iyaka a nanne sarki Hamras ibn zulaibu ya sanya aka gina masa kasaitacciyar fadar sa,
Wacce masana suka tabbatar da cewa babu wata fada data Kaita Rawatuwa da kayan alatun jin dadin rayuwar
Domin an ce sai da bakaken aljanu guda dubu shida suka shafe shekaru goma suna aikin ginin fadar dare da rana babu sassauci,
Binciken bokaye da matsafa ya tabbatar da cewa Sarki Hamras yakasance jinin wata Kabila da ake kira da Banu lahzar,
Wadanda
aka 'tabbatar. dacewa sun mamaye
rabin
sarakunan duniya,
A rayuwar sarki himras fiye da abu uku, yana matukar adawar ace akwai wani sarki a duniya da ya fisa KARFIN MULKI,
Abu na' biyu kuma' shine ya tsani ma'abota addinin musulunci.

Bakomai yasanaya hakan sai domin mahaifinsa sarki
zulaibu ya mutu ne sakamakon kwabza yaki da wani jarumi ma, abocin addinin Musulunci, Akwai wadansu muhimman sirrikan tsafi da mahaifin sa zai sanar da shi wadanda da zarar ya sanar dashi din zai mulki duniya baki daya,
Amma sai ya zamana waccan jarumin ya hallaka sa batare da ya sanar dashi sirrikan tsafin ba, Abu ná karshe da sarki Himras ya tsana shi ne wani gawurtaccen jarumin ma,abocin addinin Musulunci, wanda binciken da yayi ya tabbatar masa da cewa shine zai kawo karshen mulkin sa a doran kasa.
Lokacin da sarki Himras ya ga cewa a halin yanzu basa da abokan gaba da suka huce ma'abota addinin Musulunci sai ya zurfafa izuwa cikin halarar tsafin sa domin ya gano wata hanya zai bi ya kawar da musulmi kuma ya mulki duniya baki daya,
Abin da bincike ya tabbatar masa shine bazai taba cika • wannan, buri na sa ba face ya mallaki wata tsafaffiyar takobi mai suna TAKOBIN DAUKAKA
Amma koda ya mallaki takobin bazai samu nasarar sarrafa takobin ba face ya hadiye gashin kan wadansu mutum biyu,
Wadannan mutum ba wasu ba ne face" sarauniya lasmirat da boka Dayyubul-Barmas,
Sa'adda sarki Hamras yaga gagarumin aikin dake gabansa na mallakar TAKOBIN DAUKAKA, da silin gashin boka Dayyubul-Barmas da sarauniya lasmirat sai

ya umarci wadansu gwarazan dakarun aljanun sa domin su yanko masa gashin boka Dayyubul-Barmas da sarauniya lasmirat
Bisa jagorancin aljani Huruful-labarus, Aljani Huruful-labarus yakasance GWARZON MAYAKI da masu Bincike suka tabbatar dacewa a jinsin bakaken aljanu babu mai karfin damtsen sa,
Bayan Sarki Hamras ya tura Aljani Huruful-labarus sai ya shiga shiri sai da ya kwana arba'in ya na tsuma kansa da tsumin tsafi, sai ya fito ya shiga izuwa duniya domin mallakar TAKOBIN DAUKAKA.'
Al'amarin saurayi yaslir da sarauniya lasmirat kuwa, tafiyar dakika arba'in kacal suka yi suka iso izuwa gidan sarauta
Gidan sarautar yakasance kasaitacce mai girma da fadi tamkar gari guda, gaba daya katangun ginin gidan anyi su ne da wani irin farin gilashi
Babu wani BASARAKE ko attajiri, dazai yi arba 'da wannan gidan sarauta face ya Zamò cikekken dan kauye,
Tsayawa masalta tsaruwar gidan sarautar zai iya zamo wa kauyanci sai dai abinda idanu suka gani kawai,
Duk inda mutum ya duba bayi ne hade da kuyangi
da barori na kai komo suna hudima

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login