Showing 1 words to 1685 words out of 1685 words

Chapter 1 - TAKOBIN DAUKAKA CHAPTER 1

12 Jan 2025

845

TAKOBIN DAUKAKA CHAPTER 1



Saurayi ne kyakkyawa na gaban kwatance keta
faman tafiya a cikin kasaitacciyar kasuwar birnin,
Yana sanye da tufafi riga da wando wadanda aka
sana'anta su da fatar damisa, hatta takalmin dake
kafar sa anyi sane da fatar damisar.
A hannun sa yana rike da wata doguwar sanda, kallo daya zaka yiwa saurayin ka fahimci cewa yakasance GWARZON MAYAKI,
Saboda da kirar karfi da suka bayyana a tare dashi,
Babban abinda yakara fito da kyawun sa shine zara-zaran gashin kansa daya zuba izuwa kan kafadun sa da kasumbar sa gemun sa bakake sidik,
Haka dai saurayin yacigaba da tafiya a cikin kasuwar babu sassauci
Lokacin daya shafe tsawon rabin Sa'a yana wannan
tafiya a dai dai wannan lokaci ne sarauniyar dake
mulkin birnin ta fito yawon shakatawa tare da dakaru masu tsaron lafiyarta mutum dubu biyar.
Duk inda sarauniyar ta durfafa a kasuwar sai kaga
jama'a sun dare sun bayarda hanya;
Bakomai yasanaya hakan ba sai domin tsananin
tsoron fushin sarauniya lasmirat,
Ana cikin wannan haline sarauniyar lasmirat ta
hango wannan kyakkyawan saurayi ya tunkaro inda
Take babu alamun tsoro ko far gaba a tattare da fuskarsa

Al'amarin da yayi matukar bawa sarauniyar lasmirat
mamaki kenan kum a ya d a u r e mata kai,
Domin s h e k a r u m a s u y a w a t a n a fitowa wannan
rangadi hakan bai taba faruwa ba,
Su k u w a d a k a r u n dake bayan t a s a i zukatan s u suka
harzuka jikin s u y a kama kyarma yana tsuma saboda
tsananin fushi,
K a w a i s a i sarauniyar lasmirat t a d a g a hannun t a
sama tana mai nuni da a tsayar da tafiya,
Sannan t a d u b i saurayin t a daka masa tsawa cikin
fushi t a c e dashi" yakai wannan saurayi m e kake
takama dashi da bazaka risina agare ni ba,
K o d a j i n w a n n a n tambaya d a g a bakin sarauniyar
• lasmirat sai saurayin ya kura mata idanu batare da
y a c e d a i t a uffan b a
C i k i n f u s h i l a s m i r a t t a s a k e d a k a m a s a t s a w a a karo
na biyu tare d a maimaita tambayar t a ,
Kawai sai saurayin ya saki wani tattausar murmushi
daya karawa fuskar s a kyawu sannan y a dakamata
sarauniyar lasmirat tsawa ya dube ta yace
" Ya k e wannan sarauniya mai takama d a abinda
bazai d a w w a m a a g a r e t a b a kiyi sani cewa bazan
taba girmama ki ba,:

Domin a halin yanzu abinda na sani kawai shi ne
bambancin dake tsakani na dake shine ke diya mace
ce Ni kuma namiji, mulkin da kike takama dashi
tamkar kumfar kogi ne akoda yaushe za'a iya neman
sa a rasa shi,
Kafin saurayin ya gama rufe bakin sa fiye da rabin
dakarun sun zare makaman su yunkura izuwa kansa
suna ihu da kururuwa mai firgitar wa
Koda ganin hakan sai ya gyara tsayuwar sa gami da
sandar dake hannun s a yana dakarun
mai jiran karasowar
Inda ace mutum yana tsaye a wannan waje lokacin da
wadannan dabaru suka ruga izuwa kan saurayi sai
yayi tsammanin dandazon zakoki n e suka farma
barewa guda daya, saboda tsananin kwarjini daban
tsoron s u , .
• Yayin da ya rage saura baifi taku uku tsakanin su ba
sai kawai akaga saurayin ya dako tsalle daga inda
yake tsaye tamkar an harboshi daga cikin baka yana
Saman ya sanya sandar sa ya daki kawunan dakaru
mutum goma,
Take dakarun suka tsandara ihu sannan suka zube a kasa
magashiyan,
Sannan ya dira bisa kafafuwan sa a turba cikin gwaninta, .
Nan take aka kacame da azababban yaki matukar muni
ban tsoro daban Al'ajabi.

Dakarun suka wanzu suna kaiwa saurayin sara da suka
cikin matukar zafin nama JURIYA DA BAJINTA,
Shi kuwa ya wanzu yana kare hare haren su cikin wani
irin bakin zafin nama, kuma yana makosu da sandar sa
daga kan dawakan su suna yin MUGUWAR HALLAKA,
Na fa waje ya yamutse da ihu da kururuwar mazaje, karar
karafniyar karafa t a cika dodon kunne, gawarwakin
dakarun suka watsu a wajen gasu birjik kwance cikin jini.
Sai da aka shafe tsawon sa,a daya ana wannan gumurzun
babu sassauci,
Sa'adda sarauniya lasmirat t a lura cewa saurayin ya
hallaka fiye da rabin dakarun sai ta cika dà matukar
mamaki, domin a tarihin masarautar t u n a zamanin
mahaifin ta bata taba samun wanda ya hallaka dakarun
gidan sarauta mutum uku ba,
Kuma zuciyar ta ta harzuka bisa ganin yadda dakarun ta
keyin muguwar hallaka
Duk inda saurayin ya sanya a gaba sai dai kaga dakarun
na zubewa kasa cikin mawuyacin halin dake tsakanin :
RAYUWA DA HALAKA,
Nan fa dakarun suka dimauce bisa ganin iri kisan da*
saurayi keyi musu,
Amma koda kwarzane daya basu samu nasarar yi masa ba,
Daga can nesa jama'ar kasuwar suna kallon fafatawar da
ake y i wadansu ta tagogin gidajen su suke leken abinda
yake faruwa,

Kuma suka cika d a mamaki bisa ganin yadda saurayi
yazamewa dakarun sarauniyar lasmirat ANNOBA DARI
wanda a tarihi hakan bai taba faruwa ba,
Lokacin da sarauniyar lasmirat ta fahimci cewa
idan h a r a k a cigaba d a wannan artabu a haka dukkan
dakarun t a zasu rasa rayukansu sai kawai t a dakamusu
tsawa suka j a d a baya sannan ta dako tsalle daga kan
dokokin t a tamkar a n harbota daga cikin baka t a sanya
kafafuwan t a biyu t a daki saurayin
l a kirji d a dukkanin
karfin ta,
Saboda karfin dukan sai da saurayin ya yi katantanwa sau
uku sai ya turje aka sake yin sabon kallon kallo tsakanin
lasmirat da saurayin,
Lasmirat t a kasance mace mai madaidaicin jiki ba
doguwa ce b a gajera ba, tana da kyakkyawar fuska mai
d a u k e d a f a r a r e n i d a n u d a r a d a r a t a n a d a siririn hanci
wanda akasan s a aka yanka wani dan madaidaicin baki,
wuyan yana kyawu tamkar na barewa, gashin kanta baki
n e sidik mai sheki d a kyalli,ya zuba h a r izuwa kasan .
kwankwason ta,
Kirjinta a cike yake kuma a tsaye kyam bai rankwafa ba,
cikin t ạ a shafe yake tamkar bata taba cin komai ba, daga •
sama kugunta ya tsuke daga baya baya kuma ya bude yayi
tudu sosai, tana d a zabga-zabgan cinyoyi, fatar jikin ta
farace mai kyalli,
Wohoho Hakika d u k inda kyawu yake tabbas
sarauniyar lasmirat ta kai, domin babu wani da namiji mai
hankali d a zai yi tozali d a lasmirat face y a kamu da
m a t u k a r k a u n a r t a .

Yayin d a a k a shafe tsawon dakika talatin a n a wannan
kallon kallo, sai lasmirat ta zare wata zabgegiyar takobi a
damtsen t a kaiwa saurayin wani wawan sara d a nufin
tsinke m a s a w u y a ,
Cikin bakin zafin nama saurayin y a sunkuya takobin
lasmirat ta sari iska,
Kawai sai suka kacame d a azababban yaki suka wanzu
suna kaiwa juna sara d a suka cikin tsananin zafin nama
JURIYA DA BAJINTA,
Ana fara wannan gumurzu n e lasmirat t a fahimci cewa
tsananin KARFIN DAMTSEN saurayin ya nunka nata sau
biyar gami da zafin nama.
Sai da sa,a daya ta shude ana fafatawa batare dayan s u ya
samu nasarar lakutar jikin dan uwan sa ba,
Bisa dole lasmirat t a sake zare wata takobin yazamana ta
kai wa saurayin hari da takubba biyu,
A n a Cikin wannan artabu n e saurayin y a shammaci
lasmirat y a gabza m a t a wawan naushi a fuska saboda
karfin naushin sai d a sarauniyar lasmirat tayi sama
tamkar an janye ta kugiya,sannan ta fado kasa a matukar.
galabai ce,
* * * * *
Bayan shudewar mulkin sarki Hulbaru n a birnin Misra
anyi wata gagarumar sarauniya d a ake yiwa lakabi da
lasmirat bintu kazmal
Lasmirat ta kasance kyakkyawa t a gaban kwatance kuma
gagarumar basadaukiya,mace m a i kamar maza,dadin

dadawa kuma mashahuriyar attajira t a shara ainun a
fagen sanin ilimin tsafi,
A gaba daya nahiyar babu kasa mai karfin tattalin arziki
kamar ta ta
Sau tari manyan sarakunan duniya kan kaiwa lasmirat
HARIN BAZATO domin mamaye kasar t a kuma su
mallaketa a matsayin matar aure amma sai abu ya ci tira,
domin duk sa'adda aka gwabza yaki sai dai sarakunan suyi
asarar dakarun yaki da dukiya mai tarin yawa bisa dole
suka janye aniyar su
* * ⽔ ⽕ *
Lokacin da sarauniya lasmirat ta fara kwadaituwa da son
d a namiji sai ta gudanar da bincike bisa halarar tsafin ta
domin taga irin namijin da ya dace ta aura
Abinda binciken ya tabbatar mata shine mijin da zata aura
. shi ne wanda yafi kowa talauci a duniya
Binciken yakara tabbatar mata da cewa matsawar ta auri
wani d a namiji b a shi h a r t a tara dashi tofa zata rasa
komai nata da ta mallaka a duniya,
Sa'adda sarauniya lasmirat taga wannan al'amari a
cikin halarar tsafin t a s a i t a cika d a matukar b a k i ciki
maral musaltuwa
Tava 'ayi ace sarauniya, abayr ni acena nuri aoda yar.
BASARAKE karfin mulki d a t a r i n dukiya a wannan
nahiya baki daya,

Tabbas hakan kaskanta daraja ta ne da kimata a idanun
sauran sarakunan duniya
Kuma idan na auri talaka dukiya ta da mulki na zasu
zamo bisa karkashin ikon sa,
Lokacin da sarauniya lasmirat ta zo nan a tunanin ta sai
hankalin ta ya sake dugunzuma fiye da ko yaushe kuma ta
rasa abinda ke yi mata dadi,
A wannan lokaci lasmirat n a zauna n e a bisa wata
kasaitacciyar kujera amma sai ta mike tsaye ta shiga kai
komo a cikin turkar ta,
Daga karshe dai lasmirat t a yanke shawarar ta ziyarci
wani boka dake zaune a wani gari dake iyaka da Birnin
misra,
* * * *
Lokacin da sarauniya lasmirat t a isa gidan boka
Dayyubul-Barmas ta kadaita dashi a cikin turakar sa
Nan take ta kwashe labarin abinda ta gani a cikin halarar
tsafin ta ta zayyanewa boka Dayyubul-Barmas tun daga
farko har karshe, sannan ta dora da cewa
Yakai wannan boka mafi girma a halarar tsafi kayi
sani cewa Babban burina shi ne na auri mijin da yafi kowa
Arziki a duniya sannan ina da burin na rayuwa
k a m a r
shekaru dubu biyu domin nazamo nafi dukkanin
sarakunan duniya dadewa a bisa karagar mulki,
Yayin da boka Dayyubul-Barmas yaji irin bukatar dake
tafe da sarauniya lasmirat sai ya jinjina al'amarin a cikin
r a n s a ,

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login