Showing 1 words to 3000 words out of 3441 words

Chapter 1 - GORAN DUMA BOOK 1 PART 2

13 Nov 2024

1676

GORAN DUMA BOOK 1 PART 2







"Zolayata kawai kike Momi, yarinyar da ta
fi sonku da ni zan 6atawa kaina lokacin zuwa ganinta takanas?"
Suna dariya su duka Sa'a ta shigo da farantin kayan ruwan zafi.
25/12/2012
Ratar kwanaki goma sha hudu aka samu da zuwanta Abuja cikin kwanakin nan duk yadda
Mahaukacin
Masoyi ke son nuna
mata
hatsabibancinsa ta hanyar sakonninsa, ya nuna mata kwarewarsa a wayoyinta biyu, a kala-kalar toro da hasashe babu wanda ba ta gayyatowa zuciyarta ba har idan abin ya yi tamari sai ta kashe wayoyi, duk lokacin da ta kunna kuma zai shayar da ita toro da mamaki a tsarin kalamansa
Wannan fargaba da tashin hankalin suka dinga motsa mata larurarta ta hawan jini da ta gamu da ita wasu shekaru da suka wuce, abin boyewar ya zamar mata biyu, wato boye barazanar Mahaukacin Masoyi da take fuskanta. Da kuma
• boye cutar da barazanar ke haifar mata gudun kada. ta tashi hankalin iyayenta da marikanta.
Cikin dabara take zuwa asibiti gain likita, haka zalika cikin dabara take shan magungunanta.
Akwai wani 'civ nata mai hadari da ta

tada haduwa da shi na rudewar kwakwalwa da gazawar was sassanta a can lokacin baya.
Faruwar wannan rudani da motsawar hawan
• jininta ya sa likitanta ya bata shawarar ta rika kwantar da hankali da ba wa kwakwalwarta hutu saboda gudun motsawa wancan ciwon.
Sanin girman hatsarin ciwon a tare da ita ya sa take son watsar da shaftar Mahaukacin Masoyi ta Gauke ta miyar da babu gishiri, amma sai hakan ya faskara, wani lokacin sai ta zabi kashe waya, in ta kashe kuma sai ta rasa abin. dauke kewa, ko sadarwa tsakaninta da mutane:
30/1/2013
Yau laraba da dare wajen karfe tara, ta gundura da kallon talabi in sai ta dauko na'urá mai Kwalwarta ta lika: Modem ta hau yanar gizos kai tsaye ta nufi kafar sada zumunci ta: facebook cike da dokin shiga dandalin DUNIY AR MARUBUTA da wata Rawarta marubuciya mai suna Kamshi (Hauwa Abubakar Lawan Maturare) ta gayyace ta.
Dandalin Duniyar Marubuta na facebook cike yake da daruruwan marubuta da makaranta ana ta harkokin arziki tare da kuma abubuwan karuwa da na nishadantarwa. Tana shiga ta ci karo da wani rubutu da marubuci Muh'd Lawan Barista yayi mai taken.

"ZAMAN 'YA'YANA NAKE".
Duk lokacin da wani sabani ya shiga tsakanin Mamuda da matarsa Aliva, sai la bude baki ta ce masa, "Mudi ni fa zaman 'ya' yana nake yi, in banda su, wallahi da tuni ka manta da ka
taba sanina"
Abin na damunsa kwarai, tun yana ji ya hadiye abin a ransa, yau dai ya yunkura ya sanar da ni, yana kuma jira ya ji daga gare ni, shin matar ta la tana sonsa ke nan? Kuma wane mataki ya kamata ya dauka a kanta?
Ni dai ya rantse min ya ce, babu wani abu da yake mata na cutarwa, sai dai ma tsabar kyautatawa. Wacce shawara ya kamata na ba shi?
Da dokinta ta shiga rubutun tana juya abin a ranta, "Zaman 'ya°ya kamar wata kalmar ado ce. ko ta fanshe. takaici a bakin mace lokacin da
•sabani ya shiga tsakaninsu da mazajensu, duk da akwai masu fada da gasken kuma su yi a aikace, amma daga matar har mijin ba su kula da hatsarin da suke ciki na gaza sauke hakkokin juna lokacin da suka ki daukar mataki akan kalmar ba da yake ta fi gain laifin matar ta tashi nata sharhin sai ta
ce.
"Mata fa akwai kwakwazon korafi, tare da gaza hakuri in an kwatanta musu irinsa, na

tabbatar duk matar da mijinta ya ce mata.
Don 'ya' yana nake zaune da ke.
Mawuyacin abu ne wannan auren nasu ya dore saboda yadda zata tattara kauna ta yanke masa.
Ta fito ta cigaba da bin ragowar labarun da marubuta suka aiko. Ta yi tsokaci (comment) a wanda ta ke muradi ta yi jinjina (like) a wadanda suka burgeta.
Ranta ya fara hake Kirinta ya dan samu sarari, dama can kafin Mahaukacin Masoyi ba Karamin kaye da sanya nishadi Duniyar Marubuta ke ba ta ba.
Ta bar nan. ta tafi Dandalin masoya jaridar
Aminiya, zaba66iyar jaridarta ke nan tun kafin ta zama marubuciyarsu, saboda haka ita ma wata ginshiki ce a fadada mata zuciya.
Jakar sakonninta (inbod) ya rika kuka, ta duba, akwai wulgawar sakonni kusan goma a ciki.
Kamar zata share su ba tare da ta duba ko daya ba
•kasancewarta marubuciya, bugu da kari kuma mace wada ba ta tsallake neman maganar maza marasa mafadi a facebook, amma da ta tuna fila akwai wadanda za su iya dangantaarta a masu sakon yan uwa ko abokan aiki da kawaye, sai ta tafi inbod din.

Kamar yadda ta vi tsammani ta tarar da sakon Yayarta Balaraba, wadda ke ta faman yi mata mitar ta je Abuja ta ki zuwa gidanta, kuma ta tsiri wata muguwar dabi'a ta kashe wayoyi. Ta amsa mata da ban hakuri da alkawarin share mata hawaye.
Tana barin Balaraba ta ci karo da sabon sakon Mahaukacin Masoyi, username dinsa ke nan
"MAHAUKACIN MASOYI'.:
Zuciyarta ta fara bugawa fat-fat, amma dan
Karfin hali ko karanta sakon ba ta yi ba ta tafi bincike bangonsa (wall).
Abin da ta tarar ba zai mata amfanin komai ba, sabon account ne hahuwar shekaran jiya, babu komai a cikinsa na dorarwa, adireshin ma ban da suna babu komai a bude, ba ta tsawaita wani tunani ba ta toshe shi, yadda ba zai sake sa ido a kanta a facebok ba, cikin jin karfin gwiwar abin da ta yi ta ci gaba da harkokinta tsawon awa daya.
Tana shirin sauka saboda lokacin baccinta ya yi, ta koma inbod saboda tunanin kar ta bar sakon da suka kamata, ai kuwa ta ci karo da sabon Mahaukacin Masoyi mai karin i a karshe, wato Mahaukacin Masoyii, shaidar ya harbo jirginta, ya kuma dana mata wani tarkon. •
Na fara mamakin , vadda kike son bude

Kwanji ki guje min, duk da ban bude nawa na fara sonki da yanke Kaunar rabuwa da ke la dalilin wani abu ne mai sauki ba.
Idona a kanki ya ke Rumaisa'u ki daina wahalar da kanki da tsammanin zaki iya kubce min. Wannan wane irin zalunci ne don Allah? Kin kashe wayoyi saboda ni na share wanna takaicin, kin shizo dandalin sada zumunta na cika da doki na biyo ki, amma kawai dan rashin adalci sai ki Gulle tsakanina da ke? Ki daina tsammanin zan yarda da wannan.
Ba ta ko Karasa karanta sakon ba ta yi baya a guje ta fice daga facebook din sannan ta kashe na'urar gaba daya ta bige da rafka tagumi.
Ta tabbatar wa kanta in ta kai karshen* sakon Kila Mahaukacin Masoyi ya fada mata kalar? kayan da ke jikinta da irin yanayin zaman da ta yi a yanzu. Amma duk da wannan rudanin a yanzu ne ta fara ji a ranta ya kamata ta san waye Mahaukacin Masoyi.
31/1/2013
Tana zaune a gida dab da Zahar Mubarak autan Hajiya ya kirata a waya.
"Anti kin fita binciken da kika ce za ki?"
A tausashe ta ce.

"A'a mubarak, wani abu ya faru?"
Ya amsa a ladabce yana dariya.
"Babu abin da ya faru dama neman alfarma zan yi ki Karaso nan B.UK ki dauke ni, na bada aron mashin dina, kin san kuma hana goyon nan ya janyo Karancin abin hawa"
Ta yi 'yar dariya ta ce.
"Ban fita ba, amma bari na zo na dauke ka".
• Ya ce, "Godiya nake Anti, amma dai a dan gyara laifin aron babur din da na bayar'
Ta ce masa.
VB'
"Kar ka damu"
Ckin sauri ta debi wayoyinta da tun hantsi ta kunna ta ke jiran sakon Mahaukacin masoyi Wanda ta yiwa tanade-tanade marasa lissafi bai kira din ba, har ta sallaci azahar ta dawo da tammanin zata tarar da sakonsa nan ma shiru, har zuwa lokacin da Mubarak ya nemi agajinta.
*Hajiya taimaka ki ara min mota in dauko
Mubarak".
Ta samu Hajiya a falonta ta fada mata haka tana 'yar dariya. Hajiya ta yi mata kallon tsab ta ce.
"A'a kin yi dariya da kyau, kina fama da kanki zaki je wani dauko Mubarak? Ina babur dinsa?"

Kai tsaye ta amsa.
"Ya yi faci ya ce min ya rasa mai liki saboda matsalar masu gyaran, sannan ga Karancin abin hawa a gari
"Shi ne sai ke za ki dauko shi?"
Ta wuce kan talabitin ta dauko makullin
motar tana cewa.
"To ya ya za a yi Hajiya? Ni ma ina son ganin wulgawarsa a gidan tun safe bakina ke tsami ba abokin hira"
Hajiya ta yi dariya ta ce.
"Allah Ya bada sa'a,
•Allah Ya kiyaye
hanya"
Tana ficewa ta amsa, "Amin".
Hajiya ta sauke kai tana girgizawa zuciyarta cike da tausayin Rumaisa'u, tattausar mace mai kirkin gaske, amma Allah Ya kaddaro rayuwarta cikin jarrabawarsa.
Ba ta taba jin wanda ya zauna da Rumaisa'u ya fadi rashin kirkinta ba, duk kuwa wanda ya ce ba ta da kirki da zarar ka dube shi zaka ga rashin kirki a fuskarsa.
Tun kafin ta shiga makarantar ta yi kiransa a waya.
"Mubarak kar fa na shigo ka cika min mota da abokanka in ba haka ba, kar ka kuma taso ni

zuwa daukarka"
Yana dariya ya amsa.
"Na san da haka, shi yasa ma na ware gefe"
Ta ce da shi cikin dariya.
"Aha! Ka shirya na shigo".
Ya ce, "Amma-akwai 'yan uwanki mata, na
san..
Ya ki karasawa yana dariya, ita ma ta yi dariyar ta ce.
"Babu matsala"
Tana shiga ta ciko mota da Mubarak da abokan karatunsa mata, sai wani nataccen abokinsa Shu'aibu da ya matsa sai an dauke shi har yana cewa Rumaisa'u.
"Anti in ma ba zaki dauke ni ba sai na daura dankwali ko na yafa gyale, sai in ara cikin
"yammatan nan ba zaki rasa mai spare a jaka ba"
Dole Rumaisa'u ta vi dariya ta ce.
"Mai ya yi zafi? Shigo mu tafi"
Ta hada su a gaba shi da Mubarak ta tashi motar, yayin da was tunanuwa masu nauyi suka wulga a zuciyarta, tunanin da ke fawar sa ta kukan
• jini in da ana yi duk da ta san akan su tana kukan da ya fi jini ciwo.
Haka ta tashi motar ta fice a guje tana satar kallon wurare a makarantar wadda ta kasa hadiye

wa sai da ta fara zubar da hawaye, sannan ne Mubarak ya tuno Katon kuren da ya talka, ya yi saurin dora hannu a ka ya kame baki yana satar kallon titi cike da nadama.
Ba yau ya fara gayyato Rumaisa"u ta zo daukarsa ba, amma yana sane da yadda matsayar dalibai jiran shigowa bus a nan makarantar ke zama wani katon abin fami a raunin Rumaisa'u, dan-haka sai ya kan yi gaba su had a hanya ta dauke shi su fice, to ko zata yi hawaye kadan ne.
Saboda haka ne ita da Mubarak suka yi dif a motar, matan baya ke ta hirarsu, Shu'aibu da ya rasa abokin hira yake saka musu baki, Mubarak ya rasa bakin ba wa Rumaisa'u hakuri, it kuma ta kasa daina zubar da hawaye, har suka fito makarantar suka hau babban titi.
"Mubarak dubo min gilas dina a jaka"
Rumaisa'u ta fada dan tsananin kaunar ta manta abin da ke sa ta hawaye da kunan zuciya.
Cikin doki Mubarak ya dauko jakarta yana
cewa.
"Ina ga dai Anti gayyatar Karshe na yi miki ta zuwa ki dauke ni, in dai ramu zai dinga baci haka"
Ta kardi gilas din tana dariyar yake, ta ce.
"Ko ba ka gayyato ni ba Mubarak in na

sur: tawa kaina makarantar nan ina yin abin da ya fi haka, gara ma ka dinga gayyato nin ina zuwa kila na saba da kallonta gwauruwarta...
99
Ta kasa ci gaba da magana saboda kukan da ya toshe mata makogwaro, ta bige da bude gilas kawai ta saka sannan ta hadiye kukan.
Motar ta yi tit har suka kawo mahadar tituna na Kabuga, yanzu ta hakura da kukan duk da Karfin hatsi ta sa masa, amma dai ya bi umaminta ne da taimakon hango wasu mata bivu da ta yi suna bara a tsakanin motoci.
• Matan ba wai tsoffin almajirai da ido ya saba, gani ba, a'a matasan mata "yan shekaru ashirin da biyar zuwa talatin, kuma abin da ya fi shayar da takaici shine da yanayi irin na mazan da suka yi kaurin suna wajen hawa gajimare (shaye-shaye).
Ba ta gama cika jakar mamaki da albininta ba sai ga su gabanta. Dayar ta zuro hannu ta rike sitiyari tana layi.
"Hajiya ki taimake ni kamar yadda Ubangiji
Ya yi miki sutura ki ba ni na siye abinci da dan hayaki.."
Dayar kuma ta cafe da cewa.
"Ko shafa motar nan aka yi dai an san babu ba ta wulga ta kanta ba... Kuma hada mutum da

Allah ba ya nufin an rasa vadda za a yi, in molar nan cancakat ma so sacewa na rantse yanzu zan muku rufa ido in dauke she... ko ba haka ba?"
Suka dubi juna ita da su Mubarak, zai yi magana da hama shi da vi masa inkiyar ya bude mata jaka, amma sai ya Kankame jakar ya juya keya. Ta fahimci manufarsa saboda iaka ta yi 'yar dariya ta dube su da kyau, ta ce.
"Ai ni ma da na ganku mura na yi da Allah ko 'yar naira ashirin ce ku ba ni, goro zan ci".
"Yawa ki ke Hajiya".
Nan da nan kamar walkiva suka face daga gare ta. Duk motar kowa ya rude da dariya lokacin da suka sami hannu suka wuce. Shu'aibu ya ce.
"Anti yaya aka yi kika san mashayan nan ba sa son a roke su kudi?"
Tana dariya ta ce.
"Ko daya, na dai san wanzami baya son jarfa, amma dai na yi mamaki in labari aka ba ni shaye-shayen mata ya kai matakin fito da su kwararo da dabi'u irin na 'yan daba wallahi Karyatawa zan yi... Amma sai idona ya ga zahiri..."
Shu'aibu ya tareta da fadin.
"Anti ai gara wadannan da ganinsu kin san dama sun gagari iyayensu ne, akwai wata budurwa

a unguwarma, ba zan iya kirga sau nawa na ganta g make ba. Na sha kama ta na kai ta gidan yayata a isare la ya fi a Kirga. Ina mata gudun Gata-gari su cimma wata mummunar manufarsu a kanta".
"Innalillahi wa inna ilaihi rail'un"
Rumaisa'u ta fada cikin Kololuwan bayyana takaici da alhininta, sannan ta dubi Mubaak ta ce.
"Mubarak ko akan shaye-shayen mata zan vi batuna a wannan watan ne?"
"Good! Wannan zai kayatar kuma zai fadakar"
"Za ka taimake ni da bincike ke nan?"
Y a amsa mata da Karfafawa
"*Babu matsala, yau zuwa gobe ina cikin
'yanci"
"Ko ba ka cikin 'yanci ma na ga ai kana dagewa ka yi aikina".
Ta fada ba tare da ta dube shi ba, da ya yi dan nazarinta sai ya vi dariya ya ce.
"Allah Y a sa ban kauce hanya na yi kuskure
a maganata ba"
Ta yi dariya kawai, Sha' aibu ya ce.
"Ka kawota gidanmu ta ga yarinyar da na yi maka maganarta idan tana da bukata"
Cikin sauri Rumaisa' u ta ce.
"Me zai hand? Idan Ahu damuwa mu je

gida ku ci abinci sai mu fito tare".
"O.K babu matsala".
Inji
Shu'aibu,
Mubarak ya dora da cewa, "Sai kuma ina?"
Ta ce, "Da safe ka raka ni freedom na yi cigiyar Hajiya Maryam".
1/2/2013
Ta wayi gatin ranar yau da kumajin da ta jima ba ta tanadarwa kanta shi ba, har ga Allah tana ji a ranta sun yi hannun riga da Mahaukacia Masoyi tunda dai ga shi kwana biyu ke nan babu sakonsa a waya, saboda shi ma. ta Kara lokutan hawa facebook, amma ya bacewa ganinta, wannan ba karamin dadi ya yiwa ranta ba, ta shirya Karasa
•watsar da shi da tanadin yadda zata gungura ragowar tsumman rayuwarta da take wa taken
GAY
gawa ta ki rami ba.
ewsesh
Ba kamar yadda ta so ba,
wato zuwa
Freedom tare da Mubarak, sai Alhaji ya ba shi wani aiki na wakiltarsa daurin aure garin Katsina, a ranar juma'ar da jiran bikin nadin sarauta a washegari asabar. Wanan ya sa ita kadai ta ie Freedom bayan an sauko masallaci. Ba ta sami gain Hajiya Maryam ba kan abin da ya kai ta, sai dai ta samu garantin ranar samunta. Ba ta dawo haka ba, sai da ta shiga sashin labarai neman ji daga wanda ya kawo wani rahoto game da yadda

m ata "yar maye ta dabawa wani matashi wuka.
A ranar yau Rumaisa'u ta Kara godewa
Ubangiji da Y a hukuntota a mai son bincike da yin rubutu game da abubuwan da za su amfani alumma, saboda yadda ta ke haduwa da ayoyinsa iri-iri masu Kara mata tsoron Allah da gode masa, da kuma masu sanyata gudun yi maSa butulci da daukar sabonSa ba a bakin komai ba.
Tana Freedom radio aka yi sallar la 'asar dan haka kafin ta fita: sai da ta vi alwala ta shiga masallacin mata tayi sallah.
R
Bayan ta idar ta bude jaka ta hau goge-gogen fuska da gyara daurin kallabi ta gama tana mayar da kayan jaka taken shigowar sako ya kada a wayarta.
Da karfin hali irin na dan daudun da ya karo kadangare ta cafko wayar ta fara duba sakon.
Rumaisa'i
Ban kasance ma'abocin sauraron wakoki ba, amma abin mamaki wata waka ce yanzu take. gilmawa kunnena wadda ta motsa min dubun taki kaunar a makoshi nan. Kin san wakar? Ita ce wakar 'YAR MAYE, wakar ta shige ni! Ta sa ni tausayin kaina fiye da tausayin matan da ke jefa

Kansu a halin shayc-shaye, saboda na san Biyar Kaunarki ta make ni fige da vadda ko wanne irin kayan maye ke make ma 'abotansa.
Idan Kin taa nazari akan van maye, ki zace ni da kalar tausayi fiye da yadda kika san Su.
Mahaukacin Masoyi.
Ta yi iyakar Kokarinta waien hadiye rudaninta saboda wasu mata biyu da ke sallah a gefenta, kuma wannan dakewar tata ce ta bata damar yin wani tunani na zaton, duk yadda aka yi Mahaukacin Masoyi akwai kafar da yake samun labaran halin da ta ke ciki, ya turo sakonsa a kansa, in dai shi ba jinnu ba ne.
Ba ta tsawaita tunani ba bare ta samo abin da zai kore mata wanda ya gaskata ta fara latsa wayarta ta kira Mubarak.
"Mubarak wa ka sanarwa cewa zan yi rubutu akan masu shaye-shaye, kuma wa ka sanarwa zuwana Freedom?"
Mubarak ya jima yana jan numfashi kafin ya amsa mata.
"Anya na yi maganar nan da wani? Kusan ma fa wallahi na manta maganar tun jiya da muka ie unguwar su Shu°sib ""
Ta vi ajiyar zuciya ita ma ta jima tana jan numfashi, sannan ta ce.

"Ina Shu'aibu?"
Ya ce, "Mun yi waya da shi yau da safe yake ce min yana kwance a gida saboda ya gamu da masassara, wani abu ya faru?"
Muryar Rumaisa'u na rawa la vi saurin girgiza kai kamar yana a gabanta.
"A'a babu komai, kana jin babu wanda zai
¡ya sanina wajen Shu' aibu har ya bashi batun ina bincike akan mashayan

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login