Showing 1 words to 2555 words out of 2555 words

Chapter 1 - Amarzadan da Zoben Farsiyas Part 1

12 Nov 2024

1457

Amarzadan da Zoben Farsiyas Part 1


Kairu Nainu
Kufaru Kairu Nainu ya yi Karaji da fushi
irin wanda ya dade bai yi ba. Wuta na fita daga bakinsa; idanuwansa kuwa kai ka ce su ma wani gar-washin ne. Kahonninsa biyu na gaba, murdaddu, sun tankwara har sun kusa hadewa da dogwayen kunnu-wansa. Jelarsa a fike dauke da Kananan Kahonni wad-anda suka biyo tsawonta har zuwa doronsa, sai wutsil wutsil take yi cikin arashi da karajinsa da wuni wun-
insa.
Dukkanin shaidanu da ifritai a wannan hali a tsorace suke, domin sun san, a cikin wanna fushi nasa, ba irin ta'annatin da Kufaru Kairu Nainu ba zai iya zar-tawa a kansu ba, musammam ma wadanda suke da hannu a wannan al'amari na takaici. Ba was shakku, aika-aikar da Amarzadan tareda dakarun mayakan Jin- nun Yarima Ibrahima na Salmendahar suka yi masu
kwanakin baya a Kakula, sun kai makura, kuma ba su
taba zaton hakan za ta iya faruwa ba. Kufaru Kairu
Nairu ya sake yin wani irin juyi cikin matukar fushi
har sai da kamaninsa suka cania cikin na wasu mi-
yagun dabbobi da halittu har sau biyar a dan lokaci
Rankani kafin ya sake juyowa. Duk kuwa a yayinda
yake nuni tareda tuhuma ga babban kwamandansa,
Kan-Kan. Kananan shaidanu da ifiritai da suka hallara
a wannan Katon rami na bautar Iblis, suka zube Kasa a
firgice, zaton ba wani bayani da Kan-Kan zai yi wanda
zai wadatar da sarkinsu, uban mabauta Iblis, Kufaru
Kairu Nainu.
Amma, Kan-Kan yana tsaye kikam kamar
bishiya, a kufule, yana tsuma, yana gurnani kamar ya
fashe, har wani kore-koren hayaki yana burtsowa ta
tsakanin zara-zaran bakaken gasun jikinsa da ta cikin
kunnuwansa, wadanda suka yi sak da na uban gidansa,
Kairu Nainu, domin shi ma Ifiriti ne.
A wannan babbar Majalisa ta gaggawa wadda
Kairu Nainu ya kira, ba wani muhimmin Ifiriti da
shaidani a Kasar Balzakakul da Kasar Kawancensu ta
Mudasani da bai halarta ba. Hakika, a shirye yake ya
y1 ikirarin yaki tsakaninsu da Salmendahar, kafin ko
bayan ya baje Samandar; kuma ba abinda Kan-Kan ya
ke jira irin a ba shi wannan umarni don su shawo fan-
sarsu. Ba wani jawabi ko dalili da zai kare Kan Kan.
Kuma wannan daba ita yake dokin a sa a hannunsa.
A waje kuwa, sojojin Balzakakul fiye da dubu
arba'in, cikin makurar shirin yaki, rukuni rukuni, kowanne da kwamandansa, suna jiran nasu umarnin daga Kan-Kan. Kuma ba shakka a shire su ke su mutu da su rayu da bakin cikin bazaar da aka yi masu a Kakula, can Kudu-maso-Gabas da dajin Tamassi.
"Kyar! Kyar!! Mutuwa ga Salmendahar!!!" Kairu Nainu ya sabe bakar alkyabbarsa mai dugo dugon launin ja, ya jinjina wani irin jan mashi nasa mai tsini uku, ya bude makogwaronsa da wata irin murya mai ban toro wadda amonta ya cika wanna kogon dutse, kai ka ce aradu ce ta fado.
"Kyar! Kyar!! Kyar!! Mutuwa ga Salmenda-har!!", suka amsa tare cikin matukar fushi da ihu, suna jinjina takubbansu da garkuwarsu da masunsu, wuta tana tartsatsi daga bakunansu. Kan-Kan ya sake mai-mata wannan muguwar aniya tasu har sau uku, kuma duk suna amshewa cikin fushi da dokin aikata hakan.
Kufaru Kairu Nainu ya kusanto Kan-Kan a fusace, ya cafo wuyansa da wannan hannun nasa mai kamar Kafafun mikiya, yana wani irin gatsine fuska, yana wasa hakora, ya ce,
"Kaiconka Kan Kan! Sakacinka ne ya jawo mana wannan takaici! Na ba ka zuwa gobe ka gama shirin yaki, domin aiki biyu ya samemu cikin gaggawa.
Dakarunmu zasu farma Kasar Salmendahar, su fatatta-kata; sannan kuma was zaba66u zasu turfafi Saman-dar su murkusheta su kamo mana Amarzadan da sara-kunansu duka.
Ya yi wata irin dariyar Reta, sannan ya
ce, "Da su za mu yi godiya ga iyayen-gijinmu!!"
Yana fadar haka, amma tun kafin ya saki wuyan Kan-Kan, sai babban jakadan Mudasani, Dorko Kwak, ya tashi ya yi hanzari da Kwakwarar murya.
"Mai daraja Kufaru Kairu Nainu! Ya kai mai
Mashi tsini uku! Ya kai mafi kusanci da Azazel dan Lis! Ya maji-dadin Tir! Da Zalambur! Jin wadannan kirari, sai hankalin Kairu Nainu ya koma kan wannan jakada. Jakada ya ci gaba da cewa, "Kufaru Murti Agar ya umarce ni na shaidawa Kufaru Kairu Nainu cewar Mudasani za ta ba da gudun-mowar dakaru dubu ashirin, shiryayyu, domin a tabbata an gama da wadannan makiya namu.
Jin haka, sai Kairu Nainu ya dan saki fuskarsa, ya saki wuyan Kan-Kan, sannan ya juyo ga jakada, har yanzu dai cikin murtukakkiyar fuska da murya wad-anda ba su san sassauci ba.
"Ka isar da godiyarmu ga masoyinmu Kufaru
Murti Agar. Yaushe za su iso?"
"Muna bukatar kwana bakwai domin mu kam-mala shirye-shiryenmu, Kufaru."
"Amma, ba mu da kwana bakwai!" Kan-Kan ya sa baki tamkar shi ya gama nasa shirin.
A wannan lokaci, Kairu Nainu ya koma kan kujerarsa da aka kera da wani bakin Karfe, ya zauna yana wasi-wasin wannan gudun-mowa da kuma lo-kacin da Mudasani suka bukata. Ya sani a ransa cewar tunkarar Salmendahar babu cikakken shiri kasada ce babba, domin bai manta da kashin da suka sha a wan-can karon da suka yi a sanadin mutuwar Sultan Kurra na biyu ba, da kuma satar da suka yi masu ta Zoben Farsiyas. Hasalima dai, saboda bukatar wannan tai-mako ne ya gayyaci wakilan Mudasani a wannan taro na gaggawa domin suna da yarjejeniyar taimakon juna a hali irin wannan. Amma, kwana bakwai sun yi yawa a nasa tunanin. Can ya yi ajiyar zuciya, da kuma san-yaryar murya ya ce,
"Da za ta yiwu ku iso nan a kwana hudu da zai fi ma'ana, domin ba ma son tsarinmu ya karye saboda jan lokaci. Azazel ba zai yi murna baaaaa!"
Dorko Kwak ya kallo wani mutukakken Ifiriti, wai shi Daramba Is, wanda shine babban kwamandan dakarun Mudasani, kamar mai neman izni. Shi kuwa ya vi masa alama da ka. Sannan Dorko Kwaf ya ce,
"Toh, shugabana Kufaru. Wannan mai yiwuwa ne, idan da za mu rage tafiyar, mu hadu da ku a wani gu a hanya.
Kairu Nainu ya tashi tsaye ya ce, "Wannan ya vi daidai." Sannan ya dubi Kan-Kan, "Sai ka sadu da Jarmansu ku shirya komai, sannan ka sanarda ni gobe.
Amma Samandar ta bi Rasa jibi. Kyar!!!!" Ya yi Karaji da wani irin juvi yayinda yake sabe alkyabbarsa.
Yana ba da wannan umarni, sai ya fuskanci wani shirgegen gunkin Iblis, yana mai sujjada a ga-reshi. Wannan gunki an gina shine a tsaye ya tale ka-fofinsa, domin ta tsakaninsu ake shiga wani daki mai suna 'Jehenma' wanda sai Kairu Nainu da was yar-daddu ne kadai suke shiga. Bakin wannan gunki a bude yake, kamar mai hamma, kuma wuta ce fara-fat take ci haikan a cikinsa, harsunanta suna fesowa kamar masu dokin tande wasu halittu. A gefen dama, gunkin matar Iblis, Sakibas, sannan kuma, a kewaye da su, wasu kananan gumaka ne na 'ya'ya da dangin Iblis, wadanda shaidanu da Ifritai da matsala a cikin bani-Adam su ke bauta masu don biyan bukatunsu. Gunkin Tir, babban dan Iblis ne kusa da uwarsa, sannan na Kannensa: al-Awar da Sut da Dasim da na Zalambur. A can Karshe daga daya gefen kuma, gunkin Kairu Nainu ne a tsave yana fuskantar na Iblis. Daga shi kuma sai na wasu sarakunan Ifiritai da shaidanu har da na Kufaru Murti Agar, sarkin Mudasani.
Kairu Nainu yana sujada, sai kuma nan take dukkanninsu suka gaggauta ga sujjada, sannan suka zame suka yi rub-da-ciki suna murginawa hagu da dama, suna wa su irin take na ibada ga Iblis. Da Kairu Nainu ya dago, duk kuma suka dago bayansa, sai ya yi wani irin Karaji. A wannan lokaci wasu jeren samari, na mata da na maza na ifritai suka shigo suna karanta wasu canfe-canfe. Matan suna dauke da bani-Adam namiji, mazan kuma suna dauke da mace, wadanda su ke ta ihu, amma suna daure tamau yadda ba za su iya kubuta ba.
Suka iso gaban Kairu Nainu. Ya duba wadan-nan bani-Adam, sannan ya yi isharar a shige da su.
Suka shige suka je suka kwantar da su a mirgine a kan wasu bakaken dandamalan duwatsu. Nan da nan kuma sai wani mugun Ifriri tsirara ya bayyana yana rawa yana kirari yana zagaya su. Can, ba zato ba tsammani, sai ya zaro wata sharbebiyar wuka ya datse kawun-ansu, jininsu ya kwarara cikin wasu gidauniyoyi da aka ajiye a gefenunansu. Da jinin ya gama fita, sai aka dauke gidauniyoyin, aka juye jinin macen a cikin wata babbar randa da ke gaban gunkin Iblis. Jinin namijin kuma a cikin randar da ke gaban gunkin matarsa.
Can kuma, sai ga wasu jeren shaidanun sun shigo, su ma matansu suna dauke da mutum namiji; mazan kuma suna dauke da mace. Suka yi kamar wad-ancan na farkon, kuma aka sake maimata abinda aka yi dazu. Can kuma, sai was suka fito. Haka aka yi ta yi, har sai da tukwanen nan suka cika da jinin bani-Adam, sannan Ifritin ya je ya yi sujjada a gaban Kairu Nainu, wanda ya sake yin wata isharar aka dauke gawawwakin mutanen a ka shiga da su cikin wannan dakin da ake bi ta tsakanin Kafafun gunkin Iblis din. A yayinda ake yin haka, kowa kuma ya fara wasu ihwe-ihwe, ana zagaya gumakan, Kairu Nainu na gaba yana ihu da tsalle-tsalle, ana binsa ana amshewa.
A duk lokacin da Kairu Nainu ya zagayo wajen gunkin Iblis, sai ya yi sujjada a cikin tsammanin wani abu zai faru. Amma Ina! Haka ya yi ta yi ba abinda ya faru, har ya gaji. Hankalinsa ya tashi, kuma ba shakka bai iya boye bakin-cikinsa dangane da wannan rashin motsi na Iblis ba. Can dai, ya hakura ya shige wannan dakin da ake shiga ta tsakanin kafafun Iblis, manya suka bi shi, kananan kuma suka dakata a waje. Bayan wani lokaci, sai aka fito da ragowar Kasusuwa aka ba wa kananan shaidanu da ifiritai, suka karba suna rububi a tsakaninsu.
Kairu Nainu ya yi wata irin gyatsa, Kwart, kwarrrrr; dukkaninsu kuma suka yi haka. Sannan ya tashi ya fara jawabi cikin fushi.
"Kyar! Kyarr!! Kyarrr!!! Yadda mu ka yi kalaci da wadannan bani-Adam, a wannan babbar rana a wa- tan Zalambur, haka za mu yi da Ibrahima da Amar-zadan da duk wadanda muka iya kamowa zuwa nan a bukin rana mafi muhimmanci. Ranar farko ta watan Lusifa.
"' Kafin ya ci gaba, sai Kan-Kan ya yi wuf ya tashi yana Karaji yana girgiza mashi yana cewa,
"Mutuwa garesu!" Mutuwa garesu!! Duk kuma aka dauka, "Mutuwa garesu! Mutuwa garesu!!" San-nan ya zauna yana huci. Kairu Nainu ya kalle shi da isharar ya yi na'am da wannan dabi'a tasa, domin ya san wannan da ma ita ce shawarar Kan-Kan, tun a ga-nawar da suka yi kwanakin baya.
Watan Lusifa shi ne watan da Balzakakul su ke bukin sabuwar shekararsu, kuma suna yi ne saboda girmama Iblis wanda was ke kira da sunan Lusifa.
Zalambur kuwa, shi ne karamin dan Lusifa, kuma duk
"'ya'yan Iblis da matarsa da sauran danginsa da wasu manyan kafirai na shaidanu suna da watansu ko ranar da ake yi masu buki, yawanci a farkon wannan watan.
Haka, saboda canfi, ba sa yin was abubuwa ko neman wasu bukatu, kamar yaki, ko illata wani, ko sata, sai a watan gunkin da aka san shi da wadannan halaye.
Hakika, al'amuran Yarima Ibrahima, dan Sultan Kanuka Uzairamu na Kasar Jinnun Salmendahar, da kuma Amarzadan, sarkin yakin Samandar, suna ci masu tuwo a Kwarya. Bayan ta'adin da suka vi masu wajen 'yanto Sultan Nur Umar a Kakula ta dajin Tamassi, akwai kuma wata babbar hasara da kafiran Balzakakul suka yi. Wata adaka mai dauke da ilahirin sirrin tsafi na Kairu Nainu wadda Ikir da Bidir suka taimakawa dakarun Salmendahar suka dauke, ba Raramar hasara ba ce a gunsu. Hasali ma dai, shi kansa
Kairu Nainu ba shi da wata kafa ta kusantar Iblis a lo-
kacin bauta masa wadda ta shige ta hanyar wannan sirri
wanda ke Rulle a cikin wannan muhimmiyar adaka wadda su ke boyeta a wani babban gini a Kakula. Wan-
nan ma shi ne dalilin da ya sa ba abinda ya faru lokacin
da yake zagaya gunkin Iblis duk da jinin da suka ba shi.
Wannan abu ba shakka, yana azabta Kainu Na-
inu. Tunaninsa da shirye-shiryensa gaba daya a kan
wannan adaka suke, tun ranar da labari ya iso cewar
sojojin Salmendahar sun dauketa. Amma kuma ya san
su ma suna rike da Zoben Farsiyas wanda suka sato.
Sun san amfanin wannan Zobe ga al'ummar Jinnun
Salmendahar, amma kuma har yanzu ba su iya sanin
sirrin sarrafa shi ba. Wannan aiki kuwa yanzu a hannun
wani Ghuli yake, wai shi Tula Mugus.
Da wannan tunani ya fado masa, sai Kairu Na-
inu ya juya, ya kalli wannan bulelen Ghulin da ke
zaune a daya geten.
"Tula!" ya yi tsawa, "Ba mu labarin abinda ake
ciki gameda Zoben Farsiyas, domin muna dokin mu
fara amfani da shi a kewayowar ranar Lusifa. Tashi ka
yi mana bayanin nasararka.
99
«Ko rashinta.
" Kan Kan ya fada a radance.
Jin wannan umarni, sai nan take fuskar Tula ta
fice daga cikin yanayin nishadin da take ciki, domin ba
shakka wannan tambaya kunyata shi za ta yi a wannan
taro. Tula, yanzu shi ne ma fi muhimmanci a cikin
Ghulai masu hikima, kuma a hannunsa aka maida bin-
ciken Zoben Farsiyas da yadda za a yi amfani da shi. Yau shekaru wajen hamsin kenan shi ma yana famar ya fahimci sirrin wannan Zobe wanda suka sato daga Salmendahar tun zamanin Sultan Kurra na biyu; kuma hat yanzu sun kasa sanin yadda za su sarrafa shi, su ma su sami Kofar ziyayar wasu kasashe a can biranen Tarurarin Filyades masu nisa, kamar yadda, a da, Jin-nun Salmendahar su taba yi cikin sauki da sauri ma fi sauri zuwa farfajiyar Farsiyas.
Kairu Nainu na ambatar wannan suna, ' Zoben Farsivas', sai Shaik Iman Abdallah na Salmendahar ya yi farat ya tashi tsaye, kamar an tsikare shi. Kodayake Shaik Abdallah saurayi ne, amma shine wanda ma fi yawancin ilmin sarrafa Zoben Farsiyas yake kansa, domin ga kakansa talikan biranen Farsiyas suka danka wannan ilmi da yardar Sultan Kurra na biyu. A hade da wannan ilmi kuma akwai asararun gain abinda ke kewaye da Zoben a cikin da'ira mai fadin kamu dari.
Tundayake mahaifinsa ya rasu shi ma, yanzu shi ne magajin duk wadannan ilmi, kuma haka Sultan Kanuka ya amince. A kowanne lokaci, Shaik Abdallah yana sane da duk abinda wannan Zobe yake ciki daga ko' ina yake. Amma gain abubuwan da suke kewaye da shi, sai ya yi wasu karance-karance na asararu tu-kuna. Don hakama, duk da yana gidansa a Salmenda-har, amma ya san an ambaci wanna suna, saboda

cucuwar al'amarin wannan Zobe da ilahirin tunaninsa.
Kamar yadda ya saba yi duk lokacin da ya ji kafiran Balzakakul sun ambaci wannan Zobe, sai nan da nan ya bayyana a gaban Waziri Maisur.
"Ya abokin mahaifina, Wazir Maisur! Lokacin da muke jira ya iso.
99
"Sun fara wata kankambar gameda Zoben!"
"Ba shakka, Ya Wazir."
Waziri Maisur ya daga kansa sama kamar mai vin tunanin abinda zai cewa Shaik Abdallah, amma ma-gana ya ke yi da Yarima Ibrahima da kuma Shaik Ahmad Bin Ulum Makkafaka, wadanda ba a dade ba su ma suka bayyana a gurin. A duk fadin Salmendahar, ba wadanda suka fi wadannan shugabanni na Jinnu mu-himmanci, kuma duk abinda suka shawarta, Sultan Kanuka ba ya canjawa, in ba ya zama tilas ba.
Yarima Ibrahima ya kalli Wazir Maisur ya ce,
"Menene abin yi yanzu?"
Wazir Maisur ya kalli Shaik Bin Ulum ya yi masa ishara ta iznin magana.
"Bismillahir Rahmanir Rahim."
Shaik Bin
Ulum va fara.
"Ba shakka, dukkannin al' amura su na
gurin Allah, subhanahu wa Ta'ala. Lallai mu yi godiya gareShi, domin yadda abubuwa suke a kasance a wan-nan hali da muke ciki, sun dace da shirinmu.
" Wazir
Maisur da sauran suna jinjina kai, alamar sun yi na'am da wannan magana tasa, domin sun san abinda yake nufi. Shaik Bin Ulum ya ci gaba da cewa, "Kasancewar Ikir da Bidir a tareda mu, da kuma sirrin tsafin Bal-zakakul da suka nuna mana a cikin wannan adaka, ba

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login