Showing 3001 words to 4583 words out of 4583 words

Chapter 2 - YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA PART 5

11 Nov 2024

1467

son in sanar da kai cewa gobe da Asuba, takobi da mashi da sirdi da darduma a su fito daga cikin wannan rijiya, kuma daga daren yau 'yata ba za ta sake zuwa wannan wuri ba, ni kuma zan koma garinmu ba zan sake gain ta ba sai lokacin da kamar yadda muke fata, ka sami nasara a kan Sarkin aljanu ka ceto su, sai dai kuma zan ci gaba da samun labarinta daga wurin dalibata aljana Dailanu, don kowace Asabar takan je wurinsu.
Mai yiwuwa tambaya ko tunani ya iya zuwa maka a cikin zuciya cewa ni da na san duk wannan sirri me zai hana ni zuwa da kaina? To ya kai Idrisu lallai ya kamata ka san cewa wannan ba aikin tsoho iri na ba ne, a'a, wannan aikin yaro ne mai jini a jika. Kuma ina kyautata zaton kai ne Allah Ya nufa da dacewa da wannan falalar.
Saboda haka sai ka shirya, don kuwa gobe za mu rabu, sai kuma Allah Ya sake hada mu. Ka je ka kwanta don yanzu dare ya vi."
Saurayi Idrisu ya koma dakinsa yana mamakin irin wannan labari.
Ya yi rigingine, ya tsunduma cikin tunani, shi da ya fito neman ilmi amma kuma ga shi zai kare masa da gwagwarmaya. Ya yi tunanin ko ya tafi abin sa ne kafin

wayewar gari, sai kuma ya tuna da karamcin malaminsa dattijo Ibrahim, kuma ya tuna da yarinya Nur, 'yar malaminsa da ke ciki kangin Sarkin aljanu, ya kuma tuna irin kyau da cikar halittarta tare da tabbatar wa kansa cewa matukar ya tafi ba ya gain ta, to tabbas rayuwarsa za ta kare ne cikin bege da da-na-sani.
Yana cikin tunanin yadda zai fuskanci duniya, sai ya ji wakar yarinyar nan ta iso, ita da sauran tawagarta suna rera waka mai dadin ban mamaki. Idrisu ya fito waje ya zauna kusa da dokinsa Jagora yana wasa da gashin wuyansa.
Yanzu kam Idrisu ya fahimci bakin zaren, saboda haka wakar da suka sa ta bankwana, nan da nan ya fahimci abin da take nufi, wato ba za su sake dawowa wurin ba daga wannan dare. Can sai yarinya Nur ta sauya salon wakar tana kiran sunan sauravi Idrisu tana vi masa sai wata rana, sai sun hadu. Ta dago hannunta tana vi masa sai wata rana shi ma yana mayar mata.
Bayan duk sun kammala, sai 'yan matan gaba daya suka shige cikin dakin lambu, shi ma Idrisu sai ya tashi ya shige cikin nasa dakin, ya haye gadonsa yana ci gaba da tunani.
To ashe 'van matan ba tafiya za su yi ba, a'a, don kuwa bayan wani lokaci sai suka fito daga cikin wannan daki suka nufi dakin dattijo Ibrahim, suka gaishe shi kuma

suka yi sallama da shi, suka rabu suna kuka. Malam ya yi musu du'a'i, kuma ya tabbatar musu cewa in Allah Ya so Zai bai wa Idrisu nasara a kan Sarkin aljanu. A haka suka yi sallama, ko da yake kafin nan sai da Nur ta bai wa mahaifinta takarda zuwa ga Idrisu.
Lokacin da suka nufi lambu, sai dattijo Ibrahim ya fito ya tsaya yana kallon su har sai da suka isa cikin harabar lambun nasu sai suka tsaya, wato yau ba su shiga cikin dakin lambun ba, kuma kasancewar a daren akwai hasken wata sosai ana iya hangosu sosai. Irisu yana cikin dakinsa sai ya ji rugumniya, nan da nan ya fito don gain ko mene ne, sai ya ga lambun su Nur a cikin sararin samaniya yana tafiya, kuma ga 'yan matan nan suna dago musu hannu shi da malaminsa, can kuma kafin 'van matan su bace sai yarinya Nur ta sako wa Idrisu adikonta, nan da nan ya yi iyakacin kokarinsa ya ruga kafin adikon ya fadi kasa ya cafe shi ya dora a wuyansa, ya sake dubawa ko zai gan ta ko da sau daya ne amma ina!
Bayan 'yan mata sun bace tare da lambu, sai Idrisu da malaminsa suka ci gaba da kallon sama gefen da lambun ya yi, suna zubar da hawaye saboda irin wannan rabuwa, wato rabuwar da babu wanda ya san lokacin da za a sake haduwa sai Allah, in ma za a hadu din. Dattijo ya yi kuka kamar ransa zai fita ta yadda sai

da Idrisu ya tashi tsaye sosai wurin rarrashin sa tare da alkawarin cewa in Allah Ya yarda sai ya dawo masa da
'varsa ko da kuwa wurin kokarin haka zai rasa ransa ne.
Da gari ya waye, sai malam ya cewa Idrisu, "Zo mu je wurin rijiyar nan, ko sakonmu ya iso." Ya wuce gaba Idrisu yana biye. Suna isa kuwa sai suka ga rijiya ta ciko har baki, ruwa ya dago sirdi da darduma da takobi da mashi.
Suna gain haka sai murna ta kama su tare da farin ciki mai yawa. Dattijo ya ce, "Je ka dauko, naka ne."
Nan da nan Idrisu ya nufi rijiya ya sa hannu ya kwashe wadannan kayayyaki, kuma wani abin mamaki shi ne yana dauke na karshe sai kawai rijiyar nan ta hadiye ruwanta kamar ba a taba yi ba.
Suka koma dakin malam suna ta duba wadannan kayayyaki suna mamakin su. Ya cewa Idrisu, "Na yi farin ciki da Allah Ya sada mu da kai, bayan mun yi zama na shekara daya tare ga shi za mu rabu, kuma rabuwa ta mutunci. Ina so ka sani ya kai Idrisu cewa za ka yi tafiya mai nisa, za ka shiga gwagwarmaya mai yawa, to amma kada ka damu, in Allah Ya yarda kana tare da nasara. Kai dai ka ji tsoron Allah.
Ina fata za ka zama namiji mai juriya da dauriya, kuma ka zama mai yawan gaskiya da rikon amana.
Kada ka yi zalunci, kada ka yi girman kai, kada ka yarda

a cuce ka, kai kuma kada ka cuci kowa. Ka zama kana mai neman ilmi har zuwa karshen rayuwarka, kuma kada ka kuskura ka vi wasa da addininka."
Bayan ya gama yi wa Idrisu gargadi, sai ya mika masa wata takarda ya ce masa, "Nur ce ta ce in ba ka." Nan da nan Idrisu ya sa hannu ya karba. Yana budewa sai
¡danunsa suka ci karo da rubutun yarinya 'yar Shehin malaminsa,
"Daga Nur 'yar Ibrahim, zuwa ga kyakkyawan saurayi Idrisu, gaisuwa zuwa ga wanda raina ya ratayu da so da kauna da kuma bege. Ina sanar da kai, ko da yake ba mu taba magana ba, cewa ina godewa Allah da kuma matukar murna da alfaharin cewa kana nan tsundum cikin kogin soyayya musamman saboda abubuwan da na lura da su. Ni fairin nawa imani da fahimtar ke nan. Ko ba haka bane?
Ya kai wanda nake so tun ranar da na fara hango ka a wannan daji, duk lokacin da na yi tunanin ka sai in ji nishadi saboda tsananin so da nake yi maka. Kai ne kadai mutumin da a doron duniyar nan na taba jin cewa na kamu da son sa.
Sai dai kash!.. Jin dadin soyayyar tamu ba na yanzu bane, saboda mugun aljanin nan.

Na san cewa malaminka, wato mahaifina, ya ba ka labarin komai, kuma babu wani dalili na maimatawa. Ya kai farin cikin ganina ina yi maka addu'a zuwa ga nasara, kuma ina so ka yi kokari matuka wurin karya wanna makigi na Allah.
Wannan fama za ka yi ne saboda abubuwa masu dama. Daga ciki na farko in ka sami nasara, to ka taimaki 'ya'yan mutane da wannan aljani ya sace har mu hamsin da dori wanda har yanzu maganar nan da ake yi, akwai yiwuwar in ya ga wata mai kyau ya karo. Na biyu malaminka zai kara farin ciki da murna da kai har abada. Sannan kuma sai na uku, wato soyayyar da nake zato a tsakani. Ko da yake duk wadannan kadan ne in an auna da irin tasirin da wannan yunkuri naka zai iya samarwa dunbin al' umma.
Ya kai Idrisu, zan yi maka wani alkawari, in Allah Ya ba ka nasara a kan wannan aljani kuma kajicewa baka so nako kuma ban yi maka ba, to na yi maka alwashin kowacce kake so daga cikin 'yan matan nan daga daya har hudu, in kuma duk ciki babu wadda ta yi maka, to zan ba ka kawata aliana Dailanu. Kai na tabbata dole

ne ma a cikin 'yan matan nan ka sami wadda ta yi maka, don dukkan su zababbu ne a garuruwansu a fagen kyau da natsuwa ko kuma har da ilmi, shi ya sa ma na hada da ce maka
'dole'. Amma kafin lokacin, za mu rika samun labarin juna a wurin Dailanu.
Ka huta lafiya, ya wanda nake so Idrisu.
Taka, har abada, Nur'yar Ibrahim."
Bayan Idrisu ya kammala karanta wasika sai murna da dadi suka lullube shi, ya yi kamar ya yi tsuntsu ya bi ta, kuma tun a wannan lokaci sai ya rika jin cewa da a ce za su hadu da Sarkin aljanu Sham'una, to lallai da sun kara, can kuma sai Idrisu ya kanne fuska, zuciyarsa ta baci don a cikin wasikar Nur ta ce wai in ya ji ba ya son +a za ta ba shi wata daga cikin kawayenta.
Sai ya cewa malaminsa Shaihi Ibrahim, "Allah Ya gafarta malam, duk irin abin da ka fada mini na dauka kuma na amince, tare da murna gami da godiya zuwa gare ka a game da duk abubuwan da ka yi mini. Ina rokon Allah Ya yi maka sakayya da alheri, kuma ina shaida maka ya malamin malamai cewa, ko da babu wani tallafi na kayan aiki wato makami da muka rika, to ina jin in na ga aljanin nan, zan iya taren sa gaba da gaba, kuma ko don wadda nake dimaucewa a kan ta,

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login