Showing 1 words to 1981 words out of 1981 words
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA PART 3
wanka yana tunanin irin karfin wanna dattijo, yana kuma tunanin, "Ni da na fito makaranta neman ilmi ga shi na buge da koyon yaki? ... amma dai ba a kin ta
manya."
Ya gama, ya sa suturarsa ya je wurin malam, suka ci abinci tare da yin Sallar Azahar. Bayan sun idar ne sai malamin ya shiga karantar da shi hilar yaki a karance cikin darasi har sai da Idrisu din ya fara yin hamma saboda gajiya da kuma tsamin da jikinsa ya yi.
Dattijo ya ce, "Kamata ya yi ka je ka dan huta."
Idrisu ya yi matukar jin dadin wanna kalami.
Cikin dan kankanin lokaci sai ga shi a kan gadonsa, kuma kafin ka ce haka, barci ya kwashe shi. Malam ya ga Magriba ta karato babu ko motsinsa, sai ya tabbatar da cewa lallai gajiyar dazu ce ke tambayar sa, saboda haka sai ya je kofar dakinsa. Ya kira shi karo na daya, a na biyu ya ji ya tashi.
Dattro ya ce,
«Ya kamata ka tashi don Magriba ta
kusa. Na kyale kaka dan kara ko da sa'a daya ne don ka dan warware."
Idrisu ya tashi ya gabatar da Sallar La'asar sannan suka yi Magriba tare. Isha'i ta yi suka yi tare da cin abinci kamar dai yadda suka saba.
• da bin umurninsa, kuma a kullum dare yana ganin yarinyar nan mai tsananin kyau amma bai san labarinta ba kuma babu dama ya yi tambaya. Ya kamu da tsananin son ta amma ba su taba magana ba, kuma a duk ranar da ya yi nufin tsallakawa zuwa wurinta, sai dokinsa Jagora ya hana shi.
Yana nan a cikin wanna kungurmin daji daga shi sai malaminsa da dokinsa da kuma abubuwan mamakin da ya ke ta gani har na tsawon shekara amma bai taba tambaya ba kamar yadda aka umurce shi.
Cikin shekara daya Idrisu ya sami karatu mai dumbin yawa a wurin dattijo, kuma bugu da Kari ya koyi dabarun yaki iri daban-daban da tsananin juriya. Daga cikin mafi muhimmancin dabarun da ya koya akwai kariyar kai da zamiya a wurin yaki ba tare da amfani da
garkuwa ba, alhali kuwa hakan babbar baiwa ce wadda samun irin ta sai an tona a duk fadin duniya da wajenta.
A kwana a tashi ba wuya, wata rana sai dattijo
Ibrahim dan Yahaya ya ce masa, "Gobe ne kake cika shekara daya cur a nan muna tare ba ka taba saba mini ba, na tabbata ka yi mini biyayya kamar yadda na umurce ka. Na tabbata kai yaro ne mai cikakken ladabi, kuma wanna ya nuna irin ingantacciyar tarbiyyar da ka samu daga wurin iyayenka, babu shakka kana da iyaye nagari, kuma ga shi za ka shiga duniya. Ni dai na tabbata za ka yi nasara in ka ci gaba da kyawawan halaye irin wadanda ka nuna mini a nan."
Dattijo ya sa hannu ya dauki kushin dabgen naman jiminar da ke gabansa ya ajiye gefe yana mai ci gaba da yi wa Idrisu bayani.
"Ya kai dana Idrisu, a yau zan ba ka labarina da sauran abubuwan da kake gani a wannan wuri na mamaki. Na farko dai shine, wannan doki naka da ka sa wa suna Jagora, to babu shakka ka rada masa sunan da ya dace da shi don zai yi maka jagoranci har sai ka sami nasara.
Babu irin rukukin da ba za ka iya shiga da shi ba, kuma sauran abubuwan mamaki na wannan doki sai nan gaba za ka rika gani. Sannan kuma dai, matukar ka kasa mane hanya, to duk inda ya nufa da kai ka kyale shi, in Allah Ya yarda zai kai ka inda alheri ya ke."
Dattijo ya ci gaba da cewa Idrisu, "Kamar dai yadda na taba shaida maka ne ceva al'umma tana sa ni daya daga cikin shahararrun malaman zamani, wanda kuma shine dalilin da ya sa mutanen kasarmu suke kira na da suna Shaihu kuma suke gain a wurinsu babu masanin fannoni kamar ni. Da a ce ana gadon karatu, to da sai in ce ni na yi gadonsa ne daga wurin mahaifina shi kuma daga wurin nasa mahaifin. In dai girmamawa ce daga
Sarkin kasarmu sai ni.
Abin da ya faru da ni shine Allah da ikonSa Ya ba ni
'ya guda daya tak, ita kuma wannan 'ya tawa Allah Ya jarrabe ta da wani abu wai shi kyau, tsananin kyan nata har mamaki ya ke ba ni, ko da yake babu abin da ya fi karfin Allah. Saboda tsoron yawan surutai na mutane, ya sa gaba daya ma na hana ta fita waje.
Na karantar da ita karatu mai dumbin yawa, kuma fanni-fanni. Ta fuskar manyan harsuna na duniya kuwa, Allah Ya yassare mata iya yin magana da masu yawa daga cikin su. Da wuya a sami malamin da zai kure ta ta fannin ilmi sai dai in an yi da gaske. Saboda wannan ne da kuma hankalinta Allah Ya sa nake matukar kaunar ta. Kaunar kuma mai tsanani.
Mutane sun yo ca kowa vana kawo caffa amma Allah da ikonSa ba ta fitar da mijiba.
Ya kai dana Idrisu bayan almajirci kuma Allah Ya sa
ina da wadata irin ta dukiya daidai gwargwado, don har ina da kuyangi mata guda bakwai tsarorin 'yata.
Sannan kuma ita wannan 'ya tawa, Allah Ya yi mata baiwa da wani abu da ake kira fasaha, sannan ga dadin murya. Ta gauraya wadannan abubuwa biyu a cikin daya daga cikin abubuwan da ta fi sha'awa wato waka, babu shakka wannan yarinya ta shahara a fannin waka, in suka hadu ita da wadancan kuyangi nawa tana bayarwa suna amsawa, to ko kai wane ne sai bege ya kama ka.
Kullum dare abin ka da yara, sai su shige lambun cikin gidana suna wasanni tare da rera wakokinsu.
Wani dare kamar yadda suka saba, sai hanya ta biyo da wani Sarkin aljanu ta wurin, yana kuma ganin ta sai ya rude, hankalinsa ya tashi kuma son ta ya kama shi yana mamakin wai dan Adam ne da irin wannan kyau.
Tun daga ranar sai ya kasance shi wannan Sarki na aljanu babu daren da ba zai zo wurin ba don sauraren wakokinsu, kuma abin ka da aljani, ka san shi yana kallon su amma su ba sa iya ganin sa. Ya shiga tunanin vadda zai hudo wa lamarin. A karshe dai ya yanke shawarar dauke 'yar tawa kawai ya kai can inda babu mutane ta zama mallakinsa. Ya vi tunanin wani sibiri a daya daga cikin manyan tsibirai uku da ke bayan duniya. Babu dan Adam din da ya taba sa Rafarsa a
wurin.
Bayan yanke wannan shawara sai alianin ya nufi wancan tsibiri ya gina wani kasaitaccen gida, ya rika zabo 'yan mata 'ya'yan mutane daga sassa daban-daban na duniya yana fyauce su yana kaiwa yana ajiyewa.
Babu wadda ya kyale, 'ya'yan sarakuna, malamai, masu dukiya da talakawa, kuma kowacce ko kadan ba za ka yi kuskure ba in ka ce ita ce Sarauniyar kyau a gari ko kasarsu.
Kamar kullum, wani dare yarinyar nan tawa da wasu daga cikin kuyangina suna cikin lambu suna wasanni da wake-wakensu sai wanna Sarki na aljanu ya sammace su da barci mai nauyi, ya dauke 'yata ya nufi wancan gida na bayan duniya da ita, yana zuwa sai ya tashe ta. Farkawa da kuma tsintar kanta a wannan wuri suka sa hankalinta ya tashi, toro ya kama ta, ta yi nan a guje, ta ruga can. Ta gama guje-guje da koke-kokenta kafta koma ta zauna tare da zuba wa sarautar Allah ido, tana mai mamakin irin halin da ta sami kanta.
Ganin ta natsu sai aljanin ya rikida ya zama mutum, ya fito, tana gain sa sai ta sake rudewa, amma darasin da ta samu a baya ya tabbatar mata da cewa babu wurin gudu a wannan wuri, saboda haka ko tunanin hakan ba ta sake yi ba, amma dai a firgice ta ke.
Ya ce mata, "Ki kwantar da hankalinki, babu abin da
zai same ki. Ni ne na gina wanna wuri kuma ni na kawo ki. Nan kina bayan duniya ne, babu wani dan Adam da ya taba zuwa nan cikin mutane sai wanda na kawo, kuma babu wanda zai taba zuwa. Kai ko aliani ma zuwa wanna wuri ya gagare shi sai dai irin gidanmu kawai. Don yankinmu ne, kuma kowa ya sani."
Ya shaida mata cewa shi ne babban Sarkin aljanu na babbar daular aljanu ta Jarirul Waki-waki, sannan kuma ya nuna mata hadarin wanna gida da take ciki, cewa a kan wani dogon tsibiri ya ke cikin tsakiyar ruwa, saboda haka kokarin gudu yana nufin mutuwa ke nan.
Ya ce a cikin wannan gida akwai duk abin da za ta iya tunanin nema.
Ya fuskance ta ya ce, "Duk wannan abu na yi saboda ke ne, saboda irin Kaunar da nake yi miki, shi ya sa ma na shiga cikin duniya da kaina na zabo miki mutane
'yan'uwanki don su rika debe miki kewa."
Yana gama fadin haka sai ya bude wani sashe daga cikin gidan, sai ga 'yan mata zuka-zuka su hamsin, ya cewa 'yata, "Wadannan duk bayinki ne." Su kansu sun vi mamakin kyan 'yar tawa.
Bayan ya gama labarinsa sai ya bace, ya tafi ke nan.
Bakin ciki ya rufe 'yata har ta rera wakar bakin ciki mai ban tausayi. Ta yi ta koke-kokenta sauran 'yan matan
nan suka zagaye ta, was suka rungume ta, suna ba ta hakuri don su har sun saduda sun fara sabawa.
Bayan hankalinta ya dawo jikinta sosai, sai ta yi musu jawabin cewa,
"Ya zama dole mu kwantar da
hankalinmu don tabbas babu vadda za mu kubuta daga wannan aljani, dole sai mun yi hakuri watakila Allah Ya kawo mana hanyar kubuta. Tilas ne mu sami natsuwa ta yadda za mu iya hilatar wannan mugun shaidani yadda za mu yi masa irin tamu ta mata mu kai shi mu baro, amma in muka ce za mu tayar masa da kayar-baya, to babu shakka halaka mu kawai zai yi.
Shawara dai guda daya ce, ita ce kada mu kuskura ya gane cewa muna cikin bakin ciki. In mun ji alamar zuwansa sai mu saki jikinmu mu shiga 'yan wake-wake har shi ma ya saki jiki da mu, wanda daga nan ne a hankali zan sami damar binciken sirrinsa."
Bayan yarinya ta kammala bayaninta sai dukkan su suka kara sakankancewa da ita, suka sakar mata komai a hannunta, suka kuma saki jikinsu kamar suna gidajensu. Sai dai su yi wanka, su yi kwalliya don ga kayan kwallivar nan birjik, kuma iri-iri sai wanda suka zaba. In sun ji aljanin yana zuwa sai su shiga kida da waka, suna rawa da rausaya da rangwada. In ya iso ya ga irin halin da suke ciki sai dadi ya lullube shi. 'Yata ita ce ke ba da waka sauran suna amsawa. Ba alfahariba, idan
ka gan ta a tsakaninsu, sai ka ce wata ne dan daren goma-sha-hudu a tsakiyar taurari.
Yadda suke gane zuwan aljanin kuwa shine, wani irin Kugi sukan ji yana cida kamar ana hadari.
Bayan wani lokaci mai tsawo aljanin nan ya saba da su sosai, ya saki jikinsa kamar da ma sun yi shekara da shekaru tare. A duniyar nan kuma ya kasance babu abin da ya ke so kamar wannan yarinya 'yata.
In suna wakokinsu sai ka ga kafin lokaci kankani barci ya kwashe shi saboda tsananin natsuwar da yakan samu a dalilin haka. A kullum yana tare da su, kuma ba ya barin wannan tsauni sai yamma ta yi likis sannan zai koma cikin 'yan'uwansa aljanu. Ranar Asabar ce kawai ba ya zuwa saboda ranar bauta ce a wurinsu.
Wata Asabar 'yan matan nan suna cikin wani katon daki mai shimfidun alfarma suna kewar gidaje da garuruwansu don sun san cewa aljanin ba zai zo ba, sai kwatsam suka ji wani irin ruri mai karfin gaske kamar gidan zai tsage. Dole suka firgita don ba su taba jin ruri mai tsoratarwa kamar haka ba.
Nan da nan suka shiga addu'a suna neman tsari wurin
Allah.
Bayan lokaci kadan da jin waccan mummunar kara, sai suka ji shiru. Daga nan sai wani irin kanshi wanda ba su taba jin mai dadin sa ba ya budade wurin gaba