Showing 30001 words to 32126 words out of 32126 words

Chapter 11 - YAR ZAMAN WANKA BOOK 1

27 Sep 2024

2988

bawa amma haka na kwana a tsakanin katakwaye, sauron duniyar nan ya gama cinye min ƙauri, ga riga a jiƙe duk sanyin nan amma rigar tana naniƙe dani da lema da komai haka na jure na kwanta, yanzu hallaw daga garin Allah ya waye a rufe ni da miciji a ɗaki" Ta faɗa tana jin haushin kan ta da bata fito daga ɗakin ba lokacin da Imran ya karɓi Hassan.


Da sauri ta nufi akwatunan Sadiya da aka musu ɗaya kan ɗaya, guda huɗu ne, hakan ya sa ta hau kan su amma tana iya hango jelar Hassan na kaɗawa tana motsi, da sauri ta diro daga kan akwatuna ta taka gado, ta buɗe drower step ɗin wardrobe ɗin ta kalla ta ce.

"In ka ji mutum na cewa ba zan iya ba to bai kama shi bane, ƙafafunta ta ɗora a kan step ɗin cikin drower ta ƙanƙanme a haka ta yi matakala da step ɗin sai gata ta haye saman drower can saman ta hau kan ta na gab da silin.

"Taimakona ɗaya da Allah ya yi lokacin sanyi ne da ace zafi ake fanka a kunne ai da an yi gudun gara an tadda zago, da fil fanka za ta ɗauke min kai" Ta faɗa tana kallon ƙasa inda Hassan yake har lokacin yana nan a micijinsa.


Sai da ta ji ta zaune dandam, ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ta ce.

"Allah raba bawa da wahala, na san dai komin nisan dare gari zai waye, amma ban da dai matar mutum kabarinsa babu yadda za a yi Halima ta auri wannan yaron marar imani" Ta faɗa tana rafka uban tagumi.

Ƙaran buɗe ƙofar bayi ne ya sanya Imran daina dariyar da yake ya tashi zaune sa sauri ya koma kan kujera ya zauna ya ɗauki Husaini ya riƙe dan ba ya so ko Sadiya ta san gashin ƙumar da zai ke yiwa Inna a gidan dan ya san ko ba komai kakarta ce kuma ba za ta ji daɗi ba.



Da sallama Sadiya ta shigo falon, amsa mata Imran ya yi mamaki ta yi da ta ganshi ɗam a zaune fuskarsa fes da alamar yana cikin nishaɗi, mamaki take yi daga jiya zuwa yau Imran ya sauya ya zama mai yawan fara'a kumai magana ba ta masa wahala yanzu, danganta hakan ta yi da ƙaruwar da aka samu.

"Ina Innar?" Tambaya tana kallonsa.

"Tana ciki Hassan take yiwa wanka"

"Ikon Allah shi ne har da rufo ƙofa" Ta faɗa tana sanya hannunta ta tura ƙofar, ashe kafin ta shigo falon Imran ya buɗe mukullin da ya sanya, dan haka ƙofar kawai ta tura ta shiga. Inna da ke saman drower tana jin duk abin da suke cewa, a ranta ta ce

"Lallai Imirana ya cika maƙaryaci, kuma maƙetaci wallahi yau duk abin da za a yi sai na yi jarumta na yi ta maza na rama abin da ya mini" Ta faɗa tana jijjiga kai.

Sadiya da ta shigo idanunta suka sauka a kan Hassan da ke kwance a siffar miciji ya fasa kai kamar zai sara, idanu ta zaro cikin kiɗima ta fara waiwayen inda za da ga Inna dan bata ganta ba kuma tana tunanin kar dai saran Innar ya yi.

"Sa'adiyya kin ganni nan" Inna ta faɗa cikin raɗa-raɗa, ta shaƙe murya kamar wanda aka riƙe mata maƙoshi sai da ta faɗa sai biyu sannan Sadiya ta tsinkayo muryarta ɗaga idanu ta yi ta sauke su a kan Inna da ke kan drower ɗare-ɗare kamar biri ya samu saman bashiya.


"Inna" Ta faɗa tana kallon Innar yadda ta yi wani wujiga-wujiga ta yi sharkaf da gumi kamar wacce ta fito daga filin restiling, sai ka ce ba sanyi ake ba. Amma kuma sai ta ga Inna tana sanya hannu a baki alamar ta yi shiru mamaki ya kama Sadiya sai kuma ta yi tunanin tsabar tsoro ne ya sanya Inna bata so a ɓuga magana saboda micijin, tana ƙoƙarin juyawa ta kira Imran ya zo ya ga abin al'ajabi dan ta lura da yanayinsa bai san abinda ke faruwa ba dan cewa ya yi Innar wanka take yiwa Hassan. Inna ta gani ta ƙanƙame drower ta sanyo ƙafarta cikin drower ta ya fara taka step ɗin drower da ke drower a buɗe take kawai sai gani ta yi Inna ta dirƙo a kan gado da ta faɗo gadon ma har da wata adungure ta yi alkafira sannna ta sauke idanunta a kan micijin nan wani yawu ta haɗiye midik amma duk da hakan bata karaya ba a kan abin da ta yi niyyar yiwa Imran.


Tsaye ta miƙe a kan gadon sai da ta saita yadda za ta tsallake micijin sai kawai ta yi wani tsalle sai gata ta tsallake miciji ta zo kusa da Sadiya da ke bakin ƙofa, tana zuwa bata yi wata -wata ba ta riƙe Sadiya ta ce mata a kunnenta

"Ƙwalawa Imran kira ki ce ya ajiye Husaini ya zo amma kar ki faɗa masa Hassan ya zama maciji dan kar ya razana" Inna ta faɗawa Sadiya hakan cikin raɗa a kunne. Sadiya kuwa da bata gane menene ba sai ta shiga kiran Imran da cewa ya ajiye Husaini sai da ya yi dariya sosai sannan ta taso dan shi duk tunaninsa fatar miciji Inna ke yiwa rangwangwan ɗin wannan.

Yana dai dai shigowa ɗakin Inna ta riƙe hannun Sadiya gam, yana gama shigowa ɗakin kafin idanunsa su kai kan Hassan Inna ta ja Sadiya ta shammaceshi sun fita daga ɗakin, suna fita ta banke ƙofar ta cire mukullin ta sanya a aljihun ɗan tofinta (Siket ɗin da ake ɗinkawa tsoffi suka sanyawa cikin kayan jikinsu) Ta ja zip ɗin ta zige hakan ya yi dai dai da saukar idanun Imran a kan danƙareran miciji da ya fasa kai yana ciccira ido. Wani uban juyawa ya yi tare da yin kukan kura zai gudu yana taɓa ƙofa a jita a rufe. Sadiya kuwa da bata gane abin da Inna ta yi ba sai ta shiga tambayarta dalili nan Inna ta kwashe komai ta faɗa mata.

"Saboda Imirana ya raina ni dan rashin Imani har da cewa in ke addu'a tun da ni matar Malam ce, yo ɗiyar nan ina ma na tuno da wata addu'a kawai dai na ji ina karanto alif, am baki ,waw zal, yo banda ruɗewa da gigicewa ina waɗannan baƙaƴe zansu zama addu'a kai Allah raba bawa da wahala, ji yadda na koma yau ne kika shiga wanka amma azabar da na sha wallahi kamar wata na yi a cikin ɗakin, yadda kika san a cikin rijiyar macizai aka saka ni haka na tsinci kaina cikin fargaba amma Imirana bai tausaya min ba bai dubi tsufana ba ai yau ko sama da ƙasa za su haɗe sai ya ɗanɗani abin da na ɗanɗana dan wallahi ba zan buɗe ba gwara ma ki ja bakin ki ki yi shiru ki toshe kunnuwanki dan ba magiyarki ba zan ji".

"Sadiya miciji ne fa, Sadiya da ke za a haɗa baki a sanya ni a ɗaki a rufe da miciji"

"Babu mai buɗe ka sai ka masa wanka tas ka shirya shi, ni ma da yake ɗan jikata muka zauna bare kai da ka yi fush ya fito duniya" Inna ta faɗa tana zaunawa a kan kujera Sadiya kuw sai magiya take Inna ta bada mukulli ko ta buɗeshi amma taƙi.

Kuka Imran ya saki ganin micijin ya fara gangarowa daga kan shawul ɗin kamar ma wajensa zai zo. Ya dadage cikin ihu da ɗaga murya yana kuka ya ce.

"Inna dan Allah ki min rai wallahi ban san ya zama miciji ba da na buɗeki duk tunani na a yadda yake a haka yake".

"Sai ka lissafo min sunayen limaman da suka yi limanci a masallacin makka da madina tun daga wanda suka fara har zuwa na yanzu"

"Haba Inna ya za a yi in iya wannan aiki"

"Ni kuwa ka ce sai na faɗi sunanka ba wanda nake faɗa ba bayan ni ma ba iya na yi ba.


Sai da ya shafe sama da awa guda a ɗakin nan yana kuka da magiya amma Inna bata buɗe ba, sai da ta ga Sadiya na kuka sannan ta haƙura ta buɗe tana buɗewa ta ga Imran a jingine a jikin bango ya yi sharkaf da gumi har da fitsari ma ya yi a wurin, ga macijin ya fasa masa kai a daf a daf suke da shi.

"Imran haka kake manne da bango kamar wani ƙadangare" Inna ta faɗa tana dariya, da gudu ya miƙe har yana neman hankaɗe Inna da ke bakin ƙofa, Inna ta juya ta bishi tana dariya har lokacin yana share hawaye dan bai taɓa shiga mawuyacin hali irin haka ba.

"Imran ka ganka kamar wanda ya fito daga rijiyar maciji"

Banza ya mata , Sadiya kuwa ta ɗanta take ɗakin ta nufa tana zuwa cikin jin tausayin Hassan ɗin ta sanya hannu ta ɗan dungureshi, cikin tsoro dan ta san ko zai cutar da kowa ita ya ɗaga mata ƙafa ko dan kasancewarta mahaifiya a wajensa.Tana dungurinsa kuwa ya kanannaɗe jikinsa sai kuwa ya koma jariri tare da tsallara uban kuka, da sauri ta miƙa hannu ta ɗaukesa tana jijjigashi, ta zauna tana share hawaye ta sanya shi a nono tinɓir da shi ko wando babu da Inna ta masa tsirara za ta masa wanka.


Inna ce fa shigo ganin tana bashi nono ta kama haɓa ta ce

"Lallai uwa da ɗa sai Allah yanzu nono kike baiwa miciji Halima"


"Haba Inna dan yana zama miciji sai na hana shi nono bayan na san ɗan mutum ne, kakarmu ta wajen uwa ta taɓa bamu labarin wacce ta haifi ɗaya mutum ɗaya miciji, kuma ta taɓa cewa wata maƙociyarta ta haifi yan biyu in aka kwamtarsu idan aka zo ɗaukansu sai a ga wani ya zama miciji kuma ta ce da za ave za a cillar da su to sao su koma mutum kuma za a ga sun ji ciwo"
Taɓe baki Inna ta yi ta ce

"Sai ki ajiyewa Amina ko Rakiya in sun zo su masa wankan. Ta faɗa tana fitowa daga ɗakin, tana fita tsakar gida suka yi ido huɗu da Imran yana wani muzurai.


Haka dai Ashrof ta zo ta girka abinci da yin ayyukan gidan, Hajiya ma ta zo Mama kuma sai yamma ta zo. Ƴan uwa da abokan arziƙi da maƙota suka ringa shigowa suna yin barka.



```DARE```

Kowa ya yi bacci amma Inna idanunta biyu dan gani take kamar aljanin nan ma jiya zai kawo mata ziyara, haka ta matse fitsarinta, can cikin dare ta tashi Sadiya ta ce su yi macanjan bargo ita dai Sadiya bata ce komai ba, dan bata son rikicin Inna kuma ga bacci a idanunta, Inna kuwa ta yi haka ne dan idan aljani ya zo nemanta sai ya ga bargonta a jikin Sadiya wataƙila ba zai yiwa Sadiya komai ba dan ita ƴar gidan ce, ca haka bacci ya yi awon gaba da Inna, da goronta da ta ɓalgata ta gama taunewa ma bata haɗiye ba.

```IMRAN```


Gabaɗaya ya kasa bacci burinsa kawai ya ji shi a jikin Sadiya, zuwa can ya yanke shawarar zuwa ya shiga bargon Sadiya ya ɗan sanyata a jikinsa ko ya rage zafi tun da Inna nauyin bacci gareta. Cikin sanɗa ya shigo ɗakin, da wayarsa ya haska ya gansu suna ta bacci, haka ya kashe wayar ya ajiye akan mudubi yana mamakin yau Inna bata munshari. Bargon Sadiya ya ɗaga a hankali ya shige ciki, ya sanya hannu ya rungumota jikinsa, dan bai san Inna bace kawai ya yi amfani da bargo ne dan bai san sun yi canjan bargo ba, bakinsa ya sanya ya haɗe da na Inna da bai san ita bace Inna kuma jin an ruƙunƙumeta da ta falka sai ta yi zaton aljani ne hakan ya sanya ta fara kiciniyar ƙwatar kan ta, Imran bai ankara ba ya ji wani goro a bakinsa mai uban ɗaci, da sauri ya ɗauke bakinsa yana zaro idanu Inna sakin uban ihu ta yi da ta tashi zaune wanda ihun nata ya sanya Sadiya miƙewa zaune , Imran kuwa gefen gado ya samu wani ɗan sukurutu ya laɓe dan ya ana yau ko sama da ƙasa za ta haɗe ba zai fidsa kan sa ba ga goron da ya gogo garin yin kiss ya haɗe masa baki...

😂😂😂😂😂



To fa readers dandandan dan dan dan dan, ga akuya ga kura dan jin yadda za ta kaya ki siya ki karanta dan nishaɗinki ki sha walwala da dariyarki, labarin ZAMAN WANKA yanzu aka fara.


Ku nuna soyayyarku ga marubuciya mmn afrah ta hanyar siyan littafin mai zaman wanka ngd


Dan ƙarin bayani
09030283375

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login