Showing 27001 words to 30000 words out of 32126 words

Chapter 10 - YAR ZAMAN WANKA BOOK 1

27 Sep 2024

2992

ba zan iya tashi in ɗorashi a gadonsa ba saboda yadda jikina ke tsuma ga arangamar da na yi jiya da dare duk jikina ciwo yake, ka karɓeshi kar in je in luntumashi a ruwa, dan ni ban ma yarda ɗan mutuma bane wannan"

"Ɗan nawa ne ba ɗan mutum ba, to wallahi kika saka shi a ciki sai mun yi shari'a"

"Yo in ba ɗan aljan...Shiru ta yi da faɗar aljannun tunowa da ta yi da yadda suka kwashe da aljani da dare har ta ƙarasa kwananta a ƙasan gado hakan ya sa ta saki akalar maganar ta kama wata.

"Da za ka yarda ku kai shi bakin ruwa a gani indai ya gangara ya shige ruwa to dama ɗan ruwa ne, in ba haka ba tayaya zai yi rabi mutum rabi miciji"

Kan ta kai ƙarshen maganar Imran ya sanya hannu ya karɓe ɗansa cikin zafin nama da jin haushin Inna yana raya wani abin da zai mata dan bashi ta ɗauka cewa ɗansa ɗan ruwa da ta yi.


"Wash Allah, ai gwada da ka karɓeshi, ai dama kowa da kiwon da ya karɓeshi wai maƙocin mai akuya ya sayi kura, wato ga Inna ƙaramar danga mai daɗin tsallaka, kamar ni a ce a sanya min linzami a baki yo da bakina wa zai hanani magana, aikin banza harara a duhu" Ta faɗa lokacin da ta sauke wata ajiyar zuciya ta tashi ta zauna a bakin gadon tana sakin maganganu. Wani kallo Imran ya watsa mata yana ji kamar ya shaƙeta.


"Aikin banza harara a duhu, ni ban san harara ba sai ido ya faɗo" Ta faɗa tana tana gyatsinan gefen hanci.Imran da ke ƙoƙarin fita daga ɗakin sai kawai ganin kan Hassan ya yi yana wani kamar lanƙwasa kawai sai ya koma kamar yadda kan maciji yake lokacin da ya fasa kai, sai ganin fatar cikin yaron ma ta fara komawa irin fatar bayan, Inna bata lura da abin da ya gani ba dan haka cikin sauri ya kalli ƙasa inda shawul ɗin Hassan da Inna ta ajiye ya ɗorashi a hankali, cikin hanzari ya fita daga ɗakin tare da rufe ƙofar ɗakin ya sanya mukulli.




Inna da ta lura da fitarsa bata san ya ajiye Hassan ɗin ba sai ƙaran rufe ƙofar kawai ta ji, Ta zabura za ta tashi sai ji ta yi Imran ya ce

"Inna kalli Hassan ki gani gashi nan na ajiye miki shi"

Idanu Inna ta zaro ganin fatar cikin yaron ta rikiɗe zuwa irin fatar bayansa, wani uban ƙara ta ƙwalla, dan yaron a setin hanyar da za ta sada ta da ƙofa yake gashi ma ta ji Imran ya rufe ƙofar tare da sanya mukulli...



Masu son grp na zaman wanka

MMN AFRAH 09030283375








🤱ƳAR ZAMAN WANKA👩‍🍼

(KWANA ARBA'IN)

NA

MAMAN AFRAH


🅿️1️⃣0️⃣

Last 🆓 page

Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134



```MALAM```


Sai da aka yi sallar isha'i sannan ya shigo gidan dan tuwansa ma ƙofar gidan aka kai masa inda suke cin abinci shi da abokansa. Cikin gidan ya nufo bayan almajirai sun shigo masa da tabarma da butarsa cikin gidan dan dama yanzu basu da wasu yara a gidan sai almajirai. Duk an aurar da matan suna gidajensu haka ma mazan babu wani ƙaramin yaro yanzu. Sallama ya rinƙa kwalawa daga tsakar gidan Tasalla da ke cikin ɗakinta ta amsa masa dan yanzu dakyar ta daure ta ci tuwo kaɗan shi ma dan tana jin yunwa na neman kwantar da ita shi ne ta daure ta ci, amma ko tuwon ta ɗauka za ta sa a baki sai ta ji wani ƙululun takaici a zuciyarta dan tana tunanin Inna Azumi na can birni tana asuwaki da kaza.


Malam kuwa turakarsa ya sanya kai bayan ya ƙwalawa Tasalla kira kyawawa guda uku, haka ta tashi ta nufi ɗakin nasa tana kitsa yadda za ta yi kisisinar da zai barta zuwa birni dan ko sau ɗaya ne dai a rayuwarta ya kamata ta je birni ko da kuwa kwa Inna Azumi za ta tsireta idan ta je. Da sallama t shiga ɗakin ya amsa mata tana shiga ya ce.

"Wai ni Tasalla me yake damunki ne, ya za a yi ki bar ɗakin nan babu garwashi kin san dai ja fi so a kawu wuta ɗaki kafin in shigo gida ɗakin ya ɗau ɗimi" Ya faɗa yana kallonta.

Shiru Tasalla ta yi dan ita gabaɗaya ma yau ta manta da zancen kaiwa wutar ɗakin na Malam.

"Wallahi Malam sha'afa na yi ka san yau da gobe sai Allah"

"To sai ki je ki ɗakko yanzu idan baki kashe wutar ba in kuma kin kashe sai ki hura ko dai ki tafi maƙota ki samo" Ya faɗa yana ajiye hiraminsa da ya cire.

" A'a ban kashe ba ma dai cire itacen ne kawai amma akwai garwashi bari in ɗakko maka" Ta faɗa tana ɗaukan ƙaton kaskon wutar Malam ɗin.


Sai da ta ciko shi da garwashi sannan ta dawo ɗakin ta maida ƙofar ta rufe dan dama al'adar Malam ce daga isha'i ta yi yake shigowa gida ya rufe sai kuma gobe in Allah ya sa ana raye. Sai da ya yi shirin kwanciya ya kwanta amma Tasalla tana gaban kaskon nan tana kara hannayenta a jiki tana jin ɗumin wutar.


"Wai kam Tasalla yau duk wani iri nake ganinki ko baki so Azumi ta tafi ba?"


"kai, kai kai, Malam bar faɗa dan Allah, ni da ƴar uwata Azumi abokiyar zamana mai zai sanya na ƙi son tafiyarta"

"Yau ɗin kuma Azumi ce ƴar uwarki Tasalla ko dai kin yi makuwa ne?".

"Ras nake wallahi, dama ai an ce zo mu zauna zo mu saɓa, amma ai ina ƙaunar Azumi"

Zaune Malam ya tashi da sauri yana ƙarewa Tasalla kallo dan bai taɓa jin hakan ba daga bakinta ko a mafarki.


"Allah sarki ashe akwai ranar da Allah zai nuna min irin hakan nan ɗaya tana yabon ƴar uwarta ku da bakwa jituwa ko da wasa tun daga girmanku har tsufanku amma kuna faɗa sai gashi yau komai zai zama tarihi"

"Yoa ai ka san duk irin makaman yaƙin da mutum ya ɗauka idan ya ajiye nasa kaima ajiyewa kake, wai ɗazu baka ga shigowar Tsahare gidan nan ba?"

"Ni kwa na ga shigowarta dan har gaisawa mun yi"

"Wayyo ashe sai haƙata ba za ta cimma ruwa ba ashe sun gaisa ta faɗa masa me ke tafe da ita" Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma ta ce.


"Ashe ma ta faɗa maka saƙon"

"Wane saƙo ai gaisawa kawai muka yi da yake da mutane sai kawai ta shigo ciki"

Wata ɓoyayyar ajiyae zuciya ta sauke jin bata faɗa masa ba dan hakan zai bata dama ta sheƙa ƙaryarta son ranta.


"Saƙon meye?"

"Malam kenan" Ta faɗa tana ɗan sunkuyar da kai alamar tana jin nauyinsa da kunyarsa..

"Dan Allah ki faɗa min Tasallata daga ke ba ƙari"

"Yo na nawa kuma an ce da gwauro ya iyali, Azumin kuma fa da ka ƙaromin ko ka ɗauka na manta to ai in maye ya manta uwar ɗa ba zai yu ta manta ba"

"Ni ba na son tone-tone kawai ki faɗa min ko da na ƙaro Azumi ma ai kece babba kuma matsayinki da ban yake a wurina"

Wani irin washe baki Tasalla ta yi daɗi fal ranta masoyinta a yabe ta tare da jaddada yadda take a wurinsa.


"Dama Azumi ce ta baiwa ɗan machine ɗin saƙo ya je gidan Tsahare ya faɗa mata ta je birni sunan jikarta Sadiya, kuma ta zo har gida ta faɗa min mu tafi tare a sha shagali" Ta faɗa tana kallonsa.

Wani irin kallon mamaki yake mata wanda har ya so ya bata tsoro.

"Haba Malam kamar an faɗa maka wani mugun abu"

"Yo ba gwara mugun abu ba da wannan kk ma in ce meye marabar dambe da faɗa, Azumin da za ta tafi ya kuka kwashe da ke a ɗakin nan nawa, me yasa bata gayyaceki ba da bakinta sai bayan ta tafi za ta bada saƙo?"

"Malam kenan kai baka san sauyi ya kan zuwa wa mutuɓ lokaci guda ba, ina ga bayan tafiyarta ta ga dacewar hakan"

"Ko jikina kunne ne ai ba zan yarda ba cewa Azumi za ta gayyaceki sunan jikarta ba"

"To ai gashi nan yanzu ka gani ta aiko har gida ka san dai ba zan zauna in shirga ƙarya ba dan kawai ina so in je birni" Ta faɗa tana sanya hannu ta share hawayen kissar da ta ƙwaƙwulo.

Hakan ya sanya jimkinsa yin sanyi, ya ce.

"Ban ƙi taki ba Tasalla kawai dai abin ne da mamaki wai kiɗa a gidan makoki, amma tun da har ta faɗa babu dalilin da zai sanya na hanaki zuwa ai hakan kamar kawo gyara ne a zamantakewar ku Allah nuna mana"

Wani daɗi ne ya baibaye Tasalla har tana rasa inda za ta sa ranta dan daɗi, cikin murna ta yi kan Malam ta ƙamƙameshi tana ta dariya.



"Wayyo kin cukuikuye min wuyan riga Tasalla duk kin shaƙe min wuya, yashe rabon duniya da ayyaraye"

"Wallahi Malam duk daɗi ne ya cika min ciki"

"Daɗin daidaituwarki da sobar zamanki?"

"Daɗin zuwa birni dai" Ta faɗa a ranta a fili kuma ta ce.

"Wallahi kuwa Malam zama lafiya ai ya fi zama ɗan sarki"
"Allah ƙara haɗa kawunanku"

"Amin Malam"

Haka suka kwanta Tasalla ko baccin kirki bata yi ba tana ta tsara yadda komai zai kasance Allah-Allah take gari ya waye ta je ta san ƙaryar da za ta yiwa Tsahare dan ta tafi da ita ranar sunan.

Da gari ya waye Tasalla bayan ta gama komai ta tafi gidan Tsahare ta same ta tana tuyar ƙosan siyarwa nan suka gaisa ta faɗa mata abin da ke tafe da ita kan cewa Malam ya tilasta mata zuwa sunan Sadiya dan a samu maslaha tsakaninsu, duk da Tsahare ta yi mamakin amma sai ta ce mata babu koɓai Allah ya nuna mana ranar, tun da dai ta san da kuɗinta za ta yi kuɗin mota kuma sauran diramar ta sha kallo tsakaninta da Azumi dan ta san ba za a kwashe ƙalaw ba muddin Azumi ta ga Tasalla a gidan sunan da ba ta gayyaceta ba dan lo lokacin bikin Sadiyar cewa ta yi babu inda Tasalla za ta je bare kuma suna.Haka ta baro gidan Tsahare ranta fari ƙal.

Wannna kenan.





```MAMA```

Da asuba bayan sun idar da sallah sun yi azkar sai Ashrof ta shiga gyara gidan da yake yanzu bata zuwa makaranta sai islamiya da yake ta kammala secondry school kuma bata cigaba ba da karatu da yake ƙa'idar babansu ce tun kan ya rasu cewar babu wacce za ta cigaba da karatun sai dai in ta yi aure ta cigaba a ɗakin mijinta. Ko Sadiya ma tana kamamala secondry school aka mata aure. Bayan ta kammala komai suka karya ta yi wanka ta shirya sai Mama ta ce ta bari sai kamar ƙarfe tara sai ta tafi dan kar ta yi musu sakko.



```Hajiya```


Tana idar da sallah ita ma ta shiga hada hadar gyara gidanta da yake wuni biyu kennan bata zauna ba dan haka gidan yana buƙatar gyara sosai dan haka ta shiga gyarawa a ranta tana ta tunanin yadda Imran da Inna suka kwana ko ya aka ƙarshe.




```INNA```


Rawar sanyi ta fara tamkar wacce masassara ta yiwa mugun kamu, ta shiga wani irin tashin hankali da ya sanya ta kasa gane ina mafitarsa take, so take ta je ta buga ƙofar tare da roƙon Imran ya fiddota dan ta san matsawar ta ƙara wasu lokuta tare da Hassan a ɗakin to tabbas babu abin da zai hana ta suma in ma bata yi gawa ba. A tsaye take amma kuma ƙafafunta sai rawa suke kallon Hassan take da ke kwance kan shawul gaba ɗaya ya gama sawaya daga mutum zuwa miciji kan sa ne kaɗai na mutum amma dai yana a inda aka ajiye shi ko yunƙurin motsawa bai yi ba.


Ganin yadda Hassan ya mata shamaki da zuwa wurin ƙofa hakan ya sanya ta yanke shawarar neman ɗaukin Imran duk da ta san da gayya ya rufe ta amma ya zame mata farilla tusa a masallaci ta nemi ya buɗe ta.


"Imirana, Imirana, dan Allah ka taimaka ka buɗe ni kai ma da ɗan nan ya zame maka dole ka gudu daga ɗakin bare ni ɗorin ɗosano kakar uwarsa" Ta faɗa tana magiya amma shiru kake ji wai malam ya ci shirwa ko motsin Imran ɗin ma bata ji. Amma hakan bai sa ta saduda da neman ɗaukin daga gareshi ba dan haka sai ta ƙara ware murya ta ce.

"Imirana indai mutuwa kake so in yi billahillazi ba sai ka rufe ni da Hassan a ɗakin nan ba lokaci na ma yana tafe zan mutu ba sai ka haɗani da wannan abun ba"

"Inna in kin ga na buɗeki to tabbas sai kin wanki yaron nan, ya zaki yi ki wanki ɗan uwansa amma shi kiƙi masa wanka, sannan bayan haka ma har ki ce wai shi ɗan ruwa ne bayan kin san baiwa ce Allah ya masa, ba ke ce jiya kika ce kar ake raba kan su ba, tun da har Allah ya halicce su a ciki ɗaya? Amma shi ne ke kika fara nuna musu banbanci, baki san ba a yiwa tagwaye haka ba ransu ɓaci yake"

"Haba Imirana ya za ka faɗi haka da bakin ka, son dai ka sanya Hassan ɗin ya min wani abu, ni ban nuna musu banbanci ba, kuma da kake batun ba a nuna musu banbanci ni dai na san ba a ɓata musu rai in ransu ya ɓaci suna ɓatawa mutane abinci ko ayi ta dafa abinci yaƙi dahuwa amma tun da uwata mai daddawa ta haifeni ban taɓa jin inda aka yiwa ɗan mutum baiwar komawa miciji ba"


"Wai wa ya ce miki miciji ne bayansa ne fa kawai fatar ta miciji"


"Ƙur'ani miciji ne, dan baka ga yadda ya koma ba yanzu wallahi kan sa ne kawai na mutum" Inna ta faɗa idanunta a kan Hassan tana sakin kuka dan sai ta ga girman macijin ya yi yawa.

"Ki wankesa sai na buɗeki"

"Wallahi ba zan wankeshi ba, ta ina zan fara wanka wannan abu himili guda wallahi da in wankesa gwara ya kasheni in san mutuwar shahada na yi, ai da uwaka Amina ce ba za ka rufeta a ɗaki ɗaya da maciji ba"

"To zage ni Inna sai in buɗe miki"

"Ni shegiya in ji ɗan daudu ba zan fara ba ma ina so ka buɗe ni ta ina zan fara zaginka ai ko banza ba zan ce maka ba"

"Gashi kwa kin faɗa kn ce banza"

"Sa'adiyya, Sa'adiyya, dan Allah ki fito daga bayin nan, ima dalili kamar wacce za ta koma budurwa in kin yi zaman ruwan zafin, bayan har ƴaƴa biyu sun keto ta gabanki ba yadda za a yi ki koma kamar da, in kuma wanka kike in ba fatar za ki canja ba dan Allah ki zo ki ga halin da Innarki Azumimi take ciki duk na fita hayyaci na...

"Sadiya fa bata jinki kawai ki min abu ɗaya in buɗe ki ya katse mata magiyar da take yiwa Sadiya.


"Me kake so, ko goyaka ka ce in yi Imirana zan goya ka in dai ka fito dani"


"Kin ji matsalar ai, so nake ki kirani da suna na, na asali wato ki ce IMRAN inda kin faɗa to zan buɗeki"

"I,Imir, Imirana" Ta faɗa dakyar dan ta kasa faɗar yadda yake so.

"IMRAN kawai nake so ki ce"

"Haba wnnnn rashin imani har ina tayaya bakin tsohuwa zai iya faɗar wannan abu ban da ɗaukan alhaki wallahi Imirana duk ranar da na fito za ka san ka min wannan wulaƙanci" Ta faɗa tana rushewa da kuka.

"Sai ki bari sai kin fito ɗin, ke ba matar malam bace ki yi addu,a kawai ki kuɓuta"

"To ai mutum ba ya ƙin ta mutane" Cewar Inna.Jin abin da Imran ya ce sai ta tarki yin addu'ar amma ruɗani ya sa ta manta komai, tunani ta shiga yi can sai kawai ta ji wani karatu ya faɗo mata a baki.

"Alif, am baki, waw, zal, ba, alif, baƙi, lallam, hakuri" Ta faɗa da ɗaɗɗaya kamar yadda ta ji almajiran Malam na biyawa da allo. Imran yana kwance rigingine tsabar dariya yana tunani wai dama matar nan akwai maganinta aka bari ta addabi mutane, dariya yake tun ƙarfi can ya ce.

"Am, baki,"

Sai Inna ta karɓa da cewa 'Waw zal"

Ƙaran dariyar Imran kawai Inna ke ji, hakan ya sanya ta fara neman yadda za ta samu mafita dan ta ga bashi da niyyar taimakonta. Idanunta ta mayar inda Hassan ke kwance aikuwa ta yi arba da gabaɗaya ya koma maciji har kan, idanunta ta zaro ta ce.


"Hassan kai ne ka koma haka,duk da hausawa sun ce kaƙi naka duniya ta so shi, ka so shi duniya ta ƙi shi, to yau dai ga ranar, ni dai na ƙika dama ba wani haɗi garemu ba,Allah tsari gatari da saran shuka, uban gyatumarka kawai na haifa, ni ma ban da shishshigi shiga dangin miji da ganamasgo me ya kaini zuwa ZAMAN WANKA, ya Allah ka raba bawa da wahala gwauro a teburin mai shayi" Tana faɗar haka ya fara ja baya har sai da ta ji ta tokare da jikin drower waigen mafaka ta fara amma bata gani ba, idanunta ne suka sauka a ƙasan gado inda ta kwana jiya kawai sai fashewa da kuka ta yi ta ce.


"Ni Azumi na ga takaina, tun da na zo birnin nan nake yin angamo da abubuwa, na yi angamo da mazaƙutar (Al'aura) abokin Imirana, na yi gamo da aljani cikin dare lokacin da ake cewa mahutar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login