Showing 135001 words to 138000 words out of 200410 words

Chapter 46 - A RUBUCE TAKE COMPLETE HAUSA NOVEL

HUGUMA   

22 Aug 2024

11947

kwata kwata,taja tsaki qasan ranta sannan ta yunqura zata miqe wayarta ta dauki tsuwwa,saita dakata ta daga wayar ta sanyata a kunnenta

"Hello.....kin qaraso?,kina falo?, okay gani nan" sai ta katse wayar,ta sunkuya ta dauki mimi ta fita a falon.

Miqewa yayi ya shige bedroom dinsa ya zarce toilet,yayi brush ya sake alwala,sanann ya fito ya rage kayan jikinsa ya dawo falon,har a sannan bata dawo ba,bai dauka zata dauki tsahon lokaci haka ba,sai ya kunna tv ya kama labarai ya fara kalla,duk kuwa da cewa hankalinsa baya wajen.

Kusan minti talatin ba ita babu labarinta,kamar ya shareta sai ya fasa,ya koma ya dauko jallabiyya mai santsi saqar qasar oman ya zuba,ta masa masifar kyau ta qara fidda wannan sirritaccen kyansa,ya dawo ya dauki nawwara suka baro sashen.

Ba kowa a falon,amma da alama anyi baquwar ta tafi,dakinsu ya kai nawwara sannan ya dawo ya wuce dakinta.

A gaban mudubi ya sameta tana hada kudi,suka hada ido,tasha jinin jikinta amma ta basar,ya zube hannayensa a aljihun jallabiyyar jikinsa yana mata duban da yasan yana ratsa qashinta da kyau

"Gani na biyo sahu" ya fada cikin wani salo,ta lumshe idonta, muryarsa ta tabata da kyau,amma girman kanta sai ya motsa

"Baquwa nayi,kuma yanzun ma wata baquwar gareni tana hanya" bai sauraren ta ba ya taka zuwa bayanta ya kuma rungumeta da kyau ta bayan,baiyi qasa a gwiwa ba ya fara aike mata da wasu saqonni masu nauyi da tsuma zuciya,sun isketa da kyau kuwa,ita kanta tasan waye abbas din fiye da kowa a duniya,ta wannan fannin idan ana taron bada award.....ba award ba idan akwai abinda ya fishi ya cancanci a bashi,tun tana dojewa har sai da ya zaqulo dukka wani qwarin gwiwarta yayi watsi dashi,ya gigita tunaninta da kyau ya kuma yi mata masauki saman gadonta ba tare data ankara ba,sadai tafiya nayin nisa,yana gab da kaiwa inda yake da muradi hudubar shaidaniyar zuciyarta ta dawo mata,ta tattara qarfinta gaba daya ta tureshi ta koma gefe tana cika tana batsewa.

Da qyar ya daga kansa ya kalleta,idanunsa sun canza launi sosai,a sannan idan ka kalleshi zakayi tsammanin barkono aka watsa masa

"Me kikeyi haka?" Baki ta turo masa

"Sai yanzu kasan ina da amfani?,bakasan fushina ba balle damuwata ba"

"Kinsan me kika aikata?,kinsan matsayin yin hakan har a wajen Allah?" Qeya ta juya masa tana kada qafa,tana jin itama a yanzun lokacinta ne da zata murza kambunta,batasan ma me ta tsaya jira ba da har yake mata haka take daga masa qafa,bayan tasan tana da wannan makamin a hannunta

"Kai bakasan naka hukuncin ba saini?,meye naka hukuncin tukunna" shuru ne ya biyo baya,yayi qas da kansa yana dafe da mararsa data fara yi masa ciwo,hafsat itace musababbin samuwar ciwon mara a wajensa,a baya kafin yayi aure bashi dashi,duk da yana da qarfin sha'awa,to amma a lokacin baisan meye aure ba,bai kuma qwallafa ransa akan mata ba,hasalima basa cikin tsarinsa kwata kwata,har sai daya samu halalinsa.

Shurun da taji bai sanyata ta juyo ba,abu daya take jira ya roqeta ya lallasheta,tana jin a sannan ne zata iya haqura ta san masa,shima saita shimfida masa dokoki ya kuma tafe mata kudin da take so wanda zata qara jari a business dinta,duk da zuciya da ruhinta suna d'ar d'ar, zuciyarta na gaya mata zaiyi wuya abbas din ya roqeta.

Wata babbar ajiyar zuciya ya fidda,kamar zai hada da zuciyarsa,ya motsa ya miqe ya jawo jallabiyyar sa ya maida jikinsa,tayi tsit tana sauraren motsinsa,a yadda ya kamu da yawa bata dauka zai iya motsawar bama,ya tsaya qyam saman qafafunsa,cikin mamaki ta waiwayo tana dubansa.

Kallo daya ta yiwa fuskarsa gabanta ya fadi,tayi hanzarin dauke kai tana gayyato dakiya

"Ina da qarfi da ikon da zan iya danneki nayi dukkan yadda naga dama dake.....amma bazan aikata hakan ba,bawai don kinfi qarfina ba...... a'ah,saidai dalilai guda uku,na farko auren soyayya mukayi dake ba qiyayya ba,na biyu ban haquri da lallashi kikeso daga wajena......wallahi wallahi muddin wadan nan dabi'un naki zaki ci gaba dayi,ba zaki taba samun wannan daga gareni ba har abada.....abu na uku kuma.......bake kadai bace Allah ya halattamin ba,sannan kuma bake bace autar mata,ki jiqa abinki ki shanye,indai abbas ne na haifu,kuma dan halak ne ni gaba da baya" daga wannan ya fara takawa a hankali yana ficewa daga dakin,yana tafiya yana cije labbansa saboda yadda yakejin mararsa kamar zata tsage.

Gaba daya maganganunsa sun gigita ta,babu zance mafi gigita kuma a ciki daya ce mata ba ita kadai Allah ya halatta masa ba......yana nufin widad?,shi yanzu sai ya kusanceta?,bazaiji kunya ba?,yarinyar da ya kusa haifarta?,zumbur ta miqe,tana jin kamar taje ta dawo dashi yayi abinda yayi nufin yin.....don da ya aikata abinda yake nufi a zancansa gwara ta bada kanta ta dawo dashi,amma kuma tana taku uku wata zuciyar ta dawo da ita

"Zaki zubda mutuncinki da ajinki a wajensa" sai taci gaba da gamsar da kanta cewa abbas din bazai iya ba,yarinyar tayi quruciya da yawa,bazata taba iya gamsar dashi,kai ba zata daukeshi bama,ko ita da yaya suke qarewa bare widad din dako qasusuwanta basu gama yin qwari ba,ta tabbatar bashi yiwuwa

"Namiji nefa,idan komai bai kawoshi ba buqatarsa zata dawo dashi,basu da haquri ta wannan fannin" ta sake tabbatar wa da kanta,sai taja tsaki ta koma tayi zamanta,har fana tuhumar kanta

"Kin faye rawar kai akan abbas din nan,shi yasa ya rainaki,ya kasa ganin kimarki" wata zuciyar ta sake gaya mata,da wannan taja mugun tsaki ta miqe ta dauko wayarta dake ringing tana duba me kiran,baquwarta ce da zata kawo mata biyan bashi,saita aje wayar ta shiga bandaki tayi tsarki da alwala ta fito,saidai har a sannan itama tana ji a jikinta,don ba qarya tayi missing abbas din,sannan tarkon daya dana mata banda akwai wani quduri a ranta.....ta kuma yi da gaske ta dace da zuciya mai tauri bata isa ta tsallake ba,a ranta taji tana fatan tattaurar zuciyarsa ta sauko da wuri ya karyo ya nemeta,don itama a buqace take.

Tunda ya zube a dakinsa bai iya tashi ba,a nan yayi sallar magariba ya kuma yi isha'i ya koma ya kwanta saman abun sallar,rub da ciki yayi tun tsahon awannin yana fatan ya samu sassauci na zuciya da kuma gangar jiki,gaba daya ya manta zaije dauko widad,sai da yaga kiran hajiyarsa.

Bayaso yace mata baya da lafiya,yanzu zata daga hankalinta,kuma yasan babu driving din da zai iya,sai yace mata yana zuwa.

Number k'aninsa umar wanda daga shi sai auta ya kira yace yazo ya karba key din motarsa ya kawo widad din,idan hajiya ta tambaya ya gaya mata baqi yayi,a ladabce ya amsa masa,ya katse kiran,ya aje wayar yana cusa hannunsa cikin fuskarsa.

Ita kuwa hakimar tana falonta a zaune,duk sanda taji wani motsi saita leqa taga waye,so take taga shigowar widad din ta tsareta da ayyuka,idan da hali ma yau kwanan dakin su mimi zata sakata yi,taso acema key din part dinta yana wajenta tace mata ya bata,batasan me yasa bata saka mata dokar ajeshi a wajenta ba,amma daga wannan zuwan abinda zatayi kenan,ta dinga barinsa a hannunta,idan suka dawo ta dinga karba.

*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Page 69


A idanunta akayi sallar magariba bataga gilamawarsa ba,akayi isha'i ma haka,sai jikinta ya bata lallai ciwon cikinsa ya tashi ne,indai kuwa hakanne babu inda zai iya tafiya dauko yarinyar,hankalinta taji ya kwanta,ta kuma sake abinta,gwara yarinyar ta kwana a gidan hajiyan akan ta dawo cikin gidan yana cikin wannan yanayin,ta sanshi sarai,tamkar mayunwacin zaki yake,haram ce kadai baya iya dosa a irin wannan yanayin,saita koma ciki taci gaba da lissafin kudinta da kuma sabgoginta.

Ta riga ta gama saddakarwa,wannan ya sanya shigowar umar da fita da motar duka bata jisu ba,ta gama abinda takeyi ta dawo falo ta kunna kallo abinta,saurana abincinsa da bai cinye ba shi ta zubawa yaran sukaci abincin dare dashi,hakanan suka tsakura,saboda sun gaji daci,shi sukaci tun rana sukaci da babansu yanzu ma kuma gashi shi dinne,sunata wasansu tana chart, hankalinta ma baikan tv din,tana bawa anty ummee labari ita kuma tana cin dariya

_shegiya,wannan mafa hanyar samun kudi ce a wajen mace bana wasa ba_ anty ummee ta gaya mata

_wallahi a wani group wata hamshaqiyar hajiya ta bamu sirrin,ina nan ina zuba ido,idan ya gaji ya kawo kansa ya kuma biya price sannan a bude masa gate_

Daga can anty ummee tana ta dariya,cikin ranta kuma tana gulmar hafsat din,sai kace wata hamshaqiyar mace,banda ma abin namiji,ai ita qoqarin abbas take gani,duk da tsananin tsaftarsa amma yake iya tarayya da hafsat din,harda qulafucinta haka?,lallai abar rai da abinda yakeso kawai.

Sun jima suna hirar anty ummee na sake dorata akan keken bera,don itama tanaso idan ta yagi kudin ta yagi nata kason itama,tanason canza kayan kwalliyar falonta, hankalinta ya dauku ga hirar ta wuce kitchen dauko lemo,tafison tana yi tana korawa dame sanyi,dai dai sannan motarsu widad din ta shigo,ya tsaidata a parking lot.

"Matar yaaya,yace ki sameshi a bangarensa,ga key din motar,saiki tafi masa dashi"

"To,sannu na gode" dariya ya danyi kadan,itakam halinta dabanne,duk da sun girmeta,bai taba jin hafsat ta aikesu tayi musu ko sannu ba bare godiya.

Tare suka fita a motar,shi ya doshi gate ba tare da yayi tunanin zuwa su gaida da hafsat ba,don sai suyi zuwa dari ba wanda ya kalli sashenta,sai dai idan sunga idanun abbas din,ko shi yace su shiga su gaisheta.

Kallon sashen hafsat din tayi,gabanta yadan fadi,ta tuna kiran data dinga mata bata dauka ba,wanda shine tun daga ranar bata sake kiranta ba,saita dauke kanta,ta doshi sashen abbas din da dan hanzari,tana Allah Allah ne ta shiga ta bashi ta fito ta wuce sassanta.

Tayi mamakin ganin wutar falon gaba daya a kashe,babu hasken komai sai na wutar bedroom dinsa,sarkin tsoro tsoron nata ya motsa,duk da bawai duhu can can yayi ba,don hasken fitilun waje suna ratsowa ta labulayen falon,ta fidda wayarta ta kunna torche sannan ta doshi dakin.

Da siririyar muryarta tayi sallama tana shiga dakin,bata lura dashi ba har sai daya dan motsa daga kwancen yana amsa mata sallamar,ta danja baya adan tsorace,sai ya koma rigingine yana kallonta da rinannu idanunsa

"Uncle.... Lafiya?" Ido ya lumshe sannan yayi qoqarin miqewa yazauna yana cije bakinsa kadan

"Lafiya lau,ina umar din?"

"Ya wuce,ga key din yace na kawo maka" ta qaraso gefansa ta duqa ta ajjiye,qamshinta ya huro masa har inda yake,sai ya maida idanunsa ya rufe

"Yunwa nakeji,zan samu abinci?" Da mamaki ta kalleshi

"Mommy hafsa fa?"

"Zan samu abinci?" Ya sake maimaita tambayar tasa ba tare da yabi takan maganarta ba,sai ta gyada kanta da sauri

"Okay,dafamin wani abun mai sauqi mai ruwa ruwa" sai a yanzun ta lura da yanayin fuskarsa,gaba daya ta nuna bashi da lafiya,jikinta yayi sanyi,ta matso sosai kusa dashi,tasa hannu tana dan taba fuskar tasa

"Uncle kamar baka da lafiya fa" ji yayi kamar ta zuba masa wani abu me sanyi a gangar jikinsa,ya rufe idanunsa ya budesu a kanta

"Bani da lafiya weedad" sosai fuskarta ta nuna damuwa qwarai,ta tsugunna gabansa tana ajjiye jakarta

"Amma uncle ne yasa ba zakasha magani ba?" Ido ya zuba mata sosai,yana ji a ransa inama zata iya dauke lalurarsa,inama tace zata zame masa maganin?,ya sani matarsa ce.....amma yasan halittar da Allah yayi masa a shekarunta yana ganin indai ya fuskanceta da wannan zai iya cutar da lafiyarta

"Zansha weedad......bani wani abun tukunna" da saurinta ta miqe ta zame mayafinta da jakarta duka ta aje a wajen,suman zaune ya kusayi,dogon sassalkan gashinta na kwance a bayanta,tunda ta shigo daman dankwalinta yana jakarta,ba kasafai take daura dankwali ba don basa shiri, skert din ya fidda shape dinta sosai,ta baya zata dauka takai shekaru ashirin da wani abu,sai a lokacin yaga girman da yaji 'yan uwansa na fadin tayi,ya koma da idanunsa luuuuu ya rufe yana kiran sunan Allah.

Faten dankali ta shirya masa,duk da yadda yayi dadi amma gaba daya baya gane taste dinsa akan harshensa,zamanta kusa dashi yafi komai dagula masa lissafi,ita kuwa ta zauna ne bilhaqqi tana matsa masa yaci

"ko baiyu dadi bane na sake maka wani uncle?" Ta fada a shagwabe saboda sam bata jin dadin yadda taga baya ci din sosai,kansa ya girgiza dankalin yana wuce masa wuya da qyar,sai ya aje plate din ya zuba mata idanunsa gaba daya yana mata wani mayunwacin kallo

"Maganin zaki bani" ya furta da wata birkitacciyar murya,itama shi take kallo,karon farko da taji kallonsa ya saukar mata da wani abu mai nauyi a jikinta da zuciyarta

"Ina maganin yake saina dauko maka" tayi masa tambayar tana janye qwayar idanunta daga kansa,saboda wani nauyi da taji ya saukar mata lokaci guda.

Kanta ta daga sanda taga ya miqo mata hannunsa,ta kalli hannun ta kuma kalleshi,bata fahimci komai ba

"Zo na gaya miki inda yake" a mamakance ta miqa masa hannunta,bata kai ga tuna komai ba ta samu kyakkyawan masauki a jikinsa daya dauki dumi,cikin qirjinsa ya lullubeta gaba daya yana sauke wani irin numfashi a jejjere,komai ya fara koma masa sabo,tunaninsa ya fara nisa ya fara daina gane komai.

Yamutsa ta ya fara yi,abinda ya tsorata ta ta fara kiran sunanshi tare da qoqarin kama hannuwansa dake yawo a sassan jikinta,ko harafi daya bai gane ba cikin maganganunta,illa dai yana jin sautinta kamar mutumin daya sanya bakinsa cikin kofi yana magana(sama_sama),a yau ya ware dukka hannayensa a kanta,duk inda suka kai bai musu shamaki,haka nan bakinsa.

Sanda ya hade fatar jikinsu waje daya daukewa numfashinsa yayi cak na wucin gadi sannan ya samu ya qwatoshi da qyar,qasan da suke yaji tayi masa kadan,ya dagata zuwa tafkeken gadonsa ya shimfidar da ita,zuwa sannan tsoro ya kusa halakata,abinda bata taba gani ba,bata kuma taba zata ko tsammani ba.....yayin da abbas yayi nisa a wata duniya, duniyar da tunda yake bai taba tunanin ana kaiwa har can ba,tun daga tsarin lallausar fatarta zuwa daddadan qamshin jiki dana sumar kanta komai ya sake kwance masa,ya rasa ta inda zai juyata,ko ina ya juyatan sai yaji yayi masa kadan.

Kuka mai qarfi ta saki sanda taji ya soma rabata da sutturar jikinta,ta shiga roqonsa da kyau akan kada yayi mata komai......ummu ta hanata......idan yayi ummu zata kasheta,amma ina samm samm baiji ba,abu daya ne ya maidoshi duniyar sa,daukewar numfashi daga gangar jikinta bayan taja wani dogon numfashi sanda ya soma buda hanyarsa zuwa sabuwar rayuwa da sabuwar duniya.... dole ya zare jikinsa daga gareta ba tare da yakai ga cimma gaci ba,ya koma qoqarin ganin daidaituwar numfashinta.

Tun da safe ta tashi da sha'awar cin awara,sai da yaran sukayi bacci sannan ta fita da 200 zuwa bakin gate dinsu,ta bawa yaron gidansu ya siyo mata

"Ka riqemin kudi na da kyau,don idan ka yarmin sai ka biyani" kudin ya kalla sannan ya dubeta

"Hajiya dari biyu ce fa" ya fada qasan ransa fal mamaki,kaf unguwar kowa yasan waye ASP abbas din,amma ita sam bata jin kunyar yin aike da qaramin kudi

"Na sani,ko bani na baka ba?" Sai ya gyada kai

"Hakane" daga haka ya juya yana fita daga gidan,cikin ransa yana tur da irin halinta.

A hanyar dawowa ta kalli motarsa,har yanzu bataji motsinsa ba,wani sashen na zuciyarta yana mintsinarta kan ta shiga ta duboshi,wani sashen yana fadin ki shareshi,zai kawo kansa da kansa,kulawa ma yabawa ce ai.

Kamar giftawar iska taji fitar sautin qaramin ihu,wanda banda hankalinta dama akan sashen yake babu lallai taji,birki taja ta tsaya,gabanta yayi wani mugun faduwa,ta tsaya cak tana duban sashen nasa,muryar tayi mata kama da muryar widad,to amma yaushe ta shigo gidan?,tunda dai ita bata ji shigowar kowa ba,hakanan bataji fitar kowa ba,ta zubawa sashen idanun sosai ko zata sake jin wani motsi amma bata ji komai ba,sai hankalinta ya rabu biyu,wani sashen na zuciyarta na bata shawarar ta shiga ta duba,wani sashen kuma yana cewa tsarguwa ce kawai tayi,duk da haka saita kasa gamsuwa,ta dawo farfajiyar gidan ta zauna saman fararen kujerun da abbas din ya zuba a wajen saboda baqi,idanunta nakan sashen tana nazartarsa.

Babu ma alamun haske gaba daya,wanda wannan sign din da take gane abbas din yayi bacci,don baya kwanciya da haske a kanshi,sai taji zuciyar dake gaya mata tsarguwa ce tafi rinjaye,amma duk da haka zata jira dawowar yaron,tasan zaiyi wuya wani ya shigo ko ya fita baya wajen.

Bai jima ba ya dawo da awarar a farar leda karrr kana hangota quru quru,tasa hannu ta karba tana dubansa

"Babansu mimi ya fita ne dazu?" Kai ya girgiza

"Anya?,tunda ya dawo dai banga ya fita ba"

"Bayan shi fa ba wadda ta shigo gidan nan?" Kai ya jinjina

"Babu gaskiya" saita gyada kai tana sauke ajiyar zuciya

"Shikenan jeka" sai data qara wasu sakanni sannan ta miqe ta koma ciki,tana tafe tana waigen sashen, zuciyarta taqi gamsuwa,amma ranta ya aminta da abinda yaron ya fada,tsaki taja daga qarshe,ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login