Showing 48001 words to 51000 words out of 200410 words
Cikin sa'a kuwa tana buda gate din ummun ta hanga tsaye a farfajiyar gidan ita da kawunnanta,sanye da atamfa da kuma hijabi,hannunta riqe da carbi,da alama salla ta idar suka tasota,akwai zancan da sukeyi.
"Ummunaaa" ta fada da qarfi sannan ta kwasa da gudunta,ta isa gabanta ta fada jikinta tana ruqungumeta.
Sai da ummun tayi taga taga zata fadi kawu ya tareta
"Ashsha,ashsha,zata kada mana uwa" sai ta saki dariya tana sakin ummun suka miqe tsaye dai dai ummun itama tana dariya idanunta akan fuskar widad din,kamar fa shekara bata ganta ba.
"Ke dawa?,yanzu kike tafe?" Ummu ta fadi tana dubanta
"Ni kadai yanzu yanzu na qaraso"
"Iyeee,muhsin din barmin ke yayi ke kadai kika kamo hanya?,tabdijan ,zamu hadu dashi kuwa"kafin ta qarashe drivern uncle muhsin din ya shigo da jakankunanta,suka gaisa yace zai koma,ummu tace a'ah sai yaci abinci,suka wuce ciki ita da widad tace taje ta kawo masa abincin,su kawu kuma suka fice bayan an bashi wajen zama anan farfajiyar gidan.
Zuwa wani lokaci sai ga sassan ummu ya dan cika da sauran yaran gidan,su Aafiya rafi'ah fareesa da sauran wadanda suke shekaru kusan daya,sun baibayeta tana ta basu labarin bauchi.
"Kano fa tafi dadi Allah" ta fada daga qarshe tana yamutsa fuska,dariya sukayi mata
"Daga baya kenan,bayan kin gama kwanakinki" dariya tayi tana cewa
"Da gaske nake muku,bari kuga" sai ta wuce daki ta janyo jakarta,ta fidda jakar ledar kayan makeup din da hajjaa ta damqa mata tace inji abbas,tunda ta taho kayan suke daukan hankalinta,komai na ciki ya burgeta ya kuma yi mata kyau,harda takalmi me tsini irin nasu basma da aka sako musu a lefe,tayita maitar takalmin sai basman ta jefa mata harara
"Ba baki zanyi bafa,kiyi addu'a kema Allah ya kawo me siya miki" fushi tayi tana tura baki tabar gurin,sai gashi ta sameshi sama ta ka,bayan shi harda mayafi da hand bag qarama mai matuqar kyau,a nan ta zazzage musu kayan,suka dinga santinsu,daga baya ta daukarwa kowa wani abun daga cikin kayan kwalliyar.
*************
Kwana biyu a tsakani tana kitchen tana cin abinci suna hira da latifa,ta ajjiye warmer din data zuba abincin alhaji a ciki tana cewa
"Ashe dan bauchi kika samo mana kuma" kallonta tayi tana ci gaba da cin abincinta,don ita har ga Alla ma ta manta da wani batu
"Dan bauchi?"
"Eh mana,naji abba mahmudu yazo suna zancan da alhaji ai"
"Auho,wai abokin uncle muhsin"
"Shifa" sai widad din tayi shuru kawai,don batasan me zatace ba,itadai ba sanin soyayya tayi ba bare ta tantance tana sonsa ko bata sonshi,kawai dai taji bata damu ba bata takura ba kamar sands ake zancan mahfood da ma'aruf.
Sosai ummu ta dinga juya zancan bayan da mahaifin widad ya zartar da cewa an bawa abbas widad don,amma bata taba kawo cewa zasu nema aurenta a nan kusa ba haka,taji abun sosai a ranta,a yadda ta lura kuma shi mahmudu din a shirye yake da auren diyarsa,tasan watarana komai tsahon zaman da zatayi da qaunar da takewa widad su rabu dole ta aurar da ita,so a yanzun bataga nata hurumin da zata hanashi bada auren 'yarsa ba,tunda dukkan bincike da shaidu sun tabbatar da nagartar me neman auren kamar yadda musulunci yayi umarni.
Amma babban abun shine,kishiya daya tabbata widad din nada ita,ta yaya yarinya kamar widad din zata iya fuskantar abu me wahala da zafi kamar kishi?,bata sani ba,saidai tana fatan ko mai zaizo da sauqi fiye da yadda suke zata.
Kwanan widad din biyu da dawowa maneman auren abbas din suka iso kano qarqashin jagorancin uncle muhsin,sunga karamci irin na kanawa,duk da cewa su din ba kanawa bane usul,amma tunda an haifi 'ya'ya da jikokinta suna amsa wannan sunan.
Cikin girma da mutunci gami da karamci suka gabatar da neman auren abbas ga widad din,aka sake jaddada basu,suka nema alfarmar karbar kudin aurensu harda sadaki,take alhaji yasa aka karba komai,suka karbi roqonsu na daurin auren sati mai zuwa.
A ranar zancan auren widad ya fara yawo a dangi,abinka da family house,kowa idan yaji zai gayawa na kusa dashi,bugu da qari widad din 'yar gatan ummu,mai masoya da kuma tarin abokan adawa.
"Uhmmm,sunje sun zaba mata miji ba,ai dama wannan yadda akaci buri a kanta nasan sai me abun hannu zasu bata" wannan shine abinda wasu suka dinga fada,musamman da suka samu labarin muqamin da ya riqe a gwamnatin bauchin,da kuma wanda yake kai yanzu,gani sukeyi uncle muhsin ya dauketa ne dama kawai don ya aikata hakan.
Ita kuwa sam batasan ma me akeyi ba,don har ta koma islamiyya,wadda tun tafiyarta qaunar makarantar bata bar ranta ba,sanda ta koma din sai ta samu basu wani tsere mata ba,tunda ta dora daga inda ta tsaya a bauchin.
**********Karfe shida saura na yamma suka iso gidan ita da Aafiya rafi'ah da widad din,bayan tasowarsu daga islamiyyar,gab da zasu shiga gate din gidan Aafiya ta kalleta
"Nifa zancan bikinki naji ummanmu tana yi,wai nan da sati daya"
"Nifa abinda yake hadani dake tsokanarki" widad ta fada tana watsa ragowar alawar data siya cikin jakarta
"Wallahi nima haka naji,don kafin mu tafi islamiyya naji umma tana waya a karbo atamfofi akai mana wajen mai dinki"
"Mahaukata,sai kuyi ai" widad din ta fada tana yin gaba abinta tana dan waqenta.
Bata ma tsayasu ba ta zarce sassan ummu abinta,tana sallama a falon ta soma zare hijabinta daya dameta,gashinta mai santsi ya ware,don dama ita din ba ma'abociyar saka dankwali bace,tafi sanya hula,itama ba ko da yaushe ba,sai ummu tayita fama da ita.
Ummu da anty halima ne a falon
"Anty halima ina nabiha?,kikace idan zaki sake zuwa tare zaku zo?" Widad ta fada tana barewa alewan ta tura bakin yaron anty halima dake kan cinyarta.
Da kallo anty halima ta bita,tana dan jin tausayin widad din
"Oh ni sadiya?,wannan wacce irin amarya ce ummu?" Dan murmushi ummun tayi,ita kanta tausayin widad din takeji,har yanzu ma bata zauna tayi magana cikakkiya da ita ba kan auren da tasan widad din batasan meye shi ba,bata kuma da labari cikakke akan yinsa.
"Au ina yini?" Ta fada tana dariya bayan ta tuna nata gaidata ba,ba kuma tare data maida hankali ga maganarta ta farko ba
"Lafiya lau widad,nabiha zasuzo,sai satin biki in sha Allah"
"Allah ya kaimu" ta fada tana gyada kai hankalinta kwance,saita dubi ummu a shagwabe
"Yunwa wlh nakeji ummu,dazu banci abinci ba Aafiya ta matsamin na taho mu tafi"
"ki wuce latifa tana kitchen ki karba"
"Tom" ta fadi tana wurga jakarta ta zarce kitchen din,yayin da dukka su biyun suka bita da kallo.
Ummu ce ta fara dauke idanunta tana sakin ajiyar zuciya,anty halima tace tana dariya
"Wai,wa yaga widad amarya" kai ummu ta kada
"Tausayinta nakeji halima,ban taba kawo rabuwarmu a nan kusa ba" tabe baki anty haliman tayi
"Kaji ummu,to mu da aka rabu damu din tun bamu kai haka ba me ya samemu?,gamu ragal damu?,itama zata ware ne kamar kowacce mace" kai ummu ta girgiza
"Ba zaki gane ba halima,dukkanku kunfi widad wayo sanda aka muku aure,kawai don lokaci yayi ne ba yadda zanyi,amma ban shirya kaita wani uwa duniya ba"
"Tunda dai babanta ya bada ita,alhaji kuma ya goyi baya dole saidai ayi haquri,yanzu kawai yadda za'a tattarata akaita bata iya komai ba,kunbi duk kun shagwabata,bata iya komai ba,komai yi mata akeyi" anty halima ta fada tana mele baki,ta rasa wanne irin so ummun takewa widad?,tamkar ma ba mahaifin widad din ta haifa ba,ita ta haifa,ko ita diyarta ta cikinta bata jin tana mata son da takewa widad din.
KI KULANI miss xoxo
DAUDAR GORA Billynabdul
RUMBUN K'AYA hafsat rano
IDON NERA Mamuhghee
A RUBUCE TAKE huguma
_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_
_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_
0022419171
Maryam sani
Access bank
Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070
*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261
*Al'ummar nijerπ³πͺπ³πͺπ³πͺ zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63
*Thanks for choosing us*π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*H U G U M A*
*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*
Page 25
Murmushi kadan ummu tayi,qarara ta hango kishin widad a idanun halima,ta rasa me yasa haliman ta kasa sabawa da hakan,sai ta gyara zama
"Mu dinma uwayenku da sanda aka aurar damu banajin munkai ya widad din,a gidan muka iya abubuwa,tun mun kwamacala har muka qware,yanzu gashi ba'a ce mune muka haifeku ba" kauda kanta anty halima tayi,tasan dama duk yadda takai bakai isa ka fadi wallen widad ko ka kusheta ga ummun ba.
Yau din tun qarfe takwas ta qudunduna a bargo cikin dakin ummu,bayan ta gama qarewa kayan data gani jibge a dakin ummun kallo,tun shekaran jiya taga ummun nata jibge kaya a dakin nata,itadai bata ce ga dalili ba,ta dan tura baki taja bargo abinta,bacci yau takeji da gaske,don ko sassan anty madina da aka cika ana hira yadda aka saba taqi zama,bugu da qari kuma yadda suketa faman kiranta da sunan amarya,wanda ta dauka duka tsokana ce irin tasu yau ta sauka a kanta suka tasota gaba,ita kuma bataso.
Fakare tayi tana jiran bacci ya iso,gefe daya tsoro tsoro takeji saboda ummun tana wajen dattijon mijinta,buda qofar dakin akayi a hankali,sai ta tada idonta tana kallon me shigowar ba tare data tashi ba,ummun ce,hannunta dauke da babbar baqar leda
"Yauwwa,gwara ma da bakiyi baccin ba,tashi" kai tsaye ta miqe din,don itama tanason yiwa.ummu tambayar
"Ummu...wai wannan kayan,na wanene duk sun cika miki daki?"
"Kayan aurenki ne" ta amsa mata gaba gadi tana kallon fuskar widad din,cike da fargabar yadda zata kalli zancan,kada ta watsa musu qasa a ido.
Idanun ta fitar,fuskarta babu wani emotion saina mamakin
"Aurena ummu?,duka wadan nan kayan?" Kai ta gyada mata
"Eh,harda wasu ma" ta fada tana bude mata ledar
"Wannan babanku yace ki zaba iya wadanda kikeso za'a dinka miki" da mamaki ta sake duban ummu
"Wai duka nawa ne?"
"Kadanma kika gani shalele ta,za'a kawo lefe a kawatuna duka naki" murmushi ya subucewa widad,kawai taji farincikin na kamata
"Harda kayan kwalliya ma irin nasu anty ramziyya?"
"Sosai,inajinma yafi nasu" ta fada tana murmushi ganin bata dauki zancan da zafi yadda ta saba ba,da wannan hirar ummun ta dinga hilatarta tana jaddada mata zancan auren,quruciya ta sanya widad din bata wani damu ba,saima cika da tayi da zumudin zuwan ranar da za'a kawo mata kayanta,wanda ummun tace mata sai ranar daurin aurenta.
********Wasa gaske saiga shirin biki nata kankama daga bangarensu widad,sam bata wani damu ko daga hankalinta ba,abinda ya baiwa kowa mamaki,yayin da wasu kuma hankalinsu ya kwanta ganin bata qi yadda ta saba ba,'yan adawa kuma fadi suke
"Shegiya dama da guntun wayonta,gashi tayi luff kamar ba ita taqi 'yan uwanta har mutum biyu ba" oho,ita dai sabgar gabanta takeyi kawai,tana lissafin ranar da za'a kawo mata kayan kwalliya.
Daga bangaren su abbas kuwa maganar ta fara yawo,da yawa daga cikin dangi wadanda sukaci burin zuwan wannan rana,ranar da abbas zai qara aure labarin baije musu a dadi ba,wadanda suka jima suna addu'ar hajiyan ta sanyashi qara aure saboda halayen hafsa,duk sai gwiwarsu tayi sanyi,hajiyan ta musu ba zata,irin abbas din shi kowa ke kwadayin samu,saboda alamun wadata da aziqi dukka sun fara bayyana a tattare dashi.
Tabbas hajiyan tasan da wannan,shi yasa tayi musu wannan ba zatar,ta kuma zartar da wannan hukuncin,fatanta daya abbas din ya samu inuwar da zai huta,ya kuma samu sanyin idaniyarsa.
Har a sannan hafsat din bata da labari,gidanta ba gidan zuwan 'yan uwan abbas bane,bama su kadai ba,hatta da nata dangin,saboda wata iriyar jarrababbiyar rowa da take da ita,muguwar sa'a ka taka idan kaje gidan ka samu tarbar pure water bare abinci,kusan anty ummee ce kawai ke samun wannan daga gareta,shi kuwa abbas,bayan ya ajjiye wa hajiya dukkan wani abu da yasan zata iya nema daga gareshi,komawa yayi kaduna,amma yace mata cikin satin daurin auren zaiyi qoqarin zuwa da wuri,da fatan alkhairi ta bishi,domin kuwa ita ya gama mata komai,sai fatan dacewa bisa niyyar alkhairin data nufaci rayuwarsa dashi.
************
Daga can tsakiyar 'yan jaridar dake dauke da nau'ikan kayan aiki daban daban,ASP ABBAS SARKI ne tsaye,sanye da uniform din 'yan sanda daga dace da structure na jikinsa,ya kuma yi masa kyau ainun,iya yadda yake tsayen kadai ya isa ya gaya maka cewa jajirtaccen police ne,wanda ya qware a aikinsa
"Wannan shine abinda ya faru a taqaice,we will let you know when the investigation is completed". Sai ya zare hannunsa daga aljihu yana shirin wucewa,amma suka sake yunquro masa da tarin tulin tambayoyinsu,rasa wacce zai amsa yayi,saidai akwai wani cikinsu da yafi kowa matsa masa da tambayar
"Amma yallabai,labari ya iskemu cewa kai da kanka ka gudanar da wannan aikin,kuma kaine ka samu nasara cafko su,shin meye gaskiyar wannan al'amari?,don dama jama'a sun dade da saninka da kuma ficenka wajen gudanar da aiki?"
Wani miskilin murmushi yayi wanda yake cike da tarin gajiya,murmushin da har yau hafsa ta gaza gane irinsa har sai ya buda baki ya magantu,yasa hannu ya cire hular police din dake kansa mai zubin P-cap,cikin muryarsa mai zurfi da kwarjini ya fara amsa tambayar tasa,bayan tarin jama'ar dake wajen sunyi shuru suna jiran amsa
"Ko ni nayi wannan aiki,ko bani nayi ba nasara ce,nasarata kuwa nasarar dukka jami'an tsaro musamman na 'yan sanda dake wannan qasar ne,muhimmin abu aci gaba da yi mana addu'a,fatan nasara" ya fada yana saluting nasu,sannan ya juya sa sassarfa ya shige ciki gudun kada su sake tsaidashi,sai wajen ya rude da muryoyinsu cikin farinciki kowanne na bawa kafar yada labaran nashi cikakken jawabi.
Tsaye yayi gaban table din office dinsa bayan ya ajjiye hular hannunsa a kai,saiya zare agogonsa ma ya dorashi saman hular,ya furzar da iska yana duba lokaci,ya riga yayi alqawarin barin Kaduna a yau zuwa bauchi,lokaci yanata quracewa ba tare da ya shaidawa hafsa komai ba,yanason ta fara ji daga bakinsa shi yasa ya hana kowa ya gaya masa,duk haukar da zatayi ta yita ta gama,yasan tabbas akwai case babba
Uwa uba kuma mai girma gwamnan bauchin yanason ganinsa,ya bashi appointment gobe da yammaci,zai sameshi gidan gonarsa,to dole tafiya ta kamashi a yau,saidai yana jin komai ma zaizo masa da sauqi da yardar Allah,tunda aikin da yake kwana ya kuma tashi dashi ya kammalashi,duka suspect dinsu suna hannu.
Wayarsa ya ciro da sirritaccen layinsa da ba kowa ya sanshi ba,ya kira wata number yayi confirming samun flight daga kaduna zuwa bauchi sannan ya aje wayar,ba kasafai ya fiya zirga zirga a jirgi ba,yafi ganewa yayi driving da kansa wani lokaci,yana tafe yana karantar hanya da inda tsaro yayi qaranci ko kuma inda komai yake tafiya dai dai,amma a yau din bashi da zabi illa yabi jirgin.
Taku biyu ya qara kamar zai fita,sai kuma ya fasa,ya sake daukar wayar yayi kira na sakanni ya ajjiye,ya shiga toilet ya kama ruwa sannan ya fito,ya duba dukka wani abu da yake da buqata cikin office din ya hada waje guda,bayan yayi wasu rubuce rubuce a wasu files sannan ya fito.
Daya daga cikin juniors dinsa ne yake driving nasa zuwa gida,yana a motar ya kira hafsat din don ya shaida mata tahowarsa,mimi ce ta fara daga wayar,sai data gama shirmenta sannan uwar ta karba wayar
"Kuna lafiya keda yaran?" Ya fadi don yasan zaiyi wuya ta fara tambayarsa lafiyarsa kota gaisheshi
"Lafiya qalau muke" ta amsa masa cikin ranta tana mamakin yadda ya sauko daga laifin data masa haka da wurwuri,duk da dama shi din bai cika riqo ba,amma a yadda taga ransa ya baci jikinta yayi sanyi,ta kuma aza zai mata hukunci mafi tsauri ne
"Am on my way to bauchi in sha Allah,two to three hours"
"Tooo....basai Friday ko Saturday ba?" Goshinsa ya murza kadan,ya salam,a nashi zaton tayi murna da yace zai dawo din ko?,amma saita buge da tuna masa ranar dawowarsa batayi ba?
"Na sani,inda muhimmin abu ne da zanyi a nan"
"Okay to,a taho mana da tsaraba"
"Yayi.....me zan samu?" Ta fahimci sarai me yake nufi,amma sai tayi kamar bata gane din ba
"Kamar me kenan?" Ta fada tana dan bata fuska,duk da ba ganinta yakeyi ba,zai dawo yanzu zai fara damunta da tsarabe tsarabensa.
"In so samu ne tuwo nakeso" tanason musa masa amma kuma batason bata saukowa da yayi daga fushin da yayi da ita ba tare data bashi haquri ba
"Xan qoqarta" ta fada cikin ranta tana jin ba zata iya yi ba
"Alright,saina qaraso" ya amsa ta ba tare da yaja doguwar hira da ita ba.
Bai wuce hutun awa yayi cikin gidan nasa ba,ya shirya ya wuce airport,gab da sallar isha'i cikin gidansa tayi masa, samuel ne yaje ya daukoshi ya ajeshi,ya shiga gidan nasa dauke da jakarsa,wata a hannu wata a kafada,sabida baya barin kowa da kowa ya shiga masa gida.
Yana shiga falon yanayinsa ya canza gaba daya,saboda qarancin tsafta da falon yake da,babu wani alamun qamshi ko qanqani da zaka iya ji daga falon,wala'alla ma idan ka taki mummunar sa'a hancinka ya iya shaqo maka qauri mara dadi dake ratsowa tun daga kitchen din dake falon zuwa