Showing 48001 words to 49030 words out of 49030 words
ransa,saboda mugun haushi abun ya bashi,dukka su aminata suna wajen,waye ta gani ya firgita haka ko ya gudu?,sai ita?. Bibi din ya yiwa sallama kamar ko yaushe
"A sauka lafiya" ta amsa masa da shi tana binsa da kallo sanda suke fita shida goumar,baki ta tabe tana jinjina kai
"Miskili kafi mahaukaci ban haushi" ta fadi a fili qasa qasa,har yanzun bai nuna mata komai ba akan batun daura auren,so ko qi duk bata fahimci komai ba.
To koma meye can ta matse masa,itadai da wata barnar gwara wata,hankalinta zaifi kwanciya idan sultana ta amsa sunan matarsa,ko mene zai biyo baya kuma me sauqi ne.
Kamar yadda suka qudurta a ranar juma'a din aka daura auren SULTANA MAHMOUD MAYAK'I da angon ALIYYU MUHAMMAT MAYAK'I. Daurin auren da yayi matuqar daurewa dangi kai,saboda muguwar ba zata da ya yiwa kowa.
"Maina din da ya raini sultana?,ya zame mata kamar uba ko wani shaqiqin yaya?,ashe shi zai aure kayarsa? Maganganun da suka dinga yawo kenan.
"Ina almurin,ashe kansa ya yiwa kiwo" wata qanwar bibi ta fadi sanda ta iso gidan. Itadai bibi murmushi kawai tayi,domin kuwa ita kadai tasan dalilin da yasa hakan ta kasance,kuma ita daya take tunanin me gobe zata haifar?,ya zata kasance musu dukkansu a gaba?.
Ga sultana kuwa a ranar ma suna sharafinsu ta sulale tayi ficewarta gurin rawar taron sunan maman qawarta da akeyi. Ranar ta jijjigi rawa yadda ranta keso,sai daga bisani wata maqociyarsu da taje taron sunan ta kamota ta jata gefe tana tsareta da ido
"Halan bibi batasan kin fito ba?"
"Eh suna can suna taro" ta bata amsa cikin halin ko in kula. Kai sosai fattu ta girgiza,batasan wacce irin zallar wauta ke damun sultanan ba
"Kinsan me ake nufi da aure kuwa sultana?,zauna dai tukunna" fattu ta fadi tana gyara mata wajen zama. Bata musa ba ta zauna saboda dama ta gaji sosai saboda rawar da tasha.
Ba abinda ta boye mata,ta warware mata komai game da abinda ake nufi da aure. Mugun baci ranta taji yayi,wato abinda bibi ke nufi kenan?,dama tasan abinda ake nufi din tace a aure mata maina din dan iska?,sun bashi damar yayi mata fyaden kenan,yama kasheta a cikin gidan kenan tunda daga yau yafi kowa da kowa dake cikin gidan iko da ita,to ita kuwa daga yau su zuba da yaa maina din,zai gani idan zai juyata yadda yakeso yake kuma buri.
Driver dinta fattu ta sanya ya maidata gidan,bata qi ta fattu ba don ranta a bace yake,hakanan kuma jikinta a sanyaye yake,ta dinga juya maganganun da fattu tayi mata a ranta sanda suke hanyar komawa gida
"Tabdijan" ta dinga maimaitawa lokaci lokaci tana gyada kai. Ita za'a yiwa irin wannan abun?,taga yadda hakan zai faru kuwa ita.
Sanda ta koma cikin gidan ba wanda ta kula,ta wurwuce abinta har zuwa quryar dakinta ta kulle ta shiga hidimar data dameta.
Ko bayan an watse fushi ta shiga yi da bibi,kusan kwana uku bata shiga sabgar bibi,saboda tana ganin ai an hada baki da ita ne za'a cuceta kawai. Saida bibi ta gaji da halin nunqufurcinta sannan ta isketa a daki ranar. Vest ne a jikinta da wandonsa iya cinya tanata game abinta,ta zare ribbon din kanta taqi ta hade sumarta waje daya,taqi kuma yarda tanja ta taje mata a gyara.
"Ke me yake damunki ne sultana?" Bibin ta fada cikin fada fada
"Ni ki qyaleni,bayan an hada baki dake za'a kasheni a gidan nan" idanu bibi ta fidda waje
"Kisa sultana?,ashe baki da hankali"
"Allah bibi,kawai sai ku auramin maina?,idan aurenne saiku bari na sake girma naga wanda nakeso ba wannan....."
"Ya isa,kiyimin shuru haka haba" bibi ta dakatar da ita kafin ta sake ballo wata maganar,don a yanzun dole a hankali a hankali ta soma nuna mata yadda zata darajta maina din,tunda ko banza igiyar aure nauyi da girma gareta.
A nan tayi borenta ta gama suka kuma shirya da bibi,don dama tsakaninsu ba'a shiga.
Ganin bai sake waiwayar gida ba kuma babu gilmawarsa saita sake abinta sosai,taci gaba da sakalcinta cikin gidan,duk da a wannan karon abubuwa da dama bibi tana tarota,tayita zuba ido taga ko ama zata nuna wani abu ko zata dinga sanya baki cikin sha'anin sultana din amma sai tayi kaman bata cikin gidan,koda a gabanta sultana zatayi abu kaman da can baya dauke kai takeyi ta wuce abinta. Bawai don bata sane ba,tana sane da komai tana kuma biye da komai,ta watsar dinne saboda kama girma da mutuncinta kamar can baya.
*_FAREWELL_*
_But_
_A new chapters unfold_
********** Satittika har guda gudu cur yayi babu shi ba labarinsa cikin gida. Haka kawai yaji baya sha'awar komawa gidan,sai kuma abubuwa sukayita shigowa na uzururrukan makaranta da suka sake riqeshi,don haka ya fidda batun ma zuwa gida,har sai da aka shiga sati na biyar. Satin da yazo da wata GAGARUMAR QADDARA......QADDARAR da ta zama sila ta wanzuwar komai. Qaddarar da dukkanin ahalin mayak'i basu taba koda hakaitota cikin tunaninsi ba. Qaddarar da ta d'aid'aita farincikin wasu da dama ta qulla wasu alaqoqi ta wargaza wasu........ta nesanta na kusa ta kuma kusanto da na nesa. Ta jefa ALHINI TARIN BAQINCIKI NADAMA DA TAKAICI ME TARIN YAWA A ZUKATAN WADANSU.
_NAYI AJIZANCIN NAWA,A YAU NASO NA BADA DUKKA SHAFUKAN SAI WASU HIDIMOMI SUKA RIQENI,AMMA A GOBE IN SHA ALLAH ZAN BADA WANDA YA RAGE DIN_
_KARKI BARI A DORA TAFIYAR GUDUN K'ADDARA BAKI KASANCE DA GROUP DIN BOOK DIN NA HALAL BA_
_JAZAKUMULLAH_