Showing 3001 words to 4349 words out of 4349 words
juya ce bata haihuwa? Tana yawan yiwa kanta wannan tambayar wanda har ta kai bata boyewa Hafiz damuwarta ba, shi kuma as usual kwantar mata da hankali yayi har yana tsokanarta da cewa dama bai gama moreta ba ta kara wasu watannin kafin ta dauki ciki. Ire-Iren wannan barkwancin Hafiz din yasa ta rage nuna mishi damuwarta tana kuma addu'ar Allah yasa ta samu ciki ta rike yayanta a hannunta itama.
Minti goma da haka Abbati Kanin Muhammad yayi parking a gefensu ya fito ya karbi abun hannunsu ya shigar cikin booth kana ya shiga motar suka wuce gidan
Saliman kamar yanda suka tsara.
Wani gida madaidaici da ke unguwar Jekadafari suka
shiga wanda nan ne gidan Salima da Muhammad, Abbati ne ya fita ya bude musu gate kana ya dawo cikin motar ya shigar da su harabar gidan mai daukan mota daya. Suna tsayawa wata budurwa mai taya Salima aiki mai suna Nanayo ta fito daga cikin gidan ta musu sannu
da zuwa tare da karban kayan abincin daga hannun Abbati ta shige dasu ciki bayan Salima ta umurceta da
ta yanka karkashin ta kuma daura mata ruwan tuwo.
Sallama tare da godiya suka yiwa Abbati wanda ya kara
fita da motar domin kaiwa mai ita.
A falon Salima daya gaji da haduwa suka sauka wanda yake cikin tsafta ga kamshi sai tashi yake yi a ciki, tuni Juwairiyya ta cire gyalenta ta ajiye a gefe tana sauke ajiyar zuciya irin ta gajiya.
"Wash Allah na."
"Oh mutum sai sakalci. Tsakaninki da Allah aikin me kika yi yau da har kike cewa kin gaji?" Fadin Salima tana ciro kayan cikin ledan tana ware wanda zata shigar kitchen da kuma wanda zata kai dakinsu a gefe.
Dariya Juwairiyya ta yi. "Baza ki gane ba. Amma in kina da miji kamar Hafiz kullum a gajiye zaki dinga jinki."
Shewa Salima tayi har da tafa cinya tana dariya. "Da alama ku bakwa gajiya da wannan harkan. Mu sai mu yi sati biyu ma wallahi wani abun bai shiga tsakaninmu ba musamman in ya kwanta rashin lafiyar nan. Wani lokaci ina so amma sai inyi shiru gudun kar in 6ata mishi rai idan na nema."
Fara'ar da ke fuskar Juwairiyya ce ta dauke domin ta
tsani ta ga ana kwara ko cutar mutum alhali babu yanda ta iya. Ta lura duk hiran da zasu yi da Salima matukar maganan Muhammad ta shigo ciki sai ranta ya baci saboda halinsa kaff da yake gwadawa matarsa babu na dauka. Tana kuma jin tausayin Saliman domin ta lura har da sonshi yake dawainiya da ita, wanda har ta kai bata iya ganin laifinsa.
"Kin san kowa da halittarsa, watakila shi ba mai son yawan sex bane." Cewar Juwairiyyah wanda zata iya rantsewa wannan shine karo na farko data taba kare Muhammad bata kusheshi ba idan an gwada mata halinsa.
To yaya zata yi? Yawan kusheshi a gaban matarsa zai iya jawo wani matsala tsakaninsu don haka tun suna asibiti ta yiwa kanta alkawarin daina hakan tunda ita wacce take cikin rayuwar bai dameta ba, kuma a hakan suke zaman auren ba tare data nuna mishi bata son hakan
ba.
Murmushi Salima tayi tana cigaba da ware kayan.
"Shima haka ya fada, yace inyi hakuri da yanda na sameshi ba yin kanshi bane."
"Ohh dama har wani hakuri yake baki? Wallahi na dauka bai taba furta kalmar hakuri ga kowa ba tun da yake. Ikon Allah, ashe idan kuka kebance soyayya yake nuna miki mu kuma kin bar mu da jin tausayin ana takura miki." Juwairiyya ta Karisa maganan cikin
mamaki tana murmusawa don har wani relief ta ji a zuciyarta.
"Shiyasa kika ga ba komai ya mini nake bata rai ba, sometimes ya kan nuna mini kulawa sannan babu abun dana nema na rasa a gidan nan, shi dai ki barshi da saurin hawa idan aka yi abunda baya so."
"Dama tsakanin mata da miji sai Allah, wanda kuma ya shiga tsakaninsu shi zai ji kunya." Juwairiyya ta furta ba tare data daina murmushin ba.
Suna hiransu har Salima ta gama aikin nata ta sunkuci
trolley din tare da sauran tarkacen ta nufi dakin Muhammad sannan ta fito suka kwashi na kaiwa
kitchen suka yada zango a can suna hira Juwairiyya na tayata girkin. Sune basu gama tuwon ba sai da aka kira sallan isha suka yi sallah sannan suka ci tuwon, bayan sun gama suka fara kallo Juwairiyya na recommending wa Salima wasu zafafan Korean series akan ta nema zata ji dadin su.
Takwas da rabi suka ji karar bude gate din gidan mota
ta shigo wanda suka ayyana a ransu mazajensu ne suka dawo, tun kafin a kashe motar wayar Salima tayi kara tayi saurin dauka tare da yin kasa da murya ta fara gaishe da wanda yayi kiran nata.
"Ya jikin naka? Da fatan baka jin komai?"
"Ki zo ki hada mini ruwan wanka." Ya fada ba tare da ya
amsa gaisuwar tata ba, kafin ta amsa ma ya kashe wayar.
Juwairiyya ma wayarta ce tayi kara ta dauka cikin doki da kuma murmushi a fuskarta tace,
"Bee."
"Awanni kadan da rabuwa da ke amma nayi kewarki.
Gani a waje ki fito mu tafi gida."
Lumshe idanunta tayi cike da annushuwan yanda yake nuna mata kauna a fili babu oye-oye.
"I missed you too. Bari in fito yanzu." Da haka ta kashe wayar ta dubi Salima dake jiranta ta gama wayar don ta mata magana.
"Ba dai tafiya zaku yi ba?"' Ta tambaya tana rike kugunta wanda yin hakan ya fallasa tumbi da kuma manyan hips dinta, da yake Salima irin matan nan ne chubby, farare kuma kyawawa masu jikin hutu don iyayenta suna da wadata, sai gashi kuma data tashi aure Allah Ya hadata da dan lukuti irinta duk da cewa bata kaishi kiba da tumbi ba.
"Wallahi tafiyan ne. Allah ya bashi lafiya sai kuma gani na gaba." Fadin Juwairiyya tana yafa gyalenta kana ta dauki wayarta.
"Ina son miki rakiya har waje amma Muhammad ya sakani aiki kar yayi ta jirana ban mishi ba. Kiyi hakuri don Allah." Ta karisa maganar tana marairaice fuska.
"Wallahi kar ki damu babu komai I understand. Sai anjima kar shima ya gaji da jirana."
Da haka suka yi sallama Juwairiyya ta fita daga gidan ta
samu Hafiz a waje a cikin motarshi. Tana shiga ya jawota jikinshi ya fara kissing dinta tana dariya tana kaucewa.
"Laaa me haka? Irin wannan ambush kamar kayi shekara baka ganni ba." Ta sa hannu ta rike kanshi da yake kwantarwa kan kirjinta.
"Ina gwada miki irin kalar kewarki da nayi ne. Ya kike?"
Ya zuba mata mayun idanunshi da suka canja kala dalilin abun da ya faru tsakanin su, duk da cewa cikin motar akwai duhu kadan bai hana Juwairiyya gano fitina a kwayar idanunshi ba.
"Lafiya kalau." Kawai ta iya cewa dashi domin itama
tuni ya canja mata yanayi saboda ta zama rainon Hafiz
don ya mayar da ita kalarsa tuntuni.
"Mu tafi?" Ya tambayeta cikin sarkewar murya.
"Yes Bee."
Nan take ya tayar da motar suka fita daga unguwar suka
fara tafiya akan babban titi zuwa unguwarsu.
"Zan mana take away me zaki ci?" Ya fada yana kokarin
karya kwana zai shiga wani restaurant da ke nan bakin hanya.
"A koshe nake domin naci tuwo a can, da yake miyar karkashi suka yi shiyasa ban dauko maka ba saboda baka ci."
Gyada kai Hafiz yayi kana yayi parking ya fita zuwa cikin restaurant din Juwairiyya ta bishi da ido cike da wani zazzafan sonshi dake fisgarta. Tafiyarshi ma kadai abun kallo ne domin bayan kyan sura da yake dashi, Hafiz ya san wankan da ya dace da shi.
Tana zaune a cikin motar tana kwatanta irin son da take mishi ya dawo ya mika mata ledojin hannunsa ta karba ta ajiyesu a seat din baya.
"Na saya miki ice cream ki sha yanzu kar ya narke." Ya tayar da motar ya fita daga harabar restaurant din, ita kuma cikin murna ta dauko ice cream din tare da mishi godiya ta fara sha suna hira har suka iso gida.
Yana gama cin abincin ya jawota jikinshi suka fara hira har lokacin baccinsu yayi suka kwanta. Kanta dake kan damatsanshi ta daga kadan tana duban fuskarshi tace,
"Bee menene ya faru da kai dazu? Kace idan ka dawo zamu yi magana."
"Juwairiyya akwai maganar da nake so mu yi da ke amma bana son ki d'aukeshi da zafi ko kuma ki mini mummunan fassara don girman Allah. Kina ji na?"