Showing 1 words to 3000 words out of 4349 words

Chapter 1 - TAFIYAR MU CHAPTER 1 HAUSA NOVEL

25 Dec 2025

116

TAFIYAR MU CHAPTER 1 HAUSA NOVEL




Bismillahir Rahmanir Rahim
4:00pm
Ruwa ne yake ke sauka daga sararin samaniya a garin Gombe, hakan yasa baza ka ji sautin komai ba sai karan ruwan dake dukan rufin gidajen mutane dalilin kowa ya shige cikin gidansa. A wannan daddadan yanayin kuma a wata unguwa da ake kira Tumfure wasu ma'aurata ke zaune a wani babban falo akan kujera daya, manne suke da juna a lullube da wani karamin bargo suna magana jefi-jefi dalilin kallon TV da suke yi bai bari sun samu hankalin junansu ba, ana gama film din da suke kallo suka ja ajiyar zuciya a tare kana suka dubi juna suna murmushi.
Mijin ne ya gyarawa matarsa zaman bargon ganin Kafarta daya ta fita daga ciki, bayan yayi na'am da aikinshi sai ya dubeta da tsantsar soyayyarta a kwayar idanunshi.
"Riya kin koya mini kallo, and the worst part of it shine wai Korean Series nake zama ina kalla ni Hafiz." Ya nuna kanshi da yatsa don emphasizing maganarshi.
Wacce ya kira da Riyan ta kama yatsar tashi tayi saurin
kaiwa bakinta ta ciza wanda hakan yasa Hafiz ya janye cikin jin zafin cizon yana dubawa yana kuma kokarin
tsumewa amma yanayinshi ya fallasashi, wato murmushin da yake yi har yanzu bai bar fuskarshi ba.
"Sorry." Ta furta tana kama kunnenta daya tana dariya
Kasa-kasa.

"Kin dauki bashi kuma zan rama a lokacin da baki yi tsammani ba, I swear." Ya Karisa maganan yana dandana yatsarshi a harshenshi alamar rantsuwa.
Murmusawa tayi wanda har sai da fararen hakwaranta suka bayyana gefen kumatunta daya kuma ya lotsa.
"You look childish idan kayi wannan abun. Amma Bee ba nace kayi hakuri ba?" Ta zumburo baki cikin shagwaba wanda hakan yasa Hafiz ya girgiza kanshi.
"Duk maganar da zaki fada ki fada amma ba zan hakura ba sai na rama, shiyasa na rantse. Oya ki tashi mu yi sallah mu je gaishe da Muhammad, bana son har a sallameshi baki je ba." Ya mike tsaye tare da mika mata hannunshi daya ta kama kana ta tashi suka fuskanci juna bayan ta yaye bargon daga jikinta gaba data ta ajiye a gefe.
Ido ta tsura mishi tana kallon surarshi dake burgeta tun mafarin haduwarsu. Hafiz baki ne mai tsantsar kyau a idanunta, ba kuma irin wanda ake fada a littafin Hausa da za'a ce ya zarce tunanin mai tunani ba, a'a, shi Hafiz dinta daidai ne wanda bata son a kara mishi komai haka kuma bata son a rageshi da komai. A gurinta Hafiz shine perfect example na namijin duniya da kowacce mace zata yi farin cikin samu. Dalilin tsayinshi yafi nata yasa dole sai da tayi dagelgel ta tsaya kan yatsun
Kafafunta kafin ta samu damar kissing din bakinshi mai fadi game da duhu.

Idanunshi ya lumshe yayi saurin zagayeta da hannayenshi wanda hakan yasa ta mannu da jikinshi har tana dafa kirjinshi a yayin da itama take rufe nata idanun. Sun kai minti daya a haka suna exploring jikin juna kafin Hafiz ya sunkuceta duk da nauyinta yayi daki da ita.
A kan gado ya direta yana kokarin cire singlet din jikinshi ta tashi zaune tare da mishi farii da ido tace,
"Bee kace zamu je asibiti gaisuwa fa!"
Hafiz da kashi casa'in na hankalinshi na ga abun da yake muradin yi ya hayo kan gadon yana cewa,
"That could wait, but for now let's make love."
Wani shu'umin murmushi tayi domin tun farko
Kudurinta kenan na hanasu fitan, babu wani dogon bayani ta biye mishi suka yada zango a sansanin ma'aurata.
Awanni biyu da haka ruwan saman ya tsaya wanda hakan kuma yayi daidai da karfe shida na yammacin asabar, Hafiz da matarshi ce suka fito daga cikin gidansu sun yi wanka sun shirya tana kulle kofa tana zumbura baki. Hankali kwance kuma cikin jindadin yanayin daminar Hafiz ya shiga cikin motarsa ta gani ta fada a gari da ke harabar gidan ya kunnata, maigadinsu na jin karar motar ya fito daga dakinsa ya fara kokarin bude musu gate.

Second biyar da haka itama bude gaban motar ta shiga tana kallon window fuskarta a kwaye. Briefly Hafiz ya dubeta a yayin da yake yin reverse zai fita daga gidan, murmushi yayi bai ce komai ba har suka fita daga gidan ya dagawa maigadin nasu hannu bayan ya aiko mishi da gaisuwa. Sai da suka fara tafiya ya daura hannunshi daya kan cinyarta yana mata tafiyan tsutsa yana kuma kara yin gaba wanda hakan ya fara canja mata yanayinta cikin kankanin lokaci.
Ture hannun nashi tayi tana kara zumburo bakinta ita ala dole tayi fushi amma shi bai bar murmusawa ba, a karshe ma mayar da hannunshi yayi yana mai cigaba da tsokanarta.
"Allah ka bari bana so."
"Allah ka bari bana so." Ya kwaikwayi muryarta yana dariya kadan har Adam apple dinshi yana sama yana
Kasa.
"This is not funny." Ta fada tana fuskantarshi a karo na farko tun shiganta cikin motar, harara ta dalla mishi wanda ya mayar mata da martanin alamar kiss har da hurawa a gareta.
Kwafa tayi ta harde hannayenta saman kirjinta ta kara juyar da kanta ga window tana kallon gidajen da suke wucewa har suka hau titi tafiyarsu ta daidaita.
"Seriously me yasa bakya son zuwa gaisheshi? Mutum ya kwanta bashi da lafiya har kwana uku kuma kina

kawance da matarshi amma kice baza kije ki gaisheshi ba? Ranar da aka kwantar dashi nace ki kirashi kika ki, jiya nace muje in kaiki amma kika ce kanki na ciwo, yau kuma kika shammaceni na kwashi gara wai duk don kar mu je amma baki san na gane wayon naki ba and here we are, mun kashe arna kuma mun fito gaisuwan. Yanzu ki fada mini dalilinki na tsanarshi Juwairiyya, wallahi wani lokaci har kunya nake ji idan naga kina mishi wasu halayen, ke ko kunyar matarshi bakya yi?"' Ya karisa maganan fuskarshi babu yabo babu fallasa domin tun ba yau ba yake sane da rashin jituwan da ke tsakanin matarsa da babban abokinsa.
First impression din Muhammad a gurin Juwairiyya shi ya jawo duk wannan bashin gaban, fadan da Hafiz ya yiwa Muhammad yasa yayi kokarin gyarawa amma ko da ya nuna sakin fuskarsa ga Juwairiyya wacce take cike da haushinshi sai ta basar ta nuna bata san yana yi ba.
Hafiz ya so tankwara matarsa amma abun ya garara domin ta kafu ne a kan dalilanta na wasu halayyar Muhammad din wandanda shi haka ya tashi da
su babu mai canjashi kamar yanda itama tana da wasu halayen da mutane basa so kuma ba zata canja ba.
"He is always grumpy kullum mutum a tsume kamar
kashi, ga dan banzan wulakanci ana gaisheshi ba zai amsawa mutum da murya babba ba sai kace shi mace ce. Na rasa yaya aka yi ka iya abokantaka da wannan mutumin for all these years. You are nothing like him,

kana da sakin fuska shi kuma kullum a tsume yake, kana da son mutane amma shi wulakanta mutane yake yi wanda har matarshi bai bari ba. Kana da son taimako shi kuma idan ya ga mutum na neman taimako baya ko tsayawa zai yi wucewarsa."
Murmusawa kawai Hafiz yayi hankalinshi na kan titi ya
ce,
"First of all, thanks for the compliments. Wasu abubuwan da kika fada a kanshi haka ne wasu kuma ba
haka bane, yana da wasa da dariya da kuma son mutane wanda ya ga sun dace da shiga circle dinshi.
Batun taimako kuma sau nawa zan fada miki ki daina
judging mutum akan laifi daya? Don kawai bai miki taimako sau daya ba a rayuwarki bashi zai sa kice kullum haka yake ko kuma haka yake da kowa ba. I know he is different kuma ba kamar ni yake ba, but that's how he is! And ba zai yiwu a canjashi ya zama yanda ake so ba don bakwa son halayenshi. And idan kika yi hakuri sai kiga ya sake miki fuska ku zauna ana raha tare."
"Allah ya sauwake. Kuma dama kai kullum cikin karesa kake yi kamar biyanka yake. Ni nafi tausayawa matarshi da Allah ya hadata da Rock irinsa." Fadin Juwairiyya tana dunkule hannunta guri guda don misalta yanda yake.
Wannan karon dariya Hafiz yayi yana kada kanshi yace,

"Wallahi duk ranar da ya ji kina kiranshi da sunan Rock
batawarku zata fi na yanzu."

Itama Juwairiyya dariya tayi a karon farko tana
hasashen yanda lukutar fuskar Muhammad zata turnuke idan ya ji. Ai kuwa nan take ta ayyana a ranta watarana sai ta fada din yaji, domin idan hakan zai bata mishi rai ita dadi zata ji. Tuni ta manta da wani bacin rai na tilastata da Hafiz yayi kan zuwa gaisuwan suka cigaba da hiransu gwanin ban sha 'awa har suka tsaya a bakin hanya suka sayi fruits suka wuce asibitin FTH
(Federal teaching hospital).
Hafiz ne ya musu jagora hannunshi dauke da ledan da
suka sayi fruits din yayin da dayan hannunsa yake rike da na Juwairiyya wacce ke fatan Allah yasa an sallami Muhammad ba sai sun hadu dashi ba. Male ward suka shiga daga nan kuma suka kutsa kai cikin side room B inda suka samu Salima matar Muhammad tana tattare kayansu tana sakawa a wani babban leda, shi kuma mara lafiyan yana kwance akan gado ya kuma daura hannunshi daya a kanshi alamar yana tunani.
Shigowar Hafiz da Juwairiyya yasa Salima ta dakata
daga tattaren kana ta fadada fara'arta tana musu barka
da zuwa.
"Ya jikin naka?" Fadin Hafiz yana isa bakin gadon ya
mikawa abokin nashi hannu suka yi musabaha bayan
ya tashi ya zauna.
"Da sauki sun sallamemu, yanzu tafiya gida zamu yi." Muhammad ya bashi amsa yana duban Salima wacce ta tsaya magana da Juwairiyya ta daina aikin da take yi.

"To Allah ya Kara sauki. Kace da mun Kara minti kadan baza mu zo mu sameku ba."
"Kai ma rigima ce tasa ka dawo, dazu da safe kafin ka tafi office ka zo mun gaisa. Da mun tafi kam, don wannan mai nawar ta kasa gama kimtsa kayan ne amma da tuni mun isa gida." Yayi maganar da karfi yanda Salima zata ji yana kuma aika mata wani mugun kallo.
Ai kuwa tana juyowa ta hada idanu dashi ta bar gefen
Juwairiyya ta koma bakin aikinta ba tare da ta kara
cewa komai ba. A hankali Hafiz ya take kafar Juwairiyya wacce tun shigowarsu ta samu plastic chair ta zauna bata ko kalli in da Muhammad din yake ba, dago kanta tayi suka hada ido yayi mata nuni da mara lafiyan da bakinshi. Bata fuska tayi sannan ta dubi sashen da mara latiyan yake tace,
"Ya jikin?"
Bai amsa ba illa kawar da kanshi da yayi bayan itama ya
aika mata mummunan kallon irin wanda ya yiwa matarsa dazu. Kwafa Juwairiyya tayi a ranta tana jin haushin wulakantata da yake yi tun ba yau ba, a ranta kuma zaginshi take yi tare da Hafiz din da ya matsa mata tilas sai ta zo nan.
"Ana gaisheka." Fadin Hafiz ga Muhammad ganin bashi
da niyyar amsa gaisuwar tata.
"'A ina?"' Yayi tambayar kamar da gaske bai ji ba.

Hafiz yayi ajiyar zuciya cikin gajiyawa da halinsu kana
ya mikawa Salima fruits din yana cewa,
"You know what? Ya wuce. Salima ga fruits and idan kin gama tattaren ku samemu a waje mu mayar da ku gida.
Kai kuma ka tashi mu fita kasha iska kafin su fito."
"Hafiz na kira Abbati zai taho da motata nasan yana
hanya ko ma ya iso." Muhammad ya bashi amsa yana saukowa daga kan gadon sai kara take yi dalilin nauyin shi.
Juwairiyya ce tayi siririyar tsaki tana ayyanawa a ranta cewa lukutancinshi kadai ma ta isa tasa cututtuka su dameshi tun da ba'a iya wata biyu sai ya kwanta rashin lafiya. Suna fita Salima ta dakata da abun da take yi tana murmushi tace,
"Sorry fa Kawata, yau laifina ya shafeki gashi ko gaisuwarki ba'a amsa ba."
Tsaki Juwairiyya ta ja wannan karon ba tare da ta boye
sautinsa ba ta dubi Salima tace,
"Kina hakuri da wannan mutumin, amma gaskiya ko sau daya ne ya kamata ki nuna mishi bakya tsoronshi kuma ke mutum ce. He should stop ordering you around da kakkausar murya cikin bainar jama'a saboda hakan bashi da dadi kuma girmanki yake zubarwa."

Salima tana jin Juwairiyya ta fara fadan data saba
muddin tayi witnessing Muhammad yana treating dinta irin haka sai kawai taci gaba da aikinta wanda dama ta
kusa gamawa.
"Hmm, ba zaki gane bane. Mu tafi kar suyi ta jiran mu bamu fito ba mu Kara yin wani laifin." Ta fadi hakan tana daukar katuwar ledan tare da wani mini trolley wanda Juwairiyya ta tabbatar suturun Muhammad ne a ciki.
"Ai komin rashin lafiyarsa bai kamata ya bar miki duk
wannan kayan ki dauka ba, he had to atleast take the mini trolley tunda janshi zai yi yana da taya, ke kuma sai ki dauki ledan." Fadin Juwairiyya tana tuna yanda Hafiz baya barin ta dauki komai idan sun je shopping ko kuma zasu fito daga gida. Cewa yake yi zai yi spoiling dinta saboda ita din abar tattalawarshi ce.
Salima ta kalli kayan hannunta cikin confusion don ita bata ga laifin hakan ba, ai shine mara lafiya bai kamata ma tun tarko ta barshi ya dauki kaya ba, da haka suka fita daga dakin tana cewa,
"Ni kuma dai bana ganin laifinshu, don sau da dama in ya mini fada to laifi nayi, kawai don Hafiz ya sakaltaki ne yana miki duk abun da kike so shiyasa kike ganin kamar ni a takure nake. But rayuwarku tana burgeni saboda yana nuna miki so da kulawa a duk inda kuke baya gajiyawa, ni kuma gogan nawa soyayyar ce bai iya ba kuma na kasa koya mishi."

"Alhamdulillah Hafiz is good to me, but | really hope one day kema a nuna miki so kamar yanda yake nuna mini, wallahi daga ranar zaki gane zaman da kike yi da Muhammad akwai takura da kwara a ciki. Allah kuma ya Kara miki hakuri akan wanda kike yi shi kuma ya shiryeshi. Ni na manta ne ma nayi magana, don na lura daga ke har Hafiz bakwa son laifinsa ko kadan sannan kullum cikin karesa kuke kamar wanda ya muku asiri." Ta Karisa maganan cikin raha ganin Salima ta fara shiga damuwa akan maganar da take yi wanda har ga Allah ba wai kusheshi take yi don ta ji zafi ba, a'a ita ta ki jinin ta ga ana cin zarafin mutum ne kuma yana shiru ya kasa tabuka komai. Halinta na rashin daukan wulakancin mutane yasa wasu suke cewa tana da rashin kunya da kuma masifa.
Da haka ta canja musu hirar sannan ta karbi ledan
hannun Saliman suka fita daga building din zuwa waje inda Hafiz yayi parking. Wayam babu su babu alamarsu sai wasu tsiraran motoci da kuma Keke Napeps da suke ficewa da mutane daga asibitin tunda lokacin visiting patients din ya wuce. Juwairiyya ce ta dauko wayarta ta danna kiran Hafiz tana cewa,
"To ina suka yi?"
Hafiz yana daukan wayar ya fara magana,'Riya dama yanzu nake da niyyar kiranki wani abu ne ya taso mana cikin gaggawa muka tafi amma ga Abbati yana zuwa zai mayar da ku gida. Ina fatan hakan ya miki?" Yayi maganan cikin sanyin murya kamar yaron da yayi laifi

yana neman tuba.
Wani sanyi ne ya ratsa zuciyar Juwairiyya tana tunanin ta yaya zata iya fushi mai tsawo da mutum kamar Hafiz?
Mutumin da yake treating dinta kamar ita ce kadai
mace a duniya kuma baya son fushinta?
"Babu komai Bee, zamu karisa gidan Saliman idan ka gama abun da kake yi sai ka biyo ka daukeni mu koma gida."
"Good girl. Sai na dawo."
Kafin ya kashe wayar tayi saurin dakatar dashi da
cewa,"Bee, ya naji muryarka wani iri, lafiya kam?"
Tana saurara yayi ajiyar zuciya kana yayi murmushi mai
sauti ya ce,
"Har na daina mamakin yanda kike gane canji a tattare
dani daga sauraran muryata kadai. I'm fine sai na dawo zamu yi magana."
Bata musa mishi lallai sai ta ji me yake damunshi ba
saboda ta lura kamar ma driving yake yi, sannan ta san ba zai taba boye mata damuwarshi ba kuma kamar yanda yayi alkawari, yana dawowa gida zai fada mata kuma da shi da ita zasu zauna su magance matsalarsu ba tare da kowa ya sani ba. Sallama suka yi ta juyo tana kallon Salima wacce ke waya har tana rage tsayinta idan tana magana, hakan yasa Juwairiyya ta gane cewa da Muhammad ne domin shi kadai take bawa wannan girman kamar zata nitse cikin kasa.

Salima tana gama wayar ta mayar da ita cikin jakarta ta dubi Juwairiyya da ke waige-waigen ta ina zata hango mai daukan nasu domin zaman asibitin har ya fara
gundararta.
"Zamu kara minti kadan domin Muhammad ya aikeshi
kasuwa zai sayo karkashi zan mishi tuwo." Fadin Salima
tana gyara tsayuwarta.
Wani takaici Juwairiyya ta ji domin ta lura Muhammad
sam baya tausayin Salima, tunda ya kwanta rashin lafiya tare dashi take kwana kuma a hakan da safe zata koma gida ta mishi karyawa ta bayar a aiko mishi kafin nan kaninshi zai zauna dashi, da azahar zata dawo da abincin rana har dana dare wanda wai shi gogan baya cin abinci iri daya sau biyu a rana. To idan ta zo tun azahar din shine baza ta koma ba sai washe gari da safe, kuma ko ta koma gidan ba hutawa zata yi ba abinci zata dafa ta kara dawowa dashi.
To duk wannan dawainiyar da tayi mishi meyasa yau
ba zai iya mata hakuri ya barta ta huta ba? Anya mutumin nan yana da tausayi kuwa? Har ta bude baki zata yi magana sai kuma ta rufe domin yawan maganar ma bashi da dadi, domin ita Saliman zata ga kamar fada take son hadasu, sannan ita ta ganshi tace tana so kuma take son zama dashi a haka ba tare da ta yi kokarin canja musu Tafiyar tasu ba. Sannan Juwairiyyan ta sani idan ta yawaita magana da kusheshi watakila Saliman zata ji haushinta saboda har ga Allah ita ma baza ta so taji wani yana aibata Hafiz dinta ba.

Wannan karon Salima ce ta canja musu hiran ta kawo musu hiran cikinta da ya shiga wata na uku amma tana nan garau babu rashin lafiya babu laulayi kamar ba ciki ne da ita ba. Ai kuwa ta tabowa Juwairiyya gurin da yake mata kaikayi domin tana son duk wata hira da za'a sako maganar yara a ciki saboda tana son haihuwa, gashi yanzu shekarar aurensu daya kenan da Hafiz amma ko batan wata bata taba yi ba. Salima kuma sun shiga wata na shida kenan amma gata da ciki har na wata uku, ko dai ita

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login