Showing 1 words to 3000 words out of 3072 words

Chapter 1 - YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA PART 10

Unknown   

25 May 2025

539

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA PART 10




a murtuke tsaye a kansa da takobi tsirara a hannu.
Nan take a cikin zuciyarsa ya yi addu'a, "Allah Ka kiyaye ni daga sharrin wannan mutum."
Cikin ladabi ya gai da mutumin, kuma lallai mai lambu ya ji dadin irin wannan gaisuwar girmamawa da ya yi masa.
Mai lambu ya ce,
"Wane dan Sarki ko Waziri ko
kuwa wane dan mai arzikin ne kai? Ko kuwa kai dan wani gawurtaccen malamin ne? Mene ne labarinka?
Me ya sa ka sata kana saurayi kyakkyawa kamar ka?
Babban abin da ya sa tun kana barci ban cire maka kai ba shi ne don na ga alamar mutunci a cikin fuskarka, kuma na yi tunanin ban san asalinka ba kada in kashe ka in jawo wa kaina jangwam. To amma kuma in kana ma da wata daraja ko wani asali, yaya za a yi ka yi sata? To yanzu na yanke shawarar ba zan kashe ka ba, zan bari sai Sarki ya zo zan sanar da shi cewa gwandar da ya ke ta tsimi ka zo ka cire." Ya kara tambaya cewa,
"Mene ne labarinka ya kai
barawo?"
Sai Yahaya ya ce, "Ya kai mai lambu, babu shakka ni ne na ciro wannan gwanda, dalili kuwa shi ne ni bako ne wanda yunwa ta nemi zautawa. A cikin irin wannan halin ne na ciro gwandar sai kuma hankalina ya dawo jikina na tuna cewa haram ce zan ci

kasancewar ban tambayi mai ita ba, shi ya sa na yanke shawarar sai na ga mai wannan lambu sannan in nemi izininsa, in ya yarda in sha. Tsananin gajiyar da ke tattare da ni ne ya sa har barci ya kwashe ni ka zo ka same ni a cikin wannan hali. Kuma zaton kasancewata dan masu mulki ko wadata ko tarin ilmi da ka yi, to a gaskiya ni ba daya ne daga cikin su ba, amma na san mahaifina sunansa Hamidu dan Usman, almajirin ilmi ne, kuma ya ba mu kyakkyawar tarbiyya, muna kuma godiya Allah Ya saka masa da alherinSa.
Sannan kuma ka yi hakuri, babu shakka kana da damar kira na duk abin da ka ga dama don kuwa na shigo cikin muhallinka kuma na taba kayanka.
Amma gaskiya ni ba barawo ba ne."
Jin zancen wannan yaro, sai tausayi da mamaki suka kama mai lambu saboda irin gaskiyarsa, kuma ya kara tausaya masa saboda irin tsananin yunwar da ya ba da labarin cewa yana ciki, amma saboda ba ya son cin haram bai sha gwandar ba.
Nan da nan mai lambu ya shiga can ciki, ya debo kayan marmari iri-iri masu dadi ya kawo wa Yahaya.
Akwai wata gasasshiyar tantabara a burgamensa, ya ciro ya hada masa. Yahaya ya ci nama da kayan marmari ya koshi ya yi hamdala, ya yi wa mai lambu

godiya sannan ya tambayi labarin lambu da kuma shi kansa mai lambun.
Mai lambu ya ce, "Kafin komai, farko dai sunan wannan gari da ka iso shi ne Burdan-Yamma, wannan lambu kuma na Sarki Salahuddin ne, mai mulkin kasar. Ni kuma sunana Haladu.
Ni ne Sarkin lambu, akwai masu aiki nan kamar mutum dari karkashina, yau ranar hutunsu ce, kuma a irin wannan ranar ne Sarki kan zo gewaye, shi ya sa ba ka ga kowa ba."
Sarkin lambu ya ci gaba da cewa, "Babu shakka ina da tambayar da zan amsa a kan wannan gwanda da ka tsinko. In Sarki ya ji, in ban yi sa'a ba yana iya yanke mini mummunar hukunci don a gaskiya Sarkin namu yana da zafi. Abin da kake ganin ba a bakin komai ya ke ba, shi wannan Sarki sai ya dauke shi da babban muhimmanci don ya sami damar hukunta mutum."
Da Yahaya ya ji jawabin Haladu Sarkin lambu sai ya ce, "To tun da ya ke haka ne, mu gudu mana kafin Sarki ya iso."
Mai lambu ya ce, "Yaro dai yaro ne in na gudu to lallai Sarki zai yi zato! ta gwanda daya, saboda haka zai dangina, a kama iyalina duk, kum Ka ga kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba ke nan. Ina ranar da namiji zai gudu ya bar iyalinsa cikin wahala?"
Sarkin lambu ya ci gaba da yi wa Yahaya bayanin cewa, "Abin da nake so da kai yanzu shi ne, ka fita daga cikin wannan lambu ka kama hanyar zuwa wani gari, ba na so Sarki ya zo ya same ka nan." Yahaya ya ce, "Yallabai ai babu yadda za a yi in tafi in kyale ka cikin hadari."
160
Sai Sarkin lambu ya zaro takobi ya ce masa, "Ko ka bar wannan lambu yanzu ko kuma in fille maka kai." Da Yahaya ya ga da gaske ya ke yi, sai ya kama hanyar ficewa, amma sai Sarkin lambu ya kira shi ya ce, "Zo nan Yahaya."
6 ПОГ
Sarkin lambu ya cika jaka da kayan marmari sannan ya kawo wasu 'yan kudi ya hada masa ya ce,
"Ga wannan ka dan yi guzuri." Suka yi sallama suna kuka.
Yahaya ya ci gaba da kukansa yana tafiya yana tunanin irin karimcin Haladu Sarkin lambu da kuma irin abin da zai faru a kansa in Sarki ya zo. Da ya dan
• yi nisa da lambu sai ya zauna a gindin wata itaciya.
⁃ Shi ma bai san dalilin zamansa bani Bai dai san tsawon lokacin da ya kasance a cikin wannan hali ba sai dai kawai ya rika tambura suna tashi, ashe Sarki ne ya tunkaro. Fahimtar haka sai Yahaya ya gaggauta ya koma ta baya, ya haura dannin lambun ya shige. Ya sami wuri ya labe kamar ya sani don kuwa in Sarki ya shiga, to askarawa kan yi wa wurin zobe ne, ba shiga ba fita. Yahaya ya sauya shawara daga labewa a cikin sarkakiya zuwa hayewa wata itaciya mai duhuwa, kuma duk abin da ake yi Sarkin lambu bai gani ba.
⁃ Shigowar Sarki kai-tsaye sai ya fara kewaya wani bangare na lambun wanda aka daddasa tushe dubu biyar na wani irin dan itacen inabi da aka kawo masa caga kasar Misra. Kafin ya gama har an kafa tanti an shimfida kilisai da matasai, an baje kayayyakin jin dadi mabambanta, sannan Sarkin lambu ya kawo wankakkun kayan marmari iri-iri ya ajiye.
⁃ Zaman Sarki ke da wuya sai Sarkin lambu ya zo ya zube a gabansa, fadawa suka dauka gaba daya, "An gaishe ka Sarkin lambu."
⁃ Sarki ya ce, "Sarkin lambu yaya lambu?"
⁃ Sarkin lambu ya ce, "Lambu lafiya lau ranka ya dade."
⁃ Sarki ya ce, "To yau dai ina so in sha gwandar nan da na yi ta cewa ka kula mini da ita da kyau, saboda haka sai a je a zunguro ta, amma kada a kuskura a bari ta fadi kasa. A ba mai dafa mini abinci ya fere ta, zan ci kadan yanzu, saura kuma ina so in tafi da ita gida.
⁃ Gwandar ce ma ta sa na shigo, don a gaskiya yau ban yi niyyar zuwa nan ba, kilisa na so tafiya.
⁃ "
⁃ Da Sarkin lambun ya ji dogon jawabin da Sarki ya yi game da gwanda, sai ya yi kasake gabansa ya fadi, zuciyarsa ta shiga bugawa uku-uku, ya ce a cikin ransa, "Ta faru ta kare."
⁃ Sarki ya dube shi ya ce, "Ko ba ka ji ba ne?" Sarkin lambu ya dukar da kai kasa ya cewa Sarki,
⁃ "Ranka ya dade tuba nake yi, na yi laifi tuba nake yi, ina rokon Sarki ya yafe mini. Ba zan sake irin wannan kuskure ba."
⁃ Sarki ya juyo gaba daya cikin fushi ya ce, "Mene ne ya faru?" Sai Sarkin lambu ya ba shi labarin saurayi Yahaya, ya kuma je ya dauko gwandar ya nuna masa.
⁃ Cikin kankanin lokaci kamannin Sarki suka sauya, ya yi fushi mai tsananin gaske, ya tashi ya dakawa Sarkin lambu tsawa, "Wato wulakancin da aka ce kana yi har ya iso gare ni ko? Ni ina Sarki kuma gona tawa, na danka maka amana har na yi maka Sarkin lambu, kuma ita wannan gwanda ba sau daya ba sau biyu ba ina yi maka gargadi a kan ta, amma don tsananin raini a gare ni shi barawon gwandar ma sai ka kyale shi ya gudu. Saboda haka yanzu za a yi ta zabga maka bulala ko za ka mutu ne." Duk abin nan da ke faruwa Yahaya na sama yana kallon su, a cikin zuciyarsa yana cewa, "Lallai wannan mutum yana da mulki, ga kuma kwarjini, lallai da ganin sa ka ga babban Sarki."
⁃ Sarki ya ba da umurni, nan da nan 'yan cika aiki suka shiga bulale Sarkin lambu, tun yana tsaye har sai da ya fadi. Da Yahaya ya ga haka, sai ya duro daga itaciyar da ya boye ya rugo a guje, yana isa sai ya fada kan Sarkin lambu yana tare bulalar, yana cewa, buge ni ku bar Sarkin lambu."
⁃ Sarkin lambu ya ce, "Kai Yahaya mene ya dawo da kai? Ba ka jin tsoron ranka?" Yahaya ya ce, "
⁃ "Na dawo ne saboda karimcin Sarkin
⁃ lambu da kuma tsoron abin da zai faru gare shi bayan na tafi. Ina tafiya zuciyata ta kasa natsuwa, saboda haka na dawo, zan yi farin cikin rabuwa da raina saboda rayuwar Sarkin lambu ta dore. Ai darajarsa ta fi karfin sarautar lambu, sai dai Sarkin wannan gari.' Jawabin Yahaya ya sa Sarki ya dada gyara zama, ya ce, "Kai yaro ka san gaban wanda ka ke kuwa?" Yahaya ya ce, "E na san a gaban Sarki na ke." Sarki ya tambayi Yahaya, "To mene kake nufi da cewa Sarkin lambu shi ne ya kamata ya zama Sarki a wannan gari?"
⁃ Yahaya ya amsa da cewa, "Saboda ka ga shi Sarkin lambu karimcinsa da gaskiyarsa da tausayinsa da sanin yau da kullum ne suka jefa shi cikin wannan wahala. Kuma duk wadannan abubuwa da na ambata abubuwa ne da suka kamata a ce duk Sarki
⁃ mai adalci yana da su.
⁃ Na tabbata in da a ce shi ke da wannan katon lambu, to zai iya bar wa talakawansa su rika amfana da kayan marmarin da ke ciki, amma sai ga shi Sarkin yanka guda zai halakar da bawansa mai tsananin yi masa biyayya saboda kwayar gwanda daya tak. Ba kwa tsoron a rubuta mummunan tarihinku ya zama abin tunawa ko karantawa na har abada? Ko da yake an ce kai Sarki ne mai tsananin zafi, in kuwa ka ji an ce haka game da kowane irin Sarki, to azzalumin Sarki
⁃ "
⁃ ne.
⁃ Da Sarki Salahuddin ya ji maganar Yahaya sai ya sake tambayarsa, "Yaya aka yi ka sami labarinmu
⁃ alhali kana bako?
⁃ Yahaya ya ce, "Ai labarinka ya kai ko ina, kuma ni ga shi na shaida, a kan gwanda kwara daya tak. Dama ni tsananin yunwa ce ta tsayar da ni, kuma ba tare da na sani ba na shigo cikin wannan lambu naka mai halakar da mutane."
⁃ Fadawa da duk sauran jama'ar da ke wurin sun yi mamakin irin yadda Sarki ya dauki irin wannan lokaci mai tsawo yana mayar da yawu da wannan saurayi.
⁃ Sarki ya tambayi Yahaya cewa, "Me kake nufi da halaka mutane?"
⁃ Yahaya ya amsa, "Abin da ya sa na ce lambu mai halaka mutane shi ne, ga shi a idona za a halaka
⁃ Sarkin lambu saboda kwayar gwandar da ya raine ta da hannunsa. Saboda haka ashe ba mu san mutum nawa wannan gona ta halaka ba zuwa yanzu, ni ma sai dai Allah Ya kwace ni."
⁃ Sai Sarki ya ce, "Yahaya kake ko? Ba ka jin tsoron da wanda kake magana ba?"
⁃ Yahaya ya amsa masa da cewa, "Ai duk Sarkin da ba a fada masa gaskiya, to kuwa ya halaka, don kuwa idan na kusa da shi suka fahimci cewa ba mai son gaskiya ba ne, to kullum karya za su shirya masa."
⁃ Yahaya ya kara da cewa Sarki, "A irin haka ne in runtsi ya yi runtsi a fagen fama, dakaru kan bar
⁃ Sarkinsu. Duk kuwa Sarkin da ka ga dakarunsa sun bar shi a filin yaki, to ba Sarkin kirki ba ne, yana
⁃ zaluntar talakawansa.
⁃ Ranka ya dade shi adalin Sarki a kullum za ka gan shi ne tare da malami mai tsoron Allah wanda da zarar ya ga Sarkin zai kauce hanya, to zai kwabe shi don kada ya fada cikin halaka. Amma in ka ga Sarki ko shugaba babu hulda tsakaninsa da malaman warai sai dai na tsibbu, to babu shakka azzalumin Sarki ne."
⁃ Ga alama Sarki ya riga ya fara damuwa da maganganun da wannan yaro ke ta zuba masa, ko kuma watakila sarautar ce ta motsa, sai ya cewa Yahaya, "Yaro ambaci bukatarka ta karshe in biya maka, don kuwa zan sa a dauke maka kai ne." Yahaya ya ce, "Ai ranka ya dade adalin Sarki ne kan ce a fada ya cika alkawari."
⁃ Sai Sarki ya ce, "Wato dai kana nufin ni ba adali ba ne? To da farko dai na yafewa Sarkin lambu laifinsa." Yahaya ya ce, "Adalcin farko ke nan."
⁃ Sarki ya ci gaba da bayani, "Tun da nake kan karagar mulki ba a taba samun talaka ya tsaya gabana ya fada mini maganar da ya ga dama kamar wannan yaro mai tsaurin kai ba. Kai Yahaya fadi bukatarka ta karshe sannan a sare maka kai."
⁃ Yahaya ya ce, "Ranka ya dade ka yi alkawarin za ka biya mini bukatata ta karshe?"
⁃ Sarki ya ce, "Kwarai kuwa, ai ni ne Sarki ba kai ba." Sai wani bafade ya sa baki, "Kai yaro fadi bukatarka kada ka bata mana lokaci."
⁃ Yahaya ya ce, "Ran Sarki ya dade, bukatata ta karshe ita ce, ina son in Sarki ya kashe ni, to ya sake rayar da ni. Wannan ita ce kawai bukatata."
⁃ Da Sarki ya ji bukatar Yahaya, sai ya yi shiru ya daga kansa sama, yana hango itaciyar gwandar nan da ta kawo wannan takaddama. Ya tsunduma cikin tunani, yana cewa a cikin zuciyarsa, "Lallai wannan yaro sha'aninsa akwai ban mamaki, ka ga yaro da iya magana kurfa-kurfa?"
⁃ Can bayan wasu 'yan dakikoki sai aka ga Sarki kamar ya tashi daga barci, ya daina kallon itaciyar gwandar. Ya kalli fadawa ya ce a saki Sarkin lambu amma yana so a bankare masa Yahaya. Nan da nan fadawa suka cika aiki.
⁃ Ya ba da umurni ga Sarkin dogarai cewa a je Jakara a zo masa da daya daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin kisa. Ba tare da bata lokaci ba Sarkin dogarai ya cika aiki, ya kawo wani murgujejen kato.
⁃ Sarki ya sa aka fere gwanda tsaf, sannan aka ba katon nan aka ce ya shanye ta. Ai kafin ya kammala shanyewa sai aka ga ya fadi kasa, yana ta shure-shure, kumfa ta cika bakinsa, kafin ka ce haka, har ya ce ga garinku nan.
⁃ Nan da nan sai Sarki ya ce, "Abin da nake zato ke nan. Shi ya sa saurin fushi ba shi da amfani, don kuwa ba don yaron nan Yahaya ya zunguro gwandar nan har abubuwan da suka faru sun faru ba, to lallai da ni ne zan bakunci lahira a dalilin wannan gwanda.
⁃ Ku dubi itaciyar gwandar can da kyau, ga wata macijiya gamsheka can ina hango ta, kuma lallai ita ta sa guba a cikin gwandar, abin da na hango ke nan ya sa don in tabbatar, na ce a zo da wannan mai laifin, kuma ga yadda ta kasance.
⁃ Kun ga da a ce na yi saurin cire musu kawuna, sannan yanzu na farga, to lallai da na yi nadama. Kai kuma Yahaya duk abin da ka fada mini na ji shi sosai, kuma yanzu ya shiga kunnena. Kuma daga yau na nada ka mataimakin Sarkin lambu, kai ne za ka rika kai mini kayan marmari gidana, duk bayan kwana uku. Kana zuwa ka shiga kai-tsaye abin ka, zan sanar da Sarauniya."
⁃ Bayan Sarki ya gama magana da su Yahaya, sai ya hau ya koma gida yana tunanin abubuwan da suka faru a lambunsa, da irin maganganun Yahaya da kuma irin basirarsa. Yana isa bai zame ko ina ba sai wurin Sarauniya Zizaratu, matarsa ta gaban goshi, ya ba ta labarin abin da ya wakana na daga al'amarin Yahaya da irin jajircewarsa a kan gaskiya tare kuma da irin kyau da Allah Ya yi masa, sannan kuma da irin yadda abubuwan da suka faru din suka zama sanadin tsirar shi kansa Sarki. Kuma ya sanar da ita cewa Yahaya ne zai rika kawo mata kayan marmari duk bayan kwana uku.
⁃ Abin ka da sharrin shaidaniyar mace, da matar Sarki ta ji labarin sai ta ji a duniyar nan babu wanda take so tun kafin ta gan shi kamar Yahaya.
⁃ Ranar kawo kayan marmari ta zo, Yahaya ya cika® kwando ya nufi gidan Sarki, ya je ya tarar ana ta fadanci. Sarkin fada ya shiga da shi ya yi gaisuwa sannan aka shiga da shi wurin Sarauniya.
⁃ Yana zuwa aka yi masa iso ya shiga, ya gaishe ta, ta amsa cikin murmushi sannan ya ce, "Ga kayan lambu."
⁃ Sarauniya ta kawo abinci irin na alfarma ta ba shi ya ci. Bayan ya kammala sai ya yi godiya ya dauki kwandonsa da aka juye zai tafi, Sarauniya ta kawo kudi masu dama ta ba shi ya amsa ya sake yi mata godiya ya juya. Zai fita dai sai ta sake kiransa ta ce,
⁃ "Ya kai Yahaya ina fata Sarki ya sanar da kai cewa bayan kowadanne kwana uku ne za ka rika kawo kayan lambu nan ko?"
⁃ Yahaya ya amsa, "E ya sanar da ni ranki ya dade."
⁃ Ta ce, "To shi ke nan, ka tafi."
⁃ Yahaya ya fita ya je ya yi sallama da Sarki. Sai Sarki ya ce masa,
⁃ "Yahaya ga malami, don an ce kana son
⁃ yin karatu."
⁃ Yahaya ya gaishe shi cikin ladabi, sannan ya sake yi wa Sarki godiya.
⁃ Sarki ya ce, "Ya kai Yahaya. Na ga maganar ka tana da kanshin gaskiya, shi ya sa na kawo wannan shahararren malamin kusa da ni don in wani abin ya shige mana duhu, ya rika nuna mana gaskiya." Sai Yahaya ya ce, "Ranka ya dade ka yi daidai.
⁃ Allah Ya ja zamaninka."
⁃ Bayan Yahaya ya kammala da wurin Sarki, sai ya bi malaminsa a baya don ganin inda ya ke don zuwa daukar darussa. Daga nan sai ya wuce lambu cike da farin ciki ya sanar da Haladu Sarkin lambu duk yadda ta kasance tsakaninsa da Sarki, malami da kuma Sarauniya Zizaratu.
⁃ To, abin da ke faruwa shi ne ita wannan Sarauniya dai ta rigaya ta shanye Sarki, ba ya iya yin komai sai ta yarda, karewa ma, Sarki duk ya kori sauran matansa saboda makircinta. Sauran matan da ke gidan yanzu su kamar talatin

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login