Showing 1 words to 1182 words out of 1182 words
HAMADA BOOK 1 PART 3
Zainab Kabir Biroman*
Don haka suke da rassa daban-daban a
leafatanin yankin kasar, musamman ma manyan biranensu da ya hada da wannan reshe nasu da ke cikin garin na Jiddah.
Yana da tarin Ma'aikata masu kwazo a sassa daban-daban, a gidan akwai sassan gudanarwa da sassan da ke kula da girka abinci da sassan da ke kula da amsar kudi da bada Tikitin Abinci da ma sassan da ya ke karɓar Tikitin.
Haka zalika da sassan da ke kula da tsaftar kayan Abincin da sassan da ke kula da tsaftar Kwanonin girkawa da Kwanonin zubawa a sassan da ke kula da tsaftar shi kansa Mut'am din baki daya.
Kwa
wana biyu hanya ba kyau ana yawan tsare hanya, anan ne ake kamen bakin haure da suke zaune ba bisa
Zainab Kabir Biroman
sk
ka'ida ba, don haka kwanaki kamar biyu zuwa uku Haraj ta yi wuyar shiga, sai dai aci a sha cikin abin da yake hannu.
Irin hakan a wasu lokutan daman tana faruwa musamman idan aka sami ɓullar wasu laifuffukan da suke kai komo a yankunan da bakin hauren ke da zama da sauran wuraren.
Da ya ke a wannan lokaci an soma lalata musu gari da yawaitar sace-sace a manyan Kantunansu, akan datse hanya da nufin bincike a kuma cafke bakin hauren da ke zaune ba bisa ka'ida ba madamar tsautsayi ya gifta maka, domin kuwa kullum cike suke da dabarun kaucewa kaman Askarawan Saudi Arebiya.
Tuni al'amura sun soma kan-kama a lokacin da suka iso Ganyari domin shiga Motar Haraj, kasancewar al'amura sun soma komawa yadda yakamata, sai dai ba har can ba.
Yana "Hadit, Haraj". Ya dubeta yana dan murmushi da farar Jallabiya kal! A jikinsa, a
Zainab Kabir Biroman*
saman kanshi jan Rawani mai ratsin fari da akai, irin na shigar mutanen Saudi.
"Babu shakka yau na kasance cikin samun tsananin sa'a".
0
Abdallah ya fada yana dan murmushi. Ya daɗe yana kaunar Yagana, gashi kuma ita din kamar ta raina kurarshi.
Ta dan harareshi.
"Bani wuri in shiga".
Ya dan bude gidan gaba, ta ko kara hararar tashi.
"Mugu! Muguntar ku ta mutanen Chadi za ka gwada min?
Askarawan Saudi sun dade hanya ka arce ka guje ka barni su tunkuda keyata zuwa kasata Nijeriya. Bana tunanin ko a tunani za ka kara tunano ni".
Yagana ta fada cikin gaggausan harshe.
A'a ke dai kawai ki ce ina ke ina wani dan kuci ku bamu Abdullahi, irin amasan yanzu sai manya, mu din ba komai bane. Hajiya Zaliha ya al'amuranki? Kina jin mu da mutuniyar taki ko?"
Zainab Kabir Biroman
*
Zaliha ta yi murmushi.
"Bani wuri in shige Abdallah Garin da sauki-sauki ai ka sani, mu zauna a bayan ya wadatar duk dai wuri guda zamu isa".
Tuni ta tattare doguwar Jallabiyarta har kasa ta yunkura ba tare da wasa ba ta dare bayan Akori-Kurar Abdallah. Kafin wani loakci Motar ta cika.
Sai kacacar-kacacar ka ke ji, kasancewar tini an saki sayiyiyar hanyar yanke ne ko ko mu ce ratsen gefen gari hanyar da ko Kwalba babu duk domin kaucewa Askarawan Saudi Arebiya.
Yadda mutanen cikinta suke zaune ba bisa ka'ida ba hakan nan Motar da mai ita da ke jihilar Jeddah zuwa Haraj duk ba bisa ka'idar ake ba, don haka suke kaucewa dukkanin wata hanyar da hukuma ta san da shi.
Fasinjojin kuma suke tsoron shiga gidan gaba ko na tsakiya sabo da, tsoron haduwa da Askarawa, don haka sun gwanancewa zama a bayan Motar inda da zarar ka ji wani motsio za ka dira ka arce ba tare da wani ɓata lokaci ba.
Zainab Kabir Biroman*
Lokaci zuwa lokaci ta kan yi ajiyar zuciya
sabi da tsabar rashin kyawun hanyar duka jiki sai ya sami motsuwa, al'amari ne da ya ri ga ya
zamewa bawa dole.
Ita kam Yagana sai 'yan guna-guni take, ga hanya babbar Kwalta daga Jedda zuwa Hajar a saukake sai dai babu halin ratsawa. Ga dai tsadar abin hawa Riyal dai-dai har goma, (Ashra Riyal) motoci ne na isa na alfarma (Limozine) musamman ma a kasashen Afrika, ko da yake ba tsadar abin hawan aka fi dubawa ba, a'a hatsarin da ke ke tattare tattare cikin bin sahihiyar hanya kasancewar za ka iya kiciɓus da jami'an tsaro.
Don haka suka gwammacewa shiga ruɓa66un motcin da akan bi a hadasu ta ɓarauniyar hanya a kudi da bai gaza fam arba'in zuwa hamsin ba.
Cikin wannan yanayi suka karaso Haraj ko kuma Hadit da Larabawan Saudi suka fi fada,.
Abdallah ya karbi hakkokinsa daga wurin Passenger tuni Yagana ta yi gaba, Zaliha kam ita.
Zainab Kabir Biroman
*
ta tsaya tana yi masa godiya, duk dai albarkacin Yagana kusan tun saninta da Abdallah bai taɓa amsar kudin Motarta ba, gashi kuma Yaganar ba ta duban Abdallah a matsayin wani mutum mai daraja.
Kasuwa ta yi kyau fiye da tsammani musamman da ya ke kwanaki masu dan dama ba a sami damar isowa Haraj ba, don haka bolar sintsir take da ababen alfanu musamman wannan rana da Arab Supply Treading Company (Kamfanin da ke harkar amfanin Gona) suka iso da bolar Kamfaninsu.
Abn tsinci na tsinta, an sai da na sayarwa, 'yan wadanda suka yi saura an yi nufin komawa da su gida. Anan din ma akan ci kasuwar su musamman ga mutanen da ba su da ra'ayin shiga Haraj da kuma baki da ba su ma wanye da Haraj ba.
A dai-dai bakin Vera Pizza Restaurant, kiris su karasa ciki, Zaliha na daga gaba Yagana na bayanta tana cikin tarin nishadi, an jima ba a yi samuwa irin ta yau ba.
Zainab Kabir Biroman*
A lokaci guda al'amuran suka yi kokarin sauyawa mutane da dama galibi da suka fito daga yankin Afirika suka shiga gudun in ba ka yi bani waje. Ba a duban gaba bare duban baya, kokari e na tsira da kai.
Baka wani bukatar bayani balle dogon nazari. A lokacin Askarawan kiris ya rage su karaso.
Yagana ta yi wani tsalle ta dire, ta yi kwana ta lakwasa ɓarinta na hagu ta miki layin Kantunan Shagunan Haraj.
Kafin wani lokaci ta ɓace cikin jama'a. Tana da saurin motsi. Wani lokacin kana iya dubanta matsayin hatsabibiya.
Ta rude ta kidime ta ma diririce baki daya. Akwai rashin tabbas sai dai duk da hakan tayi amfani da lakaninsu ta dora kafa bakin kofar Vera Pizza Restaurant.
Bisa SHAHADAuka idanu ya dawo kanta, cikin rufaffen dakin da aka tanada domin abokan cikini.
Zainab Kabir Biroman
*
Baki ne masu izinin zama a kasa da ma tsirarun Larabawan na saudi sai ko wasu daga cikin ma'aikatan da ke kulawa da walwalar abokan ciniki. Ke nan babu wani idon sani, sai shi daya tal! da ya duka gaban katon Teburin da yake harhaɗawa abokan hulɗa abinci,
Ya dubeta ta dubeshi, ta kuma kara dubansa cikin wani irin karayar zuciya, yanayinta kadai zai nunar maka da tsagwaron firgici da tashin hankalin da take ciki.
Zuciyarsa ta shiga wani irin kunci na banzatar da kai da al'amarinsu na kasashen Afirika ke yi, abin da kan janyo musu raini.
A lokaci guda Askari guda ya sako kafafunsa cikin rufaffen gurin Vera Pizza Restaurant.
Ba ta sani ba ko ta sani? Ta dai cusa kai a takure, a kanannade a kuma cure wuri guda a karkashin Teburin da suka basu da nan nan da hidimarsu take ya ta ta wai ta fadawa hannunsa, ya kau da kai ya kuma ci gaba da ayyukansa duk da kasancewar hakan matukar hatsari ne a