Showing 1 words to 1364 words out of 1364 words

Chapter 1 - HAMADA BOOK 1 PART 2

01 Mar 2025

718

HAMADA BOOK 1 PART 2





KASUWA TA YI KYAU, saura dame? Mu wuce Italian Vera Pizza Restaurant mu yi guzurin Pizza Vera (Nadadden Burodi mai nama da kayan lambu a ciki) sannan mu ci Abinci mu wuce gida Hindawiyya ko ma kai hakarkarin mu kasa mu sami afuwa (Kasancewar tunda Asubahi ake sammakon fitowa).
Zaliha.
Yagana ta fada a lokacin da take duban
Ta kuma ja hannunta, taki kaɗabn ya sanar da su Vera Pizza Restaurant anan dai cikin kasuwar ta Haraj.
Gidan abinci ne da yake da matukar farin jini a idanun Bakaken Fata ga saukin farashi ga kuma galibi nau'in abinci ne da yake kamanceceniya da nasu.
Kusan koda yaushe kusan kowacce rana matukar sun tako Haraj anan suke cin abinci su kuma yi guzurin tafiya da shi.

Da farar riga, bakin mashakin wuya (neck tail) da bakin wando, bakin takalmin sau ciki da bakar Safar kafa ya karaso hannunsa rike da katon tire mai launin zinariya shake da kwanonin masu tarin sheki a ciki.
Dukkansu suna da tarin tsafta, sai dai kamar wannan din ya daresu, kawai dai yana wani ji-ji da kai ne kamar ya mance shi din boyi- boyi ne mai wanke kwanonin da muka ci Abinci, yaushe ne likkafar ta ci gaba har ya sami mukamin rarraba mana abinci? (Service).
Yagana ta fada muryarta sake. Haka take ba ta iya munafurci ba, balle ma da wannan da suka sha bam-ban ta fannin harshe.
Zaliha ta dubeta ta kuma dubeshi sai kawai ta gyada kai cikin nuna rashin jin dadi.
Ita din ma ba wai gwani ne a idanunta ba, sai dai a kalla tozarta dan adam ba shi da amfani. Dalilin da ya sa bai zamo gwani a idanunta ba kuwa shi ne, wani lokaci da ya taɓa gaya ma ta magana wai suna zubar da mutuncin jinsin su (bakake).

Dama duka African su baki daya suna tsince-tsince a bola?"-
Ta tuna ta bashi amsa, "Da ta je ta dauko na wani fa? Ko kuwa ta yi aikin banza?"
Kusan komai da suke bukata ya ajiye musu ya kuma kara koda akwai wani abu da suke da bukata?
Ya fada ne cikin harshen Larabei kamar yadda al'adar Mut'am (Gidan Abinci) din yake karrama abokanan hulɗarsu.
Yagana ta kashe ido tana murmushi lokaci guda ta juye harshe.
"Kawai dai muna bukatar sakin fuskar Oga abokanan huldarmu, har lokacin tana kashe idanu.
Ya yi tsai yana dan nazari ya ma gano babu abin da ya hada wannan da daya daga cikin nauye-nauyen da aka dora a wuyan Ma'aikatan PIZZA VERA RESTAURANT.
Ke nan kaucewa wannan babu abin da zai shafi sana'ar da yake ci da sha a cikinta.

Sai kawai ya yi gaba ba tare da ya kara ko
ɗaga kai ya dubi Teburin su ba balle ma ya dubeta, hasali ma ya karkata ga hidimar abokanan cinikinsu da suke ta kai da kamo.
nan cikin Hindawiyya gidansu yake, gini ne mai hawa shida ba dai na zamani ne har can ba, ginin sama yana daya daga cikin tsofaffin gine-ginen da ke cikin Jeddah. Sai dai sabo ne dal! Na zamani ne shar! Idan aka kwatantashi da gine-ginen da ke cikin kasashenmu na Afirika musamman kasarta Nigeria da suka fito daga cikinta.
suke.
A hawa na uku, daki mai lamba hudu
Gidane na hadaka kamar yadda rukunin ɗakunan suka zamanto na hadakar mafi karanta mutane biyar a daki guda ba don sabi da komai ba, ba don kowa din baya so ya sake ba sai don

tarin dan karen tsadar da haya take yi a Jeddah da ma kasar ta Saudi take da shi.
T
a bude bakin tatattaciyar Madarar (Halib Sa'udi) ta soka tsinken tsotsa ta fara tsotsa cikin dadin rai, domin kuwa yau kasuwar ta yi riba, ga hanya wasa yau babu matsala.
"Ana idar da sallah asubahi zamu nutsa Haraj ina da labarin Heraq International Mall za su iso da sharar katafaren kantinsu. Babu ko shakka samun da ke ciki ya wuce misali, ki kwan da shiri, kada ma in tada ke ki mike kina mini layin nan naki".
Zaliha ta dan taɓe baki, gajiya kam ta gaji matuka gaya.
"Kamar zafin nema baya kawo samu, 'yan kuɗaɗen da muka samu a kwanakin nan basu ishemu rayuwa na wani lokaci mai tsayi ba? Ehem Yagana...

Yan kawowa wani sa'in, ehem zafin nama ba, irin dai yau din nan ai lallai kwazo da kokarin mu ne ya kaimu ga samun abin da aka samu, da mun zauna nan kwance da bamu kai ga samu ba".
Zaliha ta ja ma ta tsaya daga tsotsar Madarar tana dubanta.
"Wai in tambayeki ma Zaliha? Uhum in tambaye ki?"
Ta kara zakuɗowa.
"Ke din ba ki da wani tanadi ne? Ba ki da wani tanadi da ki ke fatan tsinanawa kanki abun kirki balle ki hango dangi na gaba da suke cikin tsananin bukata.
Me ye ne a kasashenmu face fatara da yunwa da ya yiwa mutanen mu katutu".
Haka ki ke so ki kare shahadarki a banza ba tare da kin amfanawa kanki da komai ba balle na gida ya saka ran tsattsaga da zarar kaddarar komawar gida ta afko mana (kame)".
Zaliha ta mike ranta a ɓace. Ban taɓa tunanin na iso kasar nan domin
tattara dukiya ba, ban taɓa tunanin na zo ne domin in azurta ba, ban taɓa tunani.....ban taɓa tunani.....
"
Haka ta shiga jerowa cikin wani irin yanayi mai tsoratarwa, ka yi tsammani ta fice daga hankalin tane haka nan ta kan kasance a lokutan da motsin wani abin da ya shafi gida ya ratsa zuciyarta.
Bebi mutuniyar Yola daya daga cikin mutanen da suke daki guda ta yi kwafa ta ma ja tsaki.
"Da gan-gan ma Yaganar ta ke kokarin shiriritar da kanta akan yarinyar da alama yunwar abin da za ta kai baka ne ya kawota Saudi ba neman dukiya ba".
Ita kam Mai gado fadi take, "Dama dai duk kun tsai da hankalinku guri guda, ga wata samuwar nan a Al Hijrayi". (Kauye ne a cikin yankin Jidda).

Ban taɓa tunanin na iso kasar nan domin tattara dukiya ba, ban taɓa tunanin na zo ne domin in azurta ba, ban taɓa tunani.....ban taba tunani..."
Haka ta shiga jerowa cikin wani irin yanayi mai tsoratarwa, ka yi tsammani ta fice daga hankalin tane haka nan ta kan kasance a lokutan da motsin wani abin da ya shafi gida ya ratsa zuciyarta.
Bebi mutuniyar Yola daya daga cikin mutanen da suke daki guda ta yi kwafa ta ma ja tsaki.
"Da gan-gan ma Yaganar ta ke kokarin shiriritar da kanta akan yarinyar da alama yunwar abin da za ta kai baka ne ya kawota Saudi ba neman dukiya ba".
Ita kam Mai gado fadi take, "Dama dai duk kun tsai da hankalinku guri guda, ga wata samuwar nan a Al Hijrayi". (Kauye ne a cikin yankin Jidda). Mutanen Chadi sun nutsa sósai suna
samun alheri mai zai hana muma mu gwada tamu sa'ar"
(Haka zaman ya ke ba a yiwa juna kyashi akwai matukar hadin kai).
Cima ita daya da ta fito daga kasar ta Niger, ta ke ku a cikinsu baki daya ta dubesu.
"Ku ma wasu wawaye ne duka ma kamar Iskance ta ke yawo da mai kayan Kara...kamar yadda ku 'yan kasar Hausa ku ke fada, ban ga dalilin da zai sa in wahalar da gangar jikina a banza ba alhalin ga jari guda a tattare dani". Ta yi nuni da gangar jikinta.
Washe gari ma an ci kasuwar sosai a Haraj, kamar yadda Yagana ta so, suka wuce Pizza Restaurant, wannan karon Chicken Burger aka yi nufin ci.
Da farar riga da bakin wando da bakin Takalmi.
Tsaf! Shar! Tas! Ya karaso rike da katon Trey a hannunsa kamar rashin sa'ane kusan kowace rana (sai fa dai-daiku) al'amuransu sukan fado hannunsa duk da kasancewar ba shi ne kadai mai hidimar raba abinci a Mut'am din
ba.
Baki ne kamar mu, sai dai yana da kyau irin na Sa'udan garin nan.
"Shi yasa yake mana shan kamshin nan". Yagana ta fada cikin saitin Kunnen Zaliha.
Ko da yake ba rada ba ce muryarta a bude take maganar.
Zaliha ta kau da kai, ta rasa dalilin da zai så ka damu da al'amuran wanda ma bai san kana yi ba.
Bai dubeta ba balle ya dubi Yaganar da ko da ido yana iya fahimtar sakonnin da take aika mishi, ya wuce abinsa.
Kai ya ma bar sassansu ya nutsa cikin yiwa wasu Abokanan huldar nasu hidima.
Mut'am (Gidan Abinci) ne mai girmaa a mutanen kasar Italiya (Italia), ya sami karɓuwa da farin jini a kafatanin kasar ta Saudi.

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login