Showing 1 words to 3000 words out of 4583 words

Chapter 1 - YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA PART 5

11 Nov 2024

1466

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA PART 5





dardumar akwai takobi da mashin da ake magana.
Wadannan su ne kayan fadan da kawai za su iya kashe Sarkin aljanu da kurwarsa, kuma wannan sirdi shi ne sirdin dokin jarumin.
Sai dai kuma duk wanda zai isa wurin Sarkin aljanu da wancan nufi na kisa, to kafin ya isa tabbas zai sha
¿wagwarmaya mai tsanani, zai yi karo da dodanni da aljanu da mutane, kuma dole hanya daya ce tak zai bi don babu wata hanya sai ita."
Yarinya Nur dai ta dakatar da wannan bayani tare da cewa sauran 'yan matan, "Lallai wannan mugun aljani ransa zai yi wuyar kashewa, amma in Allah Y a so za mu sami nasara a kan sa." A wannan lokaci dare ya riga ya yi, sai suka tsayar da shawara a kan cewa su bari sai ranar Asabar in Dailanu ta zo, 'yata Nur za ta ba da sako a kawo mini.
Wannan makon ma haka ta kasance, Sarkin aljanu ya rika zuwa kamar yadda ya saba har zuwa ranar Juma' a da ya yi sallama da su sai Lahadi ke nan. Gari na wayewa sai ga aljana Dailanu cikin farin ciki da walwala, suka gaisa tare da sanar da ita cewa sun fahimci duk abin da suka juya a wancan makon, amma sun fahimci cewa lallai abin zai yi wuyar gasken-gaske.
Dailanu ta ce, "Ai dama na riga na fada muku." Sai Nur ta ce mata, "Ina da wata shawara ya ke

Dailanu wadda ina fata za ki taimaka."
Aljana Dailanu ta ce, "Ya ke aminiyata Nur, ai kamar yadda na ce ne tun tuni, kuma ina kara maimaitawa yanzu cewa ko zan rasa raina ne, to na yi alkawarin zan taimake ku. Kuma ai ni yanzu sunana aljana ce kurum, amma ai na zama daya da ku, kuma mu aljanu ba ma karya alkawarin aminanmu.
'Yata Nur ta ce mata, "Wata shawara ce muka yanke cewa wannan bavani na rayuwar Sham'una, zan rubuta takarda ki hada da shi ki kai wa mahaifina. Daga nan in kin je sai ki yi masa bayanin kanki. Ki je masa cikin siffar mutane ne. Zan sanar da ke sunan garinmu da misalin gidanmu. In kuma kin gan shi, to ina so ki roke shi ya karantar da ke karatun Alkur'ani mai tsarki da kuma ilmin addinin Islama, don kin san shi addinin Musulunci ba a yin sa da jahilci. Kuma idan kin amince ya ke Dailanu, ina so ki je gefen dajin nan, ki gina wa mahaifina katon daki da kuma wani karami kusa da shi.
Shi wannan daki a ciki za ki rika koyon karatu, kuma ina so ki rika yi masa abinci safe da vamma. Sauran bayani kuma za ki ji a wurin mahaifin nawa. Kuma zan sa Sarkin aljanu ya yi lambu kusa da dakunan inda zan rika zuwa kowane dare har tsawon shekara daya daga ranar da aka sami jarumin da muke kyautata zaton ceva zai iya, don mu rika debe masa kewa." Aliana

Dailanu ta ce, "An gama ya ke Nur." Dattijo ya bude wani littafi ya janyo wata takarda yadda shi ma kansa Idrisu yana iya kallon abin da aka rubuta. Shaihi ya ce, "Yauwa Idrisu, ga takardar da ta rubuta din. Ta ce,
"Zuwa ga mahaifina wanda nake kauna har abada, kuma wanda nake girmamawa fige da duk wanda ke numfashi.
Ya wanda haskensa shi ne nawa, ina fata ka yi mini gafara saboda rashin gani na wanda na tabbatar kana cikin juyayi, kuma na tabbata za ka yi mamaki ya kai mahaifina mai girma, irin ilmin da ka karantar da ni, da kuma irin tarbiyyar da ka yi mini, kai kanka ka san ni ba irin 'ya'yan da kan gudu su bar iyayensu ba ne ba tare da wani kwakkwaran dalili na Sharia ba.
Raddara ce ta faru da ni, amma ina so ka kwantar da hankalinka don ina nan lafiya lau.
Ya babana mai daraja, na tabbata kuyanginka da muke wasa da su sun ba ka labari cewa ba su ganni ba bayan farkawarsu daga barci mai naugin da ya dauke mu gaba daya, to ni dai na farka ne kawai na gan ni a cikin wani makeken gida wanda akwai wahala a sami dan Adam da

а taba ganin mai kyansa, kuma shi wannan gida yana kan wani tsibiri ne daga cikin uku mafi girma da ke bayan duniya.
Dalilin zuwana wannan gida shi ne wani mugun Sarkin aljanu ne mai suna Sham'una dan Sarkin aljanu Damsalu ya dauko ni ya kawo ni. Ba ni kadai ya sato ba, akwai sauran wasu hamsin duk 'ya'yan mutane, kuma 'yan mata.
Ya nuna cewa ni ya ke so, shi ya sa ma wai ya kawo mini sauran 'yan matan don wai su debe mini kewa. Da muka fahimci haka sai muka kwantar da hankalinmu don mu sami labarinsa.
Babu dama in zo da kaina wurinka, don in Sham'una ya sani, to duk zai halaka mu. Shi ya sa na aiko wannan baiwar Allah don ta kawo maka wannan takarda.
Ita wannan aljana kawarmu ce, sunanta
Dailanu, ita da Sarkin aljanu Sham'una dan wa da 'yar kani suke. Ita ma wannan aljani ya yi mata wulakanci bayan ya karya alkawari. A dalilinsa ta kashe 'ya'yan mutane da yawa ba tare da hakkinsu ba, mu ma Allah ne Yaginufin kwananmu na gaba, don kuwa har ta yi niyyar halaka mu, amma daga baya ta zama kawarmu har ma ta Musulunta. Sannan kuma dai ita ce ta

kawo mana wanna bayani na asirin ran Sarkin aljanu Sham'una. Ta yi mini alkawarin za ta kai ka dajin da aka ambata ta gina maka dakuna babu nisa sosai da rijiyar da aka ambata, sannan kuma za ta rika kawo maka abinci sau biyu a kowace rana, kuma tana son yin karatu a wurinka don sanin addinin Islama sosai.
Zan bukaci Sarkin aljanu ya yi mini wani babban lambu a cikin dajin don a rika kawo mu a kowane dare muna shakatawa a ciki har zuwa lokacin da bukata za ta biya, kuma na tabbata zai yarda.
Za ka rika samun labarina daga wurin almajirarka Dailanu. Ka huta lafiya, nice 'yarka Nur.
Dattijo ya ci gaba da ba saurayi Idrisu labari cewa,
"Lokacin da 'vata ta kammala rubuta wannan wasika, sai ta ba aljana. Ran nan Dailanu ba ta bari yamma ta yi ba, kuma abin ka da aljan, da Magriba na yi Sallah ina cikin turakata ina jiran lokacin Sallar Isha'i sai na ji wani irin kanshin turare wanda ban taba jin irin sa ba, can sai na ji muryar mace ta ce, "Assalamu alaikum." Nan da nan sai na amsa, sai na ga wani hayaki ja, sai ga

shi wannan hayakin ya koma wata mace kyakkyawa, sai na ji gabana ya fadi, na tsorata, amma kuma na tuna cewa da sallama ta fara, sai na sami natsuwa.
Duk da haka dai sai da na vi addu'o'i irin na neman tsari kafin yarinyar nan ta zauna kusa da buzuna ta gai da ni cikin ladabi da girmamawa, sannan ta ce, "Ko kai ne Ibrahim dan Yahaya mahaifin Nur?" Nan da nan na amsa cewa nine, "Mene ne labarinki?" Sai ta miko mini takarda. Ina budewa sai na ji gabana ya fadi ras a dalilin gain rubutun 'yata. Na fara karanta takarda ina hawaye wanda ya samu a sanadin begen 'yata da kuma farin cikin cewa tana raye. Na karanta takardar tun daga farko har karshe.
Bayan kammalawa, sai na gode wa Allah Madaukakin Sarki saboda amsar rokona da Ya yi a game da gudan jinin zuciyata. Aljana ta miko mini bayanin ran Sarkin aljanu na amsa. Bayan mun gaisa ta yi mini alkawarin za ta dawo bayan kwana uku, don tana so ta je ta gina dakin nan a wannan dajin kusa da rijiyar da ke cikin bayani, na ce mata daidai ne. Ta tafi ni kuma na ci gaba da nazarin bayanin da ta kawo din wanda kuma na fahimta daidai gwargwado. Cikin kwanaki uku na shirya tsaf, na hada litattafaina kiriga-kiriga, wadanda zan taho da su wannan daji.
Bayan kwana ukun da La'asar sai ga yarinyar aljanar

nan ta iso, ta ce ta gama gina dakina, kuma kusa da rijiya, duk abin da nake bukata yana ciki. Sai na tambaye ta ko za a iya kai mini litattafaina can? Ta ce,
"Yanzu kuwa ya Babana." Kafin ka ce mene ne wannan littattafaina sun bace tare da aljana, bayan kamar rabin sa'a sai ga ta ta dawo, ta ce mini, "Mu tafi."»
Ta ce in runtse idanuna, na runtse, sai na ji an yi sama da ni, kafin lokaci kadan sai na ji an sauke ni a bakin kofar wannan daki. Na gan shi kamar yadda kake gain sa, an dan kewaye shi saboda namun daji. Na shiga ciki sai na tarar da wurin ashe katon daki ne, babu abin da babu a ciki, kuma ga littattafaina nan an shirya su gwanin ban sha'awa.
Ya kai Idrisu, bayan an kawo ni wannan daji, sai ya kasance wani lokaci in kwana nan wani lokaci kuma in sa almajirata Dailanu ta kai ni gida in kwana. Kuma a kullum sai Dailanu ta zo ta dauki karatu.
A takaice dai dalilin zuwana wannan daii shi ne don in sanar da mai rabo asirin wanna rijiya, don in mutum bai san asirin ba, to har abada ba zai gane komai ba.
Wata ranar Lahadi, ana sauran 'yan kwanaki kadan ka iso nan, kuma kamar dai yadda aka saba Sarkin aljanu Sham'una ya tafi wurin 'yan matansa, sai ya tarar kowaccensu ta yi wata irin kwalliya ta musamman.

'Yata Nur kuwa a ranar in ka gan ta sai ka dauka wata ne dan daren goma sha hudu a cikin taurari.
Sham'una ya samu suna ta kade-kade da wake-wake da wata irin rawa da rausaya mai daukar hankalin duk wanda ya gan su. Suna yi suna sa sunansa a ciki.
Tarar da su cikin wannan hali ya sa shi Barkewa da rawa tare da su. In ya yi juyi saboda tsananin in nishadi da murna, sai ya daga hannunsa sama, nan take ya cika da lu'ulu'u da jauhari da yakutu da azurfa da zinare, ya watsa cikin su, su kuma sai su yi ta warwaso da tureneniya shi kuma yana jin dadi don 'van mata kyawawa suna kokawa a gabansa.
Bayan sun gama nishadinsu sun gaji, sai suka zauna suka kewaye Sarkin aljanu, shi kuma yana ce musu, "Ya ku wadannan 'yan mata, tun da nake babu wani abu da ya taba damu na. Ga shi ina da mulki, ban taba rasa komai ba, ga shi kuma ni kasaitaccen jarumi ne, aljanu ma su kan su bayan toro na da suke ji har bauta mini suke yi, tun da na karya Ifritu na wargaza rundunarsa, na kashe masa jarumai da dakaru, saboda haka ni ne Sarkin aljanu na duk duniya. Ba na tsoron komai, kuma ba na tsoron kowa, amma duk daular nan da nake ciki, ban taba samun abin da nake jin dadi da murna da sha'awa ba kamar in zo wurinku."
Da ya gama labarinsa sai yarinya Nur ta matsa kusa

da shi ta ce, "Ya kai wannan kyakkyawan Sarki mai karfi, babu shakka ni na amince fiye da kowa cewa babu mahalukin da ya isa a karan kansa ya karya ka, kuma ya kai Sham'una, muna in dadin kasancewar ka tare da mu. Sai dai kuma akwai abin da nake son in fada maka, cewa ka san mu mutane ne, kuma al'adarmu da ku ta sha bamban. Wani abu ne ya dame mu, muna fata kuma za ka share mana hawaye."
Jin wannan zance sai Sarkin aljanu ya yi zumbur ya ce,
"Ya ke yarinya mai kyau, mene ne bukatarku, ko kuna so in kai ku duniyar wata ne ku vi kallo?"
Nur ta amsa, "A'a, ko kadan ba muna son zuwa duniyar wata ba ne, sai dai gani muka yi kasancewar kana tafiya ka bar mu, in dare ya yi kuma been ka yakan hana mu sukuni, shi ne sai muka ga cewa maimakon mu yi ta zama a wannan wuri wanda ke sa mana shauki da kewar ka, sai muka yanke shawarar cewa akwai wani daji wanda ake kira Surkukin-gagara can cikin duniya da muka taba jin labarin cewa babu wani dan Adam da ya taba zuwa wurin sai dai namun daji kawai. Shi ne muke son ka sa a yi mana lambu a wurin, a kullum dare a kai mu can mu yi wasanninmu, in kuma lokacin barci ya yi a dawo da mu, amma fa sai in Sarki ya amince."
Yana jin wannan zance na Nur sai ya kyalkyace da

dariya, ya ce, "Ku kuwa mutane kukan ba ni dariya, abin da bai taka kara ya karya ba, sai ku dauke shi wani babban lamari. Bayan wannan kuma babu wani abu da kuke bukata?"
Ta ce, "'a bayan wannan babu wani abu da muke bukata, da ma ai mu babbar bukatarmu ita ce mu rika ganin ka a kullum."
Nan take sai Sarkin aljanu ya yi tafi sau uku, ya yi wata irin magana wadda ba su san abin da take nufi ba, sai ga wasu kattan aljanu su goma da siffar mutane sun bayyana, suna zuwa sai suka zube suka yi gaisuwa. Nan da nan ya ba su umurnin gina lambu irin wanda ake ya dauka, a kawata shi da duk kayan alatu, sannan kuma a gina daki guda daya wanda 'yan matan za su rika shiga in za a kai su lambun da kuma in za a dauko su. Sannan kuma lallai dakin ya kasance ma'abucin fitilu masu haske a bayansa don ya rika haska musu wasanninsu.
Yana so kuma a kammala wannan aiki ne a cikin kwanaki uku.
Kartin aljanun nan suka ce an gama sannan suka bace.
Wata rana suna zaune suna tsotson tatsattsun kayan marmari, shi kuma Sarkin aljanu yana kashingide a kan kilishi, wato kwana uku ke nan da ba da wancan umurni, sai suka ji wata irin rugumniya, aljanun nan sun dawo. Suka zo suka fadi suka yi gaisuwa tare da

cewa ga lambun nan ya shiryu. Sarkin aljanu ya cewa
'yan mata su leka ga lambunsu can an gama, suka tashi tare da shi suka je taga suna lekawa, sai ga lambu an ajiye shi a gefe shirim, kuma abin mamaki shi ne babu abin da babu irin na lambu a ciki.
Shi wannan lambu dai da bakin karfe aka yi shi, daga baya kuma aka cika shi da wani irin rairavi mai launi iri-iri. Itatuwa kuwa har da irin wadanda ba su sani ba akwai. Kai daga gani ka san aikin aljan sai dai kallo kawai.
Suka yi ta mamaki don ba su taba gain haka ba.
Sarkin aljanu ya yi tambaya, "Ko wannan lambun ya
'vi?»
Nan da nan suka ce, "Kwarai kuwa ya yi, fiye da yadda muke zaton zai iva yiwuwa."
Ya umurci alianu su dauki lambu tare da yarinya Nur a ciki don ta nuna musu inda take so a ajiye. Kafin kiftawa suka vi sama har cikin sararin samaniya, suka iso wannan daji, suka yi ta zagayawa kasa-kasa har sai da ta hango wadannan dakuna biyu sannan ta ce a ajiye mata lambun kusa da dakunan, amma koramar ta raba tsakani."
Shaihin malami Ibrahim ya ci gaba da yi wa saurayi
Idrisu bayani cewa, "Ina daga nan ciki sai na ji diririm, in leka sai ga lambu shirim, na komo cikin dakina cike

da ta ajjubi mara misaltuwa.
Bayan an sauke lambu kuma ya zauna sosai, sai yarinya ta shige cikin dakin nan na tsakiyar lambu ta umurci cewa a dauke ta a cikin sa a maida ta wurin sauran 'yan'uwanta, can inda Sarkin aljanu ya ke.
Da komawarsu sai Sarkin aljanu ya umurci aljanu uku da umurnin cewa a kullum dare su rika zuwa suna daukar 'van matan nan suna kai su, in sun gama wasanninsu sun shiga cikin daki a dauko su a dawo da su. Kuma kamar yadda 'yan matan suka bukata, Sarki ya ba da umurnin cewa duk in an kai su, to aljanun su rika nisantar su sai kamar bayan sa'o'i biyu sannan su dawo inda suke, don su rika samun cikakkiyar damar sakewa da walawa ba tare da sa ido ba, a matsayin su na
'yan mata.
Haka aka ci gaba da yi, a kullum in dare ya fara shiga sai aljanun nan su zo su kawo su wannan lambu. Su yi wasanni da kade-kadensu, har sai in sun kusa kammalawa sai 'yata Nur ta zo ta gaishe ni.
Ka ji dalilin wannan lambu ke nan, wannan yarinya da kake gani tauraruwar cikin su kuma ita ce Nur din, wato 'yata. Har yanzu suna nan a wancan gida da aljanin nan ya gina, kuma duk wannan shirye-shirye da muke yi har yanzu Sarkin aljanu bai sani ba."
Dattijo ya dauki ruwa ya kurba sannan ya ci gaba da

cewa, "Muna nan muna ta fatan Allah Ya kawo wani wanda zai iya fuskantar wanna kalubale na ceto
'ya'yan jama'a, kwatsam sai ga ka, kuma wani abin sha'awa da burgewa na gan ka tare da wannan shahararren doki, kuma ga ka saurayi kakkarfa kuma kyakkyawa, sannan kuma ga shi kana da son yin ilmi.
Shi ya sa na hakikancewa kaina cewa kai ne za ka karya wannan aljani Barawon 'ya' yan mutane.
Da farko da ka zo idan ba ka manta ba na dan jarraba ka, na ce kada ka yarda ka makara, to dalili shi ne ba a son namiji ya cika barci da yawa. Haka nan kuma lokacin da kake jin wakokin 'yan matan nan, in ka tashi za ka tsallaka zuwa cikin wancan lambu amma ka ji haniniyar dokinka hankalinka kan dawo maka ka juyo, to da a ce ka biye wa zuciyarka ka tsallaka ba ka ji shawararsa ba, to da kuwa kai da shi dokin naka kun rabu ke nan, amma sai ka yi sa'a ka hankalta da ishararsa.
Ya kai dana, yaki kuma da nake koya maka don ka san hiloli ne da dabaru irin na yakin tare da kuma juriya, kuma ga shi kana da doki wanda babu mai irin sa, kuma ga shi za ka sami takobi da mashi da kuma darduma, duk kayayyakin ban mamaki.
Ya kai Idrisu, yau shekara daya ke nan kana zaune a wurina. A nan ka karu da yawa na daga abin da Allah

Ya ba ni, ka yi ilmi mai yawa da sanin hikimomin rayuwa. Ina

1
2

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login