Showing 1 words to 2452 words out of 2452 words

Chapter 1 - YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA PART 2

17 Oct 2024

936

Yarinya nur da sarkin Aljanu sham’una part2


karatu."Ya yi wa dattijo godiya, ya nufi inda daki ya ke, ya shiga ya tarar akwai gado da kujera da komai na more rayuwa fiye ma da yadda ya ke zato. Ya zauna bakin gado yana ta tunanin maganganun da suka yi, musamman ruwa da zai rika zubawa a cikin rijiya maimakon ita rijiya a debi ruwa daga cikin ta, amma an ce kada ya tambaya. Kuma ga irin wannan lambu mai ban mamaki. Sannan kuma babu wani mutum ko daya a wannan wuri sai dai wanna dattijo, duk dai an ce kada ya tambaya.
Tun da Asubahin fari ya dauki tulu ya fara debo ruwa yana zubawa a cikin rijiya kamar yadda aka umurce shi, har sai da ya zuba tulu goma daidai.
Bayan ya kammala sai ya je wurin dokinsa Jagora ya shafa shi, shi kuma dokin ya yi haniniya mai kamar gaisuwa kafin ya juya ya shige cikin daji kiwo abin sa.
Shi kuma Idrisu sai ya nufi dakin malam ya yi sallama aka amsa tare da umurnin cewa ya shiga. Ya gai da malam cikin girmamawa shi kuma ya amsa cikin murmushi irin na kauna.
Idrisu ya ce, "Na zuba ruwan." Dattijo ya amsa, "Ai na sani."
Idrisu ya yi mamakin yadda aka yi ya sani alhali kuwa ba ya fito ba ne, sai dai kuma babu dama ya yi tambaya.
Suna gama karya kumallo sai Shehi Ibrahim ya ce,
Ya kai Idrisu, kafin mu fara, ina so ka ba ni dalilin da ya sa kake so ka sami ilmi ko ta halin Kaka, ko kuma a takaice in ce ba ni labarin muhimmancin ilmi." Sai Idrisu ya ce, "Ya kai wannan malami mai daraja, ni dai yaro ne, saboda haka na san cewa lallai kadan ne kawai abin da na sani game da muhimmanci da amfanin ilmi.
Ilmi yana fitar da mutum daga duhu, ya yi masa jagora zuwa ga haske, kuma in kana da ilmi, to kana da mutunci, kuma komai ikonka, dukiyarka da kwarjininka in ba ka da shi, to da kai da jaki bambancinku halitta, kawai kai mutum ne shi kuma sunansa jaki.
Ilmi bargo ne da duk wanda ya lulluba da shi ba ya tozarta. Sai ka ga mutum dan talakawa amma matukar ya sami ilmi sai ya zama babban mutum mutane suna ba shi girma har ma ya iya rike mukaman da mai unguwarsu bai taba mafarki ba.
Ilmi shine babban makamin da ko lahira za ka tafi, to tare za ku, kana tafiya yana yi wa rayuwarka jagora, kuma duk inda za ka shiga, to kana gani radau don ko idanunka ba sa budewa, to kai ba makaho ba ne, wato ko idanunka a rufe suke matukar dai kana da ilmi, to ka fi jahili wanda idanunsa ke bude sau dari. Wannan wani abu ke nan daga cikin abin da na sani na muhimmancin ilmi."
To, da Shaihi Ibrahim ya ji zancen sauravi Idrisu sai
ya ce, "Lallai ka ambaci dan kadan daga cikin muhimmancin ilmi. Amma duk da haka ka yi kokari, kuma a hankali za ka yi ta kara gani da fahimtar muhimmancin na ilmi.
Yanzu sai ka kara da sanin cewa shi ilmi takobin yanke jahilci ne. In kana son gain bakin cikin duniya, to ka zauna da jahilci, kuma yadda ilmi ya ke jagora, to shi ma jahilci babban jagora ne, amma fa ta bangaren halaka.
Jahilci ne rawanin girman kai. Jahili ne kan soki kansa da kansa amma ko kadan bai sani ba. A takaice dai dana, in maganar jahilci ce sai mu yi kwana da kwanaki muna yi. Yanzu sai mu ci gaba da karatu." Lokacin Sallah ya yi suka tashi suka gabatar, suka ci abinci sannan suka sake komawa fagen karatu. In banda Sallar La'asar ba su tsaya ba sai gab da Magriba lokacin da malamin ya ba dalibinsa damar yin tambayoyi a game da karatun da suka yi a ranar, daga nan suka yi Sallah suka ci abinci, kafin su kammala Lokacin Sallar Isha'i ya shiga. Suka gabatar da ita daga nan sai dattijo ya ce, "Mun kammala na yau, yanzu sai ka hanzarta ka koma dakinka, kuma kada ka kuskura ka sake zuwa wannan daki nawa sai gobe da safe.
Kuma kamar yadda nake jaddada maka komai ka gani kada ka kuskura ka yi mini tambaya."
Idrisu ya yi sallama ya tashi.
Yana shiga dakinsa sai ya tsunduma cikin tunani

tare da mamakin irin abubuwan da ya ke gani daga wannan dattijo, musamman irin yadda abinci ke zuwa masa. Ga shi babu wani mutum a kusa da shi, ballantana a ce shi ke kawowa, sai dai kuma an ce banda tambaya.
Ya dai Kare tunane-tunanensa ya shiga bitar karatun da ya dauko. Yana cikin nazarinsa sai ya j¡ dattijo a bakin dakinsa yana kira, nan da nan ya fita cikin gaggawa.
Dattijo ya ce, "Na manta in shaida maka cewa lallai ka lura da dokinka, muddin ka ji ya yi haniniya, to babu shakka yana yi maka nuni da wani abu ne, saboda haka sai ka kula."
Idrisu ya ce, "Na gode malam, kuma in Allah Ya so zan kula."
Dattijo ya koma dakinsa, ya bar Idrisu cikin tunani,
"To ni ko ina cikin garin aljanu ne? An ce kada in ji tambaya, kuma ga abinci mai dumi muna ci ban ga mai dafawa ba, shi ma an ce kada in tambaya, dokina kuma in ya yi haniniya wai yana yi mini ishara ne, shi ma babu halin tambaya, kuma komai na gani a cikin dare kada in yi tambaya.
*n A gaskiya ba don tsohon nan Musulmi ba ne, to
• lallai da na gudu daga wannan wuri, amma na tabbata dai ba zai yaudare ni ba daga dukkan alamu dai... to, zan zauna in ci gaba da bin umurninsa."
• Ya shige ya haye gado ya yi kwanciyarsa.

Can cikin dare bayan barci mai nauyi ya dauke shi,
kamar a cikin mafarki sai ya ji ana rera waka, kuma
lallai muryar ta mace ce mai dadin gaske kuwa, kuma tun da ya ke a rayuwarsa, bai taba jin waka da kidan molo mai dadi irin wannan ba.
Ya farka a firgice, ya bude idanunsa amma sai ya ci
gaba da jin wannan kida da waka wanda hakan ya
tabbatar masa da cewa lallai da gaske ne ba mafarki ba.
Hasali ma ba molo kadai ba ne, akwai wasu sauran
kayan kade-kaden dake tashi a hankali.
Ya tashi ya leka waje daga cikin dakinsa, ai kawai sai
ya ga lambun nan na kusa da su ya dauki wani irin
haske kau da wasu irin fitilu masu launi iri-iri gwanin
ban sha'awa, kuma ga wasu 'yan mata nan su goma
sha hudu, sun yi ado iri daya, ta cikon sha biyar din ce kayanta daban a cikin su, kuma ita ce ke ba da waka
suna amsawa.
Ita wannan yarinya duk ta fi sauran kyau, kamar dai
yadda ake iya hango wata a cikin taurari, duk inda
Sarauniyar kyau ta kai, to ba ta kai ta ba, kuma duk
inda wani mai gani ya ke ganin kyau bai taba ganin
mai kyanta ba, komai rashin begenka, idan ka gan ta, to dole sai ta dama maka tunani. Sa'arka dai kawai ba ka gan ta din ba.
Idan ta sako waka sauran suka amsa, sai ya ji kamar
zai narke saboda tsananin dadi.
Idrisu ya tabbatar da cewa ko mafarkinsa bai taba

nuna masa wata yarinya da ta yi kusa da ita a fagen kyau da cikar halittar jiki ba. Abin da ya fito daga cikin bakinsa shi ne, "Tsarki ya tabbatar wa Ubangijin talikai. Ni na tabbata wannan yarinya
Sarauniyar kyau ce ta aljanu."
In yarinyar ta sake ba da wata waka sai Idrisu ya ji kamar ya tashi ya tsallake 'yar koramar da ke tsakanin su ya isa wurinta, amma sai wata zuciya ta tsawatar masa ya fasa. Can dai da ta rero wata waka wadda dadinta ke ratsa sasannin kwakwalwa ai Idrisu bai san lokacin da ya tashi ya yi waje ya nufi wurinsu ba, yana kokarin duba ta gefen da zai tsallaka koramar ke nan sai kawai ya ji Jagora ya yi haniniya, ai nan take sai hankalinsa ya dawo jikinsa ya tuna cewa haniniyar dokinsa ishara ce a gare shi. Ya fahimci lallai zuwa wurin wadannan 'yan mata ba alheri ba ne a gare shi, sai ya dawo ya shige daki yana mai ci gaba da sauraren wakokinsu.
Lokacin da Asubahi ta kusa sai ya ji shiru, ya tashi ya leka amma sai ya ga babu kowa, duk 'yan matan sun bace tare da dukkan fitilun, sai dai lambun kawai.
Mamaki ya sake rufe shi, "Da ma na san wadannan
'van matan aljanu ne." Kwanciyarsa ke da wuya sai barci mai karfin gaske ya dauke shi har sai da dokinsa ya zo ya yi haniniya sau biyu. Nan da nan ya farka. Ya tashi ya yi sallah ya roki Allah nasara da kariya, kuma cikin gaggawa ya dauki tulu ya tafi yana debo ruwa

yana zubawa a rijiya har sai da ya zuba tulu goma.
Bayan ya kammala, sai ya je wurin dokinsa yana shafa shi, kuma ya fahimci ba don dokin ba, to lallai da ya makara, alhali kuwa Shehi ya gargade shi a kan haka.
Gari na wayewa tangaran sai ya zauna a karkashin wata bishiya yana tunanin abin da ya gani daren jiya, irin wakokin 'yan matan nan, ya kuma tsunduma cikin begen kyan yarinyar nan da dadin muryarta da kuma irin kwarjininta, ya dai tabbatar wa kansa cewa lallai wadannan 'yan matan aljanu ne. Babban abin bakin cikin ma a wurinsa shine irin yadda bai sami damar yin magana da ita ba ballantana ya sami labarinta, shi kuma wanna dattijo babu damar a ji daga gare shi, don ya ce babu tambaya.
Wannan tunani shi ne a tsakanin wannan lokaci ya dabaibaye zuciyar saurayi Idrisu dan Hamidu, wani lokaci kuma sai ya rika tunanin iyaye da 'yan'uwansa, ko wane irin hali suke ciki? Ya tuna shi dai ga shi ya rabu da su ya shigo tsakiyar daji, ko a cikin mutane ya ke ko kuwa aljanu? Shi dai ba ya iya tantancewa.
Da gari ya waye sosai sai ya yanke tunaninsa, ya nufi dakin malam ya tarar da shi zaune rike da littafi a hannu. Idrisu ya gai da shi cikin girmamawa, malam ya amsa da murmushi, sannan ya gabatar masa da abinci mai alfarma da duminsa yana kanshi, suka ci suka koshi, suka dukufa cikin karatu are da sauran

al'amuransu kamar dai jiya. Dattijo bai tambayi Idrisu abin da ya faru daren jiya ba, shi kuma Idrisu bai ce masa komai ba. Ya kare karatu da tambayoyinsa a kan darussan wanna ranar sannan ya yi sallama ya nufi dakinsa, bayan ya kewaya ta wurin dokinsa don duba halin da ya ke ciki.
Kammala nazari da kwanciya da barcinsa ke da wuya, sai ya sake jin kida da wakoki kamar daren jiya, ai sai kawai ya yi waje, kuma ya tarar da lambun nan an Rawata shi fiye da jiya, yarinyar nan kuwa babu wanda zai iya bayyana hakikanin kyanta, don babu shakka Allah Ya yi ikonSa a wurin. 'T'sunduma cikin kallonta ya sa Idrisu neman fita daga hayyacinsa, yana jin dadin wakokinta, musamman yau da ya ke da shantu aka zo ana kadawa. Bege ya yi ta karuwa cikin zuciyarsa a kan ta alhalin bai san mutum ce ko aljana ba. Shi dai ya tabbatar da cewa ya kamu da son ta sai dai kuma bai san vadda zai Bullo wa lamarin ba, kowace waka yarinyar nan ta rero, sai ya ji kamar a wata duniyar ya ke.
Bai san lokacin da ya nufi lambun ba, ya daga
Rafarsa ke nan zai sa cikin 'var koramar da ke tsakaninsu sai kamar a cikin mafarki ya ji haniniyar dokinsa, ai nan take kamar wanda ya farka daga barci firgigi ya tsaya, ya dawo da baya ya koma cikin dakinsa, a lokacin Asubahi ta kusa. Yana shiga sai ya ji shiru, ya yi sauri ya leko amma sai ya tarar babu

yarinyar, babu fitilun duk sun Bace sai dai lambun nan a yadda ya ke a da.
Saurayi Idrisu ya shiga magana da kansa a kan abin da ya dauka tunani ya ke yi a cikin zuci, "To ni dai wannan yarinya ko mutum ce ko aliana in Allah Ya yarda sai na aure ta, komai wahala komai dadi, ko rai ko mutuwa ni duk daya ne a wurina, sai dai in ita yarinyar da kanta ta ce ba ta so na... amma kuwa idan ta ce ba ta so na... hmm, to ai gara in mutu kawai in huta da rayuwa cikin tunanin ta tsawon rai.
Af, to ta yaya zan gan ta har ma in ji ko tana so na din? Shike nan in dai har zan zauna a wannan daji har karshen raina kuma wanna aljana tana fitowa duk dare ina gani tare da jin wakarta, to ni na yi alkawari a nan rayuwata za ta kare."
Tun daga wannan lokaci bai sake barci ba, yana ta tunani daban-daban har zuwa lokacin da gari ya yi sha zai waye, nan da nan ya tashi ya yi Sallah wadda a ciki ya roki Allah bukatunsa. Bukatar farko da ya gabatar a kan ilmin da ya fito nema ne, sai kuma bukata ta bivu wadda yanayi ya sa shi, wato samun wanna kyakkyawar yarinya da ya ke gani cikin dare, wadda kuma bai san labarinta ba.
Ya dauki tulu ya rika debo ruwa yana zubawa a cikin rijiya har sai da ya yi sawu goma. Ya je wurin dokinsa yana goggoge masa jikinsa yana tunani a cikin ransa yana cewa,
" Lallai komai yana da dalili, kuma duk

wanda ya yi biyayya ga malaminsa, to babu shakka ba zai yi a banza ba." Yana mai kara mamakin abin da ke wannan wuri.
Gari ya waye sosai, rana ta bayyana, ya nufi dakin malam, suka gaisa tare da cin abinci kamar yadda suka saba a kullum.
Malam ne ya fara magana, "Ya kai Idrisu, yau ranar hutu ce ba ranar karatu ba, saboda haka idan hantsi ya yi sosai, sai ka zo da dokinka mu tafi ga fili can zan fara koya maka dabarun yaki iri-iri."
Idrisu yace, "To."
Idrisu ya shiga tunani a cikin zuciyarsa, "Kai wannan dattijo vana da ban mamaki, ina wannan tsoho mai yawan shekaru zai iya yin wani abu game da yaki bayan duk ya kwararrabe?"
Dagawar hantsi ke da wuya sai ya je ya janyo dokinsa, sannan ya shiga cikin dakin malam ya sanar da shi ceva shi ya riga ya shirya. Nan da nan dattijo ya yi damara kamar wani shahararren mayaki ya fito, sai
Idrisu ya cewa kansa,
"Lallai wannan mutum da
gaske ya ke."
Idrisu ya bi shi har suka isa katon filin nan, dattijo ya sa takobi ya saro wani dogon itace, ya sassake shi ya yi tsini kamar mashi. Daga nan fa ya fara koya wa Idrisu yadda ake dabaru da hilolin yaki. Suka yi ta yi har rana ta take, jikin saurayi ya yi likis sannan suka koma dakunansu suka yi wanka. Shi Idrisu yana cikin

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login