Showing 1 words to 2258 words out of 2258 words
HAJI Hamidu dan Usman mutum ne da Allah Ya yi wa baiwar ilmi da aiki da shi, ga hankali da hakuri da rikon amana da kuma rashin girman kai.
Daidai gwargwado kuma yana cikin rufin asiri.
Babbar dacewa ita ce irin yadda Allah Ya albarkace shi da mace ta kwarai, wadda samun irin ta sai an tona ta bangaren sanin ya kamata da hakuri da kyau da cikar halitta. Sunanta Ramlah.
Ma'auratan suna da 'ya'ya maza da mata, amma manyan da suka isa misali su uku ne. Babban sunansa Idrisu, mai bi masa kuma Abubakar wanda suke kira Habu, sannan sai Yahaya. Dukkan su sun sami ilmi daidai gwargwado.
Wani abin sha'awa shine irin yadda wadannan samari ba su bar komai na kyawawan halaye da siffofin iyayensu ba, hakan ya sa halayyarsu ta zama abar misali kuma kyan halittarsu ya zama abin tsegumi a gari.
Fara jin dadi da kuma taka wani mataki na ilmi ne
suka sa wadannan matasa a rayuwarsu ba abin da suka fi bukata da kauna flye da tsunduma cikin duniya don karo sani.
A karshe dai suka yanke shawarar tafiya din. Kuma saboda sanin muhimmancin ilmi da kuma daidai gwargwado aminta ko yarda da tarbiyyar 'ya'yansu suka sa ko kadan iyayensu ba su ki yarda da wannan bukata ta tafiya ba, har ma a karshe mahaifinsu ya
Kara da yi musu gargadin cewa,
"Ya ku 'ya'yana, babban abin da nake so in tunatar da ku kuma in gargade ku a kai shine, duk inda kuka tsinci kanku, to ku rike amana, kuma ku rika tuna sanadin fitarku daga gida, wato ilmi; jagoran ravuwa."
Yara suka ce in Allah Ya yarda ba za su taba mantawa ba.
A daya bangaren kuma akwai Bashari, shi ma wani yaro ne mai hankali, makwabci kuma abokin wadannan yara. Duk shirye-shiryen da ake yi na tafiya da shi ake yi, don irin shakuwar da ke tsakanin su. Shi ma ya nemi yardar nasa iyayen kuma sun amince.
Su hudu ke nan.
Bayan adduo'in fatan alheri da sa albarka irin wadanda iyaye kan yi wa 'ya'yansu, wadannan matasa suka yi sallama da jama'arsu suka bi hanya.
Kwana arba'in ba biyu suna tafiya, sai suka isa wata
mararraba wadda hanyoyin da ke jikinta suka rabu hudu, Gabas da Yamma, Kudu da Area. A nan suka tsaya don shawartawa.
Habu ya ce, "Ina gain ya kamata daga nan sai mu rabu, kowa ya bi tasa hanyar, don in mun tuna daga cikin maganar mahaifinmu ta kwanakin baya, ya ce za mu fi kwazo in har ba ma ganin juna."
Ba tare da gardama ba suka yi sallama, suka rabu kowanne zuciyarsa cikin halin raurawa.
Babbansu Idrisu ya fuskanci Gabas, shi kuma Habu ya doshi Area, Bashari ya tsinkayi Kudu, Yahaya kuwa Yamma ya nufa, kowa ya mika.
IDRISU ya ci gaba da tafiya kwana da kwanaki ba tare da sanin inda ya ke nufa ba, ba dare ba rana, shi dai nutsawa ya ke yi. Bugun ruwan sama kuwa har ya zame masa jiki.
Amma maimakon ya fara gain alamar gari ko kauye, kullum sai kungurmin daji ya ke sake kutsawa.
Ya wuce wannan korama, ya ratsa ta wancan tafki, ya sakala ta tsakanin wadancan duwatsu, namun daji iri-iri ya yi ta haduwa da su, wadanda ya sani ko kuma ya taba jin labari da wadanda ko tunanin irinsu ma bai taba yi ba, manya da kanana. Ba ya jin kukan komai sai zakoki da damisoshi da giwaye da sauransu, Allah dai Ya yi ta kiyaye shi. Wasu koke-koken ma sam bai
san ko dabbobi ko mene ne ke yin su ba, shi dai ya ci gaba da tafiya bai san inda ya ke nufa ba.
Bayan guzurin da ya riko ya Kare sai 'ya'yan itatuwa suka koma su kadai ne abincinsa, har dai ya zo cikin wani kungurmin daji da babu alamar ko dan Adam ya taba wucewa ta wurin ma. Kwatsam a cikin dokar daji sai ya rika jiyo haniniya, ya nufi inda sautin ke fitowa yana lellekawa har dai abin da ya ke zato ya tabbata daidai, wato doki ne. Shi dai Idrisu bai taba ganin doki mai kyau irinsa ba.
Yanzu kam a cikin zuciyarsa ya tabbata cewa zai sami taimako ko kuma labari, kasancewar akwai alamar ya iso inda mutane suke.
Ya duba ko ina ko zai ga mai dokin amma abin mamaki babu alama ko daya. Ya kara matsawa kusa, sai ya tarar ashe saiwar wata irin itaciya mai yado da sarkakiya a kasa ce ta rike wa dokin Rafa, amma ya kasa cirewa da kansa. Gain Idrisu kusa da shi sai ya yi ta harbe-harbe, shi kuma yana ta lallabar sa yana matsawa kusa a hankali. Ya je ya samo masa ciyawa mai kyau ya mika masa don nuna cewa ba shi da mugun nufi gare shi. A haka dai har ya kai ga shafa shi.
Idrisu ya zaro wuka daga kuibinsa ya yayyanke saiwar, ya janyo kafar a hankali, wadda ya tarar ta dan yi rauni, kuma ba tare da bata lokaci ba ya yagi rigar jikinsa ya daure masa. Doki dai ya fahimci taimakon sa ake yi, saboda haka sai ya saki jiki. Idrisu ya hada
wata 'yar bukka a wanna wuri ya yi kwanaki yana jinyar doki har Allah Ya sa ya warke garau.
Shi ke nan ya sami abin hawa. Kuma yanzu ba ya samun wata wahala wajen hawa da sarrafa shi, kuma duk abin da ya umurce shi, to babu gardama ya ke aikatawa.
Shi wanna doki da wahala duk yadda mutum ya taba gain doki a ce ya ga mai kyansa, kosasshe ne, fari, mai kwarjini. Dole ne idan ka yi sa'ar gain sa ka dimauta da son sa.
Ba da dadewa ba Idrisu ya fara tunanin irin sunan da ya kamata ya rada wa wannan ingarman doki nasa.
Can yana cikin tunani sai kwatsam ya tuna da wata kalma da mahaifinsu ya yi amfani da ita a lokacin da za su bar gida, wato nunin da ya yi musu cewa ilmi shi ne jagoran rayuwa, saboda haka sai ya shafa jikin doki ya ce masa,'
"Sunanka Jagora." Nan take dokin ya yi
wata irin haniniva ta ¡in dadi kamar ya fahimci abin da ake nufi.
Bayan dukkan su sun sami isasshen hutu sai Idrisu ya cewa Jagora, "Ya kamata mu bar wannan wuri mu nufi inda Allah Ya kai mu." Yau da kullum ta sa ya dauki wata dabi'a ta yin magana da wannan doki nasa kamar yana yi da mutum dan'uwansa.
Haka nan babu sirdi ya hau Jagora ya sake tsunduma cikin daji, ya sa masa idanu sai inda ya kai shi, kuma duk inda ya nufa ba ya kwabon sa.
Bai ankara ba sai ga su a bakin wani lambu cikin dokar daji, wanda tun da ya ke a duniya, bai taba mafarki ko in labarin mai ban sha'awar sa ba, ga furanni masu kanshi da launuka iri-iri, korama tana kaiwa tana kawowa gwanin ban sha'awa, ga 'ya'yan itatuwa nan iri-iri sai tsuntsaye suke ta wakoki da mabambantan sautuka masu natsar da zuciya. Kai a takaice dai irin wannan lambu da zarar ka gan shi, to tunanin da zai fara biyo baya shi ne, "Allah ba mu Alianna."
Sai dai kuma lambun yana da wani abin mamaki.
Shi kansa kungurmin dajin dai ba shi da alamar rairayi ko kadan a cikin sa, duk itatuwa ne da sarkakiya da sunkuru da duwatsu da koramu, amma sai ga shi lambun ya fita daban. Ga yashi nan fari fat har da wasu 'yan dunkulallun duwatsu na karau masu ba da haske kamar fitilu a cikin sa. Daga gani ka san ba aikin mutum ba ne sai dai aljan.
A can daga gefen lambun kuma was dakuna ne ake iya hangowa, guda biyu masu kyau; babba da karami, su ma suna da launuka iri-iri gwanin ban sha'awa. A tsakanin su da lambun akwai wata korama wadda ruwa ke gudana gwanin ban sha'awa. A cikin ruwan ga kifaye nan masu kyau iri-iri da mabambantan launuka karara ana kallon su. Da Idrisu ya tsallake koramar sai ya saki Jagora karkashin inuwar itace, shi kuma ya nufi inda katon dakin nan
ya ke. Ya yi sallama, "Assalamu alaikum." Abin mamaki sai ya ji an amsa,
«Wa'alaikumus salamu,
shigo."
Shigarsa sai ya ga ashe wannan daki kato ne kamar wani dan karamin gida. Wani dattijo ne a ciki mai yawan shekaru, ga dogon gemu da saje da gashi fari fat mai kyau. Da gain sa ka san yana da wata daraja da Allah Ya vi masa saboda tsananin kwarjinin fuskarsa.
Yana zaune a kan wani farin buzun rago zagaye da litattafan karatu iri-iri, masu tarin yawa.
Idrisu ya karasa kusa da shi ya gai da shi cikin girmamawa da tausasa murya. Dattijo ya kalle shi wanda kuma a cikin kallon ya nazarci cewa yaro ne saurayi kyakkyawa mai alamar natsuwa. Ya ba shi damar zama, sannan ya ce, "Ya kai wannan saurayi mene ne sunanka? Daga ina ka fito? Me kake nema?
Kuma ina za ka?"
Cikin natsuwa ya mayar da amsa,'
"Sunana Idrisu
dan Hamidu, na fito daga garinmu Dutsen-ruga ne don neman ilmi, tafiya kawai nake ba tare da sanin inda nake fuskanta ba har Allah Ya kawo ni nan."
Bayan ya gama shaida wa dattijo labarinsa sai shi ma ya tambaya cewa, "Ya kai wannan dattio mai daraja, kai kuma mene ne naka labarin? Mene ne labarin kasancewarka a wannan kungurmin daji kai kadai? Kuma mene ne labarin wancan lambu mai ban
mamaki?"
Dattijo ya ce, "Ya kai Idrisu ina so ka sani, ni sunana Ibrahim dan Yahaya, kuma labarin kasancewa ta a nan da kuma labarin lambu kada ka sake tambaya ta.
Ina so in shaida maka wata magana, in ka yarda, to zan kovar da kai abin da ka fito nema, wato ilmi, in kuma ba ka amince ba, to sai ka ci gaba da tafiyarka." Sai Idrisu ya ce masa, "Allah gafarta malam ai sai ka shaida mini, in abin da zan iya yarda da shine in yarda, in kuma ba wanda zan iva ba ne in taf." Dattijo Ibrahim ya ce, "Ya kai Idrisu, mutane suma lissafta ni daga cikin mashahuran malaman wannan zamani don irin dumbin ilmin da Allah Ya yi mini baiwa da shi."
Ya ci gaba da bayani, "Ya kai dan Hamidu, na dade a cikin wannan kungurmin daji, sai dai kuma labarina a cikin sa da kuma labarin shi kansa wurin yana da tsawo, kuma ba zai yiwu ka ji shi a yanzu ba, sai dai ko watakila nan gaba.
Sharadi na farko da zan ba ka shi ne, daga yanzu komai ka gani kada ka tambaya. Abu na biyu kuma shi ne, lokacin da za ka shigo ka wuce ta wurin wata rijiya ko? To abin da nake so shine a kullum ka je ka debo ruwa daga cikin dan rafin can kana zubawa a cikinta har na tsawon yawan kwanakin shekara daya babu fashi, kuma kada ka manta na ce maka babu tambaya, kai dai aikata abin da na ce kawai. Ga daki
can ka rika kwana a ciki, kuma kada ka kuskura a tsawon kwanakin shekarar nan ka makara har in riga ka fitowa. Sauran abubuwan da za ka rika gani in dare ya yi kuma, sai ka san yadda za ka fitar da kanka.
In har ka yarda da wadannan sharudda, to zan karantar da kai har na tsawon shekara daya. Kar ka damu da maganar abinci, wannan akwai shi.
Na hango tahowarka daga nesa a kan zakakurin dokin nan wanda daga gain yadda ya ke takawa ma kawai duk mai lura zai iya gane cewa yana da wata baiwa ta musamman, wato ba gama-garin doki ba ne, amma sai ga shi kai kana sarrafa shi yadda ka ga dama, ya zama karkashin ikonka. Shi yasa nake zaton akwai nasara a cikin lamarinka. Ina jaddada maka cewa lallai ka rike shi da mutunci don zai taimake ka taimako mai yawa."
Dattijo ya ci gaba da yi wa Idrisu bayani, "Ya kai dana babu shakka za ka yi gwagwarmaya da yawa a cikin tafiyarka."
To, da Idrisu dan Hamidu ya ji wannan zance na dattijo sai ya ce, "Ya kai wannan dattijo mai daraja, na ji abubuwan da ka ce, kuma na yarda na amince, sai dai kuma na ba ka amana, ina fata kada ka yaudare ni.
Kuma ga shi ka ce kada in yi tambaya, ba don haka ba, ina da tambayoyi masu yawa da nake matukar bukatar amsoshinsu daga gare ka."
Dattijo ya ce, "A'a kada ka yi, da sannu za ka zo ka
san komai."
Idrisu ya nemi karin bayani, "Idan muna karatu har abin da ya shige mini duhu ban gane ba kada in tambaya?"
Sai dattijo ya ba shi amsa cewa, "A'a banda in an 20 fagen karatu, ai karatu babu tambaya ya zama labari kenan."
Dattijo kuma Shaihin malami Ibrahim ya kara da cewa Idrisu, "Ya kai wannan kyakkyawan saurayi, in dai karatu ka zo nema, to kuwa ka samu in dai har za ka tsare ka'idoii. Bayan ka kammala karatu a wurina na shekara daya, za ka je ka ci gaba da karatu a wurin wasu. Amma kafin ka sadu da su ¡an aiki ne."
Yana matukar bukatar sanin abin da dattijon ke nufi, amma kuma ya tuna cewa babu tambaya, sai ya yi shiru.
Sai ya cewa dattijo, "Babu shakka zan yi iyakacin kokarina in kiyaye dokokin da ka sa mini, in Allah Ya yarda."
Cikin annashuwa dattijo ya ce, "To sai ka je ga dakin can ka shiga ka gani, a ciki za ka rika kwana, kuma ga wata 'yar Karamar rumfa can a ikin dakin ka rika daure dokinka. Kuma shi wannan daki akwai komai da dan Adam zai bukata. In Allah Ya kai mu gobe, sai ka fara debo ruwa daga rafin kana zubawa a cikin rijiyar. Kada ka manta a kullum za ka zuba tulu goma ne, kuma kana kammalawa sai ka zo mu fara