Showing 1 words to 3000 words out of 8250 words

Chapter 1 - MATAR SADIK- book2 HAUSA NOVEL

02 Sep 2024

2121

🧕🧕MATAR SADIK🧕🧕



MALLAKAR
ZAINAB DODO




STORY AND WRITING
BY
ZAINAB DODO






Free book 📖

09046495943


Kuna ina fans ku matso kusa dan jin yarda wannan littafin zai kasance na MATAR SADIK



_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 1️⃣8️⃣➡️1️⃣9️⃣

Washe gari
Sadik da yaje masallaci bai dawo ba sai da gari ya d'an fara haske sannan ya shigo gidan, d'akin khadija ya shiga, bata falo dan haka ya wuce ciki, kwance ya ganta saman gado tana sanye da wata rigar bacci red colour, rabin cinyoyin ta duk a fili, rigar kuma mai santsi ce duk ta kwanta a jikin ta, bai san lokacin da ya isa gadon ba har ya haye, hannun sa ya d'aura saman mazaunanta tare da shafawa a hankali


Cikin bacci taji ana shafata, ahankali ta bud'e idanuwanta dake cike da bacci, dan jiya bata samu wani baccin kirki ba, juyowa tayi tare da sakar masa murmushi Shima ya mayar mata, kallan idanuwan ta yake ganin sun d'an kumbura kana yace" Meya hanaki bacci? "Bakomai " gayamin dai" ya fad'a yana shafa jikin ta "Dagaske baccin ne yak'i zuwa min "Uhmmmm kodai kodai kinyi missing d'in, ya fad'a tare da ida maganar a kunnen ta, dariya tasa tare da fad'in"Bawani "


hannun sa yake k'ok'arin turawa cikin rigar tayi saurin rik'ewa tare da fad'in " Gafa matar ka can a d'aki" Ke kuma fa? " To ai kaga ba girki na bane please ka daina bana son mu shiga hak'k'inta " To wani abun nace zanyi? " Uhmmm bacci zanyi" Sauka yayi saman gadon ya nufi hanyar fita, dan maganar da ta masa ma ta 'bata masa rai,

da kallo tabi bayansa har ya fita, ta k'ara gyara kwanciyarta taci gaba da bacci



Yana fita daga d'akin yayi d'akin balkisu, itama tana nan kwance tana sharar bacci, duk da ita ce da girki amman aikin uwar komai batayi ba tayi kwanciyarta, falo ya dawo ya kwanta saman kujera, har ya kwanta ya tashi ya fito ya d'ibi ruwa yaje yayi wanka ya shirya ya je ya gaida Mahaifiyar sa ya fita




Balkisu koda ta tashi bata gansaba kuma bataji motsin sa gidan ba, ta fito ta had'a musu breakfast, ta kaima kowa nasa, khadija yau wankan k'ananun kaya akayi, balkisu da taga hakan itama taje tayi, dan ta lura idan khadija tayi irin wannan shigar sadik zai ta lik'e mata shiyasa itama taje tayi,


Da ta fito sai da dariya taso ku'bucema khadija, wallahi ko kad'an kayan basuyi mata kyau ba ga k'asusuwan wuya da take saki, tana tafiya tana wani juya jiki kuma jikin nan yak'i juyuwa

Khadija kasa jurewa tayi da taga tana wata tafiya sai da ta dara tare da fad'in " Ayi dai mu gani in tusa na hura wuta " Balkisu taji ta sarai ta kyale





Sadik koda ya dawo daya kalleta sai da ya fashe da dariya yayi mai isar sa,Sannan yasa ta cire su






Yau ma kamar jiya maganin ba aikin da yayi, bak'in ciki duk ya dameta musamman idan ta tuna bashin da ta kar'bo gashi tun jiya tayi alk'awarin zata kai kud'in amman har yanzu, gashi bata da ko sisi, tayi zaune bakin k'ofar d'akin ta tayi tagumi, muryar da taji tayi sallama ne yasa sai da cikin ta ya murd'a


Tashi tayi da sauri zata shige d'aki matar tayi saurin fad'in " Dakata dakata" ta k'ara so wajen " Ya mukayi dake eh har gida kuka sameni kuka lullu'be ni da bak'in bargo kukamin dad'in baki na d'auki kud'i na baku kuma sai da na fad'a muku uzurin da gareni kuka ce zaku bayar tun jiya nake dubin ku amman shuru ashe bakusan halarciba to idan baku zo ba ni gani nazo shiga d'auko min kud'i na" matar ta fad'a tare da Mik'a hannun ta


Susar kai balkisu ta fara tare da fad'in "Yi hak'uri shigo daga ciki muyi magana" Ke! Ke!, matar ta fad'a cikin d'aga murya " Dubi idona ki gani banda mutumci game da kud'i kafin kuje baku tambayi ko ni wace ba to wallahi ba inda zanje kud'i na kawai na sani "Dan girman allah kiyi hak'uri ki rufamin asiri mu shiga daga ciki bana son kishiyar nan tawa tasan abinda ake ciki" Au ai baki gudun abun kunya tunda har kika iya cin bashi ni duk ba wannan ba shin akwai kud'in ko babu? " Girgiza mata kai tayi tare da fad'in"Babusu " To ai ta kwana gidan sauk'i d'akin ki zan shiga na za'bi abun kud'ina" Dan Allah kiy"bata ko ida maganar ba matar ta tureta ta shige d'akin





Khadija na d'aki tana karatun al'Qura'an taji hayaniya sai da takai aya sannan ta fito, tayi tsaye bak'in k'ofar ta




Dube_dube take taga bata ga abun d'auka ba, taja tsaki ta fito, fita tayi daga gidan, balkisu har tana jin dad'i, jim kad'an sai gata ta dawo tare da wasu maza su biyu a bayan ta, d'akin ta nuna musu tare da fad'in "Babbar nan zaku d'auko"



Mama ce ta fito daga 'bangaren ta, ta nufosu tana fad'in "Lafiya kuwa" Mama lafiya k'alau, matar ta fad'a taci gaba da fad'in " Bashina aka ciyo nazo kar'ba babu kud'i shiyasa zan d'auki abun kud'i naje na siyar na rik'e kud'i na" Subhanallah y'ar nan da kinyi hak'uri in Sha Allah za'a biyaki kud'in ki"



" Hmmmm mama ina ganin girman ki dan allah ki cire bakin ki a wannan maganar "To allah ya kyauta"Amin


Fitowa sukayi da babbar kujerar d'akin ta, sukayi waje da ita itama matar tabi bayansu





"Haba balkisu! Haba balkisu!, khadija ta fad'a" Ai wannan abun kunya ne wallahi azo har gida a cimaka mutumci akan bashi gidan nan baki rasa ci ba baki rasa sha ba amman wai bashi kikaje kika ciyo" To ina ruwan ki bak'ar munafuka algunguma ta k'asa da wutar jahannama "

" Wa'iyazubillah, mama ta fad'a " balkisu wannan wane irin jahilci ne yake kan ki kike fad'a mata wad'an nan kalaman akan ta gayamiki gaskiya "


"Dallah tsohuwa dakata min, balkisu ta fad'a cikin tsiwa tana nuna mama " Nifa bana son katsalan da cikin al'amari na waya gayyato ki cikin maganar bana son shishshigi ehheeeeeee"

"Balkisu badai rashin kunya zaki mata ba" khadija ta fad'a

" Ban mata rashin kunya wacece ita ko dan ina auren d'an ta shikenan sai aka ce nima uwata ce mtsssww...................................


"Ni wallahi uwar miji ba uwata bace Allah ma ya tsare wannan ta zamo uwata" ta fad'a tare da nuna mama


Saukar mari taji a kumatun ta, tayi saurin dafe wajen ta d'ago kanta, khadija ce ta mare ta " Ya isheki haka balkisu idan kin min na kyale ki bazan juri ganin kinama mama na kyale ba sannan idan ke baki d'auke ta uwa ba dubun ki sun d'auke ta wad'an da suka fiki komai kuma ina alfahari da ita na k'asan cewar ta uwar miji na kamar yarda bazan iya d'agama Mahaifiya ta murya ba ita ma bazan iya d'aga mata murya ba na d'auke ta tamkar uwar da ta haife ni ina san ta Kamar yarda nake san mahaifiyata saboda haka zuciya ta bazata juri ganin ana muzguna mata na kyale ba"



Mama hawaye taji sun zubo mata, da sauri ta juya ta goge, allah sarki ita tasa ayo mata kishiyar nan amman gashi nan wacce tasa a auro tana ci mata mutumci ita kuma ta shige mata





Balkisu hannun ta tacire daga kan kumcen ta zata kaima khadija mari, sadik yayi saurin rik'e hannun,


kusan tunda suka fara wannan rikicin ya shigo yayi tsaye daga nesa yana sauraran su, k'ara bama khadija matsayi yayi a cikin zuciyar sa, tare da ganin girman ta



Yarfi yayi da hannun nata tare da nunata kana yace "Kin bani mamaki da ace fad'amin akayi bada kunnena naji ba da bazan yarda ba, Mahaifiyar tawa kike gayama bak'aken maganganu koda yake kince baki d'auke ta matsayin uwa ba to ni d'an ta wanda ta haifa ina san na shaida miki na janye igiyoyin aure na dake kan ki kije na sake ki saki d'aya "




" Me kunnuwa na ke jiyemin ne? Safiya ta fad'a wacce shigowar ta gidan kenan,

Balkisu hannu ta d'aura akai tare da fashewa da kuka tana fad'in "Wayyoooo na mutu na lalace wayyoooo uwata wayyoooo uba na" da sauri safiya ta k'araso wajen ta tare da fad'in "Ke lafiyar ki kuwa? " Safiya ya sake ni ya sake ni "


" Ahh saki amman dai wallahi kin bada mata yanzu saki kawai saki na aure saki na d'a namiji shine kike kuka wiywiy da hawaye kaiii ai ba'a yayin kuka yanzu k'auyan ci ne hajiya rangad'a gud'a ake a gabansa yasan cewa an dawo za'a return back "



" Return back a gidan uban wa? Sadik ya fad'a yana kallan su " ai indai ana zuwa lahira a dawo to auren nan zai dawo amman in baki ta'ba ganin wanda ya dawo ba to shikenan auren nan haihata_haihatan"



"Saddiku allah yayima albarka hakan da kayi yayi matuk'ar burgeni" mama ta fad'a kana tacigaba da fad'in "Ku kuma kuje allah ya had'a ku da dai_dai ku"




"Mtsssssww ke dan allah shiga d'auko mayafin ki mu wuce dan kisan bana jurar sauraran k'ananun maganganu ke daga ma allah ya taimakeki kin rabu da alak'ak'ai kashin shanu har zaki tsaya 'bata hawayen ki a banza ai wallahi k'auyen ci ne gud'a zakiyi a gaban sa ehheeeeeee "


"Ke badai rashin kunya zaki muna ba ki samemu har cikin gidan mu" Sadik ya fad'a


"Fitsara zan muku ba rashin kunya ba" Ohh naga abun naki fa iskanci ne bara na saita miki kanki zaki dawo dai_dai " sadik ya fad'a tare da zuwa neman sanda, ganin haka yasa safiya da balkisu da fitowar ta d'aukar mayafi suka ruga aguje sukayi waje





Balkisu suna lafiya tana kuka, safiya ta juyo ta kalleta tare da ta'be baki sannan tace" Ke dan allah kima mutane Shuru kin bi kin cika min kunnuwa da wannan kukan naki sai kace a kanki aka fara sakin aure" Nak'i inyi Shuru bak'ar munafuka ai wallahi duk kece kika kaini da hakan har aka sake ni " kar kimin sharri malama dan banma san abunda ya had'a kuba da shiga ta dai naji yace ya sake ki " Bake kika kaini wajen ciyo bashi ba naciyo nasiye wancan bak'in maganin naki ba ba aikin uwar da ya min wallahi sai allah ya sakamin kin rabo ni da gidan miji na allah ya isa tsakani na dake bazan ta'ba yafe miki ba"



" Ke karki nemi gayamin min magana fa " To idan aka fad'a fa me zakiyi" Balkisu ta fad'a tare da rik'e k'ugu tana jijjigawa


"Wallahi yanzu na darji bakin ki saman titin nan" Hehehe mudai darji bakin juna " Safiya ta cire mayafin ta ta d'aura a k'ugu itama balkisu tacire nata ta d'aura


" Idan kin isa kin haihu ga uwar ki da ubanki ki sake fad'an abinda kika ce yanzu " Wallahi na isa ko na haihu ga uwata da ubana nace sai dai mu darji bakin juna" safiya ta shak'o wuyan balkisu itama ta shak'o nata nan fad'a ya kaure tsakanin su wagga ta kaima wagga duka Wagga ta kaima Wagga, dak'yar aka rabasu, ko waccen su na huci







'Bangaren su khadija, wata shak'uwa ce ta k'ara shiga tsakanin su, burin ko wannen su ya faran tama d'an uwansa rai, mussaman khadija da duk wani abun da tasan sadik baya so ta gujeshi, burin ta ta faran tama mijin ta rai ta dad'ad'amasa


Balkisu anzo an kaushe kayan ta, bayan sati biyu da rabuwar su kasuwan cin sadik yafara bun k'asa yanzu kam alhamdulillah komai na tafiya dai_dai



Khadija auren k'anwar ta za'a yi koda yaushe tana saman hanyar zuwa gida, yau dai kam tace bara ta tsaya gida ta huta,

sadik ya dawo cin abincin rana to kafin ka iso gidan nasa akwai wata mazauna a wajen ta dattijawa da yan matasa ne, yabiyo wajen bayan ya gaidasu zai wuce sai wani ya tsayar dashi, wanda ake cema sanusi yad'an girmesa, bayan yazo suka d'an gaisa sai sanusin yace " To dan allah maganar da zan Fad'i ban sani ba ko zata 'bata maka rai ba"In Sha Allah bakomai Fad'i Kawai ina jinka "To sadik gaskiya yawon nan da matar ka keyi yayi yawa kullum tana saman hanya ya kamata kad'an tsawata mata" To in Sha Allah nagode sai anjima " sanusi ya koma ya zauna shi kuma ya wuce



Bayan ya isa gida khadija ta tarbesa ta kawo masa abinci har ta zuba abinci ya fad'a mata abun da sanusi yace " Jar uban can" ta fad'a tare da Mik'e wa ranta yayi matuk'ar 'baci hijabin ta kawai ta d'auko ta zura har k'asa zata fita sadik yayi saurin tare da tare da fad'in" Ina zakije? " Dan girman allah ka bani hanya" ganin bazai bata hanya ba yasa ta zagayeshi ta fita biyota yayi yana kirana sunan ta amman ko juyawa batayi ba sai mazaunar ta tsaya tare da fad'in


"Assalamu alaikum k'attan munafukai sallama bata ma dace da irin ku ba wato zaman da kukeyi ba zaman allah da annabi bane zaman munafurci ne da sa ido eh k'attan munafukai ai bashi ya dace ku tara ku fad'a maba ni ya dace ku tara ku fad'a ma wallahi na yagama mutum rigar mutumci har kuce wai yawona yayi yawa yawona yayi yawa gidan ubanwa nake zuwa dukan ku wajen nan wallahi in abun aje gidan ku ne baza'a tarar da matan ku ba suna can an fita sauran aikin gomnati suke saura kuma yan kasuwa ne ana can an had'e da maza ana cud'anya ana wasa da dariya ana lalewa to duk d'an bura ubar da igiyar aurena ke hannun sa in bai katseta ba yaci k'ashin bishin bura ubansa ko kuma duk wanda yake da iko da mijina in baisa ya sakeni ba yau ban gode ba azzaluman allah wai ku da kukeda abun fad'a jibge ba'a fad'a ba sai kune zaku zauna kuna maganar wasu kai wai har kanada bakin da zaka tari mijina, ta fad'a tana nuna sanusi kana taci gaba da fad'in " Nan aka kama matar ka tare da shugaban su na wajen aikin su, suna iskan ci suna aikata lalata


" Kai kuma matar ka akan yawon ta baka samunta yasa kayima y'ar mutane cikin shege y'ar mak'otanku ma saboda lalacewa da tambad'ewa, kai kuma k'awar y'arka kake ci nan da allah ya toni asirin ku y'ar ka ta kamaku "

Da haka duk sai da ta fad'i duk abun kunyar da kowa yayi cikin su......,............................

🧕MATAR SADIK🧕🧕



MALLAKAR
ZAINAB DODO




STORY AND WRITING
BY
ZAINAB DODO






Free book 📖

09046495943


Kuna ina fans ku matso kusa dan jin yarda wannan littafin zai kasance na MATAR SADIK



_____________________________
_______________
________
TASKIRA WRITER'S FORUM
💫T. W. F💫

Rubutu Baiwace Ga Wanda Allah Ya Baiwa Da Hikimar Mu Muke Alfahari

TASKIRA ASIRIN MARUBUTA📝
_____________________________
_________________
________
________
BISMILLAHI Rahmanirahim
________
Page 2️⃣2️⃣➡️2️⃣3️⃣

Cikin jin kunya duk sukayi k'asa da kansu,
"Rainin wayon banza da wofi ku gaku da abun fad'a dadda'be bayan ku amman har zaku zauna kuna maganar wasu to duk shegen da bai sake magana ta ba bai cika ba munafukan allah masu zaman munafurci da giba zaman kashen wando masu matatta zuciya"

"Khadija dan allah kiyi hak'uri ki wuce muje wannan abun ya isa haka" Sadik ya fad'a

" Ai wuce wa zanyi magana dai ce sai na fad'a dan bakina bai haila bai jinin bik'i wallahi duk wanda yayimin sai na masa idan tsoho baiji kunyar hawan jaki ba jaki kuwa bazai ji kunyar zubar dashi k'asa ba wanwasssssssss" ta fad'a tare da wuce wa


Sadik ya tsaya basu hak'uri, Sannan yabi bayan ta har ta isa gida, tana tsaye bak'in k'ofar d'akin ta,

"Amman dai wallahi khadija baki kyauta min ba yanzu daga fad'a miki magana sai ki fita ki musu cin mutumci "Auu cin mutumci namusu kenan ni akwai wanda yaci mutum ci na irin su "To naji sun miki ba dai_dai ba yanzu ni danazo na fad'a miki ai ni kika kunyata ba kowa ba" Uhmmm haba to meyasa da aka fad'a maka baka bar abunka ba sai da kazo ka sanar mini eh to wallahi yau banyi niyar fita ba amman tunda abun nasu bura uba ne sai na fita bara ma kagani " ta fad'a tare da shigewa d'aki ta d'auko jakarta ta fito


"Sai na dawo " ta fad'a zata fita" dakata izini na baki ne da zakice sai kin dawo " Ai yau bana buk'atar neman izinin Ka idan zan fita, idan ka gama ka rufe d'akin ka kaima mama mukullin " tana gama fad'in haka tawuce ta barsa nan tsaye sake da baki






Tun da ta tunkaro mazaunar kowa yayi k'asa da kansa wasu kuma suna tsinkayarta suka tashi da wajen, har ta wuce wajen tsiff kamar ba mutane a wajen




Tun daga ranar ko suna maganar kowa mazaunar nan to banda ta khadija dan tsoron ta ma suke







Sadik an hango wata bazawara tana da yara har guda biyu amman suna wajen Mahaifin su, sadik har ya kai mata yakan i see i love, nagani ina so, wannan auren kam bai boyema khadija ba da kud'in sa zaiyi dan tun kafin yakai nagani ina so ya sanar mata, itama bata wani nuna masa damuwarta ba


Sai dai gaskiya bayan idon sa taci kuka sosai, tare da tunanin dame ta ragesa ne azaman auren su da bazai iya hak'ura suyi zaman su tare ba har mai rabawa tazo ba wato ( AL'MAUT MUTUWA)




Ana sauran kwana biyu aure, yaci wanka yaje gidan amaryarsa, ita kad'ai ce zaune a gidan a tak'aice dai zaman kanta takeyi duk da mahaifan ta na raye amman gidan haya ta kama, wai bata son hayaniya bata san damuwa

1
2
3

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login