Showing 1 words to 2892 words out of 2892 words

Chapter 1 - TAFIYAR MU CHAPTER 2 HAUSA NOVEL

suwaiba   

31 Dec 2025

98

TAFIYAR MU CHAPTER 2 HAUSA NOVEL





Hafiz Isma'il shine da na hudu a cikin mahaifiyarsa
wacce ta kasance mace tilo wajen babanshi, sai Kannenshi uku mata da duk sun yi aure suna dakin mazajensu, yayunshi uku kuma duk maza ne kowanne da iyalinsa.
Hafiz mutum ne mai ilimin addini da kuma boko
sannan yana da kyawawan halayen da yasa mutane su ke son hulda dashi. Yana gama NYSC ya samu aikin gwamnati inda ake biyanshi salary mai tsoka wanda cikin ikon Allah ya tara ya sayi fili yayunshi suka dafa mishi yayi gini mai kyau na gani na fada.
Hafiz ya hadu da Juwairiyya Ahmad ne wata rana da ya
raka childhood friend dinshi Muhammad wani unguwa.
Yana zaune shi kadai a cikin mota yana jin waka yana kuma danna wayarsa ya dago fuskarsa don ya gani ko Muhammad ya fito daga gidan da ya shiga amma bai
ganshi ba, juya kanshi da zai yi geten hagu ya hango wasu yan mata hudu sun fito daga wani gida suna hira suna dariya, hankalinsa ne ya koma kan wata budurwa chocolate colored wacce ita ce ta karshen fitowa daga gidan tana gyara hijabinta tana cewa kawayen nata su jirata ta musu rakiya zuwa bakin titi. Hakan ya tabbatar mishi cewa nan ne gidansu, kenan ziyara suka kawo mata.
Har suka zo suka wuceshi idanunshi na kan oval face
dinta wanda yake cike da annuri ta kasa daina murmushi. Sai da suka bace mishi da gani ya rufe idanunshi yana hasko fuskarta mai dauke da manyan

idanu irin nashi da kuma hanci daidai fuskarta, abun da ya fi dauke mishi hankali shi ne lips dinta da suke full ta shafa musu lip gloss sai sheki suke yi har yana jin ina ma ita din tashi ce.
Yana zaune a cikin motar ta dawo ita daya ta shige cikin gidan tare da kulle kofar ba tare da ta gane cewa ana
kallonta ba.
Shiganta ke da wuya Muhammad ya fito ya shiga motar suka kama hanyar gida yana yiwa Hafiz hira wanda shi hankalinshi na kan yarinyar daya gani wanda zai iya rantsewa ya kamu da sonta ne at first sight.
"Lafiyanka kam? Ina ta magana ka yi shiru ka shareni."
Fadin Muhammad cikin hasala.
"Wata yarinya na gani ta burgeni matuka kuma wallahi in har na bincika na ji tana da hali mai kyau zan aureta."
"Su kuma Yan matan da kake waya kana chat dasu fa?"
Ya harareshi ta gefen ido.
Dariya Hafiz yayi ya sosa kai ya ce,
"Duk cikin su babu matar aure sai budurwar soyayya.
Zamu yi soyayya kam tsantsa amma ni nasan ba
aurensu zan yi ba saboda bana son mace mara kamun kai da rashin aji. Amma ka ga yarinyar nan dana gani?
Ina kallon fuskarta na gane ba shashasha bace she is a wife material. Yanzu dai kai zaka shige mini gaba tun da naga alamar ka san makwabtan gidansu yarinyar ka tambaya mini halinta."

"Babu wanda zan je in tambaya wani abu, kuma gidan da kaga na shiga gidan wani distant relative din Babanmu ne ya aikeni gurinsa nima ban taba zuwa ba sai yau."
"Don Allah kar mu yi haka da kai mana." Hafiz yayi
saurin fada cikin kwayewar fuska yana kallon
Muhammad.
"Mallam ka kalli gabanka kar ka juyemu a cikin
kwalbati. Zan yi tunani a kai."
Washe gari da yamma sakaliya Hafiz da abokin nashi
suka isa kofar gidan su Juwairiyya suka aika yaro yayi kiranta bayan Muhammad ya fada mishi sunanta a binciken da yayi na dole.
Tana fitowa ta samu Hafiz a tsaye suka gaisa ya gabatar da kanshi tare da fada mata dalilin zuwanshi babu bata lokaci domin shi aurenta yake son yi. Bayan ta ja mishi aji akan cewa bata tsayawa da samari sannan ya roketa da girman Allah kan ta bashi number wayarta kafin ya gabatar da kanshi gurin iyayenta. Kamar bata so ta bashi numbern, a nan yake fada mata tare da abokinshi yake wanda suna hangoshi a cikin mota a gaba dasu amma ko sau daya bai waiwaya ba. Hafiz ne ya kwala mishi kira Muhammad ya juyo rai a bace kamar an mishi dole.
"Ka zo ku gaisa mana." Hafiz ya fada yana rokanshi ta
cikin ido don kar ya kwafsa mishi.

Hafiz haushi da kuma kunya ce ta cikasa wanda bai
Kara minti biyu ba Juwairiyya ta mishi sallama ta shige gida akan cewa mamanta zata mata fada idan ta ga ta jima.
A mota Hafiz yayiwa abokin nashi tatas kan cewa ya
wulakantashi shi dai Muhammad yana shiru bai ce
komai ba, karshe da yaga Hafiz ya fusata da gaske sai ya bashi hakuri yace zai gaisheta idan suka sake haduwa.
Abun da basu sani ba shine ita Juwairiyya tun a lokacin ta ji ta tsani Muhammad domin bata son duk wani abu da ya danganci wulakanta mutum. Daga ganin suturun jikinsu da kuma motar da suka zo dashi ta gane suna da wadata in dai ba arowa suka yi ba, amma hakan bashi zai sa abokinsa ya wulakantata ba don bata kai su kudi ba. Duk da cewa Hafiz ya burgeta amma halin abokinsa yasa ta ji baza ta iya kulashi ba, hakan yasa da dare da yayi ta kiranta ta ki dauka har ya gaji ya daina.
Washe gari da safe ta fito daga gidansu zata tafi
islamiyya, da yake ta gama secondary school wata uku da suka wuce kuma mamanta ta hanata cigaba da karatu wai aure zata mata ta samu Hafiz rakube a katangar gidansu da alama ita yake jira da fito. Yana ganinta ya sha gabanta fuskarshi abun tausayi da alama ko wanka bai yi ba ya fito.
"Laifi ne na miki kika ki daukan wayata?"
Tsabar mamaki kasa magana ta yi domin wannan abun da yayi a littafin Hausa ne kadai ta ji ana yi wato

saurayi ya kasa runtsawa har sai ya shawo hankalin buduwarsa.
"Ko dai ban miki bane tun farko sai ki fada mini ba wai ki bani numbernki sannan ki ki kulani ba."
Ganin ana wucewa ana kallonsu ga kuma uwa uba hakan da yayi na nuna damuwarsa a kanta yayi matukar burgeta, domin ita tana son a nuna mata kulawa da soyayya don haka ta budi baki ta ce,
"Na yi bacci da wuri ne. Sorry."
Ajiyar zuciya ya sauke kana ya dafa kirjinshi saitin zuciyarshi ya ce,
"Har na ji sanyi a zuciyata, we cool?"
Murmushi ta yi don ta lura yana yawan saka turanci a maganarsa wanda ba forcing dinshi yake yi ba irin ta gane ya iya turanci, a'a ta tabbatar haka ya saba domin ko sau daya bata taba kamashi da murdewar harshe grammatical error ba.
"Yeah, we are cool. Bye." Ta fada tana ratsewa ta gefeshi don kar ya sakata latti a sakata wanke bandaki.
Bata yi taku biyar ba ta ji wayarta na kara ta zaro daga cikin jakarta domin tasan babu mai kiranta a wannan lokacin sai mahaifiyarta hala tayi mantuwa ne a gida zata kai mata asibiti inda take aiki, amma ganin numbern Hafiz wanda bata yi saving ba yasa ta juyo ta dubeshi yana tsaye a inda ta barshi da waya a

kunnenshi alamar shi din ne dai ya kirata.
Murmushi yayi ganin ta tsaya tana kallonshi kana ya mata nuni da wayar hannunta wanda hakan yasa ta farfado ta amsa wayar gami da karawa a kunnenta, muryarshi ta fara ji yana cewa,
"I know ko nace ki zo ki shiga mota in kaiki school din
baza ki yarda ba saboda it seems your parents raised you right, so Allah ya kiyaye hanya Ya kuma baki ilimi mai albarka. Take care."
Yana gama fadin hakan ya kashe wayarsa kana ya shige motarsa ya tafi ya barta a gurin zuciyarta na bugawa da
karfi ba don tsoronshi ba sai don a take a wannan
lokacin ya sace zuciyarta ya tafi da ita.
A ranar Hafiz ya zo da yamma bayan ta amince mishi amma bai zo tare da Muhammad ba, gefe guda kuma yasa an mishi binciken halayenta aka kuma sanar mishi cewa tana da hankali da nitsuwa kamar yanda yayi tsammani. Bai yi wasa ba ya turo iyayensa gurin dangin Babanta aka bashi izinin hira har aka musu baiko.
Tun rana ta farko da Hafiz yazo da Muhammad bai Kara
zuwa dashi ba har aka saka ranar aurensa da
Juwairiyya wacce ta kaucewa duk samarinta tace shi
zata aura. Sai ana ribibin auren nasu ne suka hadu wanda shi Muhammad din ne ya daga mata gaisuwa amma tayi kamar bata ji shi ba.

Da yake tana yawan jin labarin shi gurin Hafiz yasa ta
gane shi din abokinshi ne na kut da kut, sannan ta fahimci yana da girman kai amma ita neman abu ta yi a gurinshi da zai wulakantata? Har aka yi bikin tsakaninta da Muhammad babu jituwa, sannan ko bayan auren bai je gidansu ba sai da suka yi wata biyu wanda ta lura Hafiz ne ya matsa mishi suka zo nan ma bai ci komai a gidan ba ya tafi.
Juwairiyya Ahmad ita kuma ya ce ta farko a gurin
mahaifiyarta sai sauran kannenta mata biyu da namiji daya. Babansu ya rasu tun suna yara hakan yasa mahaifiyarsu ta zauna a cikin gidan mijin nata tare da Yayanta ba tare da ta sake aure ba, kuma ta dauko mahaifiyarta tsohuwa da take Kauye suna zama tare da yake ita ma mijin nata ya rasu. Cin su da shan su duk a kan mahaifiyarsu yake wacce take Nurse a wani Maternity wanda jajircewarta da kuma jimawanta tana aiki yasa aka bata matsayin Matron na asibitin gaba daya. Hakan yasa ta samu karin albashi ta kuma cigaba da kula da Yayanta har ta aurar da Juwairiyya.
Wata shida da aurensu suna zaman lafiya da nunawa
juna so Muhammad ya tayar da maganar auren da zai yi. Ko da Hafiz ya nunawa Juwairiyya hoton matar da Muhammad din zai aura sai ta budi baki ta ce,
"Dama shi lukuti ai sai lukuta ce zata iya dashi. Wannan idan aka aura mishi yarinya karama rana daya zai karya musu ya da nauyinsa."

"Riya baki da kunya fa, me ya kai tunaninki har can daga nuna hoto kawai?" Fadin Hafiz yana harararta da gaske.
"Sorry na tabo rabin ranka." Ta mishi gwalo kana ta
tashi ta shige kitchen don daura musu abincin dare.
Bayan auren Muhammad da matarshi Salima su Hafiz suka je gidan amaren a satin farko bayan Hafiz ya
tilastawa Juwairiyya zuwa. Tar6an da Salima ta musu yasa Juwairiyya ta sassauto domin ta yi zaton itama Saliman zata yi girman kai ne irin mijinta, ai kuwa kafin su tafi hira suke yi sosai har suka yi musayar number a kan zasu dinga ziyartar juna akai-akai.
Hafiz ya ji dadin wannan Kawancen nasu yayin da
Muhammad kuma ya nunawa matarsa baya son
huldarta da Juwairiyya yayi yawa, bisa la'akari da ya yi na cewa tana da raina mutane da kuma rashin da'a. Sai dai duk da cewa Salima na bin umurninshi amma wannan karon bai samu damar rabata da Juwairiyya
ba, karshe hakuri yayi ya barsu sai dai Cold War da ke tsakaninshi da ita bai ragu ba sai ma gaba da yake yi.
Tun bayan aurensu Muhammad ya fara kwanciya rashin lafiya domin Ulcer da Typhoid da suka mishi rufdugu, Hafiz na yawan bashi shawarar ya rage cin junk foods da suke sakashi kiba suke kuma kara mishi cuta amma baya ji, da yake haka ya taso a gidansu suna cin duk abun da suke so babu mai hana su. Wannan kenan.
Present

Juwairiyya ce ta gyara kanta data kwantar a kan
damtsen Hafiz ta ce,
"Ina jinka."
Shiru yayi kamar ba zai ce komai ba sannan ya fara
magana a hankali kamar mai rada.
"Kin tuna dazu na fada miki abun gaggawa ya taso
shiyasa muka tafi bamu jiraku ba?"
Gyada kai ta yi tana hadiye wani yawu mai kauri don zuciyarta bugawa ta fara yi haka kurum ta kasa nitsuwa dalilin Hafiz bai taba cewa zasu yi magana sannan yayi
using wannan tone din ba.
"Bayan mun fito ne na ga jikin Muhammad a sanyaye na
tambayeshi me yake damunshi tun da na lura ba rashin lafiyar ce matsalar shi ba a lokacin. Riya ashe muna tafiya da mutumin nan ne amma shi har ya cire rai da tsawon kwana yana ganin lokacinshi ya kusa, hawayen da naga yana yi ne yasa nace mu shiga mota kar mutane su yi ta kallonshi babu dadi ana magana. A nan ya nemi mu bar asibitin mu je wani guri zai yi magana da ni, bayan mun fita muka samu wani guri muka tsaya.
A nan yake fada mini wata magana wacce har yanzu na
rasa yaya zan dauketa."
Shiru ta yi tana jiransa ya Karisa maganan lokaci daya
kuma zuciyarta ta sassauto ganin akan Muhammad za'a
yi maganar ba wai a kan Hafiz ba.
"A nan ya sanar dani cire rai da yayi da rayuwa wanda

bai bari muka rabu ba sai da yasa na yarda da wani alkawarin da yace in daukar mishi."
"Alkawrin menene?" Ta samu kanta da tambaya don a take zuciyarta ta dawo da saurin bugawar da take yi dazu.
Tunani kala-kala kuwa babu wanda bata yi ba kwakwalwarta na bata wild ideas na wannan alkawarin
da mijin nata ya dauka ciki kuwa har da cewa idan matarshi ta haihu Hafiz ya rike mishi dan kar a barwa
Salima saboda mugunta.
Ya saka na mishi alkawarin duk ranar da ya mutu in auri matarsa Salima in kuma rike mishi duk abun da zata haifa kar yayi agolanci a wani gida."
Cikin azama juwairiyya ta tashi zaune har tana buge bakin Hafiz da kanta ba tare da ta sani ba, sosai ya ji zafi har ya dandani jini a bakinshi amma yayi shiru bai nuna mata ba saboda abun da yake gabansu yafi karfin zogin ciwonsa.
"Wannan wace irin banzar magana ce?!" Ta tambaya tana aikawa Hafiz wani mugun kallo wanda har lokacin yana kwance bai ko motsa ba yana ganin yanda fuskarta ta rikida lokaci guda da tsantsan kishi, bacin rai da kuma wani abu kamar tsoro a kwayar idanunta.
"I swear Juwairiyya ban san me yasa yayi wannan maganar ba, kuma kukan da yake tayi kamar karamin yaro yasa na dauki wannan alkawarin ba don na taba

kawo hakan a cikin raina ba. Sannan gani nayi cuta ba mutuwa bace, don yana yawan rashin lafiya bashi zai sa ya gane mutuwa zai yi ba saboda wani yana kwance ma a gadonshi lafiyarshi kalau za'a zare ransa idan lokacinsa yayi. Wani yana tafiya yake fadi ya mutu yayin da wani abinci ma yake ci zai yi lomarsa ta karshe ya kwanta ya mutu. Na amsa mishi ne don ya daina kukan da yake yi kuma ya bani tsoro ne saboda ban taba ganin yana kuka cur-cur da idanuwanshi irin haka ba, ko lokacin da mahaifiyarsa ta rasu bai yi kukan da yayi yau ba. Juwairiyyah tsakanina dake babu бoye-6oye, shiyasa nake fada miki duk abun da ya shafeni bana son na 6oye miki daga baya ki ji ranki ya aci kiyi zaton ban daukeki da muhimmanci ba."
Shiru Juwairiyya ta yi amma tuni idanunta sun fara
tara kwalla, wani irin tsana Muhammad yake mata da tun kafin ya mutu zai bada wasiyyar a kuntata mata ta hanyar mijinta ya auri matarsa wacce ta kasance kawa a gareta? Shanye hawayen idanun nata tayi ta hanyar kallon saman dakin ta bude bakinta a hankali tana jan
numfashi ta nan tana kuma furzarwa. Sai da ta daidaita kanta sannan ta dubeshi har lokacin zuciyarta bai daina bugu ba wannan karon tambaya zata mishi wanda take tsoron amsar da zai bayar.
"What if in ya mutun? Zaka cika alkawarin ne ka auri
Salima?"
Kura mishi ido tayi tana ganin rudu a fuskarsa wanda
ko bai fada ba ta gane amsarta.

"Juwairiyya ki bar maganan nan haka, shima da yayi maganar bana tunanin yana cikin hankalinshi ne sannan who does that for God sake? Ki dauki abun tamkar ba'a yi ba, don ni wallahi har na fara dana sanin fada miki saboda ban yi tsammanin zaki dauki abun da zafi har haka ba. I thought zaki dauki hakan ne a matsayin shirme mu wuce gurin."
"Zaka aureta ko ba zaka aureta ba?" Ta share duk zancensa ta kara mishi tambayar a karo na biyu.
Sai a lokacin Hafiz ya gane da gaske ta dauki maganar da zafi ya tashi zaune ya kai hannu zai jawota jikinshi ta dakatar dashi ta hanyar daga mishi hannu tace,
"Just answer me."
"Riya I told you...."
"Hafiz don Allah ka amsa mini. Please." Ta yi saurin katseshi muryarta har bari take yi wanda har sunanshi da bata iya kira a gabanshi yau sai da ta kira.
Sunkuyar da kanshi yayi kasa kana ya dago a hankali yace,
"He made me promised tare da rantsuwa da Allah akan zan nemi aurenta sai dai in ita ce ta ki amincewa sannan zan hakura, and I know itama ba zata yarda ba saboda Kawancen da yake tsakaninku."
"Baka sani ba dai, babu macen da zaka je mata da zancen aure ta ki amincewa da kai Hafiz. Kana da

qualities din da mace baza ta iya bari ka wuceta ba."
Sai a lokacin kafadun Juwairiyya suka sauka alamar defeat domin a yanda take fadawa Salima labarin kyawawan halayen Hafiz zai yi wuya idan ya je mata da zancen ta gujeshi sai dai in ta ji kunyarta ne ta ki amincewa.
Kwanciya ta yi nesa da Hafiz wanda yana ganin hakan
yaji babu dadi a ranshi domin bai ga abun tashin hankali a cikin wannan zancen ba, shi wanda ya kawo maganar ma yayi imanin tsoron mutuwa ce tasa yayi maganar amma ba don zai mutun ba duk da cewa cikinsu babu wanda yake da guarantee din kai tsufa.
"This is all stupid, da maganar da reaction dinki da kuma fushin da kike son ki mini Juwairiyya. But | will let you sleep on it zuwa gobe mu ga ko kema zaki yi tunani irin nawa. Sai da safe." Yana fadin hakan shima ya kwanta zuciyarsa a cunkushe bayan ya kashe musu wutan dakin.

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login