Showing 1 words to 1296 words out of 1296 words
HAMADA BOOK 1 PART 5
Don haka jami'an tsaron na Saudi suka tashi haikam wajen yaki da mugayen mutanen da suke neman gurbata musu kasa.
Ayyukan yi suka karanta sai zaman dari
da firgicin kame. •
Kusan dan abin da aka tara na neman karewa a biyan kuaden Haya, ci da kuma sha da sauran bukatun dan Adam na yau da gobe, balle ma wata irin rayuwa ce da aka fadadata da fadin gaske; ala tilas sai an yi zaman kece raini da jin dadi, don haka komai yawan kudaden da aka samu sukan nutse cikin wadannan bukatu, musamman ta fannin mata mazauna Shahadar.
Yagana na matukar yi musu kokarin musamman ta fannin biyan kudin hayar gidan, shi ne ma babban tashin hankali bakin hauren musamman a wannan lokaci da suka kasance su biyu kudaden sun yi musu nauyi, fama-famai na
Saudi har fam goma sha takwas, adadin Riyal dari da tamanin a wata guda daya tal!
Babbar hikimar da ta sa akan yi zaman hadakar ke nan, za ka iske kamar mutum hudu zuwa takwas a cikin dan karamin daki guda a kalla ka sami saukin 'yan kudaden hayar.
Ga dai rashin abin yi sabi da rashin tabbacin hanya. Hanyoyin duka sun lalace da jami'an tsaro.
Takamar dai ta Haraj ce, Askarawan tsaro kuma na yawan datse hanya a shiga kamen mai uwa da wabi.
Idan ma ba a Haraj din ka ke cin kasuwa ba, kana dai da abin yi, abin yin da ka rike shi ne sana'a, ka ke kuma samu, abin yin da tilas sai ka fita ka nema, a kuma jajurce wajen yinsa, koda kuwa sana'ace ta rashin gaskiya.
To kusan duk hanyoyin sun bi sun datse, don haka mutane da yawa suka shiga yin kaura zuwa garuruwan da ke karkashin yankin Jeddah, can ma ana samu ga kuma saukin fita neman na kai babu idanun jami'an tsaro a kai.
aman ya zame mana dole, ni kam ,haka ne a gurina ban sani ba ko haka ne a idanunki?" Yagana ta ce da
Zaliha.
Lokaci guda ta ci gaba tana mai dạn jan
tsaki.
"Ban taba nufin zama a wani kauye ba
Birni ba, ko a ina ne Yagana ta saka kafafu..." Ta kara yin dogon tsaki.
"Tilas ne mu bar Birnin Jeddah matukar
ba fatan aikewa da mu gida muke fata ba.
Askarawan nan sun matsa, idan ma mun nace mun zauna din ayyukan yi babu tunda babu halin shiga Hadit a halin yanzu, 'yar walwalar ma da ake duk dai hakan ta gaza samuwa, mafita kawai mu wuce KUSHA"
Zaliha ta dubeta cike da damuwa, don kuwa tana sane da cewa 'yan kudaden da za su biya na hayar gida na wata mai kamawa babu shi, kiris! ya rage a shigeshi, babu lamuni ko.
Kankani a tsakaninsụ da Kafilin gidan (wakili)
balle akai ga Saudin da yake da mallakin gidan da yake da mayatar son kudi da nuna rashin ragaya.
"Mu wuce Kusha".
Ta kara nanatawa.
"Kusha!"
"Mene ne kuma Kusha?" Zaliha ta
tambaya cike da 'yar damuwa.
"Wani gari ne ko kuwa na ce miki wani dan yanki ne da ke bayan garin Jeddah da mutanen mu suka kafashi suke kuma gudanar da sana'arsu.
Akwai samu, ga kuma kwanciyar hankali da nutsuwa, babu wani razani ko a tattare da wajen".
Zaliha ta gyada kai cike da gamsuwa.
Yagana ta kara da yi ma ta bayani.
"Mutane da yawa sun nutsa can...Ke wasu
ma a can suke tun kafin rikicewar gari.
Sun ce can din ma yafi saukin rayuwa, gashi kuma ana fita ayyuka ana kuma matukar samu.,
Idan ma mun so da zarar al'amura sun dai-daita sai mu dawo cikin Jeddah City, unguwar Hindawiyya makofciyar Babal Shariff."
Anan Zaliha ta yi murmushi.
*
*
**∞
Z
aliha ta yi kokari ta isa Haraj a bisa al'amarin da sukan kirashi da shahada.
Nufinta kawai ta gode masa.
Sama da kasa ba ta ganshi ba, duk wani
lalube da ta yi babu ko motsinsa.
A karshe wani jamilin .gudanarwar
Kamfanin ya ja kunnenta, baya son ganin 6urbushin ire-irensu a gidan Abincinsa, suje ya gode da cinikinsu, a banza suna son jazawa Kamfaninsu masiba, in kuwa ba haka ba zai hadata da Askarawan Saudi.
Cikin nuna kyara da ban-bami yake furta
hakan cikin harshen larabci na Saudi.
KÚSHA
****º
•**
RIN RASHIN KYAWUN hanyar ya wuce misali.
Suka
keta suka keto ta
tsakankanin tsaunika da kwazazzabae fetal! Filin Subahana, Sahara mai fadin gaske mai cike da tarin yashi mai kuna.
Haka suka ratsa suka kutsa ta bayan
Birnin Jeddah da Gangaren kuryar Kasuwar
Haraj.
Suka miki hanya dodar zuwa Kauye, Garl, ko kuwa mu ce tsakiyar HAMADA, garin na Kusha.
Filin Allah ne fetal! iyakar dubanka
Sahara ce gaba da baya babu ko dogon Ganye balle Tsirrai face iska mai karfi da ke kadawa a wajen.
Akwai rukunin gidaje da aka yi su da Tanti (Shema), wasu kuma na Sandaka ne (Wato
ginin da aka yi shi da Katako) shi din ne ma ya fi yawa.
Akan buga Katako ayi gida sosai a rufe saman dakin da bangon dakin da Leda, a fitar da Taga da kofa, Makewayin girki da Makewayin Bahaya da Wanka, a haka Rami mai zurfi a saka Katuwar Garwa ko Robar Fenti.
Anan ake tsugunnawa har zuwa lokacin da zai cika, mazauna Gidan su cire Garwar ko Robar su je can nesa da Kusha tsakiyar Sahara su yasar, sai kuma a kara saka wata Garwar..
Galibi gine-ginen Sandakar da Shemar akan yi su ne a tsakankanin Duwarwatsun da suke warwatse a wurin jefi-jefi, domin kaucewa karfin iskar da ke kadawa a wurin.
Wasu gidajen haya ake, akwai masu shi wadanda suka ginata daga cikin al'ummatan da ke zaune a wajen.
Sai dai Hayar tana da matukar rahusa, wata guda Riyar din da za ka biya bai taka kara ya karya ba idan ka hada da wanda ake biya a
cikin Birnin Jedda, sai ka ga ma kamar wannan kyauta ne.
Wasu Gidajen kuma bana Haya bane, wuri ne filin Allah fetal! debi da kanka, ka yanka ka diba iyakar son ranka ka kafa Shema ko kuwa ma ka gina Sandaka (Ginin Katako) matukar nufin zama ka yi sosai a wajen, idan kana da halin gina Sandakar.
Idan ko ta bangaren al'ummar da ke wajen ne, ma iya cewa ta hade galibin dukkan wani jinsi da ya fito daga Afirika dama wasu daga cikin kasashen Larabawan da tattalin arzikin kasashensu yake da matukar rauni kamar irin KASAR YEMAN.
Ta 6arin al'ummatan da ke cikin kasashen
Afirika kuwa da suka fi tasiri a wajen, akwai mutanen Somali, Mali, Sudan, Itofiya (Ehtopia) da Iritiyiya (Habasha), Chadi, Nijer da makofciyarta Najeriya, da dai sauran kasashe da dama daga cikin yankin Afirika da Musulmi ke da tasiri a ciki. Zaliha da Yagana suka kasance cikin
alfarmar Hauwa 'yar mutan Chadi.
A bisa alfarmar tata ne ma suka iso Garin na Kusha. A can baya sun san juna, sun ma taba zama wuri guda kafin Hauwa ta zabi zaman Kusha a bisa zama cikin Birnin Jeddah.
A cikin Shemar su Hauwa, domin kuwa sun yi sa'a Hauwa da kawarta Nana ne kadai ke da mallakin Shemar.
Take ta kunna na'urar girki mai aiki da iskar Gas, take ta tasar musu da ruwan Gahawa (Dakakken kwallon Dabino da 'ya'yan Gahawa da Sukari mai dama) mai karfi domin wattsaker gajiya.
Kana tayi amfani da kayan Abincin
Gwangwani, take ta tasar musu girki mai dadi.
Fried Chicken da kuma Shrimps.
Girki ne da ta kwaikwayeshi daga babban
Kamfanin nan na Sa'udi da suke matukar ji da
shi ta fannin Kaza da Abinci, wato AL-BAIK RESTAURANTA.
Yagana ta ci abincinta sosai. Zaliha kam ko tsakwari ta kasa yi, tsoro da firgici ne fal cikinta.
Wace irin rayuwa ce haka cikin dokar
daji? Ba daji bane.
Kai gwanda dajin ko digon tsirrai ka duba
ka ji sanyi
Kawai sai ta dinga jin hawaye na zubar
mata a kumatu.
Babu shakka amincin da ke tsakaninsu-đa
Yagana ba ta zaci haka ba.
Sai dai hakan ba yana nufin ta kasa dimbin alherin da tai ma ta ba, wata aba ce ba za ta taba mancewa da ita ba a kafatanin zamanta a Kasar Saudi.
Ko ita Yaganar ta dan razana a lokacin da aka nuna filin Allah fetal tsakiyar HAMADA
aka ce sun iso Kusha.
Babu dogayen gine-ginen nan na Birnin
Jeddah face tarin ginin Katako da Tanti.