Showing 1 words to 2328 words out of 2328 words

Chapter 1 - BAKAR KAYA PART 4

20 May 2025

789

BAKAR KAYA PART 4


uwanshi ba su son shi, ina tausayama Idris, maraici ya yi mashi yawa, ga na uwa ga na uba, kuma ba ya da 'yan uwa...Sai dai akwai Allah, ku yi hakuri da
"
rayuwa..
Kuka ya yi sosaim, ya rinka rokon Abbati ya rike amanar Idris. Sai da ya karya mashi zuciya shima ya rinka kukan.
Washe gari suna masauki, mummunan sako ya iso-musu cewa Alhaji rai ya yi halinshi. Da kyar kawun ya shawo kan Idris ya daina kuka suka fito zuwa gidan,. Kusan tamkar wanda ya zare haka ya koma, ya gaza tsayawa, ya gaza zama, sai sambatu yake yi, yana kuka gani yakoe yi gabaki daya duniya ta juya mashi baya, yanzu baya da kowa sai Kawun kadai.
Kawun yaji tausayinshi sosai, don haka ya dauki alkawarin ko duk abin da ya mallaka za ya kare ba za ya bari ya yi kukan maraici ba.
Bayan an kaishi makwancinshi, Kawun ya yi musu zaman kwana biyu sannan ya wuce Jos da sharadin shima Idris da an gama komai za ya biyo bayanshi. To sai dai bayan tafiyar Kawun da kwana biyu komi ya yi mashi zafi, ya ga zaman na shi baya da amfani, ba'a komi da shi, 'yan uwanshi sun ware kansu sai shige da fice suke yi ana ta shagali da dukiyar gado. Sai ya tattara ya yi tahowarshi. Sai dai Kawun na shi ya ganshi, ya fara yi mashi fada akan

don mi ya taho da wuri haka? Amma da Idris ya yi mashi bayanin abin da ke faruwa sai ya ga tahowarshi alkairi ce, irin wannan idon ma ya ce za ya ci gaba da zama yana zuba masu ido sai a nemi hallakashi a banza.
Don haka ya ci gaba da kwantar mashi da hankali ya ce, ya yi hakuri ya zuba masu ido komi suka yi don kansu, kuma dukiyar gado bata sanya mutum ya yi arziki, in da rai da rabo wata rana sai ya mallaki fin wanda mahaifinsu ya mutu ya bari, don haka tun daga lokacin Idris ya fidda ran samun komi daga cikin dukiyar da mahaifinsu ya bari, suka hau kanta suka zauna ana ta cin duniya.
Watanni kadan ya samu shiga karatun jami'a ya yin da Kawun ya yi tsayin daka wajen biya mashi dukkan bukatunsu, baya neman komi sai dai ma ya taimakama wasu. Ya yin da Idris ya zama dan halak ya shiga karatu da zuciya daya, ya mai da kai sosai, don haka bai taba samun matsala ba.
Tun da ya zo makarantar Allah ya hadashi da
Jibrin. Da farko sukan hadu ne su yi karatu tare, sabo da shima Jibrin din yana da nacin karatun. Har ta kai sun shaku sosai, shakuwar da ta kai sun kulle sosai, koda yaushe suna tare dakinsu daya, komi nasu tare har zuwa wannan lokacin babu wanda ya taba jin kansu.

Lokacin da suka kammala karatunsu an maida Kawun aikin Jahar Kano, mafarin rabuwarsu da Jibrin ke nan suka rabu kowa na alhinin rashin dan uwanshi.
Ya yin da Fatima tafi kowa damuwa tun da suka fara jarrabawa tabi duk ta sukurkuce ta shiga damuwa sosai. Idris kan lallasheta ya ce "Kiyi hakuri Fatima don na gama karatu ba yana nufin na yada ki bane. Kiyi hakuri Insha Allahu ina ji a jikina kece matata. Kiyi hakuri idon naje gida zan samu Kawu mu yi magana da shi, insha Allahu ba zan dade ba za ki ganni na dawo, idon na samu yarda na ke so ma nan zani dawo in yi masters dima".
Jibrin na jinsu sai dai ya yi dariyar mugunta, ya san fadi kawai yake yi ba wani dawowar da zai yi.
Haka suka rabu da kyar tana kuka.
Kwana biyu da tafiyarsu taji makarantar ta isheta, don haka tayi shirin tazo gida. Abin da ta tarda ya tayar ma ta da hankali matuka, Aliyu ta samu kwance babu lafiya ciwo har ya ci karfinshi amma ba a kaishi asibiyi ba. Ta tambayi Usman
"Babanmu baya nan?". Ya ce, "Yana nan, Aunty ta ce ba za a kaishi asibiti ba, wai cewa ta yi ya satar mata kudi shi ne ta rufeshi a cikin daki ta rinka dukanshi sai da ya suma, tun daga lokacin bai kara lafiya ba har yanzu".

Fatima ta daga rigarshi ta ga ko ina ciwo ne na bugu. Abin ka ga jar fata, ya yi jajiir, sai da ta yi kuka. Ta fito falonsu ba ta yi ma kowa magana ba ta fice ta kirawo tasi. Auntyn na cikin daki ta kama Aliyu suka fice sai asibiti.
Likitan kanshi sai da ya yi fada ganin yarda jikinshi yake amma an barshi kwance gida. Fatima kuma kawai take yi ta kasa yi mashi magana, sai yaji tausayinta ya shiga dubashi.
Ya yin da ita kuma ta fito zuwa banki ta fidda kudi a cikin account dinta ta dawo asibitin ta biya dukkan kudin maganinshi ta sawo mashi kayan marmari da na karin jini. Likitan ya ce har da yunwa ma ta kamashi. Sai da suka kwana sannan mahaifinsu yazo dubashi. Shi kanshi ya sha mamaki sosai da ganin halin da yaron yake ciki, sam bai sani ba. Ya rinka basu hakuri. Fatima ta sanya hannu tana share hawaye tayi imanin mahaifinsu na kaunarsu fin karfinshi ne kawai aka yi.
"Allah ya shirya mata masu irin wannan halin
na rashin imani"
Wasa-wasa sai da suka yi kwana biyar sannan aka sallame su suka nufi gida. Nan kuma suka tarda bala'in Auntyn. Ba su kadai ba hatta mahaifinsu ya sha bala'i, baya da bakin magana sai dai ya yi shiru.
Ta ce mashi, "Munafuki yaje ya kashe ma danshi kudi itama dole ya bata"

Abin haushi dole ya fidda kudin ya bata amma duk da haka baya barsu sun zauna lafiya ba. Ranar yini tayi tsegumi da koraft. Kannenta da ta kwaso na tayata babu mai ikon komi a gidan sai su. Ita dai :
yar
kallo ce. Da taji bala'in ya yi yawa ranar bata kwana gidan ba, tayi tafiyarta makaranta. Sai dai ta gargade su kooda wasa kada su kuskura su kara bari ta buge su da ta taso su ruga.
Bayan ta dawo makaranta abubuwa suka yi mata ciwo. Ga dai tunanin rashin Idris, gashi kuma tana tunanin halin da kannenta suke ciki, tana so taje ta dubasu sai dai tana gudun bala'in Auntynsu.
Bayan tafiyar Idrisda wata biyu har ta fara sabawa da kewarshi. Rannan tana fitowa daga lecture sai kawai ta hangoshi tsaye jikin mota yana yi mata murmushi. Zuciyarta tayi sanyi har hakoranta suka baiyana. Da sauri ta isa gareshi sai kuma zuciyarta ta kare, idanuwanta suka ciko da hawaye sai kuka. Ta sanya hannu ta rufe fuskarta tana jin ciwo a zuciyarta tunanin guda "Ko Idris zaya cika mata alkawari? Gani take yi shi kadai ne mutum na karshe da take jin za ya iya tallabar rayuwarta ya nuna ma ta gata ya 'yantata. Sai dai bata da tabbacin za ya yi wannan adalcin.
Idris ya tsura mata ido, kaunarta na tsuma mashi zuciya. Sai dai wani abu da yafi daukar mashi hankali shi ne yadda ya ga Fatimar tayi rama sosal Ya rungume hannayenshi akan kirji yana kallonta, a hankali ya gyara tsayuwa ya cc, "Fatima kada koi karya mani zuciya man, kin san na tsani kukanki ko?
Fadi mani mine ne yake damunki na ga kin rame haka? Kin sanyama zuciyarki damuwa ko? Kina ganin zani saba maki alkawari ne?" Sai ta girgiza kai. Ya cc, "Fadi mani mine ne?".
A hankali ta sauke kwayar idonta akanshi zuciyarta tayi sanyi, sai tayi murmushi ta ce, "Daga ina kake?".
• Ya karkace kai yana kallonta ya ce,
"Daga Kano zuwa Jos. Kuma sabo da ke na zo" Jikinta ya yi sanyi, don haka ya jata suka zauna cikin wata inuwa, ya tsarcta da tuhuma yana son ya san abin da ke damunta. Bata 6oye mashi iomi ba ta fadi mashi halin da take ciki a dangane da matsin da
'yan kannenta ke fuskanta a gidansu.
Baiji dadi ba, ya tausaya mata, yana tunanin abin da ke damun mutane na halin son zuciya irin haka. Yanzu haka shima tsakaninshi da'yan uwanshi babu ga maciji sun tsani su buda ido su ganshi.
Lokaci-lokaci ya kan shirya yaje don kawai su gaisa a sada zumunci amma duk lokacin da yaje da bacin rai suke rabuwa. Har ikirari suke yi wai ba jininsu bane. Don haka ya daga ma zuwan, ya zuba masu ido sabo da ya lura a zatonsu maganar fadi ce ke kaishi. To shi kau bai damu da wan gado ba, abin da mahaifiyarshi ta bar mashi ma na nan aje banki bai taba ba sabo da Kawunshi ya tsare mashi komai.
Ya tsura ma Fatimar ido, sai ta sanya hannu ta share hawaye, suka yi murmushi, ta ce, "Na gode da kazo na ganka. Allah kuwa Idris na shiga damuwa sosai na rashinka. Sai na ke ganin kamar ba za ka dawo gareni ba". Ya yi dariya ya ce, "Fatima ni fa musulmi ne, insha Allahu ba zani saba maki alkawari ba. Ki ci gaba da yi mani addu'a. Sai dai wata alfarma da na ke nema gareki ta ki cire ma zuciyarki damuwa kana komi, duk abin da kika ga ya samu bawa to daga Allah ne, idon da rai wata rana sai labari. Kuma masu hakurin su ne masu rabo a nan duniya da lahita, duk abin da kika ganji yana da iyaka.
Sai abua na biyu shi ne,ina so in baki hakuri akan maganar mu, ina so inyi karatun Masters dina kafin muyi aure dan haka za a dan dauki lokacin kafin ayi. Sai dai ba wani lokaci ne mai tsawo ba, kuma kema dai-dai lokacin kin kusa gama naki karatun. Ina fatan ban takuraki ba ko?"

Tayi murmushi, don ya gama wanke mata zuciya, don haka ta saki jiki suka sha hirarsu. Ta ce,
"Amma za ka leka Jibrin ko?". Ya yi dariya ya ce,
"Na so hakan, sai dai bani da cikakken adireshin shi, kin san dama yana zaune da wata Auntynshi ne a cikin garin Jos, amma iyayenshi na can cikin karamar hukumar Wase. kuma ya fadi mani da ya gama karatu can za ya koma sabo da basu jituwa sosai da Auntyn tashi. Don haka sai dai wani lokaci
¡don na dawo".
Da yamma suka fita tare ya yi mata saye-saye tana yi mashi korafin ya dora ma kanshi hidima. Sai ya tsareta da ido ya ce, "Fatima idan dai akan hidimarki ce bani fatan dai-dai da rana daya inji na gaji da ke. Wannan somin tabi ne idon da rai nan gaba nine mkai yi maki komi. Ni dai fatana ki rike alkawari kuma ki rinka yi mani addu'a."
Sai ta rabu da shi ya yi ma ta saye-saye har da sutura suka biya shagon dinki ya bada mata dinkin da sharadin za ta dawo ta amsa. Sai dare suka rabu ya dawo cikin gari ya kama masauki. Nan ya kwana sai da safe ya shiga cikin makarantar suka yi sallama ya bata lambar wayar ofishin Kawunshi da ta gida ya ce idon akwai wani abu ta rinka kiranshi. Haka suka rabu cike da damuwa.
To sai dai taji dadin zuwan na shi, ko ba komi ya nuna mata da gaske yake yi, don haka hankalinta ya kwanta ta ci gaba da karatunta.
* * *
Kwanci tashi har Allah ya sa Idris ya kammala masters digiri din shi a BUK. Zuwa lokacin ya yi hankali sosai, ya san ciwon kanshi da kanshi. Ya bukaci Kawun da shawarar ba za ta yi aiki ba kasuwanci za ya yi tun da yana da dukiyarshi.
Kawun ya yi mashi fatan alkairi da addu'a mai kyau daga nan ne ya fara buge-bugen neman na kanshi.
Ya kan fita kwatano ya shigo da motoci da ya iso da su take zaya saida a cake mashi kudinshi. Idon kuma ya huta sai ya koma. Cikin dan lokaci al'amura suka fara kankama ya yi karfi, don haka ya yima Kawun magana kan aure.
Kawun ya yi murmushi ya ce, "Nima dama na fara tunanin hakan. Ka san kudi sharri garesu, da zaran mutun na kamasu to in ba a yi sa'a ba sai ka ga halayya na canjawa. Ina fatan komi za ka samu ba za ya sanya ka canja tsarin rayuwarka ba, ka kiyayi zina bala'i ne a cikinta. Yanzu ka fara neman auren ne ko kuwa nema maka za a yi?'.
Idris ya yi dariya ya ce, "Ina nema Kawu. Ka manta yarinyar da muke magana da ita a waya Fatima?"
Kawun ya yi murmushi ya ce, "Da ita din za ayi ke nan?". Ya ce, "Gaskiya kam ina tausayinta.
Suna da matsala a gidansu kamar yadda na fuskanta mahaifinyarta ta rasu da jimawa sai ita da kannanta, to basu jin dadin matar da mahaifinsu ke aure yanzu, tana zaluntarsu, idan na aureta ba karamin taimako nayi mata ba. Hatta kannenta za su samu sassauci" Kawun ya jlinjina mashi ya. ce, "Da kyau namijin duniya, ka yi tunani. Yana da kyau idon ka tashi aure ka yishi da kyakkyawar manufa. Na goya maka baya dari bisa dari, Allah ya yi mana jagoranci"
Idris yaji dadi sosai. Kawun ya ce, "Yanzu ina mahaifin nasu yake zaune?". Ya ce, "A Maiduguri suke zaune, sai dai ita tana Jos ta kusa kare karatunta".
. Kawun ya ce, "To ke nan za a jira sai ta
gama ne?"
. Idris ya ce, "Zani je in sameta sai in ji
ra'ayinta"
Nan suka rufe maganar. Dan haka karshen satin Idris akan hanyarshi ta tafiya Kwatano ya shiga ta Jos din wajen Fatima. Duk da cewar yana yawan zuwa cikin lokaci batayi tsammaninshi ba, sabo da ko sati biyu ba a yi ba da ya zo, don haka tayi mamaki sosai.
Ya yi dariya ya ce, "Kin ganni kamar daga sama ko?'. ta ce, "Gaskiya nayi mamaki". Ya rausayar da kai yana dariya ya ce, "Shawara na zo muyi ko?".
To sai ta jashi cikin inuwa taje ta sawo mashi lemu da cake ta kawo mashi suka zauna ana hira. Ya ce, "To ke maganar aure na zo da ita fa...Kin san duk maganar da muke yi bamu taba magana kan cewa Babanki zaya yarda ya aurar mani ke ba?". Ta dan cije lebenta. Koda yake bata jin Babanta, ta san in

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login