Showing 1 words to 1702 words out of 1702 words

Chapter 1 - HAMADA BOOK 1 PART 4

28 Mar 2025

623

HAMADA BOOK 1 PART 4







Zainab Kabir Biroman*
A lokaci guda al'amuran suka yi kokarin sauyawa mutane da dama galibi da suka fito daga yankin Afirika suka shiga gudun in ba ka yi bani waje. Ba a duban gaba bare duban baya, kokari e na tsira da kai.
Baka wani bukatar bayani balle dogon nazari. A lokacin Askarawan kiris ya rage su karaso.
Yagana ta yi wani tsalle ta dire, ta yi kwana ta lakwasa ɓarinta na hagu ta miki layin Kantunan Shagunan Haraj.
Kafin wani lokaci ta ɓace cikin jama'a. Tana da saurin motsi. Wani lokacin kana iya dubanta matsayin hatsabibiya.
Ta rude ta kidime ta ma diririce baki daya. Akwai rashin tabbas sai dai duk da hakan tayi amfani da lakaninsu ta dora kafa bakin kofar Vera Pizza Restaurant.
Bisa SHAHADAuka idanu ya dawo kanta, cikin rufaffen dakin da aka tanada domin abokan cikini.
Zainab Kabir Biroman
*
Baki ne masu izinin zama a kasa da ma tsirarun Larabawan na saudi sai ko wasu daga cikin ma'aikatan da ke kulawa da walwalar abokan ciniki. Ke nan babu wani idon sani, sai shi daya tal! da ya duka gaban katon Teburin da yake harhaɗawa abokan hulɗa abinci,
Ya dubeta ta dubeshi, ta kuma kara dubansa cikin wani irin karayar zuciya, yanayinta kadai zai nunar maka da tsagwaron firgici da tashin hankalin da take ciki.
Zuciyarsa ta shiga wani irin kunci na banzatar da kai da al'amarinsu na kasashen Afirika ke yi, abin da kan janyo musu raini.
A lokaci guda Askari guda ya sako kafafunsa cikin rufaffen gurin Vera Pizza Restaurant.
Ba ta sani ba ko ta sani? Ta dai cusa kai a takure, a kanannade a kuma cure wuri guda a karkashin Teburin da suka basu da nan nan da hidimarsu take ya ta ta wai ta fadawa hannunsa, ya kau da kai ya kuma ci gaba da ayyukansa duk da kasancewar hakan matukar hatsari ne a
Zainab Kabir Biroman
*
gareshi, kusan kowa din ya ga shigarta karkashin teburin sai fa wadanda suke haramar shigowa a lokacin da ba za su iya sanin abin da ke karkashi ba, kasancewar teburin raɓe yake da bango a jikin bangon wajen ma aka likashi, zaunannen Teburi ne da ake hidimar shiyawa abukanan hulɗa abinci.
Ya karaso cikin kwarjini da isa na jami'in tsaron Saudi, ya dan yi waige-waige, daman baya tunanin akwai bara gurbi a ciki, domin kuwa ko a ruwa mara gaskiya aka ce gumi yake. Ya dan yi shawagi a cikin rufaffen ginin kana ya yi JAN KUNNE ga Ma'aikatan da ke bisa bakin aiki, shi ke nan ya fice kwas! kwas!! kwas!!!
Ko da yake, Motar Askarawan na nan kafe a bakin a bakin gidan abincin na mutanen kasar Italiya.mo
Duriya (Motar kamen bakin haure da masu laifi) ma ta iso da mutane makil da aka yi

*
Zainab Kabir Biroman nasarar cafkewa a wannan sumame da aka kawo kasuwar Hadit da ke gefen Birnin Jedda.
Ya ci gaba da gudanar da dukkanin al'amuransa yana kuma lura da dukkanin al'amuran da ke faruwa, al'amura sun soma dai- daita, sai dai har lokacin akwai kai komon jami'an tsaro.
A tsorace, a firgice, a kuma razane ta yunkura mikewa, ya gyada ma ta kai alamar hani. Ya yi amfani da sassaukan Larabci salon na Saudi wáto "Gargaliyya".
"Akwai matukar hatsari gilmawarki a wannan lokaci, al'amura basu gama komawa yadda suke ba". Shi ke nan abin da ya ce ma ta, dai ci gaba da gudanar da al'amuransa.
ya
"Babu dalilin da zai sa dan Adam da Allah Ya girmamashi ya zo yana tozartar da kansa. Rayuwar nan ba mai kyau ba ce musamman ga 'ya mace.

Zainab Kabir Biroman
*
Fuskarshi a ɗaure ya fada kamar ma baya son dubanta, ya ma kau da kai daga ɓarin da take.
Ya dai sake yin amfani da sassaukan Larabcin ya ci gaba da fadin.
"Kina iya wucewa. Sai dai akwai bukatar ki tattara nutsuwarki wuri guda, hakan zai zamo mai afani a gareki".
Har lokacin tana cikin firgici, hasalima a kidime take.
kauce.
Tana son ta gode masa, sai dai tuni ya
Ko babu komai yai ma ta abin da ba kowa- ne zai iya yi ma ta ba.
Kuma ta mayar masa da martanin su din ba su zamo masu wulakanta kansu ba face wadanda suke lalube domin nemo halaliyarsu. Har kullum cike take da jin zafin irin haka.

Zainab Kabir Biroman
*
nguwar Hindawiyya hawa na uku, daki mai lamba ta hudu ta kwankwasa kofa kana ta murda mabudin kofar, ta
yi sa'a a bude yake.
Ta yi rashe-rashe à saman Katifa sai mai da numfarfashi take.
Ta taso tana tangal-tangal kai ka ce wata bugaggiya ce.
Ba buguwa ba ce, tarin wahala da ɗimaucewa ce kawai ta yi kab da ita a lokacin da ta gama saddakarwa.
Kawai sai at saka kuka, dariya-dariya,
murna-murna.
"Na gama saddakarwa kamen Askarawan nan ya fada kanki 'yar uwa. Ya aka yi ne? Ya ya ne aka yi ku ka kuɓuta?
Ke din daman nufinki ne kullum a kamaki, kin kasa ki goge ki guje, ki jajirce da artabun jami'an tsaronnan, gashi ni ban ga wata tsiyar da ki ka taka ba balle in yi tunanin lallai kaddarar kamen ki ke so ta afka kanki."

*
Zainab Kabir Biroman Lokaci guda yanayinta ya sauya, zuciyarta ta shiga harbawa ba ji ba gani.
Duk wani hasken nan da ke zuciyarta ya gushe. Kowa din yana iya komawa gida da tunanin wani haske da yake tsammani, da tunanin wani farinciki da yake nufin tunkara, da tunanin shi din wani abin bege ne da ake marari har ma ya zamo abin so ga kowa. Ta iya yiwuwa ma shi din wani mai girman daraja da kima da mutunci ne da ake duba.
Duka ba ta yi kuskure ba idan ta ce ta hade ta tattare ta rasa duka wannan farinciki babu shakka za ta kasance mafi hasara daga cikin kamammuta nan da aka yi nufin isar da su gida. Dama dai rayuwarta ta kare, ta gushe a haka...cikin wahala da kunci, kaskanci da tozarci matuka, za ta cika da imani, shi ke nan abin da take marari.
Yagana ba ta lura da yanayin da take ciki ba ta ci gaba da surfa masifa musamman mummunar hasarar da aka jaza musu, duk cikinsu na ranar da ma 'yan kudaɗen da ke

Zainab Kabir Biroman
*
kugunta wadanda suka fice da su sun watse, sun tarwatse baya tsira da ko Riyal guda ba face tarin wahala.
Lokaci guda ta dora alhakin afkuwar lamarin akan Jabir.
Babu shakka ya munafurceta, domin kuwa ya nuna ma ta hanya ta yi kyau.
(Jabir din daya ne daga cikin Askarawan Saudi, saurayinta ne sun jima ana harkar banza, shi ne ma bangon da ya tsaida Yagana a Birnin Jedda daram! Ya kan sanar da ita a lokutan da za a yi kame, don haka sai su kauce).
Wasu 'yan kudade da Yagana takewa masifa duk ma basu dameta ba, duk da cewa kuɗade ne masu girma, basu damjeta ba, ba ta ma iso kasar domin tarasu ba, ba ta ma zo domin afkuwar al'amuran da ke afkuwa a gareta ba;
Al'amuran bawa sukan kasance cikin sauyi ba da sani ba a lokutan da Ilahi ya so.
Sharr! Sai ruwa ya shiga fitowa daga idanunta, duk dai al'amari ne da ya ratsa zuciyarta.

Zainab Kabir Biroman
Yagana ta kasance cikin mamaki a lokacin
da ta ankara da yadda Zalihar ta kuɓuta, ta dinga mamakinta tana nanantawa.
"Na yi mamaki fa! Dan bakin mutumin mai duban kowa kasa-kasa?
Yana wani dubanka kamar kashi? Yana dubanka da kaskanci? Ban yi tsammanin haka daga gareshi ba".
Zaliha ba ta ce komai ba, tunanowa take wace hanyar za ta bi ta koma Haraj ta yiwa wannan mutumin godiya, yai ma ta ccton da ba za ta taɓa mancewa da shi ba.
A wannan kame da jami'an tsaron Saudin suka gudanar sanadiyyar laifuffukan barace- barace, mayar musu da hanya wuraren saye da sayarwa, kazalika tare da haddasa musu tarin kázanta a yankunan kasuwar Hadit da Haraj, don haka suka bazama kewaye da zagayen kasuwar ta Haraj aka shiga kamen kan mai uwa da wabi, da mai laifin da ma wanda bai ji ba kuma bai gani ba.

Zainab Kabir Biroman
*
Yagana ta sambatu tana kcwar abokanan zamanta, musamman Cima, kamen ya rutsata da ita a bisa shammaci domin kuwa ba harkar saye da sayarwa ta cika ba, kai ba ma ta yi, kasancewar Cima kwankwarcriyar Kilaki ce da samunta kacokam ya dogara ne a bisa wannan mummunar ɗabi'a da take dubanta matsayin babbar haja, har ma a wasu lokutan take yiwa ire-iren su Yagana jagora, yau shin Yaganar ke
nan.
Zaliha kam na ta rayawa a ranta idan dai irc-iren su Cima jami'an tsaron Saudi suke damkewa su kuma aike da su gida, to babu shakka da an ce sun yi dai-dai matuka gaya, ba su ba da suke yunkurin neman halaliyarsu, su gurgura su karashe rayuwar da tai musu saura kafin zuwan sa'i.
Da aka dan kwana biyu aka nutsu kuwa Bebin Yola ta nutsa Makka.
A cewarta can
Zainab Kabir Biroman
*
din yafi dama-dama sakamakon kwazazzaɓar Askarawan da sukewa bakin hauren a kafatanin Birnin na Jedda, sai fa in tsautsayin bai rutsa da kai ba.
To ta ina za ka sami zarafin fita balle ka nemi na kanka?
Ita kuwa Mai Gado ta makale a can Asharbatly, wani ɓari (Kauye) da ke cikin yankin Jedda.
Ana matukar samu fiye da kasuwar Hajraj, don haka ta sauya sheka daga Hajraj din zuwa Sharbatly, a cewarta akwai samu hankali cikin nutsuwa ba kamar zaman dari da ake cikin garin Jedda ba, suna bara suna samun 'yan kudade da abinci da tarin gumama mafi kyau.
Da zarar gari yai kyau za su iso Haraj su ci kasuwarsu.
Wasun su ma sun fara yunkurina aikewa da su gida da ba su iya hakurin kasuwar Haraj ta daidaita ba.
Zainab Kabir Biroman *
Ko da yake sun ce idan aka aike da su gida (Najeriya) ai an fi samu sai dai kawai tarin 'yan kudaɗen da ake kashewa kafin isar su la karkashin (CARGO) Jirgin saman daukar kaya mallakin kasa, wato Nijerian Air Ways (CARGO).
Rayuwar ta yi matukar yi musu tsauri, wasu kabila ne da suka fito daga Kudancin Najeriya ke kokarin ɓata musu gari da sacc-sace, zamba cikin aminci (419), wasu da suka fito daga cikin kasashen da suka fito daga cikin yammacin Afirika suka fi shuhura shaye-shayen mugayen Kwayoyi, ana iya cewa daga kowanne ɓari na kasashen duniya.
A sana'ar Karuwanci kuwa 'yan kasar Chadi sun zamo Zakaran gwajin dafi!
Fataucin kananan Yara da harkar Bara 'yan Najeriya sun zamanto ja gaba a wannan fanni, bayan wasu 'yan tsirarun laifuffukan da suke aikatawa.

1

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login